Kamar wasa na dauki yayen Ramla, kuma ba ta yi mini wani rikici mai yawa ba, ranar farko da ta biyu ne kawai mu ka sha rigima, daga nan kuma ta hak'ura, dan rikicin ba yawa.
Dalilin ya haddasa karin shakuwarmu da yarinya fiye da baya, son yarinyar da kaunarta ya kuma shiga zuciyata.
Komai nake Ramla, duk wani makusanci nawa idan mu ka yi waya sai ya tambaye ta. Musamman Ummana, kanwata Yusrah da kuma Maryam.
A bangare daya kuma kimata mutumcina sun karu sosai a idanun iyayenta, musamman Babanta da kullum nake ganin tsantsar kaunata a. . .