Skip to content
Part 17 of 22 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Idan ka dauke ido babu wani abu a jikina da yake aikinsa yadda ya kamata, bana iya magana, idon ma ya bushe babu hawaye, zuciyata ba ta iya wani tunani mai zurfi.

Abinci ma sai surukata ta sani a gaba da Mamata sannan nake iya ci.

Yayin da Baban Khalil ke kwance kamar gawa.

Saboda komai sai an yi mishi.

Lokaci daya kuwa na zube, na yi baƙi, har da wasu kurajen tashin hankali suka fito min. idan ka dauke cikin jikina babu wani abu mai kauri.

Tsawon sati amma babu wani cigaba, kullum jiya iyau, har an fara tunanin fita da shi waje, da taimakon Rahma da kuma mijinta. Yanzu kam idan ka dauke ni, Inna (mahaifiyar Abban su Khalil,) Aunty Habi, Abdullahi, Hassan, Ni da kuma Maryam kanwata, to ba kowa. Sai Rahma da ba ta taba gajiyawa wajen kawo mana abinci ba. Su Affan ma duk suna wajen ta. Daga can ake kai su school a kuma dakko su.

Yau ma zaune muke a dakin, masu hira na yi, ni dai dama zan iya wuni ban yi magana ba, ni ban san ma me zan rika cewa ba. Abin da yake damuna kadai ya ishe ni. Wuni nake kuka, ga na kewar Maman Khalil, ga na rashin lafiyar mijina.

Ina lura da yadda Inna ta kafe ɗanta da ido tun bayan da suka shigo dakin.

Dalilin da ya sa kenan ni ma na mayar da hankalina a kanta, duk kuwa da kukan da nake yi.

Abdullah ta ja zuwa waje, jimawa kadan sai gasu da likita.

Maganar da likitan ya fada ba ƙaramin daga min hankali ta yi ba, sannan ta yi sanadiyyar yankewar duk wani network da yake jikina.

Saboda  cewa ya yi, wai  numfashi ya yi nisa da gangar jikin Basheer.

Kwance bisa gadon marasa lafiya na ganni bayan na farka.

A hankali kuma komai ya rika dawo min har zuwa furucin likitan, a hanzarce na yunkura da niyyar tashi.

Amma  na ji an mayar da ni, Aunty Habi ta ce

“Kwanta, jikinki akwai ciwo.”

“Aunty Basheer fa.” na yi saurin tambayarta ba tare da na koma na kwanta din ba.

“Aunty da gaske shi ma ya rasu?” na kuma tambayarta a karo na biyu.

“Kwanta na ce miki, Basheer yana nan bai rasu ba, doguwar suma ya yi.”

Na dan lumshe ido cike da jin dadin abin da ta fada min. Koda ba gaskiya ba ne, tabbas na ji sanyi.

Sai a lokacin na ji zafi a kasan cikina.

“Me ye wannan?” na yi tambayar hade da shafa wajen.

“an yi miki aiki ne an cire abin da ke cikinki”

A lokacin ne na kuma na shafa cikina don  gasgata abun da ta fada lokaci daya kuma ina tuno wata maganarmu da Maman Khalil.

Bacci nake yi sosai bayan na idar sallahr magriba, ban san ma ya daukeni ba, a cikin baccin na ji tana tashina.

Firgigit! Na bude ido hade da dorasu a kanta.

“Me ya faru?” na yi maganar cikin yanayin bacci hade da mikewa zaune

“Haihuwa kika yi.” ta yi maganar cikin murmushin da baya bacewa a kan fuskarta.

Ni ma a lokacin murmushin na yi tare da fadin “Ace ko haka ake yi, ai da kila kullum mutum sai ya haihu.”

Tare mu ka yi dariya kafin ta ce “Ke kam haka haihuwarki za ta kasance ba za ki san kin haihu ba. Sai dai a ba ki labarin haihuwa kika yi”

Har zuwa lokacin dariya nake yi, bayan da na karbi plate din da ke hannunta mai dauke da wainar Fulawa da yajin da ya sha garlic.

“na gode” na fada a daidai lokacin da da take ficewa.

Na share hawayen da suka gangaro kan fuskata, ban san ranar da zan daina kukan rabuwa da Maman Khalil ba, na yarda mutum ko namanka yake yanka, idan ka rasashi sai ka ji babu dadi. Barrantana ita da ko bakar magana ba ta taba shiga tsakaninmu ba.

“Sannu! Akwai ciwo ne?”

Aunty Habi ta tambaya hade da zuba min ido

Kai na girgiza alamar a’a sannan na ce “Ina son ganin Bashir Aunty .”

“To jira in je wurin Doctor tukun.”

Fitarta ke da wuya sauran ‘yan’ uwa da ke waje suka rika shigowa suna min sannu, wasu kai kawai nake iya daga masu.

Nurse din da suka shigo da Aunty ne ta taimakeni na ta shi zaune, sannan ta dora min Babyn a kan cinyata hade da bude mata fuska, cikin murmushi take fadin “Ya kika ga Babynki, lafiyayya kuma kyakkyawa ga gashi tamkar ba’Indiya.”

Na zubawa yarinyar ido ina kallonta, abin da duk nurse din ta fada gaskiya ne, amma zuciyata babu dadi sam da zan ji dadin kalamanta.

Hasalima hawaye ne suka gangaro kan kumatuna bayan na jingina kaina jikin bango.

Ramla nake tunawa, watarana tana danna cikina, na ce “Ke bari Baby ne a ciki”

Ta zuba min ido, kafin ta ce “Baby?”

“Eh.” na amsa cikin murmushi.

Ba tare da ta dauke idanunta akan cikin ba, ta shiga  murmusawa na san akwai maganganu sosai a bakinta amma ba hausar da za ta yi su, hakan ne ya sa na kara mata haske.

“Baby ne me kyau a ciki zan haifo miki, ki samu abokiyar wasa yadda su Affan ba zasu kara korarki ba idan kin je wurin wasansu.”

Wangale baki ta yi sosai alamun ta ji dadi, a lokaci daya kuma ta kai hannu tana shafa cikin.

Ni ma fadada fara’ata na yi, hade da janyota zuwa jikina.

Tun daga wannan ranar ko me ta samo sai ta kawo min wai a ba Baby, ku kuma ta bude cikina ta dora abun wai Baby ta dauka.

Na so ace Ramla na raye na haihu, in ga wace irin murna za ta yi? Za Ta bari a dauki Babyn ko ba za ta bari ba?. Tun ina kukan a hankali, har na bude murya sosai na shiga rera shi.

Kowa a dakin hakuri yake ba ni da fada min magana mai dadi.

Da sauri na mayar da hankali kan Abbansu Khalil da aka turo cikin keken marasa lafiya.

Kasa janye idanuna na yi a kanshi, har zuwa lokacin da Abdullahi ya tsayar da kujerar a gaban gadona, yayin da mutanen cikin dakin suka shiga jero mishi sannu.

Bayan mutanen  sun watse ne, ya zaro littafi ya yi rubutu hade da miko min.

Hawayen kan fuskata na dauke, hade da karbar littafin na shiga karanta abin da ya rubuta.

“Bana iya magana Deejah sakamakon aikin da aka yi min a muka-muki, amma kuma na damu da sanin halin da kike ciki tun da aka ce kin haihu.”

Abun da ya rubuta kenan, ni ma sai na mayar mishi da amsa.

“Ina lafiya Alhamdulillahi, amma na fi damuwa da halin da kake ciki Abban Khalil, yanzu me ye ya fi damuna? “

“Kafata ce ta fi damuna da alama yanketa za a yi, ban san ya rayuwa za ta juya min ba kuma.”

Ba tare da na share hawayen da ke diga a kan littafin ba na shiga ba shi amsa

“a ko wane irin yanayi ina sonka Bashir, zan kuma ci gaba da sonka har karshen numfashina, bare ma sha Allah za ka warware, ni bukatata kawai shi ne ka rayu, koda babu kafa zan yi ma komai, zan kula da kai”

Silent murmushi ya yi, a lokacin da ya karasa karatun, kafin ya yi rubutu ya miko min

“Ya kika ga Babynki, kyakkyawa kamar Affan ko? “

Bayan na karanta na dan yi gajeren murmushin da na manta ranar da na yi irinsa, na san ya canja salon hirar ne, dalilin da ya sa kenan na zuba ma yarinyar ido.

Gaske yake yi, tamkar Affan ne ya koma jariri yake kwance.

“Basu yi kama ba, fuskar Ramla ce.”

Murmushi ya yi, lokaci daya kuma ya shiga ba ni amsa

“Don ba ki san Affan yana yaro ba shi ya sa, amma da Maman Khalil na kusa abin da na fada na san ita ma shi za ta fada.

Shiru na dan yi bayan na karanta sakon, shirun da na rasa me ma na tuna.

” Yanzu me suka ce game da kafar taka?”

Ni ma na canja salon tawa hirar, ba na son abin da zai tayar mishi da hankali

“Basu ce komai ba, kawai dai da an gyara ne, sai gyaran ya baci”

“Ko zamu gwada na gargajiya”

Wannan karon dago fuskarsa kumburarra ya yi yana kallona.

Yayin da ni ma na zuba mishi ido cike da tausayawa, ya yi baki, ya rame, fuskarsa ba sajen nan da yake shan gyara duk an askeshi, haka ma gashin kansa.

Kuma a yanzu ne na fahimci karfin hali kawai yake yi, amma yana jin jiki.

“Bashir!” na kira sunanshi cikin sanyin murya, bayan na matso daf da shi, hade da kama hannunsa.

“Ina sonka a ko wane irin yanayi, fatana ka samu lafiya, don Allah ka rage damuwa, idan har kana son mu bar asibitin nan da wuri. Ba ni kawai ce ke bukatarka ba, hatta Sakeena da Ramla suna bukatarka a raye , saboda kullum za ka nuna kulawarka garesu ta hanyar yi masu addu’a.”

Na dan tsagaita hade da kallonsa, shi ma ni yake kallo.

“Sannan ga su Khalil da Affan, su ma suna bukatarka, idan ka tafi maraici sai ya fi masu yawa.”

Wannan karon hawayen da nake boyewa sai da suka samu damar gangarowa.

Hannu ya sanya yana share min hawayen, yayin da shi ma na shi hawayen ke sauka kamar ruwa.

Ban san ko tsawon mintuna nawa muka kwashe a haka ba, kuma a haka Aunty Habi ta shigo ta same mu, ita ce ke shaida min zuwan Yusrah kanwata. Kuma ita ce ta kira Abdullahi ya tura Abbansu Khalil zuwa dakinshi.

Zuwan Yusrah ba karamin kewa ya kara debe min ba, Idan tana yi min hirar ƴan’uwa da gida sai in rinka jin dadi sosai.

Haka rayuwarmu ta kasance a asibiti, kodai ni in tafi wajen Baban Khalil, ko shi a kawosa wajena.

Matsala daya shi ne baya iya magana, cikin sati littafai uku muka cika dam da magana, mun bude na hudu ne aka ba ni sallama.

Shi ma zuwa lokacin sosai akwai sauki, idan ka dauke rashin maganar da kuma kafarsa.

Amma ciwukan da ke jikinsa da yawansu sun warke.

Ranar da zan tafi gida, da kuka muka rabu, na so su bar ni har zuwa lokacin da za a cirewa Baban Khalil karfen da ke bakinsa, su bamu sallama tare, saboda za a koma Ruma da shi don yi mishi aikin gargajiya. Amma suka ki, wai suna bukatar gadon. Ban hak’ura ba, kullum sai na zo asibitin, saboda na fahimci yana jin dadin hakan.

Sannan Abdallah ya sawo waya ya ba shi, ni ma kuma wayata tana nan, Sai mu rika yin chat koda ban je asibitin ba. Kullum cikin lallabashi nake yi. Ba bukatar bayyana ya damu da rashin matarshi da kuma yarshi, ko bai bude baki ya fada ba ni na san yana jin zafi.

A tare da ni a gida akwai kanwar Abbansu Khalil budurwa mai suna  Jamila, ni ma kuma akwai kanwata Maryam, saboda Yusrah kwananta uku ta koma gida. Sakamakon rashin lafiyar yarinyarta. Sai kuma Aunty Habi, wacce ke kula da ni sosai a bangaren jego.

Rahma kullum sai ta zo, kuma har zuwa lokacin ba ta maido yaran ba. Ni ma kuma ban yi maganarsu ba.  makotana ma, suna dan yawan shigowa, ba kamar baya ba, don ban ma sansu sosai ba.

Gidan dai kullum sai an yi baki.

Amma kuma hakan bai debe min kewar Ramla da Sakeena ba, kullum cikin tunaninsu nake da tuna rayuwar da mu ka yi. Sai in ji kamar zan ji tashin motarta ta fita ko ta dawo. Idan na kalli motar lullube ba na sanin lokacin da hawaye ke zubo min.

Kamar mafarki Sakeena ta zo, ta kuma ta fi.

Ashe dama rayuwar zamanmu da ita ba mai tsawo ba ce.

To yanzu da ta zauna da ni da mugun hali, ta cutar da ni kamar yadda wasu ke yi wa abokan zamansu da shi kenan yanzu ta tafi ta girbi abun da ta shuka, tun da ko gafarata ba ta samu damar nema ba.

Ni ma ga shi ban nemi tata gafarar ba, kuma ba san na yi mata abubuwa marasa dadi.

Abu ma fi a’ala shi ne ka zama mutumin kirki sannan ka jira mutuwa, saboda a ko wane lokaci tana iya riskarka, ba ruwanta da kana aikata mai kyau ko akasinshi.

Shigowar Affan ce ta katse min tunanina

Na rika bin shi da kallo ina tuna mafarkin da na yi a kanshi. Abun ka da yara babu ruwansu, komai bai canja nasu ba

“Kai da wa kuka zo?”

Don na san idan ba ya canja ba, ko zamu shekara a haka, daga sallamar da ya yi da kuma gaishe ni ba zai kara komai a kai ba.

Kafin ma ya ban amsa Rahma ta shigo rike da manyan ledoji guda uku, Khalil na bin ta a baya.

Shi kam kan jikina ya fada cike da murnar ganina, rungume shi na yi tsam, lokaci daya kuma Ina ta kokawa da hawayen da ke son zubo min.

 Kan stool din mirror Rahma tan zauna, lokacin daya kuma muna gaisawa.

“Affan ya dauki Babyn?”

Ta yi tambayar hade da kallona.

“Bai dauka ba, kin san halinsa ai ba ya magana.”

“Kuma a can ya dame ni, in kai shi wurin Abbanshi da kuma Babynsu yana son ya dauketa.”

Na dan yi murmushi, lokaci daya kuma ina kallon irin ramar da Rahma ta yi, lokaci daya ta zube, sai ta kara haske fayau, har ba kyau.

Samun kawa kamar Rahma a wannan lokacin abu ne mai wahala, tana da rikon amana.

Karbar yarinyar na yi a hannun Khalil ina fadin “to zo ka dauke ta “

Ba musu ya zauna aka dora masa ita, Rahma ta rika mishi hotuna, ni ma sai na rika daukarsa.

“Wadannan kayan Sakeena ce ta saya da hannayenta, ta bar su a wajena ta ce idan kin haihu sai in kawo mata ta ba ki. Dama jira nake abubuwa su yi sauki in kawo miki.”

Ta karashe maganar hade da turo min ledojin.

Jiki a mace na rika budasu, latest kayan baby ne masu kyau da tsada, overrall, da unique sex masu kyau, sannan akwai na mata yankanti masu kyau sosai da takalma, zanen daukar baby da na goyo, socks, feeding bottles, pampers, maya-mayai na Baby, turare, kai tarkace ne cike leda biyu.

<< Hasashena 16Hasashena 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×