Daurewa kawai na yi kafin na ce mar "Ka yi hakuri don Allah, mu je in kai ka toilet din."
Da kyar na samu ya yarda na taimaka masa, sai da na tabbatar na yi mishi duk abin da ya dace sannan na koma kitchen, a lokacin kuwa miyata ta fara konewa.
Bayan na motsa miyar hade da rage gas, cigaba da zagaye kitchen din na yi da goyon Maama so nake ta yi bacci.
Yayin da a zuciyata nake jin wani irin zafi, ku san kullum Baban Khalil sai ya nuna gazawata a kan abu, kamar haushina yake ji. . .