Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tun da na gama miyar shiga goma fita goma zan yi a kitchen din sai na bude tukunya na dauki ludayin  na dangwala a hannuna na lashe, abun ka da ban taba gwada yi ba so dai nake in tantance, kar Ogan ya ci ya raina min.

Tuwon ne dai ya yi tauri da yawa ba kamar yadda mamana take yi ba, shi ba mai tauri ba, kuma ba mai taushi ba, yana nan a tsakiya dadin ci.

Amma ni nawa aka jefi kato ba abin da zai hana bai ji ciwo ba.

“To me ya sa?” Na tambayi kaina.

Kiran layin Ummata na yi

” Ummah!” na fada bayan na yi sallama hade da gaishe ta

“Na’am” ta amsa

“Tuwon shinkafa na yi, ya yi tauri bai yi irin naki ba” Na ta fi kai tsaye akan abin da nake so

“To ba sai ki dakko littafin da kike rubuta kalolin girki ba, ki duba yadda za ki gyara”

Shiru na yi, ina tuna yadda take jin haushin littafin koyon girkin can nawa, lokaci daya kuma Ina tuno yadda take fada

“Aikin banza da wofi, kullum kina like da TV wai koyon girki, idan za ki tsaya ki koyi abu a zahirance ki tsaya ki koya, wannan rubutun ba inda zai kai ki ba, ni dai kika sanya aka zageni a kan ba ki iya girki ba, sai Allah ya saka min.”

Haka take cewa duk lokacin da nake rubuta yadda ake wani girkin a TV ko a media

” Kai Umma, yanzu fa kin san ba kamar da ba ne, idan ban iya wannan abinci zamanin ba akwai matsala wallah, mazan yanzu yan zamani ne ba Yan gargajiya ba” Haka nake ba ta amsa.

“Wane namiji ne zai siya miki kayan girkin da kike rubutawa? Wani ma bai ko taba jin sunansu ba, sannan wane namiji ne zai rika siya miki kaza kina rarike cikinta kina tura dankalin turawa da su hanta da koda?  Wane namiji zai tsaya siya miki kwai kina dafawa kina dode duwawun kaza?  Sannan wane namiji zai fita tun safe ya dawo da yamma ki aje mishi cake ko wani burodi can da danyen tumaturi? “

A duk lokacin da ta fadi haka dariya nake yi, a zuciyata ina fadin “Ba ganewa za ta yi ba.”

Ashe dai ni ce ba zan gane ba.

“Kin ji me na fada dai ko?” ta katse min tunanina

“Eh”

“Yauwa” Ta yanke kiran

Fita batun tuwo na yi, na gyare kitchen dina fes kamar ban yi aiki a ciki ba.

Wanka na shiga, bayan na fito na shimfida sallaya don sallahr azahar.

Bacci ne cike da idona, don haka a kan sallayar na kwanta bayan idar da sallahr.

Bacci kuma ya yi awon gaba da ni.

Cikin baccin ne na ji kwankwasa kofa.

A firgice na tashi na nufi kofar

Khalil ne tsaye cikin  kayan shan iska na yara, kamshin  turarensu na yara da turaren mamarshi tuni ya cika kofar tawa.

“Khalil, kun dawo ne? Me ya faru?” cikin muryar bacci na jero mishi tambayoyin.

“Momyna ce ta ce idan kin rage abinci wai ki san mana kafin ta girka mana”

Hannu na kai cikin sauri na murje idanuna don gasgata mafarki nake yi, kodai gaske

Tuwona mai taurin can zan ba ta? Matar da ko ruwan zafi ta dafa sai ya yi dadi. Shi ya sa bana son ba ta abincina, ina jin tsoro ta rika min kallon ban iya girki ba

“Zo ka zauna, sai in daukar ma kada ka baras ko” na yi maganar hade da jawo hannunshi zuwa cikin falon sosai. Komai bai ce ba, ya biyo ni.

Babban tire mai kyau na dakko, na jera abincin da gorar ruwa daya, sai fruit salad mai sanyi.

“Mu je ko” Na fada a daidai lokacin da na zo wurinshi

Wannan karon ma bai yi magana ba

“Wannan yaron tun wuri miskili ne” Na fada a zuciyata ina kare mai kallo, cikin mulmulallan jikinshi da ke nuna yana samun kulawa a ko wane fanni.

“Assalamu Alaikum” na yi sallama a falonta hannuna rike da tiren abincin.

“Amarya shigo mana, na fito wanka ne” Daga cikin bedroom nata ta yi maganar bayan amsa sallamar tawa.

Daure take da towel iya gwiwa, jikin nan kamar na tarwada, iya inda na gani ban ga kurji ko alamar tabo ba.

Haka kalar fatarta mai wahalar fassarawa ta fita sosai gwanin sha’awa. Don ita dai ba za a ce mata fara ba, kuma ba baka ba.

Kamshin nan da kullum yake like da dakinta yana nan, na rasa wane irin turare take amfani da shi  kamar maye.

Ni kaina yanzu dana shiga dakin nata sai in yi awa daya kamshin bai bar ni ba

Idan kuwa ta taba kudi, ko mijina ya kwana a dakinta ya dawo dakina, to har ya bar dakina kayan da ya shigo dasu ba zasu bar kamshinta ba.

“Tuwo fa na yi miyar kuka” na fada ina murmushi

“Ai shi yaran nan suka fi so ma, haka Babansu ma” ita ma cikin murmushin ta yi maganar

“Je ka dakko min plate a kitchen Khalil” Ta fada tana  kallonshi

“Bar shi ya huta bari in kawo miki” Na fada hade da mikewa. Ta yi saurin riko ni

“Wayyoh! Rufa min asiri, wallahi ban isa ba, ke da Khalil din duk zauna na hutashassheku”

Kafin in yi magana tuni ta fice cikin sauri daga dakin. Na bi bayanta da kallo, wanda yake dauke da faffadan kwankwaso.

A zuciyata na ce “Ko yaushe nawa kwankwason zai bude kamar na ta oho”

“Wallahi Ramla ce ba lafiya, na biya asibiti shi ya sa ban dawo da wuri ba. Na ce Baban yaran nan yau ma ya shiga kwanonki” .

Maganarta ta katse min tunanina.

Murmushi kawai na yi, ba tare da na ce komai ba, lokaci daya kuma Ina kallon yadda take warware tuwan daga cikin leda zuwa kan tsabtataccen plate din gabanta

Hankali kwance take cin tuwon har da santinta wai ta fi son tuwo ya yi tauri haka.

A zuciyata na ce koma ba ki so ya kika iya haka nan za ki sassakeshi.

Na mike tsaye hade da taba jikin Ramla da ke bacci

“Zazzabin ma ya sauka, Allah ya sawake, bari in je daki”

“Amin, na gode amarya na hadaki da aiki,”

“A’a ba komai wallahi, sau nawa ni kina shan wahalar aikinki ki zubo min in cinye.”

Dukkanmu muka yi karamar da dariya a daidai lokacin da  nake fita daga dakin.

“Wannan mata wane kalar mai da sabulu take wanka da shi ni Khadija?”

Na fada a daidai lokacin da nake ficewa daga bangaren nata

“Ga inda ya kamata in bata lokacina nan, wajen koyon sabulu da turare na je na bata shi a koyon girkin  kasashen waje.”

A zuciyata na yi maganar hade da jan tsoki ina jin haushin kaina.

Saman kujera na fada raina yana min babu dadi,

Horn din da na ji ne ya sanya ni  mikewa da sauri na nufi bedroom don na san maigidan ne ya dawo.

Kuma fuskata ko mai ban shafa ba, bare  ta kai ni ga kwalliya, shi ya sa faka-faka na yi kwalliyar hade da shiryawa cikin riga da siket na atamfa.

Ina tsaka da Fess turare na ji knocking kofa a hankali, wannan ya tabbatar min da shi ne.

Na fito cikin yauƙi, a zuciyata ina kiyasta yadda zan tare shi, irin tarar da kullum yake korafin ban yi mishi, yau dai ita zan yi mishi.

Ganin hannunshi rike da Khalil ya sanya ni ja baya kadan, saboda na san ba zai so in rungume shi gaban yaron ba.

Da murmushi a kan fuskarshi ya ce

“Wata biyu da aure amma har yanzu kin kasa sakin jiki da ni, to sai yaushe?”

Ban yi magana ba, illa kokarin danne kunyar da take taso min da na yi hade da fadin “sannu da zuwa”

“Ban amsa ba ni wallahi”

Ya fada cikin muryar shagwaba, hade da kankace idanunshi a kaina.

Ba zan iya jurar kallon ba, dalilin da ya sa kenan na raba shi na wuce zuwa dinning table

“Ki sauke min abincin a kasa”

A kasan na aje mishi, na koma na zauna a kujerar da ke fuskantarshi.

Ya daga hannayenshi sama yana kallona.

Ni ma kallonshi nake kafin in gano me yake nufi.

Mikewa na yi, na cire mishi babbar rigar da yar ciki, na aje a kan majinginar kujerar dinning.

Sannan na zuba mishi tuwon hade da fruit salad.

Rike hannuna da ya yi ne ina kokarin tashi ya sa na dakata ina kallonshi.

“Ina za ki je? Ba za ki ci abincin ba ne?”

“Zan ci” na amsa shi

“To Bismillah mana”

Na juya kan Khalil wanda hankalinshi kaf yana kan tv na ce “Khalil ba za ka ci tuwon ba kai?”

Kai ya jinjin alamar eh.

Yadda na ga Abbansu na dan murmushi, na fahimci ya ji dadin tayin da na yi wa Khalil din, haka muka rika ci tuwon a nutse hade da yin yar hira.

Shi ma dai cewa ya yi na yi mishi tuwon da ya fi so mai tauri.

Ban sani ba ko suna karfafa min gwiwa ne, ko kuma dai da gaske irin shi suke son oho.

Bayan ya idar bedroom ya shiga, ni kuma na shiga tattare kayan da muka ci abincin na shigar kitchen.

Daga nan kuma na bi bayan shi. Lokacin da na isa ya fito daga toilet da alama brush ya yi.

Dalilin da ya sa mu ka hadu a tsakiyar dakin

“Ina Khalil din?” ya fara tambaya ta

“Yana falo” na amsa shi.

“Ok” ya fada lokaci daya yana gyara hannun rigarshi

Tare mu ka juya zuwa falon, sai dai babu Khalil, da alama ya tafi wurin Mommynshi

“Ta shi mu je ki rakani wajen Auntynki in kara duba Ramla, in wuce ina da meeting karfe hudu”

“Ka je kawai” na amsa shi

“Me ya sa?”

“Ba komai”

“To idan ba komai tashi mu je”

“A’a fa” na ce ina gyara kwanciyata a kan 3sitter

“Ko ki tashi, ko in daga ki, wallahi sai a gabanta zan aje ki.”

Ban motsa ba kamar yadda ban yi magana ba.

Ji kawai na yi ya yi sama da ni, hakan ya sa na fara dariya hade da kokarin sakkowa, amma ban samu damar yin hakan ba har zuwa lokacin da muka isa kofar sashinta.

Na dire kasa ina dariya, shi ma dariyar yake a haka muka kwankwasa kofar falon nata.

Khalil ne dai ya bude mana kofar, yayin da ita kuma Gimbiyar ke zaune  a daya daga cikin kujerun falon

Wando da riga ne a jikinta masu kalar ja, wandon iyakarshi gwiwa kamar skin tight yake, sai kuma rigarshi mai hannun vest da kwalliyar fulawa mai kyau a jikin rigar, cif kan kwankwasonta rigar ta tsaya, kuma ba ta matseta da yawa ba.

A gabanta laptop din ta ce take daddanawa, ganinmu ne ya sanyata dagowa tana murmushi, idanuwanta a kan mijinta.

Lokaci daya  ta mika mishi hannu tana murmushi.

Shi ma hannun ya mika mata fuskar shi dauke da murmushi, suka yi musabiha kamar dai wasu abokai.

“Ya jikin Ramla?” ya tambaya a lokacin da yake kallon Ramlan da ke zaune a kan kekenta na yara

“Da sauki sosai” Ta ba shi amsa ita ma tana kallon Ramlan.

Hancin yarinyar ya ja, ita kuma ta wangale mishi baki.

“Zan wuce office, ina da meeting karfe hudu, akwai wani abu ne?”

“Babu, amma me kake so da dare?”

“Abu mara nauyi, don kanwarki ta cika min ciki da tuwo”

Murmushi ta yi “Ta kyauta kuwa”

“Zan tafi. Waye zai raka ni?”

“Wacce ta rakoka nan” Ta yi saurin fada, babu alamar wata damuwa a kan fuskarta.

Gardama sosai muka shiga yi, daga karshe dai na mike hade da bin bayanshi.

Bayan ya daidaita a mazauni ne ya kalleni idanuwanshi a kankance

“A ba ni bye- bye”

Na janye fuskata a kan tashi ina siririn murmushi

“Sarkin kunya.” ya fada

Ban yi magana ba, sai dai na mayar da kallona kanshi, a lokacin da na ji ya kama hannuna yana murzawa

“Ba zan daina fada miki ba Khadija, ina sonki, akwai abubuwa masu nagarta da yawa a tare da ke, na san ke ba ki sansu ba, amma ni na san da su”

Shiru na yi ina mamakin bakin ganga irin nashi, kullum yabon matarshi yake, sau tari ma idan na yi abu sai ya ce wance ba haka take yi ba.

“To idan haka ne me ye nawa yake burgeshi, kodai ya fada ne kawai don ya ji dadi?  Ni wani lokaci ma rikita ni suke yi shi da matarshi,  in rasa ina ne gabansu”

A zuciyata na yi maganar a zahiri kuma kallonshi kawai nake yi, ba tare da na yi niyyar magana ba

Juya hannun nawa ya yi, yana kallon bayan hannun kamar mai son gano wani abu.

Ganin ina niyyar janyewa ne ya sa shi kai hannun nawa a bakinshi ya sum bata a hankali.

Tare muka lumshe idanu, ya saki hannu hade da murza key din  da ke jikin motar.

Na ja baya a hankali hade da rufe mishi kofar, sai da ya fice na dawo dakina, zama na yi zuciyata cike da sake-sake.

Ni dai ba zan ce bama zaman lafiya ba, amma na san abubuwa ba su zo mun yadda na tsara ko nake hasashe ba.

Kodayake yanzu aka fara tafiyar, kila rawar ta canja a gaba.

<< Hasashena 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×