Skip to content
Part 20 of 22 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ina yin break kuwa ta dawo, Sai da ta jira na gama, sannan muka fita zuwa asibitin, a can ma ba ta jima ba ta baro asibitin.

Ni kam ina zuwa na iske su Abdullahi na kokarin kar Bashir toilet, bayan sun kai shin, na ce su bari kawai zan yi mishi duk abin da yake so.

A kan toilet din ya zauna hade da dora kafarshi mara lafiyar a kan wani dan stool, a haka na yi mishi wanka, ya yi brush, na sawo shaving stick na yi mishi shaving,kafin na karbo wasu kayan na canja mishi. Su kuma suka dauke shi zuwa gadonshi. Abincin da Maman Hana ta kawo na hada mishi ya ci kam babu laifi, sannan ya shiga tambayata ya wurin Fatiman akwai dadin zama kodai a canja min.

Zuwa lokacin dai ban ga wata matsala ba, don haka na ce a yanzu dai babu. Haka na ci gaba da debe mishi kewa, yayin da ƴan dubiyarshi basu yankewa a asibitin.

Duk wani abu da ya shafe shi, idan har zan iya ni ce ke yi.

Haka na ci gaba da zaman jinyanshi, kullum safe Maman Hana za ta kawo ni, yamma ta zo ta dauke ni, ba mu da matsalar abinci, har ragewa muke yi.

Sosai nake hidima da Bashir, bana barin shi da kazanta, ina kokarin kwantar mishi da hankali.

Saboda ciwon dai ga shi nan, kullum dai sai an wanke an sanya sabon bandage.

Gami da zamana gidan Maman Hana kam shi ne abu mafi dadi gami da soyuwa a zuciyata gami da jinyar Bashir.

Maman Hana mace ce mai saukin kai da dadin zama, irin mutanen ne da ba taba zama dasu sai sun ba ka dariya. Duk irin damuwar da nake ciki, muddin tana wurin tana kokarin mantar da ni. Ina jin dadin zama da ita sosai babu hantara ko kyara.

Yau ma misalin karfe shida na yamma ta zo daukata, kamar ko wane lokaci cike da rashin jin dadi na bar Bashir saboda na fahimci yau din yana jin jiki, kawai yana karfin hali ne don kwantar min da hankali.

A hanya ma haka muka rika tafiya shiru, saboda ban cika responding maganar Maaman Hana ba.

Bayan shigarmu dukkanmu a falo muka yada zango, Maman Hana tana warware dankwalin kanta wata mace ta yi sallama, ni ce na amsa sallamar, ita kuma ta ce “To ga yar jarabar matar nan, magriba ma ta yi ba ta iya zama gida” lokacin da ta kai karshen maganar tuni matar ta shigo cikin falon, sosai na yi mamakin yadda ba ta yi shiru da maganar ba.

“An je an zo, ai gidan ba naki ba ne, yar rainin wayau, yaushe rabon da ki ganni?” matar ta ba ta amsa

“To da ban ganki ba, Umaima me ya same ni?”

“Na tabbata kin ji ba dadi” cewar wacce aka kira da Umaiman kafin ta juyo kaina tana fadin “Baiwar Allah ina wuni, ya mai jiki” na amsa da murmushi da “Jiki Alhamdulillah, yana samun sauki sosai”

“To Allah Ya kara sauki” ta yi maganar hade da bin bayan Maman Hana da ta shige dakin tana fadin “Mutum da gidanshi ba za ku bar shi ya huta ba”

“An ƙi a bari” Umaiman ta fada lokaci daya kuma suka shige bedroom din

Dalilin da ya sanya ni mikewa zuwa nawa dakin, cike da sha’awarsu, su basu da matsala har lokacin tsokanar juna suke da shi.

Maama na fara yi ma wanka hade da canja mata kaya, saboda an kawo mana kaya daga can Ruma.

Ni ma na yi wankan hade da yin sallah. Yayin da nake ta jin hayaniyar yaran a falo gwanin sha’awa. Ko yaushe ni ma zan kai wannan lokacin, in ga yarana cikin walwala ni ma cikin walwala muna farin ciki? Allah dai ni ma Ya nuna min wannan ranar.

Ina zaune a wurin su Ihsan, Beauty da Maama da kuma Khadija suka shigo dauke da abinci, a gabana Ihsan ta aje min nawa, kafin ita ma ta nemi wurin zama, suna ci ana hira. Na fahimci sosai suke sona, ban san me ke musu dadi gami da ni ba. Amma duk inda nake suna wurin, bacci ne kawai ke raba mu.

Maama babba ma da suka dawo garin shekaranjiya sosai ta fara sabawa da ni.

Maama duk ƙiwarta, cikin kwanakin da mu ka yi a gidan ta hak’ura yadda take yi su dauke ta.

A nan suka yi sallahr isha’i, sai 9pm na na sallame su. Na kira Bashir, saboda duk abin da nake yi hankalina yana wurin shi.

Satinmu daya a garin Katsina, yan gidanmu suka kuma zuwa duba jikin Bashir har da Ummata. Sosai na ji dadin hakan, ko ba komai zuwansu na kara daga kima ta a idanun Bashir da ƴan’uwanshi.

Ummata nasiha ta yi min sosai a kan in kara hakuri, in kula da mijina, kar in bari wani abu ya sa in watsar da shi. Zaman jinya ɗan hak’uri ne. Ni kaina na fahimci jinya sai da hak’uri, shi wanda kake jinya yana jin kamar ba haka ya kamata ka yi mishi ba. Kai kuma mai jinya kana jin kamar an danne ka.

Kar ma jinyar Bashir ta ji labari, shi kam sosai nake kai hankalina nesa, in gama hidima da shi ya kwaɗa sallallami ya ce ina ma ace Sakeena na kusa da ni. Ta dalilin wannan furucin na shi har zuciya na yi, na ce zan koma Ruma, Maman Hanan ce ta lallashe ni na hak’ura, amma sai da na yi kwana biyu ba na sake mishi, kuma ko a jikinshi, ya lura bai lura ba, oho, tun da bai yi min maganar ba. Haka na hakura na warware.

Sai la’asar suka dau hanyar komawa. A satin kuma kawata Samira Badiyya su ma suka zo min, sosai su ma na ji dadin ziyarar tasu, mun tattauna a kan abubuwa da yawa, suka kuma ba ni shawara a kan abubuwa da yawa.

Satinmu biyu a asibiti babu  laifi kam, amma har zuwa lokacin ana wanke kafar hade da yi mishi dressing, Sai dai ba kamar can baya ba.

Ni kam tuni na zama yar gidan Maman Hana. mu kan yi hira sosai, kasancewar ita din mai sakin fuska ce da saurin sabo.

Abin da na fahimta Sam ba ta san Sakeena ba, saboda a bakina take jin labarinta.

Ranar Asabar muka tashi da jiran zuwan Rahma da su Khalil sakamakon hutun da aka yi. Shi kanshi yau Abbansu na fahimci yana cikin nishadi, saboda yadda yake ta fara’a.

Misalin karfe uku kuwa suka iso, har da yaran Rahma guda uku duk maza, da wani irin zumudi su Affan suka dira asibitin, zumudin da na san bai wuce na son ganin Babansu ba.

Sai dai kuma yanayin da suka ganshi da alama ya sanyaya musu jiki, domin lakwas suka yi, duk murnar nan da dokin nan babu, Sai shi ne ke ta kokarin ganin ya dawo musu da farin cikin da suka shigo da shi, amma abun ya ci tura, saboda karshe ma Affan kanshi ya kwantar jikin gadon ya shiga kuka. Kukan da ya kara sanyaya duk jikin wanda yake wurin har da shi kanshi Bashir din.

Rahma kam har da kuka, dama wannan ta saba, duk zuwan duniya sai ta zubar da hawaye.

Duk wanda ya san Bashir a baya, ya kuma gan shi a yanzu dole ya shiga firgici da damuwa. Allah Ya yi ikonshi kam a kan Bashir  cikin kankanen lokaci.

“Sannu Abbansu!” cewar Rahma cikin muryar kuka

Da karfin hali ya ce “Na gode Maman Farhan, sannunku da kokari, Allah Ya bar zumunci, na gode sosai.”

Hawayenta ta dauke ba tare da ta ce komai ba, shi, kuma ya juya kan Dr Nura da hankalinshi kaf yake a kan kafar Bashir ya ce “Na gode Dr, ubangiji Allah Ya kara rufa maku asiri ya raya zuriyarku. Na gode sosai”

“Amin, Sannu Bashir Allah Ya sa ciwo ya zama kaffara”

“Amin” muka amsa gabadaya

Rahma ce ta ce “Wai yanzu babu abin da za a yi Abban Farhan?”

File din da yake budewa ya rufe kafin ya ce “Duk abin da ya dace suna yi, sai dai mu yi addu’ar samun lafiya. Kin san ita cuta ta kan shiga a gabadaya ne, warkewa kuma sai a hankali.

Komai ba mu ce ba,, Bashir ne ya ce” To ga mu nan dai, ko zamu warke din, ko kuma muna jiran lokaci ne Allah kadai ya sani”

Yanzu din ma ba mu ce komai ba, Sai Rahma da ta fara harhada kan yaran zuwa waje, ni ma bayansu na bi, a kan barandar kofar dakin muka zauna. Har zuwa lokacin jikin yaran a mace, hatta Maama shiru abun ta kamar ba ta wurin, ta dai lafe a jikin Khalil.

Rahma ce ta fara cewa wato “Auntyn Ramla mutum ba a bakin komai yake ba, Allah Ya sa mu cika da imani”

“Amin” na amsa a sanyaye

“Ina ta son mu yi magana a kan maido da su Khalil gida. Auntyn Ramla me ya sa? Ko muna yi musu wani abu da bai gamsheku ba ne?”

Idanuna na dora a kan yaran, jikinsu ya fallasa irin kulawar da suke samu, dukkansu jikinsu a murje lub-lub gwanin sha’awa. Idanun na dauke daga kansu zuwa wani bangare daban kafin na ce” Ai, tsakaninmu da ku Maman Farhan sai godiya kawai, babu wani abu da za mu yi muku mu saka muku. Sai dai addu’a. Amma babu wani abu na rashin dacewa da ya sa aka nemi su Khalil su dawo gida. Ni dai nan idan akwai wani abu ma to ban sani ba wlh.”

Zamanta ta gyara kafin ta ce” makarantar da suke they dealing okay, burin Sakeena Shi ne yaranta su samu ilmi mai inganci, za ta iya sadaukar da rayuwarta a kan hakan. Ba na jin Idan tana da rai za ta amince a cire su Khalil daga makarantar can a dawo dasu kauye. “

Sosai raina ya sosu, abubuwa da yawa idan suka faru sai ka ji an ce da Sakeena na nan, ba za ta yarda ba, ba za ta bari, ko ace ba zai faru ba. Bawai iya Rahma ce ke fadin wannan ba, dangin Abban Khalil suna yawan fada, bare kuma Bashir da ya zame mishi kamar karatun sallah.

Jin na yi shiru ne ya sa ta ce “Auntyn Ramla, ba tare da sanya hannun mijina ba, ina nufin misali ya janye hannunshi a kan Affan da Khalil, kuma sannan babu ran Bashir, to zan iya rike su hade da basu ilmi mai tarin yawa bangaren addini da na zamani. Kila na san Bashir da ƴan’uwanshi suna ganin kamar sun dora mana wahala ne, za mu iya yin abin da ya fi haka ga ahlin Sakeena, don Allah na kawo kokon barata gare ki Khadija, ki sanya baki, idan hutu ya kare su Khalil su koma makarantarsu”

Shiru na yi ina nazarin maganarta, kamar tana ganin da sa hannuna a cikin lamarin, kamar kuma da gaske tana neman alfarmar tawa ne. Da wannan tunanin na ce “To zan yi kokari.” haka mu ka shiga tattaunawa har la’asar. Sai da na je na yi wa Bashir alwala sannan na dawo ni ma na yi, a lokacin kuwa tuni Dr Nura ya kwashe yaran zuwa masallaci.

Bayan na idar da sallahr na kara yi wa Rahma ta yin abinci a karo na ba adadi, saboda akwai flasks din abinci, wasu ma ko taba su ba mu yi ba. A karo na ba adadin ta kuma cewa “Ba na jin yunwa, Sai dai ko yaran za su ci idan sun dawo”

Su din ma kadan suka taba, wai sun koshi.

Dr Nura kam zarya ya rika yi tsakanin manya likitocin da ke asibitin, saboda Bashir ya matsa lallai sai a nemar mishi sallama, don wanke kafar da sayen magani za a rika yi ko yana gida ne.

Muna zaune a barandar ni da Rahma, Maman Hana ta iso, cikin sakin fuska suka gaisa da Rahma, kafin ta wuce ɗakin da Bashir yake, nan ma ba ta ji ma ba ta fito zuwa wurin mu

“Ashe ƴan Abuja suka iso?” ta yi maganar daidai tana zama gefenmu

“Ai kuwa, tun dazu” na amsa ta cikin murmushi, Rahma ma murmushin take yi, wata sabuwar gaisuwar suka shiga yi, kafin Maman Hana ta ce “Tubarakhallah yan maza zira gasu nan. Ya kuke fama da rashin ji?”

“Akwai kam. Dambe dai kamar filin boxing” cewar Rahma cikin dariya

“Na sani ai, ni ma mai guda uku fama nake bare biyar”

Daga haka suka shiga hirar rashin jin yara maza. Ni kam ma mikewa na yi zuwa wajen Abban Khalil, tun da ya ga shigowa ta ya mayar da hankalinshi a kaina har na karaso

“Khadija!” ya kira sunana cike da kulawa

Duk lokacin da ya yi hakan sai in ji jikina gabadaya ya mutu, tausayin kaina ya kama ni, in rinka jin kamar na zama wata abar tausayi, mai kuma neman taimako, Sai na yi da gaske nake iya matse hawayena, kamar yanzu ma da na rike hawayen da karfin tsiya

“Me ya sa kake son a sallame ka wai?”

“Saboda ke Khadija, sosai tausayi kike ba ni, kalli yadda kika koma kamar ke ce ba ki da lafiyar, kin je gidan wata kin zauna a raɓe, na tabbata dole ce ta sanya ki zaman gidan nan”

“Tabbas dole ce, amma ina jin dadin zama da Maman Hana, idan don ni ce, don Allah ka tsaya a kula da lafiyarka”

“A’a, ya kamata ki koma gida ke ma ki huta, ni kaina na gaji da zama a nan. Ya fi in koma gida, idan ma fita wajen za a yi sai mu fara shiri”

Shigowar Dr Nura da wasu likitoci ne ya sanya ni yin shiru, Sai ma kunnuwana da na raba a tsakaninsu, discussion din nasu kaf a kan file din Bashir ne. Kowannensu da abin da yake fada, wani lokaci kuma maganar tasu ta zo daidai. Kiran sallahr magriba ce ta fitar dasu. Ni ma alwala na yi wa Bashir, ni ma na yi na kabbara sallah.

Bayan na idar ina kan sallaya Affan ya shigo kusa da ni ya zauna idanunshi a kan Babanshi, har zuwa lokacin bai saki jiki ba.

Da kulawa na ce “Ko kana jin yunwa ne Affan?” kai ya girgiza alamar a’a, ban yi tsammanin zai yi magana ba, su kuma na ji ya ce “Yaushe za mu tafi gida?” a hankali ya yi maganar, saboda ni kadai ce na ji

“Ruma ko Abuja?

” Kauye”ya kuma amsawa a hankali.

“Kila zuwa gobe sha Allah”

“To shi fa Abbanmu”

“Muna jiran ya ji sauki Affan” na amsa shi a sanyaye

Hawaye ya shiga daukewa, a cikin kukan ya ce “Yaushe to zai ji Auntynmu?”

Ka cinyata na kwantar da shi a hankali na ce “Affan yi hak’uri ka daina kuka, kana dagawa Abbanku hankali. Sha Allah zai ci sauki soon. Ku dai ku rika yi mishi addu’a”

“Ai muna yi kullum, har ma da Mommynmu da Ramla, Mommynsu Farhan ta ce mu rika yi musu addu’a”

Idanuna na lumshe a hankali, wani abu mara dadi yana min yawo a kirji.

“Me same shi?” sautin Bashir ya katse min tunanin da nake son fara yi.

“Babu komai, ya gaji ne” na ba shi amsa, hankalina na a kan Khalil da yake shigowa dauke da Maamah.

Abun mamaki sai ta ki yarda in dauke ta, wannan drama ita ce abin da ya sanya mu dariya yau, cikin dariya Abban Khalil ya ce “Kawo ta nan mu gani ko za ta yarda, Sai ka huta”

Ya nufe shi da ita, cikin sa a sai ta yarda, muka kuma yin dariya, Abban Khalil ya ce “Wato yaro ma ya san na shi, kalli kiwa irin ta Maamah fa, amma wai ba ta ƙin ƴan ‘uwanta”

“Abba kafar na yi ma zafi?” Khalil ya katse mana dariyar da muke da ta tambayarshi idanunshi a kan ƙafar

“Ba sosai ba Khalil, ku dai rika yi min addu’a kun ji” ya ba shi amsa shi ma yana kallon kafar.

Su Rahma ne suka shigo da Maman Hana, a nan Bashir ke fadawa Rahma Maman Hana matar Bashir Sandamu ce. Cike da mamaki Rahma ta ce “Wacce ke ta bamu wahala kenan, kin ki zaman Abuja, kuma kin hana mijinmu ya zauna”

Cikin dariya Fatima ta ce “Mijinku dai bai yi niyyar zama ba, amma ni ina ruwana” duk mu ka yi dariya.

“Rahma ya kamata ku tafi masauki, yaran nan sun gaji” cewar Bashir yana kallon yaran daya bayan daya

“Gaskiya kam, tun ba Haidar ba, kamar kaza yake, ga shi an sha tafiya.”

Daga haka mu ka shiga shirin tafiya, Rahma dai mu ta bi. Dr kuma ya tafi hotel.

<< Hasashena 19Hasashena 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×