Muka gaisa cike da girmamawa kafin doguwar ta ce "Bashir din ma baya nan ko?"
"Eh wlh, suna Batsari"
"Allah sarki, idan ya zo kin fada mishi, su Saratu sun zo duba shi da jiki"
"In Sha Allah zan fada mishi"
Mu ka danyi shiru kafin gajeruwar ta ce "Ai kafar da sauki ko?"
"Ah! Alhamdulillah Gaskiya, tun da yanzu yana taka da kanshi"
Na ba ta amsa
"To Ma Sha Allah, Allah Ya kara lafiya" cewar doguwar
"Amin Ya Rabbb" na amsa
"Yaran ma duk basu ko?" cewar gajeruwar
"Eh. Duk sun fita" na kuma amsawa.
Doguwar ta mike. . .