Na shiga bude ledojin, ledar farko dai tarkacen Assidiq ne, pampers, cerelac, custard, da ɗai Sauran tarkacen shi “
Daya ledar kuma kayan tea ne, manyan gongoni
“Wadannan na yaranki ne, kar ki je ku dora musu hidima”
Murmushi na yi kafin na ce “Mun gode”
Daya ledar ma kayan tea ne, sabulai, omo, Manshafawa kala-kala cike fal.
“Wannan na Umma ne” ya kuma fada yana kallo na
Wani murmushin na kuma yi kafin na ce “Umma ta gode sosai, Allah Ya kara budi”
“Amin” ya amsa yana ci gaba da cin abincinshi.
Daya ledar kuma zannuwa ne da yadin shadda, nan ma kafin in ce wani Abu ya ce “Turmi biyu na Umma ne, turmi daya Maryam, daya Yusra, shaddar kuma ta su Usman ce”
“Yallaboi, wannan ai, hidima muka dora maka, da na san haka zai faru ai da ban yi tafiyar nan ba”
“Ina hidimar?”
“Ga ta ka yi, da gaske abun ya yi yawa”
“Bai yi ba Khadija, Umma ta cancanci komai, suruka ce mai kawaici hade da dattako, Allah dai Ya ara mana rai da lafiya”
“Amin, to mun gode Allah Ya kara budi. Ni kam ko mai ɗangyashin kudin nan da ake ma kirari da gaske ne?” cikin zolaya na yi mishi maganar
Ba shi kadai ba, har yaran sai da suka yi dariya, shi ma cikin dariyar ya ce “Da ba ki sani ba, lallai yarinyar nan na ki wasa ne”
Wata dariyar muka kuma yi, kafin ya ce “kafin ku dawo Sha Allah za a gama saka komai na sabon gidan can, kuna dawowa sai tarewa”
Tuni yara suka fara tsalle wai za su tare a sabon gida, ni kam kayan na shiga tattarewa ina fadin “Allah Ya kai mu”
Ana fitowa sallahr asuba muka dau hanya, farin ciki wurin su Khalil ba a magana.
Tun muna wuce wurin da suka sani, har suka fara tambayarshi “Auntynmu ina ne nan?” In da na sani in yi musu bayani in da kuma ban sani ba Salisu ya yi musu bayani.
Gab za mu isa gidan mutum daya suka yi bacci, sannan motar ta yi shiru, Bashir kam kira minti-minti ya yaran nan, fatan babu wata matsala, idan akwai abin da suke so ki siya musu. Aikinshi kenan. Ni fa tafiya da yaran nan riba ta zame min, saboda ni kaina na san wani abun don su aka yi min shi. Har da buhun shinkafa, carton na taliya, manja da Mangyada wai kar a dorawa Umma wahala.
Misalin karfe biyu muka saba sa Kano, abun mamaki har mun riga Yusrah isa, aikam gida ya kacame da murnar ganinmu, ni kaina wani farin ciki nake ji mara misultuwa, karo na biyu da na zo gida tun bayan aurena.
Abinci da sallah kawai Salisu ya yi ya juya, muna ta rabon tsaraba Yusrah ta iso, aka dora murna daga inda aka tsaya. Yara kam sai tsalle, Khalil ya samu abokai, Usman da Haidar. Maama kuma ga Ammatullah din Yusrah da Ahmad. Assidiq ne ba shi da aboki, Sai ƴan dauka, Maryam kam ko ina da shi take zuwa.
Misalin karfe bakwai muna cin tuwon dare a daki, yaran kuma suna waje suna cin nasu Bashir ya kira.
“Ya kuke?” ya fara tambaya bayan na daga
“Alhamdulillah!” na ba shi amsa
“Babu wata matsala ko?”
“Babu komai”
“To Ma Sha Allah! Ina yaran?”
Affan na kwaɗawa kira, ya kara so a guje, na mika mishi wayar.
“Kai Bashir akwai son ƴaƴa” cewar Yusrah tana murmushi
“Tun ba biyun nan ba, son da yake musu babu yadda za a kwatanta shi”
“Ba za ki gane yadda yake ji ba ne, kin san babu ran mahaifiyarsu, ji yake kamar duk abin da ya yi musu sai sun yi kukan maraici” cewar Umma
“Haba Umma, me yaran nan suka rasa, da za su yi maraicin uwa, wlh daga mutuwar mahaifiyarsu kawo yanzu ba su yi kukan rashin uwa ba, yan gata ne gaba da baya. Ni idan har na san bayan na mutu yarana za su samu gatan wadannan yaran, to yanzu ma in mutu”
Yusrah dai dariya ta yi, Umma kuma ta rike Haba tana fadin “Baki da hankali, ke uwa fa, uwa ce, babu wacce za ta taba me ye musu gurbin uwar su”
“Wlh Umma ina jin yaran nan kamar yadda nake jin Maama da Assidiq, amma kullum mutumin nan nunawa yake yi dai ina yi musu ba daidai ba, kullum ban iya ba a kan yaran nan, _yaran nan sun ci abinci suka tafi makaranta kuwa, yaran nan sun tafi da abinci makaranta, abin da na sawo jiya na ce ki basu kin basu._ kullum aikinshi kenan cikin tuhuma ta, sosai abun ke ɓata min rai”
“Na ce miki ki yi hak’uri, tun da haka yake, Sai ki rinka bin shi a zauna lafiya ba shi kenan ba”
Yusrah ta yi caraf ta ce “Idan ma ban da Auntynmu, idan wata macen ce ai ta samu weak points na Shi, da wannan damar za ta yi amfani ta shiga jikinshi sosai. Yanzu ba ga shi ba, da kika amince za ki taho dasu, ba ki ci riba ba”
Umma ta ce “Idan ban da shirme ma, yaran da ba goyasu za ki yi ba, me na bacin rai”
“Kin san Allah Umma, da ace mahaifiyarsu na nan ba za ta rika yawo dasu ba, amma ni Bashir ko gidan suna zan je a cikin gari sai ya ce to wa zan bar wa yaran?” na yi maganar cike da jin haushi. Kafin su ce wani abu na kuma cewa “Ko fa gidansu na ce zan je, Sai ya ce to yaran fa, irin basu san hanyar nan ba. Kai ina ganin ikon Allah”
Dariya Yusrah ta yi tare da fadin “Gaskiya kam abun ya yi yawa”
“Ke da Allah can, to kara tunzura ta” cewar Umma tana tashi daga wurinmu
Yusrah ta kuma yin dariya, ban da ni da nake jin zafin abun kamar yanzu yake faruwa.
Daidai lokacin Khalil ya kawo min wayar ya ce “Auntynmu ga shi, Abbanmu ya ce zai turo kudi ki kai mu wurin shakatawa gobe”
“Allah Ya kai mu” na yi maganar hade da amsar wayar
Yusrah kuma ta ce “Hankali a jikin yaran nan kamar ya yi magana”
“Ai ni ba ni da case da su, da ubunsu ne, amma yadda yake min a kansu da ace suna min rashin kunya da tuni na nemi mafitata.”
Komai Yusrah ba ta ce ba, ta mike zuwa tsakar gida, ni ma sai na mike na bi bayan ta
Da safe kam sai ga kudi Bashir ya turo har 100k,wai in kaisu shoprite su sayi duk abin da suke so, idan kudin sun yi kadan in yi magana ya karo.
Na ce to. Cike da mamaki na nunawa Yusrah alert din na ce “Kin ga mutumina ko.”
Murmushi ta yi hade da karbar wayar ta ce “Da ba ki zo da su ba, ba zai turo wadannan kudin ba, bayan kwana biyu kuma ki ce mishi za ki kai su Minjibir park”
Mu ka yi dariya hade da tafawa.
Karfe biyu kuwa muka fita zuwa shoprite, yadda yaran suke farin ciki da walwala, ni kaina sai abun ya yi min dadi, su hau lilo, su hau wancan abun wasa duk su kadai.
Kayan ciye-ciye kam kaca-kaca. Haka muka juyo gida yamma lis, gajiya kam ba a magana , shi ya sa ana yin sallahr isha’i kowa ya ci abinci sai bacci.
Ba ni kadai ce nake jin dadin ziyarar Kano ba, har da su Khalil, musamman yawon da su Usman ke fita da su, Yusrah dai satinta daya ta juya, ni kuma Bashir ya ce in dawo ranar Alhamis, ranar da ya kama kwana goma cif da zuwana.
Tun bayan tafiyar Yusrah Umma ta shiga hidimar tsaraba ta, ina taya ta da yan kudin hannuna, su dai su Khalil tsarabar yar gullisuwa, kwakumeti, tuwon madara loga sune nasu.
Ni kuma rabin buhun fulawa aka saya, aka yi min fura sa, Sai kuma mu ka sayi gyada kwano uku aka yi min kuli da mai. Barkono daddawa da kuka.
Muna zaune da Umma da dare muna hirar bankwana saboda washegari zan tafi ta ce min “Kin ce kuna komawa za ku koma sabon gida, to babu abin da kike bukata?”
“Ba komai gaskiya, kayana duk sabbi ne basu sha jiki ba, dama-dama kujeru, idan da ina da hali su zan canja”
“Ai da kin sani ba ki wahalar da kanki wajen yin wannan tsarabar ba, Sai ki tattala kudin, a siyar da kujerun a yi ciko a siya miki sabbin”
Zamana na gyara kafin na ce “Ai na yi siyayyar tsarabata tun da dadewa fa, ban san zai yi mun wannan hidimar ba, yanzu haka ma dai ta dalilin tafiyar nan ina da wajen dubu hamsin, ina jin zan yi amfani da su, a canja min yadin kujerun”
“To hakan ma ya yi, Allah Ya taimaka, Sai a yi ta hak’uri, ki rika kawar da idanunki a kan yaranshi don Allah. Ko me zai yi musu babu ruwan ki”
Kai na jinjina alamar fahimta, nasiha ta ci gaba da yi min sosai a kan kawar da kaina da hidimar yaranshi.
Salisu ne ya kuma dawowa daukarmu, yanzu din ma sai da muka cika boot da tarkace, ga buhun gurasa, ga tarkacen su Khalil na tsaraba.
Haka muka dau hanya, ku san a tare muka isa da Bashir, yana isa muma muka isa, yara suka makalkale shi, suka cika mishi kunne da labarin Kano, Affan har yana cewa shi dai a can zai yi makaranta.
Ni kam aikin kakkabe gida na shiga yi, don ma an kawo mana abinci daga cikin gida. Sai 10pm na ɗan kammala abin da zan iya, zuwa lokacin yara duk sun yi bacci. Sai ni da Babansu, ranar kam na yarda da gaske Bashir yake yi, ya yi kewata, saboda ya kara tara min gajiya, ban yi bacci ba sai wajen 2am,shi ya sa sai wajen 6:30am na yi sallahr asuba.
Na shiga kitchen kuma, bayan mun karya mu ka shiga rabon tsaraba, aka kaiwa Hajiyar Maman Khalil, cikin gida, da kuma makotana da abokan arziki.
Yanzu kuma hankalinmu ya fi karkata ne a shirin tarewa sabon gida, da na yi wa Bashir shawarar yadda zan yi da kujeruna, Sai ya ce in bari, wai ba sai na tafi da komai ba.
Hakan ya sa na kara adana kudina, sana’ar nake son farawa, ba zan iya zama sai abin da miji ya miko min ba.
Kamar ko yaushe ranar Monday Bashir ya koma aiki, inda ya ce next week idan ya dawo Sha Allah tare za mu juya.
Don haka in yi package na kananun abubuwan da nake so na amfani.
Na ce to.
Na kira Umma na fada mata yadda ake ciki, ta ce to in jira mu tare tukun in ga ya abun yake.
Ni ban san me ya sa ba, ba na jin murna da karsashi a kan maganar tarewa sabon gidan nan, yaran ne kawai suke murnarsu, ni kam sai dai in yi ta yake, na rasa dalilin hakan.
Satin nan duk kare shi mu ka yi a shirye-shirye, Alhamis ne kamar ko wane lokaci Bashir ya dawo, mu ka ci gaba da kintse-kintse, juma’a da safe aka fara dibar wasu kayan namu musamman na sanyawa zuwa Katsina, safiyar Asabar kuma mu ka bi su a baya, akwai kanwar Maman Khalil Momy, Sai Aunty Habi da kuma Murja.
Duk yadda nake imagination din gidan sai ya wuce da tunanina, gida ne tangameme, mai dauke da katon farin gate, fentishi daga gaba white and ash ne, sosai ya haska hade da bayar da kala.
Kana shiga akwai dakin maigadi, wanda daga saman dakin ne, aka dora water tank Manya guɗa biyu, daga nan sai katuwar farfajiyar gida mai dauke da doguwar katanga wadanda madaidaitan fulawa suka zagaye saboda yanzu suka fara girma.
Daga can bangaren yamma wajen dakin maigadi akwai bishiyoyin mangoro, guava, cashew, umbrella, gwanda da kuma ayaba. Wadanda su ma basu gama girma ba.
Sai ka dan yi tafiya kadan sannan za ka iske part din farko, wanda yake bangaren gabas kofarshi tana kallon yamma, daga bangaren yamman kuma akwai wani part din, kofarshi na kallon gabas, wannan ya sa suke facing din juna.
Idan ka dan kara gaba, to a kawai wani part din daga bangaren kudu, kofar shi na kallon arewa, kenan part din can biyu su dan ba shi baya. Kuma duk ya fi su girma, saboda shi upstairs ne ma. Shi ma kuma a gaban entrance din akwai doguwar farfajiyar ko in ce tsakar gida, wacce za a iya parker motoci uku a tsaye ba a kwance ba.