Skip to content
Part 30 of 30 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tare mu ka yi aikin abincin rana da Bashir, don a, harkar kitchen kam Bashir Oga ne, ko mace sai haka, karfe hudu ya fita da yaran, wai zai kai su gidan ƴan’uwansu ta, bangaren shi, da kuma bangaren mamarsu.

Gidan ya yi shiru har hudu da rabi, lokacin da na ji ana buga min kofa na dauka Maman Hana ce, saboda ita kawai nake jira, sosai nake son matar, Sai dai kicibis na yi da Maman Aiman a lokacin da na bude kofar, murmushi ta yi tana fadin “Ina fatan ban katse miki jin dadi ba”

Ni ma murmushin na mayar mata kafin na ce “Ko daya, dama Ina kaɗaici ne”

Duk mu ka yi siririyar dariya, kafin mu ka shiga, kan kujera ta zauna na kawo mata ruwa da fruit sai mineral gora ɗaya na ajiye mata. Muka shiga hira, da alama tana da sakin fuska sosai kuma ba ta da bakunta.

Muna cikin hira na ga kiran Maman Hana, wani dadi na ji, saboda na tabbatar tana kan hanyar zuwa, ilai kuwa ta ce min ga ta a gate. Excusing din Maman Aiman na yi, na je na tafi bude mata kofa

Tun da ta shigo take yaba gidan da tsarin shi, abin da ya yi mini dadi, tarba ta musamman na yi mata har da abinci, kuma na ji dadi sosai yadda ta ci abincin har sama na yi mata jagora, saboda Maman Aiman ta tafi. Sai gab mangariba ta tafi, inda na yi mata alkawarin da zarar na samu chance ni ma zan zo.

Sai da aka yi sallahr isha’i su Bashir suka dawo, na sha labarai kam wajen Khalil da Maama shi Affan miskilanci hana shi magana yake sai idan ya so.

Washegari ma haka na yi ta samun baki, makotana na kusa, da kuma ƴan’uwan Bashir da Sakeena wadanda suke cikin Katsina.

Haka muka cinye wannan satin, satin sama kuma a kan hidimar makaranta ya tafi, Asabar din karshen satin Ummana ta zo ganin gida, ita da wata Goggona, da kuma Auntyna, sosai su ma suka yaba, musamman yadda Bashir ya gyara min daki, ya zuba min kaya masu tsada haka suka yi ta yi mishi godiya. Karfe hudu suka tafi.

Tun da suka tafi nake tattauna maganar da mu ka yi da Ummata a kan sana’a, ni dai zaman haka ba na son shi. Umma ce min ta yi, in yi sana’ar kayan kamshi, misali humra, kwalakca, freshners, morning fresh, Sai Kuma supliment tun da yanzu su ake ya yi, da kuma atamfofi. Amma kudin sun yi kadan, Sai dai zan fara gwada kadan mu ga abin da Allah zai yi.

Da dare bayan mun kintsa komai, muna kwance na ce “Alhajina ina da magana” sai da ya kara jana jikinshi sannan ya ce “Ina jin ki Hajiyata, za a yi min wayau ne?”

Cikin siririyar dariya na ce “A’a”

“To menene?”

Jikinshi na kara shigewa kafin na ce “Ina son gwada yin sana’a ne kafin aikin ya samu”

“Tunani mai kyau, saboda ni dai aikin nan ma ba lallai ki yi shi ba, ina son kawai ki zauna, ki kular min da yarana, har da na nan” ya kai karshen maganar hade da mayar da hannunshi kan marata

Hannun na dauke ina fadin “Don Allah ka daina min fatar ciki yanzu, ni ba ni da komai”

“To zamu gani ai, me kike son sayarwa?”

“kayan kamshi, da kayan yara, Sai kuma atamfofi”

“Lallai ke Hajiya ce, da na san kina da wadannan kudin ai da na daina fita kasuwa da wurin aiki na yi zamana”

Siririyar dariya kawai na yi ba tare da na ce komai ba, shi ne ya ce “ya  abun zai kasance to?”

“Da turaren zan fara kafin mu ga abin da Allah zai yi”

“To Allah Ya taimaka”

“Amin” na amsa kafin mu ka rika taba hira a hankali har bacci ya dauke mu.

Sai Monday su Khalil suka fara zuwa makaranta, kasancewar hutu ya kare, Sai bayan sun  tafi  na shiga kasuwa sawo kayan hadin turare, kasancewar ranar farko ce, ba karamar wahala na ci ba. Shi ya sa na dawo gida a wahale, har da su amai na sha. Abu kamar wasa sai ga shi na kasa dora girkin rana, saboda aman da nake yi duk ya kashe min jiki, zuwa azhur dakyar na yi sallahr.

Dole na kira Bashir na ce ya zo ban lafiya, after 30mns na ji bude gate din Shi.

“Me ya faru?” ita ce tambayar da ya fara jeho min, lokacin da ya shigo falon ya iske ni kwance saman center cafet.

Dakyar na mike zaune na ce “Ban lafiya, Sai amai nake yi, daga zuwa kasuwa”

“Subhnallah! Sannu, bari mu je asibiti”

Ban yi musu ba, saboda ina jin jiki, shi ne ya dauki Assidiq, ni kuma na lallaba dakyar zuwa wurin motar. Wani private hospital mu ka je ma fi kusa, bayan gwaje-gwaje suka daura min ruwa, inda Allah Ya taimake ni ma, su Affan sai 6pm za su dawo.

So wajen 5:30 aka sallame mu, shi ya sa ku san tare mu ka dawo da su Khali, Maama kam ƴan first day at school, an ci kuka an koshi, sosai ma ni ta ban dariya, musamman yadda ta fada jikin Abbanta tana kuka, wai ita ba za ta kara zuwa ba. Kamar ba ita ce ke bacci da Lunch box da school bag bag.

Bread da miya suka ci, yayin da Bashir ya shiga kitchen yaran na taya shi da wasu abubuwan, ni kam ina kwance.

Yau kam dole a gida ya yi sallahr magana, yana idarwa kuma ya zubo mana jallof din taliyar ya yi, wacce ta ji busasshen kifi.

Muna cin abincin ne ya ce “Yar kasuwa, a haka za a yi kasuwanci, farawa da iyawa da shan ledar ruwa” sai da na kusa shakewa saboda dariya

Cikin dariyar na ce, “Wlh kamshin turarurukan nan ne, suka hau kaina”

“To a canja sana’ar, Babyna baya son kamshin turaren nan”

Sai da na kalli su Khalil, na ga hankalinsu ba a kanmu yake ba, sannan na ce “Wai waye ya fada ma akwai Babyn ne, don Allah kai daina yi min maganar nan”

“Likita ya fada min yau, don haka ki kula da kanki, kar ki jefar min da yaro a wajen kasuwancinki”

Abincin da nake ji na ji babu test ko kadan, kamar zan yi kuka na ce “Don Allah da gaske?”

“Ba na fada miki ba tun ranar can, ni da zarar na jefa kwallo a cikin raga nake ganewa”

Spoon din na ajiye, idanuna suka ciko da kwalla, da, gaske ba na son ciki a yanzu, ban shirya mishi ba, ina bukatar in huta, ni ma in ji yadda mata suke ji, yayin da suke zaman ba ciki ba goyo

Hawayen na dauke hade da mikewa na haura sama, saman gadona na fada na ci gaba da kukana.

Bashir kam bai shigo ba, Sai da ya sallami yara da duk wani homework, sannan ya hauro saman sabe da Assidiq da ya yi bacci. Ni kaina baccin ne ke dauka ta, shi ya sa sama-sama na ji shigowar shi. Gefena ya kwantar da shi ya shiga toilet, sama-sama nake jin buruntunshi, har zuwa lokacin da ya kammala shirin shi ya kwanta a Gefena, ba tare da ya ce min komai ba, abin da ban tsammani ba.

Da safe tare da shi mu ka shiga kitchen, yayin da su Affan ke ta shirin makaranta, su suka shirya Maama wacce ke ta rigima wai ta ba za ta je ba. Around 7:30am mai kekensu ya zo, bayan sun tafi ya rage gidan daga ni sai shi.

kuma a lokacin ne na zauna ina cakular abincin, saboda Sam ba na jin dadin komai, ina zaune a wurin ya sakko cikin shirin fita office, kai tsaye dining din ya tunkara, dalilin da ya sanya ni hada mishi komai, da Bismillah ya fara kurbar tea din kafin ya ce “jikin ne?”

Kai na girgiza a hankali kafin na ce “Kawai bakina ne babu dadi and it seems like kana fushi” na yi maganar cikin langabar da kai gefe

“Ta ya ba zan yi fushi ba, a gabana fa kike kukan hada zuriya da ni Khadija, ba kya son jinina kenan”

Tea cup din na ajiye hade da kallon shi kafin na ce “Haba yallaboi, ya za ka juya min magana, wlh ba haka nake nufi ba, kawai dai na ga cikin ne ya yi wuri, ya kamata in dan huta, shekara hudu da aure yara uku”

“Me suka rasa?” ya yi tambayar idanunshi a kaina

“Ba komai” na ba shi amsa

“To babu ruwan ki, kawai ki yi ta haifa min, Allah ba zai hana ni abin daukar dawainiyarsu”

“To ka yi hakuri don Allah, Allah Ya bamu masu albarka”

“Amin, haka ya kamata ki ce. And cikin wata uku ne, an  ce babu yawan zirga-zirga ko aiki mai nauyi, saboda har yanzu bai zauna daidai ba.”

Kai na jinjina alamar fahimta, kila wannan dalilin shi ya sa jiya da dare bai kusance ni ba kenan, don shiga kitchen ba bakon abu ba ne a wurin shi.

A nutse ya yi break din shi muna taɓa yar hira, Sai bayan da ya gama ne zai tafi ya ce” Khadija please take good care of my baby, ba na son komai ya samu cikin nan I’m telling you. Abinci ki yi mai sauki”

“In Sha Allah” da haka na rako shi wurin mota, hade da bude mishi gate ya fita.

Bayan fitarshi aikin hada turarena na shiga yi, ina tsaka da aikin ne Maman Aiman ta shigo, don haka mu ka ci gaba da yi tare da ita muna hirar duniya.

Akwai humra, da kuma su roll on kananu masu taushin kamshi da kuma masu karfi irin na maza. Sosai Maman Aiman ta rika yabawa da turarurukan, ita ce ma ta dauki hotunansu ta daddora a status tana min talla.

Tun kafin ta fita na ga mutane na ta tambayarta nawa, kuma a ina za su samu. Abun ya yi min dadi, na rika addu’ar Allah dai ya sanya min albarka a abun.

Ragowar abincin break fast din mu na ci, na yi sallahr azhur na kwanta bacci, Sai la’asar na farka, shi ma Assidiq ne ya tashe ni, ruwan zafi na fara dorawa, sannan na yi wanka hade da yin alwala na yi sallahr la’asar, bayan na idar na yi azkhar dina, na yi wa Assidiq wanka,  na shirya mu gabadaya, zuwa lokacin kam har farar taliyar da na dora ta dahu,  na yi mana souce din cabbage. Na shirya a dining, saboda na san nan da 30mns, da maigidan da yaran gidan duk sun dawo.

Bashir dai 5:30pm ya dawo, su Affan ne sai 6pm,saboda makarantar hade take da Islamiya.

Haka dai rayuwa ta ci gaba da juyawa cike da farin ciki, saboda zamana a sabon gidan nan, farin cikin da nake samu da kulawar da nake samu, ban same ta lokacin da nake amarci ba.

Shi ya sa lokaci kankane na yi haske hade da yin ƴar ƙiba, musamman da ya kasance akwai yaron cikin. Bangaren sana’a kam, a hankali Maman Aiman ke kawo min customer na cikin unguwa da wajen unguwa, ni ma kuma Ina samun nawa, haka na matsa sai da Maman Hana ta rika yi min talla a wurin aikinsu, nandanan idan na hada turare  ya kare, tun ina sawo kayan hadi kadan, har na fara sawo da yawa. Bashir ma yana dibar na maza ya tafi dasu wurin aikinshi, kuma sosai saye ake yi, wani lokaci har nema ake yi.

Kila dalilin hakan ne ya sanya shi ba ni jarin miliyan daya, wai in gwada saro atamfofi da rigunan yaran mu gani, idan komai normal sai ya kara min.

Ranar farin ciki hana ni bacci ya yi, da safe kam na kira Ummata na fada mata, ta ce za ta hada ni da wani mai irin sana’ar a kwari.

Aiko a waya muka gama komai, ya turo min kaya latest, ni kuma na tura mishi kudi, yanzu din ma dai Maman Aiman, Maman Hana, Bashir sune ƴan tallata, atamfofi da rigunan yaran basu tafi kamar turare ba, don sai da suka yi sati jibge babu wanda ya saya, har na fara karaya, na fadawa Ummata da Bashir. Sune suka rika karfafa min gwiwa a kan kar in damu za a saya.

Sai da kayan nan suka yi sati biyu, sannan na fara ciniki, shi din ma bashi, wai  karshen wata, abu kamar wasa,  kasuwancin atamfofin ya koma za a dauka amma sai karshen wata kudin . Cikin sati biyu komai babu, har ana nema, haka Bashir ya kara min 500k na karo, cikin sati su ma suka kare, inda Allah Ya taimake ni satin karshen wata ne. Na zauna zaman jiran tsammani. Sai dai karshen wata na yi na fara jin alert, wadanda suka dauka kadan take suke biyana, wadanda suka yi siyayyar 150k,sune ke ba ni rabi, ko 100k,wasu kuma duk suke biyana, cikin sati da salary kudin dakko wasu kayan suka hadu. Wani irin farin ciki nake ji babu misultuwa.

Daga lokacin kasuwancin atamfofi ya koma na ƴan albashi. Za a dauka, wata a hada min kudi, turaren ma ana daga kafar sati.

Na yadda, idan mutum na taba kudi, ba komai ne ke ɓata mishi rai ba. Kamar ni yanzu ba komai ke ɓata min rai ba. Duk tunanina a kan yadda zan inganta kasuwancina ne. Kuma Alhamdulillah kullum gaba nake ci ba baya ba.

Assidiq dole na yaye shi da shekara daya, saboda ciki ya fito sosai, yana neman wata takwas. Na sha rigima sosai, ko in ce ina kan sha, don ma su Affan na hutu, suna janye min shi. Yau kam Murja na turawa kaya zuwa Ruma ta hanyar Bashir da ya shirya zuwa shi da yara wai weekend hatta Assidiq ba a bar min ba. Gidan shiru ba kowa, bayan duk na gama ayyukana,  na shiga  gidan Maman Aiman, a can na samu Maman Hisham, daya makociyar tawa, aiko  mu ka zauna hira, Sai 6pm na baro gidan ganin magriba ta yi. Ina isowa gida na yi alwala don yin sallahr magriba. Ina raka’ar karshe na ji cikina ya yi wani irin juyi, kamar an sanya hannu a juya shi da karfin tsiya. Kafin daga bisani na ji marata ta daure gam, dakyar na dago, ba zan iya cewa ga abin da na karanta atahiyar nan ba. Ni dai kawai na farka, na ganni kwance saman sallaya, kafin kuma in kara yin wani yunkuri wani ciwon ya kuma tashi. Wani zufa ya rika lullubeni, yayin da wani ruwa ke bin kafafuna, cikin 5mns na ji kukan jariri, ganin abun nake kamar mafarki, wai na haihu cikin 30mns.

Daga kwancen da nake na janyo wayata da ke saman gado, na kira Maman Aiman na ce ta zo na haihu. Yadda take dariya na san ba ta yarda ba, ga shi na rufe gate, babu yadda za ta iya shigowa ni kuma ban iya fita, saboda uwa ba ta biyo, ba ta kara gasgata na haihun ba, Sai da ta nemo namiji ya duro gidan ya bude mata kofa.

Mamakin haihuwar take yi ba kadan ba, Maman Hisham ta kira, suka gyara yaro da ni, da tsakar ɗakin, bayan an rage kazantar jikinta. Sai da komai ya zama normal sannan na kira Bashir na fada mishi cewa na haihu, na samu Baby boy. Shi din ma bai yarda ba, Sai da na tura mishi hoton Baby, haka na rika kiran mutane ina shaida musu na haihu. Ummata murna ba a magana, haka  Yusrah da su Badiyya kawayena.

Karfe biyu kam na safiyar Asabar Bashir na a gate din, tare ya taho da Jamila kanwarshi, yara tsalle, da murna sun yi kane, Maama kam fushi take yi, wai mace take so. Ni kaina macen na so, ina son in samu Ramla. Yarinyar na raina.

<< Hasashena 28

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×