Haka na rika amsar yan barka, musamman customers dina, Ana gobe suna yan Kano suka iso da yan Ruma, gida ya cika taf, musamman ranar suna, ban taba haihuwar da na tara mutane gami da samun abun arziki ba kamar haihuwar Aliyu Haidar. Tabbas ya zo min da goshi, Sai godiya kawai.
Raguna biyu Bashir ya yanka min, washegari aka suya hade da rabawa makota, da duk wanda yake da rabo, ranar lahadin gidan ya koma namu, saboda a ranar Jamila da Yusra kanwata suka tafi, yayin da Bashir ya dakko min wata yarinyar mace, za ta 45 years, sunanta Uwani, wai mijinta ne ya rasu, ya bar ta da yara hudu, ita ce ke taimaka min da aikin gida, za ta zo safe, ta tafi bayan magariba. Duk wata muke biyan ta.
Ina jin dadin zama da Uwani sosai, mace mai kawaici, mara kiwa ga tsabta da taka-tsan-tsan. Ga hak’uri da yara, ba ta da saurin hasala.
Har kayan siyarwa ta take dauka zuwa unguwarsu, idan ta siyar in sammata wani abu, aikin hada turare duk tare muke yi.
Yau ma da ya kasance Asabar Bashir tun safe ya tafi Ruma, wai za a yi mishi sharar gona. Gab magriba muna zaune a falo Uwani na zuzzuba turaruka a mazubi ni kuma ina ba Haidar nono mu ka ji horn din Shi. Kasancewar akwai yara a waje, shi ya sa ban damu da ta shi in bude mishi gate ba. Tare suka shigo da yaran, suna ta murna, Uwani ta fara tattare kayanta bayan ta yi mishi sannu da zuwa, shi kam sama ya hau da yaran shi, ni kuma sai da Uwani ta taya ni kintsa wurin, sannan na bi bayan shi.
Haidar ya fara dauka yana fadin “Zakina, yau ba kuka?” kamar ya ji abin da ya ce, ya wangale mishi baki
Bayan yaran sun fita ne na ce “Sannu da dawowa, ya hanya, ya ka baro su Inna”
“Duk suna lafiya Hajiyar kamshi (haka yake kirana idan yana jin Nishadi) duk suna gaishe ku”
“Muna amsawa mun gode”
Wanka ya shiga shaf-shaf ya fita zuwa masallaci shi da yara.
Sai da aka yi sallahr isha’i sannan suka dawo, aka hau dining, dukkanmu cikin Nishadi. Zuwa 10pm yaran sun yi bacci, daga ni sai shi da kuma Haidar wanda yake shirin na shi baccin. Shi kuma Bashir lissafin abin da gona za ta ci yake yi.
Bayan ya kammala rubuce-rubucen ne ya ce “Khadija an kai min kudi gidansu Saratu”
Jin maganar na yi wata kala, na rasa menene ma kai kudi yake nufi, shi ya sa na ce “Wane irin kudi?”
“kudin aure” ya ba ni amsa kai tsaye
Ilahirin jikina babu inda bai amshi wannan sakon ba, na rika kokarin danne shock din da na ji, dakyar na daidaita na ce “To Allah Ya tabbatar da alkairi”
“Amin” ya amsa hade da shiga wata sabgar ta shi.
Ni kuma na yi shiru, zuciyata na harbawa da sauri, na rasa a wane yanayi nake, a haka na kwantar da Haidar, ni ma na lallaba na kwanta, duk yadda na so in ba Bashir hadin kai wajen biyan bukatarshi sai na kasa, jikina sama baya responding stimuli din, hakan kuma bai dame shi ba, bukatarshi na biya ya hau bacci, ni kuma baccin ya kauracewa idanuna.
Na ɗauka tun da Sarai ce ba zan damu ba, yarinyar da na fi ta komai, kamata ya yi ace na godewa Allah za kawo min yar kauye mara wayewa, amma duk sai na ji na kasa aminta da ita din ta yi karama.
Har 2am idona biyu, gab asuba bacci ya dauke ni, shi ya sa har Baban Khalil ya dawo masallaci ban tashi ba, shi ne ya shiga kitchen ya fara dora abin break kafin ya dawo ya tashe ni.
Dakyar na iya yin sallah, bayan na idar na nufi kitchen kafin Haidar ya tashi. Koda ya tashin ma Bashir ya ci gaba da kula da shi, har na kammala break fast, na dauke shi na yi mishi wanka hade da ba shi nono.
Haka nan nake cin abincin ba don ina jin dadinshi ba, amma Sam babu test, ina tsaka da juya doyar da na gutsura a bakina kiran Saratu ya shigo wayarshi. Saboda da sunanta ya yi saving, ni kaina a baya can da Khadija ya yi saving lambata, Sai daga baya ne ya sanya Auntyn yara. Sosai sunan ke ban dariya, wai Auntyn yara, kamar wata yar aiki.
Bayan ya daga wayar ne ya ce “Lafiya kalau, Alhamdulillah”
Ban san me aka ce a wancan bangaren ba na ji ya ce “Ok, wata biyun ya yi daidai, Allah Ya nuna mana lokacin.”
Ya kara yin shiru kafin ya ce “Hakan ya yi miki, ba na son kananun maganganu”
Wani shirun ya kara yi kafin ya ce “To shi kenan, zan kara miki 50k a kai, kin ga ya zama 150k kenan”
Ya yi shirun kafin ya ce “Ok, Sai an jima”
Daga haka ya yanke wayar hade da kallo na yana fadin “Saratu ce, dama ana bayar da kudin lefe ne, maimakon a yi lefen?”
Wani abu ya tokare min kirji, dakyar na kawar da shi da fadin “Eh, idan haka amaryar ke ra’ayi”
“To ai ba na son kananun maganganu ne, ta ce a ba ta 100k,na kara mata 50k na hidimar biki hakan ai ya yi ko?”
Wani yawu na haɗiye dakyar kafin na ce “Eh ya yi sosai ma. Allah Ya kara budi”
“Amin.” ya amsa kafin ya dora da “An sanya bikin wata biyu, kin ga lokacin yara na cikin hutu ma”
Yanzu kam ban yi magana ba, ban san dalilinshi na yin hirar bikin shi da ni ba, da ya san yadda nake ji, da ya kyale ni.
“Yaran kin nan, ko wannensu zan ba shi 100k ki yi mishi siyayyar cin biki” ya dora daga inda ya tsaya
“Sun gode sosai, Allah Ya kai mu lokacin”
“Amin” ya amsa kafin ya ce ke kuma “500k za su ishe ki ko?”
Mamakin yadda yake ta lissafin nake yi, ko a jikinshi sai raba kudi yake yi, wai shi zai yi aure. A, sanyaye na ce “Za su ishe ni. Allah Ya saka da alkairi” kai karshen maganar tawa ya yi daidai da shigowar alert din 1million. Ya kuma cewa “Idan ba su isa ba, Sai ki sanar min”
“To” na kuma cewa, shi kuma ya mike yana fadin “Bari in shirya zuwa kasuwa, akwai wasu kaya da za a kawo min daga wani kauye”
Komai ban ce ba, shi kuma ya haura sama, na dade zaune a wurin ba tare da na san abun yi ba. Har sai da na ji takunshi alamun yana sakkowa, sannan na fara tattara kayan kan dining, da shi ke yara sun tafi Islamiya.
Yau kam ko rakiya gate din bai samu ba, yana fita kuma Uwani ta zo, ragowar break fast din na ba ta. Ta ci wanda za ta ci ta ajiye wanda za ta ajiye.
Tare muka gyara gidan tsaf, sannan muka dora a kan aikin jiya na zuzzuba turarurruka.
Muna aikin ne ta ce “Auntynmu yau kam ba kya jin dadi ko?”
Kai na cira a hankali ina kallon ta kafin na ce “Me kika gani?”
“Na ga kin yi shiru ne”
Yaƙe na yi kafin na ce “Kaina ne ke dan ciwo”
“Haba koda na ji, ai shirun naki ya yi yawa. To ki je ki huta ki bar min aikin na karasa”
“Zan iya kar ki damu” na yi maganar a kokarina na danne damuwata.
Haka mu ka yi ta hidimar gidan har yara suka dawo. Bashir kam sai 8:pm ya dawo.
Abu kamar wasa, ba na iya bacci, idan na samu na yi baccin da wuri, can dare sai in farka, kuma ban kara komawa, wani lokacin kuma sai can gab asuba baccin ke dauka ta, abinci ba na jin dadin shi, cikin sati na fara zubewa, yar ƙibar da na yi ta fara bin iska.
Ga shi na kasa fadawa kowa a ƴan’uwana wai Bashir zai yi aure, hatta Ummata ban fadamawa ba. Ni kawai nake dakon abun a zuciyata. Shi ya sa kila nake ta karewa kamar kudin guzuri. Wani lokaci har jiri nake ji. Yadda zan bude bakin in fadi cewa Bashir zai yi aure ne damuwata, Sam ba ni da courage din
Yau kam da yamma Uwani na tura kasuwa siyayyar kayan hadin turare, yayin da ni kuma nake zaune a gida ina lissafin kudin kayan da za a kawo min, kasancewar an yi salary duk an biya kudina.
A haka Maman Aiman ta shigo ta same ni.
Bayan mun gaisa ne na ce “Waye ya bude miki kofa?”
“Lawal ne, da yake ban ruwan fulawa. Na ga gwaibarku har ta fara haihuwa”
Ban dago daga rubutun da nake yi ba na ce “Ai tana samun kulawa, kullum Lawal sai ya ba ta ruwa safe da yamma”
“Ai kam tana ta kyau, matar gidan kuma na ta lalacewa”
Da sauri na dago kai ina kallon ta alamun mamakin maganarta kafin na ce “Ban gane ba”
“Ai ba za ki gane ba, amma wannan ramar ta ki, ta fi karfin karayar tsotso Maman Maama.”
Idanuna na lumshe, yayin da nake jin wani zafi a kirjina, komai ban ce ba, na duka hade da ci gaba da rubutuna.
“Barin kashi a ciki baya maganin yunwa, ba ki sani ba, ko ina da maganin matsalarki”
Daga duken da nake na ce “Ba ki da ita”
“Me ya sa?”
“Saboda haka ne Maman Aiman, ni kaina ban son damuwar da nake yi, saboda bai kamata ace na damu har haka ba, amma na kasa.”
Komai ba ta ce min ba, ni ce na ce mata “Abbansu Khalil ne zai yi aure, ina jin idan Asabar din ta zo saura sati biyar”
Cikin kwalo ido ta ce “Aure!”
“Yadda kika ji”
“Tabbb!” ta ce hade riƙe baki, ba tare da ta ce komai ba.
Ni ce na kuma cewa “Tun ina Ruma suke tare da yarinyar, bazawara ce, mijinta ya rasu, Sai kin ganta, ina jin ko sunanta ba ta iya rubutawa ba.”
“Ki ce min masu wahalar kishi?”
Cike da faduwar gaba na ce “Me ya sa kika ce haka?”
Ta ce “Raba kanki da kishi da jahilar mace, na yi ban ji da dadi ba wlh. Su da asiri suke takama, kishi da asiri kuma Sam bai yi ba”
Gabana ya ci gaba da faduwa ras! Ras!! Ras!!! Kafin in ce wani abu ta dora da “Tun ba ƴan kauyen nan ba, sun san kusfa-kusfa inda Malamai suke, wlh ki yi ta addu’a”
Cike da sanyin jiki na ce “Haba Maman Aiman, kin tsorata ni fa”
“Gaskiya na fada miki ba zuga ba, kin san an ce ruwan da ya dakeka shi ne ruwa, ki tambayi mutanen unguwar, wlh da muka kwaso kokawa daga cikin gida har wajen gate. Duk shuruna, Sai da matar nan ta koya min bala’i”
Yanzu kam dariyar karfin hali na yi ina fadin “Kai Maman Aiman. Kokawa kuma”
“Yasin kuwa haushi ta ba ni. Amma ki kwantar da hankalinki wlh ki daina saka damuwa, kishiya ba ta da wuta ba ta da aljanna. Iyakaci idan ta ce zaman lafiya kuyi, idan ta ce tashin hankali ku fara daga nan har birnin Sin”
Wata dariyar na kuma yi, ko ba komai sai na ji wani kaso na damuwata ya ragu, duk da ba maganin abun Maman Aiman ta yi min ba.
Har Uwani ta dawo hirar kishiya muke yi, irin zaman da ta yi da tata, ni ma ina fada mata irin zaman da na yi da Maman Khalil, zama mai dadi da tsafta.