Tare mu ka yi aikin abincin rana da Bashir, don a, harkar kitchen kam Bashir Oga ne, ko mace sai haka, karfe hudu ya fita da yaran, wai zai kai su gidan ƴan'uwansu ta, bangaren shi, da kuma bangaren mamarsu.
Gidan ya yi shiru har hudu da rabi, lokacin da na ji ana buga min kofa na dauka Maman Hana ce, saboda ita kawai nake jira, sosai nake son matar, Sai dai kicibis na yi da Maman Aiman a lokacin da na bude kofar, murmushi ta yi tana fadin "Ina fatan ban katse miki jin dadi ba"
Ni ma. . .