Skip to content
Part 33 of 34 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bayan na ba shi nono,  aka kira min mai kwalliya, ta dan kara gyara min kwalliya, na dora wani farin lace mai golden a jiki, haka ta yi min dauri mai kyau. Ni kaina na san na yi kyau. Haidar kuma na canja mishi kaya zuwa yan kanti masu kyau irin wanda Assidiq da Khalil suka sanya. Shi ma Affan irin su ya sanya bayan ya gama cin abincin. Na dauki lace din Maama na  sauka zuwa kasa, don in canja mata.

Lokacin da na sauka filin tsakar gidan ya kara cika, dangin  amarya ma sun bi layin yan kallo.

Tun da Mc din nan ya hango ni, aka canja waka zuwa “Uwargida ran gida…”

Ai ni da kaina sai na ji takuna ya canja, kamar wata sarauniya ta gaske, tun daga wurin kuma kawaye da abokan arziki suke zuba min kudi har cikin fili, ana ta rafka guda.

Takun rawa nake na kasaita ana dauka ta video ga kudade ana ta zuba min. Dangin amarya sai kallo da rike haba, ana gulma….

Daga lokacin da Bashir ya fada min ya kai kudin aure, ban taba jin wata rana da na yi nishadi da farin ciki kamar wannan ranar ba. Jin zuciyata nake wasai kamar an yi min sharar bakin ciki.

Shi ya sa da dare na sha bacci sosai, dama ga gajiya, dakyar na tashi da asuba, na yi sallah muka shiga hidimar abun kari, su Affan na fara sallama, saboda Babansu ya ce su tafi Islamiya, ai an gama biki.

Sauran mutane kuma zuwa karfe tara mun sallami kowa da abun kari.

Zuwa shadaya kuma baƙi duk sun fara watsewa, musamman dangin Bashir da ƴan’uwan Sakeena wadanda suka yi mana kara.

Wadanda suka rage daga Samira, Badiyya, Yusrah, Goggo Saude, Aunty Na’ima da Maryam. Su kuma duk a bangarena suke. Sai Murja da ba ta bi 6an Ruma ba, saboda za ta shiga cikin gari.

Ina zaune a falo bayan na yi kintsa kaina cikin atamfa doguwar riga da ta sha stone work Ina ba Haidar cerelac Murja ta shigo.

Bayan ta zauna ne ta ce “Uwargida ana can an fama da amaryarki, ta zo ku gaisa ta ki”

Baki na tabe ba tare da na ce komai ba, saboda ni ban san irin wannan sabuwar tsirfar da take yi ba. Matar da take zuwa har dakina, amma yanzu ta zo da sabuwar gulma.

Ni dai ta kan maganar ma ban sake bi ba, su Yusrah ne ke ta tattauna maganar.

Misalin sha daya su Samira suna shirin tafiya dangin amaryar suka shigo, amma babu amaryar.

Tun da suka shigo idanunsu a ko wace kusurwa ta dakina, tun jiya suke zuwa min kallon kurillar daki suna kus-kus. Yanzu din ma muna gaisawa suna karewa dakin kallo, a haka mu ka yi sallama, suka tafi, ni ma na saka hijab di ta don yi wa su Yusrah rakiya zuwa tasha.

Ban baro tashar ba sai da naga motarsu ta tashi, shi ya sa ban dawo gidan ba sai sha biyu saura.

Da yake na bar Uwani ban damu ba,  na san za ta yi  komai kafin in dawo.

Lokacin da na dawo  har ta sauke farar shinkafa, saura miya.

Shi ya sa ina sauke Haidar, ban huta ba, na shiga kitchen. Don taya ta sauran ayyukan.

Har muka gama komai Uwani ta kai mata abinci ban ji motsin ta ba, kuma ban lekata ba, saboda tun da aka kawo ta, kafata ba ta taka ko entrance dinta ba. Ni da ita zan ga wanda ya taras da wani.

Around 2 mun gama komai ni da Uwani, dalilin da ya sanya ni kwanciya in gwada sa a ta ko bacci zai dauke ni. Cikin ikon Allah kam baccin ya yi awon gaba da ni. Sai hudu da mintuna karar wayata ta tashe ni, Yusrah ce ke fada min sun sauka Kano lafiya, bayan mun gaisa da Umma tana kara jaddada min in yi hak’uri da kawar da kai, Sai kuma na kira su Samira, su kuma suka tabbatar min suna Zaria. Daga nan toilet na shiga, wanka na yi hade da alwala, na yi sallahr la’asar, kafin na shirya cikin atamfa dinkin riga da siket, sosai dinkin ya zauna jikina. Haidar ma da ya tashi a bacci na kintsa cikin kaya mara nauyi, sannan na sakko kasa.

Uwani zaune tana kallo, gani na ya sanya ta rissinawa ta ce “Sannu da sakkowa Auntynmu”

Na amsa fuska a sake, bayan na zauna ne, ta zube min cinikin turaren da aka yi, da kuma wadanda suka kawo biyan bashi.

Bayan ta gama min bayanin ne na ce “Abban yaran nan bai shigo ba?”

“Ya shigo, na ce kina bacci, Sai ya wuce sashen amarya.”

Kai na jinjina alamar fahimta, kafin na ce “Sai an yi abincin dare ne?”

Cikin kwantar da kai ta ce “Haka ya kamata Auntynmu, kin san ba mu kadai ba ne”

Kan na kuma jinjinawa kafin na ce “To a wanke shinkafa, Sai a yi tuwo miyar shuwaka, akwai sauran wacce kika sawo ranar can a kasuwa.”

Kai karshen maganar tawa ya yi daidai da mikewarta.

Bayan fitarta, na bi bayanta, kasancewar muna da kitchen a waje, kuma shi ne general kitchen na kowa da kowa.

Tare muke aikin har yara suka dawo school, daga nan ne na sakar mata, na koma kan yarana.

Har zuwa lokacin ban ga keyar Bashir ba, abun gwanin mamaki, koda yaran ma suka dawo bai zo wajensu ba. Ni ma kuma na hana su zuwa wajen shi, musamman da basu tambaye ni shi ba.

Sai da suka tafi masallaci ne Uwani ta dauki abincin daren Sarai don kai mata, haka ta kawo foodflask din abincin rana, cokali ba a wanke ba.

Bayan sallahr magriba Uwani ta tafi, ina kan sallaya bayan na idar da sallahr isha’i su Khalil suka dawo, wannan ya sa na sakko kasa, don zuba musu abinci, suna cin abincin ne Bashir ya shigo, sanye da jallabiya coffee color, kamshi na bin shi.

Yaran suka gaishe shi, ni ma na gaishe shi ba yabo ba fallasa. Don wani irin haushinshi nake ji.

“Dazu na shigo kina barci” kai na daga alamar eh

Ya ce “Ya hidima da baƙi?”

“An gode Allah.” na ba shi amsa

“To sannu da kokari, na gode sosai, Allah Ya saka miki da alkairi”

“Amin” na amsa.

Ya dan yi shiru kafin ya ce “An kai wa Nana Saratu abinci ko?”

A zuciyata nake mamakin sabon sunan “Wai Nana Saratu”

“Eh an kai mata, ban san ko kuna bukatar wani abu ba.”

“A’a ba komai. Amma ki yi hak’uri za ki ci gaba da dafa abincin har kwanakinta na amarci su fita”

Kai kawai na daga alamar fahimta, saboda abin da nake ji a zuciyata mara dadi ba zai bar ni in yi magana ba. Ba na son yin kuka, gani nake Saratu ba ta kai matsayin da hawayena za su zubo saboda ita ba.

Shiru ya ratsa falon kafin ya katse shirun da “Kuna bukatar wani abu ne?”

Kai na girgiza alamar a’a

Muka kuma yin shiru, so yake ya tashi, kila ya rasa yadda zai yi, wannan ya sa ni na mike sabe da Haidar na yi hanyar upstairs ba tare da na ce komai ba.

Wannan ya ba shi damar barin falon.

A bedroom su Khalil suka taras da ni, Affan ne ya bata fuska sosai kafin ya ce “Auntynmu wai Abbanmu ba a nan zai kwana ba?”

Laluben amsar da zan ba shi nake yi, amma na kasa, shi din yana aji daya a secondary, ya ɗan san wani abu gami da zamantakewar aure, wani abun kuma bai sani ba. Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce “A’a zai dawo zuwa an jima” reaction din shi ya nuna min bai gasgata ni ba, ni ma sai na kori maganar ta hanyar tambayar ba a basu Assignment ba.

Khalil dai ya ce tun a makaranta ya yi, shi ko gogan komai bai ce ba. Dalilin da ya sa na ce su je su kwanta.

Bayan fitarsu na yi shirin bacci, Sai dai tun da na kwanta idona ya ce bai san zancen ba, na dauka ko don na yi bacci da rana ne, amma abu har karfe biyun dare babu bacci. negative imagination nake yi a kan Bashir.

Jin zuciyata na neman fashewa ya sanya ni shiga toilet na dauro alwala. Raka’a biyu na yi, kafin na daga hannu sama ina rokon ubangijin sammai da kassai ya yaye min abin da nake ji. Lallai kishi ciwo ne mai girma. Sakeena ta yi kokari, ba abu ne mai sauki ga macen da aka fara aure ba, ace an karo mata wata. Gara ma amarya ita dama bakuwa ce. Yau kam Hasashen da nake yi a kan ina ma ni ce aka fara aure, kafin aka auro Sakeena, shi ma na janye shi, farkon da ta biyun duk na dandana babu dadi.

Na dire hannayena kasa ina furta “Wayyyo Allahna!” a hankali. Hawayen da nake dannewa na shiga lalubowa ko za su zubo in ji dadi amma fir na neme su na rasa. Haka na Duke kan sallayar tsawon lokaci zuciyata na kuna. Na rasa da me zan ji, da sabuwar gulmar Sarai, koda yadda Bashir ke rawar kafa a kanta. Yadda yake shigewa ɗakinta ya yi shiru kamar an aiki loma zagayar wuya, ba karamin daci yake min ba.

Numfashi na sauke mai nauyi, kafin na mike dakyar, jiki ba ƙwari na goya Haidar, sannan na saba Maama a kafadata, dama Assidiq yana dakin su Affan.

A hankali nake sauka kan stairs din kamar Ina tsoron aji karar takuna, ban yi tsammanin samun kofar a bude ba, Sai dai ina murza handle din na ga ta bude, wanda ya yi daidai da tashin Affan zaune. Kasancewar akwai fitila amma mara haske, hakan ya sa ya gane ni. A hankali ya ce “Auntynmu, lafiya?”

Maama na fara kwantarwa saman gadon, kafin na kwanto Haidar shi ma na kwantar. A hankali na ce “Koma can wurin Khalil ka kwanta ka bar mana wannan gadon”

Komai bai ce ba ya koma wurin Khalil din ya kwanta. Ni ma kwanciyar na yi bakina dauke da addu’ar Allah Ya sa bacci ya dauke ni.

Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauke ni, wanda ya sanya ko kiran sallah ma ban ji ba, sama-sama dai na ji su Khalil na shirin zuwa masallaci, daga nan kuma ban kara sanin komai ba, Sai jin muryar Bashir na yi yana fadin “Khadija, a nan kika kwana?”

Idanuna na bude masu cike da bacci na dora kanshi, Sai kuma na mayar da su na rufe a hankali. Ban bude ba sai da na ji ya zauna kusa da ni, kafin na kuma bude su a hankali na dora a kan su Affan da suka yi tsaye suna kallon mu, dalilin da ya sanya ni mikewa dakyar na shige toilet din su.

Lokacin da na fito duk basu nan, har su Assidiq da Maama, Sai Haidar da yake bacci da kuma Bashir da ke zaune a inda na bar shi.

Bayan na idar da sallah, azkhar da na karatun kur’anin da nake yi kullum na ce mishi “Ina kwana?”

“Lafiya kalau, fatan kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah” na amsa shi, hade da mikewa zuwa kitchen.

Ganin ruwan zafi a akan electric da kuma a kettle ya tabbatar min ya shigo kitchen din.

Doya na dakko na shiga ferewa, ita ce ma fi sauki da zan dafa saboda yan makaranta, ga shi kuma na makara.

Ban jima da fara fere doyar ba ya shigo,  ya sanyawa kofar key, sannan ya kwanto bayana, wuyanshi a kan kafadata, yayin da ya zagayo da hannayenshi kan cikina, a takaice dai ya rungume ni ta baya. Kamshin turarenshi ya rika ratsa kofofin hancina.

Dole na dakata da yanka doyar da nake yi. Wukar ya zare daga hannuna hade aje ta gefe guda. Cikin kunnena ya ce “I’m sorry Khadija, I’m sorry please, I don’t mean to hot you. Na san halin ki da kishi. Don Allah ki yi hak’uri, dan lokaci kadan ne, zai wuce ki ji kamar ba a yi ba”

Hawayen da na so fitar su jiya ba su fito ba sai yanzu suka zubo shar zuwa kan hannayenshi da suke saman cikina.

Kanshi ya kara kwantarwa sosai saman kafadata ya ce “Ina sonki, so ba na wasa ba. Khadija a yanzu ba na jin akwai macen da za ta kai ki kima a wajena. Rikon marayun yarana kadai ya isa ki yi ma ko wace mace fintinkau, amma Saratu kaddarata ce, don Allah ki karba hannu bibbiyu ki yi hak’uri. Na san ba ki mori komai a zaman aure ba, tun farko na hada ki da kishiya, tun ba ki so dole kika so ta da yaranta. Bayan nan kika koma zaman jinya da raino, lokacin da ya kamata ace kin dan mori rayuwar auran kuma na kara hada ki da wata. Don Allah ki dauka ibada kike yi. Please Khadija ki zama kamar Sakeena don Allah, ki samar min da kwanciyar hankali a gidana. Kin fi Saratu komai, shekaru, ilmi, wayewa da kuma hankali, don Allah kar ki bari a samu bara ka ta wajen ki. Please Khadija na roke ki”ya kai karshen maganar hade da birkito ni ina fuskantar shi. Sosai ya rungume ni hade da bubbuga bayana, kafin daga bisani ya hau kissing dina ta Ko ina yama fadin “I love you” har na fara ganin kamar ya zare.

Dalilin da ya sanya ni ture shi da karfi, na juya ina neman inda ya jefar min da wukar da ya amshe a hannuna. Har zuwa lokacin hawaye ne ke wanke min fuska. Sosai zubar hawayen ke min dadi, ina jin kamar ina zubar da dukkan damuwata ne.

Kara kwantowa ya yi jikina a hankali ya ce “Kin san idan kina fushi na fi bukatar ki, ko ki sauke fushin nan, ko kuma komai ya faru a kitchen din”

Ni dai komai ban ce ba, har zuwa lokacin kuma hawaye na saukar min.

Ganin ya amshe wukar hannuna ya sa na duke a wurin na ci gaba da kuka mai sauti, shi din ma dukawa ya yi hade da rungumoni, ganin da gaske nema yake ya yi abin da yake so din, ya sanya ni yin amfani da karfina, na kwace jikina, kafin kuma ya yunkura har na bude kofar kitchen din na fita da gudu.

Daidai Khalil na fitowa dakinsu sanye cikin uniform, yadda na fito din ne ya sanya shi fadin “Auntynmu lafiya, ko kin kone ne?” a rude yake tambayar

Komai ban ce mishi ba, na haura saman da sauri, shi kuma ya nufi kitchen din.

<< Hasashena 31Hasashena 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×