A dakin na tarar da Affan yana shirya Maama, wannan ya sa na wuce toilet. Saman toilet din na zauna ina sharce hawayena, duk yadda na so in tsayar dasu abun ya gagara. Ban san ko minti nawa na kwashe a cikin toilet din ba, kafin na fito. Gefen gado na zauna shiru, ba na ce ga abin da nake tunani ba, amma zuciyata babu dadi.
Ina zaune a wurin Khalil ya shigo ya ce min za su tafi makaranta.
Bayanshi na bi zuwa kasa, duk sun yi break, amma bread da kwai.
Sai da naga tafiyarsu sannan na dawo ciki, inda Bashir ya shirya abincin break din Saratu ya kai mata.
Tea kawai na iya sha, zuciyata Sam babu dadi, Sai da Uwani ta zo ne na dan ji sauki, musamman yadda Bashir bai fita aiki ba, ba karamin kara min damuwa ya yi ba. Na yi ta sake-sake marasa kyau.
Haka muka gama abincin rana Uwani ta kai mata, ta kwaso kaya break ko spoon ba a wanke ba, da aka kai na dare ma, haka aka kwaso na ranar ba a wanke ba.
Ban taba gajiya ba, ko ina so, ko ba na so, haka nake abinci sau uku in ba ta a rana, sannan kafarta ba ta taba ta kawo sashena ba, ni ma kuma ban taba lekawa nata sashen ba. Haka ma yara.
Ranar da muka cika kwana uku, ne na zuba ido in ga Ikon Allah, in ga abin da zai faru.
Misalin karfe takwas na dare, muke zaune da yarana cikin falo, ni dai sanye nake da doguwar rigar robber material, blue Mai yankakken hannu. Affan sanye da boxer da ya ɗan wuce gwiwa, Sai vest yayin da ya goya Haidar a baya, saboda ya hana Khalil ya yi wa Maama homework.
Khalil ma sanye yake da irin kayan jikin Affan, hannunshi rike da hannun Maama da ke tracing a littafin writing din ta. Assidiq kam kwance yake yana kallon cartoon, ni kuma hankalina a kan wayata yake. Kwankwasa kofar da aka yi ne, ya sanya Affan budewa, Bashir da Saratu suka bayyana.
Lokacin da kwayar idanuna suka shiga cikin tata, Sai da gabana ya yi wata mummunar faduwa, na lumshe idanuna tare da furta “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un, La’ila Ha Illah Anta Subhanaka Inni Kuntu minazzalumin” idanun na bude hade da amsa sallamarsu. Shi da ita a kan 2 sitter suka zauna. Ina kallon yadda take bin ko wacce kusurwa ta dakina da kallo.
Affan da ya hade fuska kamar bai taba dariya ba ya kalli Bashir, da kyar ya ce “Good Afternoon Dad?”
Ba na jin ya jira amsawarshi ya yi hanyar upstairs. Khalil MA Sai ya bi bayan shi, bayan ya gaishe shi.
Falon dai ya koma daga ni sai su. A hankali na kalli Bashir na ce “Ina wuni?”
Ya amsa min, lokaci daya kuma yana zungurin Saratu alamun ta gaishe ni. Ni dai na ɗaukarwa kaina, idan har ba ta gaishe ni ba, ni kuma ba zan gaishe ta ba.
Bayan ta gama shan kamshinta ta ce min “Ina wuni?”
Ni ma sai da na sha nawa kamshin kafin na ce “Lafiya” Daga nan komai ban kara cewa ba. Na Ci gaba da danna wayata.
Shi ne ya ce “Mun zo yi miki godiya ne bisa dawainiya damu na kwanaki uku, Allah Ya saka miki da alkairi”
Sai da na dan murmusa kafin na ce “Amin”
“Sai abu na gaba, yau Saratu ta fita daga kwanakinta na aiki, kenan zama zai koma normal yadda kuka tsara. Shi ya sa nake son in ji ya kuke son abun ya kasance?”
Duk mu ka yi shiru, jin shirun ta yi yawa ne ya sa na ce “Ni ba ni da matsala, duk yadda aka tsara hakan ya yi”
Ya juya kan Saratu ya ce “To ke kin ji, ya kike ganin abun zai kasance?”
Sai da ta tura baki kafin ta ce “Ni dai kowa ya yi girkinshi, ba zan iya girkin mutane har bakwai ba”
Ban san lokacin da na dago kai ina kallon ta cike da mamaki ba, a zuciyata na ce “Farawa da iyawa”
Da alama maganar ta zo wa Bashir a bazata, don shiru ya yi, kamar ba zai kara magana ba, Sai kuma ya ce “To ya za a yi kenan, za ki rika girkin a kitchen din part dinki ne?”
“Ga kitchen a waje na kowa da kowa. Duk mai girki ita ke da iko da kitchen, Sai ta gama abin da take yi, wacce ba ta da girki ta shigo”
Ni dai baki bude nake sauraron wannan Ikon Allah, wannan yarinyar ya aka yi duk ta san wannan, anya kuwa ba wani ne yake ɗorata a hanya ba.
Tun kafin Bashir ya ce wani abu na yi saurin fadin “Ma Sha Allah, hakan ma ya yi”
Ni nan bangaren ba ni da matsala, ko cewa ta yi wanda ba shi da girki ba zai shiga kitchen ba. Kitchen dina na ciki babu kayan aikin da babu, komai ina da shi. To me ye damuwata.
Shiru ya ratsa falon, ganin kamar babu mai abun fada, kawai na mike zuwa sama ina fadin “Mu kwan lafiya”
Bayan na zauna saman gado ne na ce “Affan me ya sa ba kwa gaishe da Auntynku?”
Baki bude alamun mamaki Khalil ya ce “Wacece Auntyn tamu? Don Allah Auntynmu ki bari, ni ba ruwana da ita.”
Affan ma ya yi caraf ya ce “Ni ma babu ruwana da ita. Ko za ta shekara dubu a gidan nan ba zan yi mata magana ba”
A hankali na sauke numfashi kafin na ce “Babu ruwana, don Allah kar ku daura min jakar tsaba ku hada ni da kaji. Babanku zai yi fada. Kuma mutane za su ga kamar ni na sanya kuke mata rashin kunya”
“Rashin kunya kuma! Mu da ba mu yi mata magana wace rashin kunya kuma” cewar Khalil idanunshi a kaina.
Shigowar Abbansu ya sanya ban ba Khalil amsa ba.
Bayan duk sun fita dakin ne ya ce “Khadija yaran nan kamar suna fushi da ni, musamman Affan, idan ya ganni sai ya hade fuska, ko ba ki lura ba”
Kai na girgiza alamar a’a kafin na dora da “Kana man ce Affan ne, amma ai shi haka yake, wani lokaci ka gan shi kamar mai jinnu”
“To Khalil fa?” ya kuma tambaya
“Khalil kuma yallaboi, na ga ko dazu kun gaisa ai, kuma ranar can da safe ma tare kuka hada break fast”
Shiru ya yi kafin ya ce “Just you’re barking them Khadija, don Allah kada ki yi involving yaran nan a cikin zamantakewarmu”
Kamar ba zan tanka ba, Sai kuma na ce “In Sha Allah”
Aje duk wani kishi na yi a gefe, na karbi mijina sosai, shi kanshi na san ya yi mamakin yadda ba tarbe shi. Da safe tare muka shiga kitchen kuka hada breakfast. Ita kam Amarya ba ta leko ba, kuma na daukar wa raina, na gama kai mata abinci, ba dai ta ce ba za ta iya dafa mana abinci ba, muma ba za mu iya dafa mata ba.
Idon Bashir na faka, na turawa mai adaidaitan da ke kai su Khalil makaranta sakon ba sai ya zo da safe ba, Babansu zai kai su.
Yaran na break na ce “Abbanmu yau fa kai za ka kai su Affan school, mai kekensu ba zai samu zuwa ba, mashin din ya lalace”
“Subhnallah! Sai su matsa kar su makara”
Jin haka ya sa na haye sama, na canja kaya zuwa doguwar riga mara nauyi sosai, na nade kaina da veil din, Haidar ma na canja mishi kaya haka Assidiq.
Time da na sakko har sun gama break din, shi ne ya kalle ni kafin ya ce “Ina za ki je” kai na langabe kafin na ce “Ni ma zan raka su ne”
Kallona kawai yake yi, wannan ya sa na mayar da kallo na kan yaran na ce “Ko ba ku so in raka ku”
“Muna so wlh” suka hada baki a tare.
Baki Bashir ya tabe kafin ya ce “in ya so ma ki zauna a can har sai an tashi kin dawo” ya yi maganar hade da daukar key din motarshi da ke kan center table
Muka rufa mishi baya muna dariya.
Burina kawai shi ne Sarai ta son ina da kusanci da mijina, kuma zuwan ta bai hana mu farin ciki ba. Na dauri ɗamarar zama kamar Sakeena, wajen danne damuwata da boye bacin raina a gaban makiyaya.
Time da muka dawo daga kai yara makaranta Uwani ta zo. Har ta share tsakar gida ta ba fulawoyi ruwa.
Cikin girmamawa ta gaishe mu, kafin ta juya wurin aikinta, ni kuma sai da na salami Bashir zuwa wurin aiki kafin na zauna break. Kuma sai a lokacin ne ya leka dakin Saratu. Sai na ji ni kamar wata Sakeena yau, ni ma na rike miji da hidimomina, ashe haka abun yake ban sani ba. Sai kawai na ji ni ina murmushi.
Bayan Uwani ta yi breakfast, kan entrance muka dawo, domin hada turaren wuta, na kamshi, humra da kuma roofreshener, aikin da ya dauke mu har 12pm. Kuma har zuwa lokacin Saratu ba ta fito ba, sosai abun ya ba ni mamaki, ni dai ban kai mata abinci ba, kuma ban ga Bashir ya sawo mata ba. Na fita batunta muka shiga hidimar girkin rana.
Sai dai misalin karfe 1pm sai ga Bashir da take away, kai tsaye kuma ya wuce bangarenta, after like 20mins ya fito, a kitchen ya same mu ya ce an gama abincin rana, na ce yana hanya dai, daga haka ya wuce abin sa, wai ya koma wurin aiki.
Sosai takeaway din Nan ya taɓa min zuciya, kun san kishi dai, bare ni mai nawa a kusa. Sai dai haka na danne ban tanka ba.
Abu kamar wasa, har na fita girki Sarai ba ta taba ko shiga kitchen din ba, bare ta dora abinci, take away ake yi mata.
Na zuba ido in ga Ikon Allah tun da girki ya dawo kanta.
Da dare Bashir ya koma ɗakinta, haka na rarrashi kaina dakyar na yi bacci. Karfe hudun asuba alert dina ya tashe ni, alwala na yi, hade da yin sallah raka’a biyu, bayan na idar na yi lazumi hade da karatun alkur’ani, ban tashi ba dai sai da na yi sallahr asuba na nufi kitchen.
Abun mamaki a rufe gam, tun ina tunanin datsewa ya yi har na fahimci an rufe kitchen din ta waje ne. Ga shi ba ni da extra key, haka na koma kitchen dina na ciki na yi tsaye, babu wani abu da zan sarrafa a ci, komai yana kitchen din waje.
Fadin takaici da bacin ran da na ji bata lokaci ne, musamman da na ga rana ta fito, ga yara har sun gama shirin makaranta. Khalil ne ya ce “Auntynmu ko mu je mu yi wa Abbanmu magana ya bamu wani key din?”
“Kyale shi kawai Khalil, dakko min jakar da nake ajiye kudi, ku sawo bread da kwai, da mai, Sai kuma Maggi.”
Na yi maganar zuciyata babu dadi.
Affan ne ya dakko jakar, ya ciri kudi, suka tafi tare da Khalil. Basu jima ba suka dawo, don haka na soya musu kwan, suka hada da bread suka karya, ni dai ɓacin rai hanani cin komai ya yi. Juice kawai da biscuits suka tafi da shi school, Sai na hada musu da kudi, koda ba a kawo musu abincin rana ba.
Haka na zauna zuciyata na ta min daci, gyaran dakin ma na kasa, Sai da Uwani ta zo, ta gyara ko ina.
Sai 10am Bashir ya fito cikin shirin fita aiki, lokacin ina sama, ina ta aikin lallashin zuciyata.
Sanye yake cikin royal blue din yadi da aka yi wa ɗinkin zamani. Sosai ya yi kyau, jikin lukui bai boye jin dadin da yake samu ba.
Daga kwancen da nake na ce “Ina kwana?”
Ya amsa min, lokaci daya yana zama kusa da ni, hannuna ya saka cikin na shi kafin ya ce “I’m sorry, na so leko ki da Asuba, Sai Nana ta tashi da ciwon ciki”
Ba tare da na kalle shi ba, na ce “ba komai”
“Me kika dafa da safen?”
Kamar in fada mishi abin da ke min zafi sai kuma na fasa na ce “Ban yi da yawa ba, ni ma da ciwon kai na tashi”
Hannunshi ya kai saman goshina kafin ya ce “Kodai ba ki yi bacci ba?”
Karon farko da na kalle shi muka hada ido na ce “Me zai hana ni bacci?”
Maganar ya kawar da fadin “Zan tafi aiki, akwai abin da kuke bukata ne?”
Kai na girgiza alamar a’a
Ya mike daga zaunen da yake lokaci daya yana daukar Haidar da yake wasa, ya ce “My lion, za a yi min rakiya?”
Ni dai yi na yi kamar ba na jin su.
Ya gama surutanshi ya aje min Haidar din ya fita.
Misalin 11am na sakko kasa, Uwani zaune tana kallo a falo. Ganina ya sa ta gyara zamanta hade da kara gaishe ni. Kafin ta ce “Dama Ina ta addu’ar Allah Ya sa ku tashi da wuri, na ji kitchen a rufe”
Sai da na zauna saman kujera, sannan na ce “Je ki wurin Amarya ki amso mana key din”
Komai ba ta ce ba, ta mike, yayin da ni kuma na zauna zaman jiran dawowarta.
Ko minti biyu lafiyayyu ba ta hada ba, ta dawo min da amsar wai ta ce ita ce da kitchen yau.
Wani kullutu, da wani mulmulallan baƙin ciki, suka taso min zuwa zuciyata suka dunkule wuri daya, wannan ya sa na shiga kokawa da su,. Tsabar ɓacin rai bishi-bishi ma nake ganin Uwani.