Bayan na ba shi nono, aka kira min mai kwalliya, ta dan kara gyara min kwalliya, na dora wani farin lace mai golden a jiki, haka ta yi min dauri mai kyau. Ni kaina na san na yi kyau. Haidar kuma na canja mishi kaya zuwa yan kanti masu kyau irin wanda Assidiq da Khalil suka sanya. Shi ma Affan irin su ya sanya bayan ya gama cin abincin. Na dauki lace din Maama na sauka zuwa kasa, don in canja mata.
Lokacin da na sauka filin tsakar gidan ya kara cika, dangin amarya ma sun bi. . .