Skip to content
Part 35 of 36 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ban san ko sau nawa na yi attempting kiran Bashir ko tura mishi sako a kan lamarin ina gogewa ba.

Karshe dai  na ba Uwani kudi na lissafa mata abun da nake so ta siyo min, da zai mana kwana biyu.

Sosai nake mamakin lamarin Sarai, a ina ta san wannan rashin mutunci? Kar dai  yar kauyen da nake raina wa ta  dora min ciwon zuciya, saboda tun yanzu na fara jin gara min kishi da Maman Khalil sau dubu a kan Sarai. Farawa da iya wa.

Inda Allah Ya taimake ni ina sana’a, kuma cikin ikon Allah ina samu, da yau kam sai raina ya fi haka baci.

Abincin rana sai wajen uku saura muka gama, da kaina na kaiwa su Maama, da yake sai yamma suke tasawo. Sosai abun abin da zai, rage min damuwa nake yi, ganin yaran kuma sai na dan ji sauki a zuciyata.

Koda na dawo gidan Maman Aiman na zarce, a can na yi sallahr la’asar muka taba hira, na kara jin kaso mai yawa na bacin raina babu.

A haka na dawo gida zuciyata ta dan rage cushewar da ta yi.

Kwana biyun nan nike ciyar da mu, abun da ya sanya ni kara girmama maza. Lallai ciyarwa ba karamin aiki ba ne, iya ta kwana biyu kawai na yi, amma ji nake duk na gaji. Ina ace aikina kenan. Watarana Ina sane za a kwana da yunwa. Yo wannan aiki ai ya isa. Allah dai ya sakawa mazajenmu da alkairi, ya sanya musu albarka a nemansu, ya basu lafiyar fita neman.

Ranar da ta fita girki sai ga shi tabar key din a jikin kofa, amma kitchen dn nan kam ya ci uwatar, saboda duk abin da ta bata a kwanaki biyun cokali ba ta wanke ba.

Haka muka yi ta fama ni da Uwani, har  kitchen din ya dawo hayyacinshi.

Ban fadawa Bashir komai ba, na ci gaba da hidimata,  kwana daya da karbar girkina, ana gobe zan fita kenan, muna zaune da shi muna hira. Ya ce min “Khadija me ya sa ba kwa ba Nana damar yin abinci ne”

Da sanena na ce “Wacece kuma haka?”

Ya ce “Saratu”

Kallon shi na yi kafin na ce “Haka ta ce?”

“Ya ina tambayarki kina tambaya ta”

Yadda ya harzuƙo ne ya sa na ce “Ni ban hana ta ba, duk lokacin da take son shiga, ba zan hana ta ba, ita ce dai ta hana kanta”

Ban bari ya kara cewa komai ba, na mike zuwa bedroom,  daga baya ya biyo ni.

Washegari da yamma bayan na gama abincin dare, kayan abinci masu yawa na ware, na sanya su Khalil su kwashe min zuwa kitchen dina na ciki. Ni kuma na haura sama.

Misalin karfe tara na dare, su Khalil ma har sun shige ɗakinsu na ga kiran Bashir. “Zo ki bude min kofa” abin da ya fada kenan bayan na daga kiran.

Na sakko kamar mai jin tsoron taka kasa, a haka na bude mishi falon ya shigo. Daga yadda na ga fuskarshi na san akwai matsala. Ni ma sai na tamke ta wa.

“Ina Khalil?”

“Me ya faru?”

Na sha gabanshi, ganin yana niyyar nufar ɗakinsu Khalil din

“Wato duk yadda nake fada miki a kan kada ki yi involving yaran nan a zamantakewarmu nema kike ki saka su ko? Haka Sakeena ta zauna da ke, ta bar yaranta sun raina ki? Amma ke shi ne kike  sanya su su raina min mata ko?” yadda ya futittike abun mamaki ya ba ni

” Me Khalil din ya yi? “

” Oh bama ki sani ba ko? To don Allah Ya kara gwadawa, zan ci ubanshi la’ada waje”

Ni dai kallon shi kawai nake yi, kafin ya ce “Waye ya ce ki kwashe kayan da ke cikin kitchen din waje, bayan kin san gobe Nana ce da girki?”

“Ni ban kwashe kaya ba, iyakar wanda za mu yi amfani da su kawai na diba” na ba shi amsa, muryata babu alamun tsoro ko kadan.

“Girki na ce a raba, ba kayan abinci ba. Khadija kar ki sake ki kawo min tashin hankali. Wlh zan ba ki mamaki.” ya kai karshen maganar hade da nufar kitchen dina.

Ina tsaye a wurin ya rika fito da kayan daya bayan daya, yana kai su kitchen din waje. Shi ko gajiya ma ba ya yi. Shi ke aikin ni ce ke jin na gaji , saboda yadda yake jan kafarshi.

Ya gama kwashe kayan tas, sannan ya fice, ko kofar bai ja min ba.

Karar bude kofar su Khalil ce ta sanya ni juyawa, Khalil ne ya fito sanye da kayan bacci, fuskar nan a dagule, har ya iso wajena ban janye idanuna a kanshi ba.

Cike da damuwa ya ce “To Auntynmu da me za mu yi breakfast gobe?”

“Me ka yi wa Auntynku?” na jefa mishi ta wa tambayar a maimakon amsa tashi.

Sai da ya kara ɓata fuska sannan ya ce “Yo ni me na yi mata, kawai fa shigowa kitchen ta yi ta same mu muna kwashe kaya, shi ne ta ce wai ubanwa ya sanya mu, kuma gidan ubanwa za mu kai su, mu ka yi mata banza, shi ne ta tare kofar fita, ni kuma na ture ta”

Mamakin abin da ya faru ne ya hana ni yin magana kan lokaci. Lallai Sarai ƴar bala’i ce da alama, daga zuwanta cikin sati daya tana neman jefa mu cikin damuwa. Ina yi mata kallon biri ashe kallon ayaba take yi min.

Ajiyar zuciya na sauke a hankali kafin na ce “Ai da ba ka ture ta ba Khalil, Babanku take aure, komai kankanatarta matsayin uwa take a gare ka, don Allah kar ka kara, ka ga dai abin da hakan ya janyo yanzu.”

Komai bai ce ba, ya nufi hanyar dakin nasu, fuskar nan kamar bakin hadari ya hadu.

Jiki a sanyaye na rufe kofata, kafin na dawo saman kujera na zauna, raina a jagule. Can kasan zuciyata kuma cewa nake.” Dama haka kishin yake? Ashe a wancan lokacin banza na ci, dadi ne ya yi min yawa har nake shirme. Anya kuwa ba Sakeena Allah Yake sakamawa ba? Ko kuma dai Allah yana son nuna min kuskurena ne, na yadda nake ganin ina ma ni ce kishiya ta taras ba ni ce na taras da ita ba. Ko kuma yadda nake ganin kishi da wayayyar mace ya sa nake shan wahala. To ga shi dai an dakko min karama, yar kauye, wacce ko sunanta ba lallai ta iya rubutawa ba, cikin sati daya kacal ta fara caza min kai. “

Na kai karshen tunanin nawa da ajiyar zuciya, a hankali kuma na furta” Astagfirullah Ya Rabbb “na yi maganar a sanyaye, yayin da hawaye ke neman sakko min. Cike da karfin hali na mayar da su ina fadin” No! Is too early in fara zubar da hawayena a kanki Saratu. “

Na kai karshen maganar hade da cije lebena na kasa cike da kunar zuciya.

Sama da awa daya na share zaune a falon ina kullawa da kwancewa, kafin na mike zuwa sama, kai tsaye kuma na dauro alwala na tayar da sallah. Sai wajen karfe daya na kwanta, kuma duk da haka ban makara ba.

Yau din ma Khalil na aika ya siyi bread, indomie da kuma kwai. Muka yi break, kafin suka wuce makaranta.

Sai bayan tafiyarsu ta bude kitchen din, ta yi kwaɓenta, ta fice.

Ganin ba ta rufe kitchen din ba, Sai kawai na shiga na dora girkin rana Uwani na taya ni.

9am Bashir ya fito cikin shirin fita aiki, zuwa lokacin kuma har mun gama miya, mun dora shinkafa.

Ina sane na ki fitowa daga kitchen din bare in bi shi. Haka ya gaji da zama a ciki ya fito, kuma shi ma bai shigo kitchen din ba ya fice.

Zuwa sha biyu saura na kammala duk wani abu da zan yi a kitchen din, har da abin da za a yi break gobe na diba zuwa kitchen dina. Muka gyare kitchen din tsab ni da Uwani, sannan muka fice.

Turarurruka muka shiga warewa, wadanda zan tura, da atamfofi da zan tura wa Customers dina.

Bayan na gama warewa, na ba Uwani don takaimin tasha, ni kuma na yi alwala don yin sallahr azhur. Ina sallahr ne na ji takun mutum alamar ana hawowa sama, Sai a lokacin ne na tuna ban sanyawa kofa key ba. Zuciyata ta ba ni, kodai Maman Aiman ko Uwani. Na fi gasgata Uwanin ma, saboda yanzu Maman Aiman ba ta cika shigowq ba. Wai mun karu.

Ga mamakina inuwar Bashir na gani, karon farko da na ji gabana ya fadi bayan na ganshi, irin faduwar ta me kuma ya faru.

Bayan na shafa addu’a  na ce “Sannu da dawowa”

“Yauwa!” ya amsa a takaice, kafin ya ce “Wato Khadija da alama ba za ki zama kamar Sakeena wajen jan girman ki ba. Dama ko wancan lokacin na fi fama da ke a kan Sakeena. Na dauka zuwa yanzu kin yi hankali ashe ba ki yi ba” ya tsagaita ba don ya gama ba. Ni ma kuma komai ban ce ba. Shi ne ya dora da “Ina jin a gabanki Nana ta yi maganar girki, kuma kika ce kin amince. Amma ranar girki ba kya bari tana shiga kitchen, yarinyar nan sai ta kai azhur ba ta karya ba. Sai dai in sawo mata abinci. Jiya kuma kin saka yara sun kwashe kayan abinci kin kai part dinki saboda mugunta, na kwashe su, still yau kin yi Kane-Kane a kitchen din kin hana ta shiga. Kuma ni shaida ne, saboda a kitchen din na bar ki”

Duk maganganun da yake ina kan sallaya kaina a kasa komai ban ce ba. Ya dora da “To ba zan dauki wannan wulakancin ba, yarinyar nan amana ce a wurina, ban dakkota don a wulakantata ba. Duk abin da kike yi ina sane, dama ranar biki haka aka ce kin tara kawayenki da ƴan’uwanki, su kai ta ci wa yarinyar nan da danginta mutumci, wai yar kauye wacce ba ta yi makaranta ba. Ina ruwanki da rashin karatunta ko kauyancinta, ni na ganta na ji Ina sonta, kuma na kawo ta gidan nan, don haka duk darajarku daya. “

Ni dai komai ban ce ba, ya kuma cewa” Daga yanzu idan ba ke ce da girki ba, ban ce ki je ki babbake kitchen ba, ki hana ta shiga “

Jin ya yi shiru ne ya sa na ce” To ka yi hakuri ka siyo min kayan nawa abincin, ka ga hidimata da tata akwai bambanci, ni ina da yara, kuma komai nawa a tsare yake, da zarar na kuskure sai a samu matsala. Ka yi hakuri don Allah “

Na lumshe idanuna hade da sauke ajiyar zuciya lokacin da na ji ya ce” in je kitchen din in debi duk abin da nake so in bar mata nata, “wai hakan shi ne kwanciyar hankalinshi.

Ina tsaye a tsakiyar kitchen din ya debar min komai, kafin ya ce idan zai dawo abin da babu zai zo min da shi. Godiya na yi hade da daukar kayan zuwa kitchen dina na ciki Uwani na taya ni.

A zuciyata kuma Ina fadin, shi ya sa aka ce tsakanin hakuri da gajen hakuri ɗan taƙin kadan ne, da ace jiya ban kwashi kayan nan ba, na hak’ura zuwa yau, da an ba ni su cikin kwanciyar hankali.

Duk da maganganun Bashir sun bata min rai, hakan bai hana min jin farin ciki ba, a wani bangaren na zuciyata, saboda kayan abincin da aka ba ni.

Tun daga wannan lokacin sai in yi sati kafata ba ta shiga babban kitchen ba koda kuwa ace ni ce mai aiki, haka ma Uwani, idan an ganni waje abu mai muhimmanci ne ya fito da ni. Kuma tun daga lokacin Bashir bai kara cewa na yi wani abu ba.

Ni ma kuma kokarin toshe duk wata ɓaraka nake yi, da na san za ta sanya Bashir yi min tujara. Don shi irin mutanen nan ne, da idan abu ya hadoku, zai rufe ido ya yi maka zagar zogale ba ruwanshi.

Yarana ma kaffa-kaffa nake yi dasu a kan shiga harkar Sarai, inda Allah Ya taimake ni, idan suka tafi tun safe sai 6pm,shi ya sa komai baya hadasu

Ni ce dai kullum nake shan wakar habaici. Ranar da take jin ƴan tsiyarta sai ta fito da wayarta kwamemiya (Sha kidanka ba ƙauye)  ta kure volume a wakar Gwanja, musamman baitin da ake cewa _”Haka za a ganmu ayye, haka za a bar mu… “_

Da kuma wata waƙar da ake cewa _” Ruwa ya ci garin maƙiya, ashe dai muke da wuri na kwana sai in ga tsiya_” da yake ni ban saba da irin wannan habaicin ba, na dauka kawai tana son waƙar ne,  daga baya na fahimci ni take yi ma. Ga shi ni ban iya irin wannan habaice-habaicen ba, bare in rama. Kai Allah Ya hadani da jarabar laƙe wai cuta bayan rai.

Yanzu ne nake tantance kishi, da kam ba kishi na gani ba. Yanzu abun har ya wuce tunanina. Da ido kawai nake bin igiyar ƙaddarar in ga inda za ta kai ni. Yar karamar yarinya tana ta ban mamaki.

<< Hasashena 34Hasashena 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×