Skip to content
Part 36 of 36 in the Series Hasashena by Hikaya

Zuwan Inna ya daidaita tsakanina da Bashir, yanzu kam normal kamar baya, da Sarai ne dai jiya I yau.

Yau kam da suna muka tashi a cikin layinmu, shi ya sa misalin karfe biyar na fito cikin saukakkar kwalliya, bayana goye da Haidar hannuna kuma rike da Assidiq, kai tsaye gidan Maman Aiman na shiga, kasancewar lokacin da na shiga ta shirya, shi ya sa babu bata lokaci, muka nufi gidan sunan.

Bayan mun yi wa maijego Ihsani, muka fito waje inda matan unguwa ke zaune, nan na rika jin labari kala da iri. Musamman makircin kishiya, kai na yarda, wacce ba ta da kishiya a gidan auranta kamar tana zaune a dakin uwarta ne hankali kwance.

Misalin shidda muka bari gidan sunan, wajen mu goma, kuma kai tsaye gidana suka nufo, za su sayi turare.

A kan entrance na baje musu Shi, suka yi ta zaba, kun san taron mata dai, dole sai an ɗan yi iya shegen nan.

Haka ko suka cika gidan, idan an yi wata maganar sai a buga shewa hade da tafawa.

Sai da aka kira magriba, sannan suka tafi, ni ma na yi alwala don gabatar da sallah.

Misalin 8pm Bashir ya dawo  tare da yara, da alama a masallacin suka hadu ya dakko su.

Duk da girkina ne, Sai da ya fara shiga part din ta, sannan ya shigo nawa. Ban damu ba, saboda ko ni ma wani lokacin idan girkinta ne, ya kan fara shigowa nawa part din, kafin na ta.

Ka dinning ya yi wa tsinke inda muke cin abinci, ya joining din mu.

Cike da Nishadi muke hira, har 10pm, in da ya kora su Affan su kwanta saboda makaranta.

Muna hira ne, na ce mishi zan yaye Haidar, na dauka zai ce wani abu, Sai ga shi ya amince.

“Khadija!” ya kira sunana

Sai da gabana ya fadi kafin na amsa

A nutse ya ce “Saboda gudun tashin hankali, don Allah na hana makota shigo min gida, ko wacce ta zauna a gidanta har Maman Aiman, ba na son damuwa”

Ban wani ja da tsawo ba,na ce “To” na san dai matarshi ce ta fada mishi wani abun. Kai ina ganin ikon Allah. Kamar tana gaba da farin cikina.

Can kuma sai na ce “To idan abu za su saya fa?”

Shi ma sai da ya dan yi shiru kafin ya ce “Babu laifi, amma iya kasuwancin kawai, ba na son ya wuce haka.”

Kai na daga alamar fahimta. Amma babu macen da zan ce kar ta shigo. Dama wacece mai shigowar Maman Aiman ce, kuma sai ta yi wata daya ma ba ta shigo ba. Allah dai Ya nuna min karshen wannan bala’i.

Koda na kwanta sai bacci ya gagare ni, na ganni kamar na zama wata wawiya, da karamar yarinya ke juya, ya kamata in yi wani motsi, ba wai in zama kamar rakumi da akala ba, duk inda aka juya ni ina wurin.

Ni yarinyar nan ta taras a gidan, ni ce ya kamata tana bi sau da kafa bawai ni in bi ta.

Lokacin da na samu marigayiya Sakeena, ni ce dole na bi ta. Ba ita ce ta rika bi na ba.

Haka nai ta tattaunawa da zuciyata, har bacci ya dauke ni.

A satin na ya ye Haidar, a kuma satin ne, aka yi wa su Affan hutu, wanda daga shi za su canza sabon session. Kenan za su shiga js 2.

Ban Sha wahalar yayen Haidar ba, saboda su Khalil suna hutu, suna taya ni raino.

Safiyar Asabar Khalil ya wanke kayan kwallon shi, ya shanyasu a igiyar bayan kitchen. Wanda dama normally a nan muke shanya ba mu faye yin shanya a tsakar gida ba.

Kasancewar Sarai ce za ta karbi aiki yau, shi ya sa ana idar da sallah la’asar ta shiga kitchen din.

Khalil kuma misalin biyar saura ya fito, don tafiya wajen kwallon shi, wai match gare su, saboda shi da Assidiq mayun kwallo ne, Affan kam in ta yi ruwa rijiya, in taƙi ruwa masai ne, a, harkar kwallo.

Bayan fitar Khalil ba jimawa Maama ta rugo inda nake ta ce “Auntynmu, ana fada da Ya Khalil da waccan matar”

Cike da mamaki na ce “Wace matar?”

Ta ce “Wacce Abbanmu ke zuwa gaishe ta, kuma har ta mare shi”

Tsakanin dire maganarta, da mikewa zuwa kofar fita ban san wa ya riga wani ba. Don kalmar marin nan ta soki kirjina. Jin ta na yi kamar kibiya aka soka min.

Lokacin da na fita Khalil na ta haurin kofar kitchen din da kafarshi kamar zai ballata.

Da sauri na isa hade da rike shi na ce “Me ya faru”

Huci kawai yake yi ya kasa magana, na juya kam sauran yaran da suka biyo ni,  na lalubo Maama na ce “Ya aka yi ne Maama?”

Khalil din take kallo kamar za ta yi kuka, kafin ta ce “Ita ce ta watsa mishi ruwan wake a kayan kwallo kuma ta mare shi”

Sai a lokacin na lura da kayan kwallon a kofar kitchen. Hannu na sanya hade daga su, abun ka ga farare duk ga baki da jirwayen ruwan wake nan

Tsakanin marin, da zubawa kayan ruwan wake ban san wanne ya fi ɓata min rai ba. Tsawon shekaru nawa ina rainon yaran, da dadi babu dadi ban taba fitar da hannu na mare su ba, Sai ita daga zuwanta ko shekera daya ba ta yi ba, za ta warware hannu ta marar min yaro.

Na mayar da kallona kan Khalil wanda ban taba ganin ranshi ya yi wannan bacin ba, haɗiyar zuciya kawai yake yi.

“Tana ina?” na tambaye shi.

Da hannu ya nuna min kitchen din.

Na shiga kwankwasawa, amma ba ta bude ba. Khalil din na janyo hade da rungume shi, kila daga ni har shi, za mu samu sassaucin abin da muke ji. Don na yi imanin yau da yarinyar nan ta bude kofar kitchen din nan, wlh da Sai na ramawa Khalil marinshi, koda za ta yi min duka. Ballantana ma na san a buge dai, ba ta isa ta doke ni ba.

After some minutes yana kwance a jikina kafin na kama hannunshi, zuwa cikin falona, sauran yaran suka biyo ni.

Da kyar na iya cewa Affan “Tun da kana da irin kayae, dakko mishi na ka”

Jiki a sanyaye ya je ya dakko mishi kayan. Da kyar na lallashe shi. Ya karba. Affan kuma ya tafi loundry don wanke mishi wadanda aka ɓata din.

Sai da Saratu ta faki idonmu, sannan ta fito daga kitchen din.

Daga ni har yaran babu wani mai kuzari, da alama abin da ya faru da ɗan’uwansu ya taɓa su. Tun ba ma Affan ba.

Kada sai ya ja tsoki. Sai gab magriba Khalil ya dawo, har zuwa lokacin kuma fuskar nan kamar kunu ya kwana. Ni ma ina daurewa ne kawai, a haka suka tafi masallaci sallahr magriba.

Yau kam basu jira Abbansu ba, kuma suna dawowa babu wanda ya saurari abinci. Ban matsa musu ba, saboda ni ma ba na ko son ganin abincin.

Takwas da yan mintuna ya shigo gidan, isowarshi falon da tambayar Ina Khalil ya fara.

Na dube shi da kyau kafin na ce “Me ya sa kake neman shi?”

Shi ma kallon nawa ya yi kafin ya ce “Ina ruwan ki, da abin da zan yi mishi. Khalil!!” ya shiga kwala mishi kira yana nufar kofar dakinsu

Ganin Khalil ya bude kofar dakin ya sanya ni saurin tashi da sauri na riga Bashir zuwa kofar dakin, na kuma tura Khalil a bayana na ce “Me za ka yi mishi? Me ya yi?”

Cikin fada ya ce “Ai shi ya san abin da ya yi, duk abin da suke a cikin gidan nan na raina min mata ina sane. Tun da Nana ta shigo gidan nan ba su taba gaishe ta ba. Shi ne har rainin ya kai Khalil ya ce zai yi dambe da ita, ke kuma kina taya shi”

Dama raina a bace yake, saboda sosai marin nan ya bata min rai, kuma idan ban rama mishi shi ba, ba zan taba hucewa ba. Na daukarwa kaina alkawari daga nan har shekara goma in Sha Allah sai na ramawa Khalil marinshi.

Sama da ƙasa na kalli Bashir na ce” Ba Zasu gaishe ta din ba, don su gaishe ta ka auro ta, abin da take so a auran ba ta samu ba ne? “

Sororo yake kallo na kafin ya ce” Wato maganar Nana ta tabbata ke ce ke zuga su kenan? “

” Kwarai kuwa ni ce nan nake zuga su, kuma don na isa, idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana. Ka kira ta, ga Khalil din nan ta rama duk abin da ya yi mata. Ni kuma yau da Sai na yi mata bugun ƴa da uwa wlh. Sannan ka gargade ta, iskancinta ya tsaya iya kaina, kar ya hauro kan yarana, don wlh ba na daukar lamarinsu da wasa. Idan da baya ba a ji mu ba, to yanzu za a ji mu. Wlh ba zan dauki wannan ba. Ka sanar mata. Kuma don Allah ka fita ka bamu wuri. Sannan ka sanar mata, ta rubuta ta ajiye marin da ta yi wa Khalil muddin ni Khadija na haihu kuma Ina numfashi sai na rama mishi wlh. Kuma don Allah ka fita na ce, ba na son ganinka” na kai karshen maganar cike da jin zafi.

Ban san me ya gani ba, ya juya ya fice ba tare da ya ce komai ba. Bayan fitarshi ne na juya bayana inda Khalil ke tsaye, ya fada jikina tare da fashewa da wani irin kuka, kukan da ya sanya hawayena sakkowa da sauri, na shiga bubbuga bayanshi cike da bacin rai, wani abu mai daci ya tsaya min a a wuyana ya ƙi wucewa.

Yadda Khalil ke kuka sai nake jin kamar na ci amanarsu, tun da mahaifiyarsu ta rasu bai taba irin wannan kukan ba sai yau.

Ji nake kamar in fita zuwa dakin Sarai in jawo ta in yi ta jibga har sai na ji na gaji.

Saman kujera na ja shi na zaunar da shi, kafin na je kitchen na dakko ruwa mai sanyi na mika mishi.

Karba kawai ya yi ya rike yana ta sauke numfarfashi. A ranar na fahimci Khalil yana da zuciya sosai. Irin zuciyar nan da kan iya sanyawa mutum ya suƙe numfarfashinshi ya riƙa season.

Ruwan na karɓa, na bude da kaina hade da kai shi saitin bakinshi, hannu ya kai ya rike kamar zai sha, Sai kuma ya janye ruwan hade da dora kanshi a kan cinyata yana kokawa da numfashinshi.

Ruwan na ajiye gefe, kafin na dago shi, na kuma rumgume shi ina shafa bayan shi.

A hankali na ce “Khalil na yi wa Mamarku alkawarin zan rike ku amana. A yau ina cike da bakin cikin saukar hawayenka a kan gaskiyarka, ina jin kamar na gaza. Na gaza a rike amanar da mahaifiyarku ta rika jaddada min. Lokaci ya yi da zan motsa, motsi na a mutu ko a yi rai. Daga yau in Sha Allah ba zan kara barin hawayenku ya zuba kasa a banza ba. Zan iya jurewa a taba ni, a taba yarana, amma ba zan jure a taba ku ba. Ka yi hakuri In Sha Allah wannan shi ne karo na karshe da hakan zai faru. “na karasa maganar ina dauke hawayen da ke sauka saman kuncina. Sai ma kawai na kifa kaina a bayan Khalil hawayen suka ci gaba da sauka a bayan shi.

Tsawon lokaci muna a haka, kafin na mikar da shi, na raka shi zuwa dakinsu, ni kuma na haura sama.

Dama dai na san babu batun bacci yau a idanuna, don ba na ma jin shi. Abubuwa da yawa nake saƙawa. Har aka kira sallahr asuba, sannan na sauka kasa don tashin su Affan, time da na shiga ma suna shirin tafiya masallacin. Shi ya sa kawai na wuce kitchen din waje, cikin ikon Allah kuwa na same shi a bude.

Key din na zare, na kulle shi ta waje, dama kofar baya a rufe take. Key din na zare na wuce part dina. Saboda yau kam na shiryawa bala’i, za ta san yau ta taɓo ni. Saboda yau ne na ji ta taɓa ni, taɓawar da ko wane jiki nawa ya amsa ta.

Har yara suka tafi school daga ita har Ogan gidan babu wanda ya leko,  wajen takwas da mintuna na ji motsin ta zuwa kitchen. A zuciyata na ce yanzu za a yi abun, wai mai ƙaryar ciki ta haihu. Sama na haura na canja kaya zuwa wando da riga, har bra sai da na cire, saboda yau din nan a shirye nake, komai ma ya faru.

Ban ji ma da sakkowa kasa ba, na ji ana kwankwasa min kofa,  na gama shan kamshina sannan na bude kofar, na kuma dogare hade da babbake ko ina ba tare da na ce komai ba.

Kila hakan ne ya sanya shi sauke tamper shi ya ce “Key din kitchen na wurinki ne?”

Na kalle shi from head to toe sannan na ce “Wane kitchen kenan?”

“Wannan kitchen din” ya yi maganar hade da nuna min kitchen din da hannu.

Na kalli kitchen din, sannan na dawo da kallona kanshi na ce “Wannan kitchen din ai na matar so ne, ni tun yaushe aka kore ni cikin shi. Ka tambayi mai amfani da shi” daga haka na mayar da kofata na rufe. Ban san yadda suka watse ba, wajen 9am dai na ji fitar shi.

Wata irin kwafa na yi ta ɓacin rai, ban so abun ya tsaya haka ba, na so ya ja magana sosai, ni kuwa in tayar musu da aljanu kowa jikinshi ya fada mishi.

Karfe goma na safe na bude kitchen din, ni har kyama ma ya ba ni, amma haka nan na yi abincin rana a ciki, kuma Ina gamawa na tattare komai na kuma kulle kitchen din.

Washegari da za ta fita girki, Sai na ga an siyo mata foodstuff an, shigar mata dasu kitchen din ta na ciki. Ni kuma kawai sai na gyare kitchen din wajen tsab, na ci gaba da amfani da abuna.

Fushi sosai Bashir ke yi da ni, saboda tun da ya dawo sashena, har kwanakina ya kare bakinmu bai hadu ba. Ba ni kadai ba, hatta Affan da Khalil baya amsa musu gaisuwa.

Abin duk sai ya damu yaran, ni ce ke kokarin kwantar musu da hankali, da cire musu damuwa.

<< Hasashena 35

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.