Skip to content
Part 38 of 39 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ga shi kuma Ina kitchen din waje ne ina girki.

Har na gama abinci tana zaune a barandar ta sake wannan waƙa, ta dakko wannan, wani lokaci har da shewarta da dariyar rainin hankali.

Ranar Laraba ya kama ranar tafiyata, yammacin talata kuma Bashir ya fita daga dakina.

Da dare da ya shigo don yi min sai da safe, da kuma daukar abin amfaninshi ne na ce “To ya zai kasance ne gami da abincin yara, in yi musu abinci har da wanda za a kai musu da rana ko kuwa?”

Ya dan yi shiru kafin ya ce “Ki yi iya na safen kawai, da rana za a kai musu, idan ma kiwa ta hanani dawowa gida, zan yi musu take away”

“To shi kenan” daga haka mu ka yi sallama, ko ba komai hankalina ya dan kwanta. Saboda jikina na ba ni Saratu ba za ta yi musu abinci ba, kuma koda ta yi ma ba lallai ya gamshesu ba.

Safiyar Laraba tare muka fita da yaran, ni aka kai ni tasha, su kuma suka wuce school. Maama kam har da kukanta.

Misalin karfe shadaya na safe mai napep ya sauke ni a kofar gidanmu, murna wurin Ummata ba a magana, da yake zuwan bazata na yi mata.

Bayan kwance tsaraba ne muka shiga hira, mu yi wannan, mu koma kan wannan, lokaci daya kuma muna aikin abincin rana, Sai da na yi sallahr azhur sannan na janyo plate din abinci ina ci a nutse muna kara hira, can tsakar gida kuma su Usman dasu Assidiq suke nasu hirar cikin murnar ganin juna.

Umma ta gyara zama sosai kafin ta ce “Me ya faru na ga kin rame ne, ko kin yi ciwo ne?”

“Ba gara ciwo zan warke ba, amma wannan yaushe na san ranar warkewa ta, an zo an hada ni da yar bala’i, masifar yau daban, ta gobe daban.” na yi maganar a zuciyata, a fili kuma sai na shiga kallon jikina kafin na ce “Umma kodai don kin jima ba ki ganni ba ne?”

“Ba wani don na jima ban ganki ba, jimawa ban ganki ba, ai ba za ta sanya in ga ramarki ba, Sai dai idan dama kin rame din”

Murmushi na yi hade da kai abincin bakina, ita kuma ta ci gaba da fadin

“Abin da na fahimta kina da zafin kishi, wannan kika sanya a ranki, shi ya sa kike ta ramewa. Kullum kuma Ina kara fada miki ki rage sanya abu a rai, ki rage zafin kishi. Ke da gida yake hannunki, duk abin da Bashir ke taƙama da shi yana hannunki. Yaranshi sune tearing Shi, kuma suna hannunki, ba sai ki juya yadda kika so ba. Idan kuma saka abu a ran za ki ci gaba da yi, sai ki je ki yi ta yi ai”

Ni dai komai ban ce ba, na ci gaba da cin abincina a hankali, yayin da Umma ke ta fada, da kuma yi min nasiha, ni din ma a hankali nake tace maganar Umma ina adanata a wuri mai tsabta.

Sosai na ji dadin zuwana gida, saboda ji na yi rabin damuwata ta tafi.

Sai da na yi sallahr la’asar na baro Kano, hankalina bai tashi ba, Sai dana getting to six Ina hanya, na san a ko wane lokaci su Khalil za su iya dawowa. Ni kuma ba na son su dawo ban isa gida ba.

Ji nake kamar in karɓu tukin in yi da kaina. Kadan sai in duba agogon waya.

Muna shiga cikin garin Katsina ana kiran sallahr magriba, drop din Keke na samu kasancewar ina da kaya da yawa, saboda har da atamfofi gami da shaddojin da nake sayarwa a tare da ni.

Keken ma ji nake ba ya sauri, kamar in fita in tafi da kafa, ban ji hankalina ya kwanta ba, Sai da na ji Ina buga gate, Affan ne ya bude min, kasancewar gari bai yi duhu sosai ba, kuma ga hasken manyan ƙwai da suka haske tsakiyar gidan kallo daya na yi mishi na ga ya rame.

Tun ban gama tantancewa ba ya fada jikina cike da ihun murna kamar ƙaramin yaro, Sai kuma ya sake ni, ya cakumi su Assidiq, kamar ya shekara bai gansu ba, haka suma suke murnar ganinshi

Sai a lokacin ne Khalil ya karaso shi da Maama, shi ma ba tare da wani tunani ba, ya fada jikina, na rungume shi sosai, yayin da Maama ta mamutseni, ita kam kuka take yi sosai, dalilin da ya sanya ni ture Khalil na daga ta sama zuwa kirjina.

Yayin da su Khalil ke ta kwasar kaya zuwa kofata.

Duk ihun da suka cika tsakar gidan da shi Sarai ba ta fito ba. Dama kuma na san ba za ta fito din ba.

Duk saman entrance dina suka jibge min kayan, na shiga kitchen wurin Khalil, saboda tun da ya rage manyan-manyan kayan ya koma kitchen.

Jerewa na yi da shi ina kallon yadda yake zuba jallof din taliya cikin plate.

Ba za ka taba cewa shi ne ya dafa ta ba, Sai kamshi take yi, ga shi a ido ma da kyan gani.

Spoon na dauko hade da diba na kai bakina, idanuna na lumshe ina fadin “Ummmmmm!” duk suka zuba min ido, kafin Khalil ya ce “Auntynmu wai me?”

Idanun na bude tare da aje su a kan fuskarshi ina murmushi na ce “Daɗi!” duk suka kwashe da dariya kafin Khalil ya ce “Auntynmu ai na sha fada miki na iya girki sosai”

Kai na jinjina tare da fadin “Na yarda”

Ina kallon shi cike da farin ciki a zuciyata, yadda yake ta sallamar kannenshi da abincin cikin kulawa. Wannan ya nuna koda ba na nan, idan akwai Khaleel ba za su shiga damuwa sosai ba. Musamman wajen abinci.

Affan ya bude mana kofa duk muka shiga, ba tare da na kwashe kayan da suka jibge a kan entrance din ba.

Bayan sun zauna cin abinci ne Maama ta ce “Auntynmu yau ba a kai mana abinci ba”

Na dakata da kai spoon din da na ciko da taliya bakina, kafin na ce “Me ya sa?” na yi tambayar ina kallon Khalil, Kai ya juya gefe kafin ya ce “Ni ma ban sani ba, Abbanmu dai ya ce za a kawo mana kuma ba a kawo mana ba. Ga shi yau abinci ya bare a school”

“Shi ya sa Affan ya yi ɗan wuya kenan” na yi maganar ina kallon Affan da yake ta zuba loma

Khalil ya yi dariya ba tare da ya ce komai ba. Haka nai ta jan su da hira, a kokarina na mantar dasu yar damuwar da suka shiga kafin in dawo.

Sai da muka gama cin abinci, na taya su muka shigo da kayan cikin falo, sannan muka ware ko wanne zuwa mazauninshi. Bayan mun gama ne suka tafi masallaci sallahr isha’i.

Ni kuma a lokacin ne samu damar yin tunani a kan abin ke damuna, na rashin kai wa su Khaleel abinci, ni fa abu kadan ya shafe su to girmanshi nake gani.

Na san Bashir abu ne mawuyaci ya manta da kai musu abinci makaranta, tun da ta san kome yake yi dole hankalinshi na kan yaran.

Ji na yi ba zan iya dannewa ba sai na magantu, don haka na kosa ya shigo.

Ana idar sallahr isha’i kuwa sai ga shi, kai tsaye ya hauro sama zuwa wajena, shi din ma yadda yake murnar dawowa ta shi ma na gan shi kamar Maama,  kamar ya yi shekera bai ganni ba, haka muka shantake hira har wajen 9pm,kuma Ina sane na ki tuna mishi ya kamata ya tafi.

After 9pm ne na fahimci hankalin shi ya fara komawa wurin matarshi. A zuciyata na ce ni ma dai bari in gwada kissar nan ta mata, yau daya in bata mata wannan daren.

Don haka na ɗan bata fuska hade da maraicecewa na ce “Yallaboi yau shi ne aka ƙi kai wa yarana abinci, suka wuni da yunwa. Bayan ka ce min za a kai musu”

Take kuwa mood din Shi ya canja, ya ce “Ban gane ba a kai musu ba?”

Na ce “Haka dai suka fada min”

Ya dan yi shiru, reaction din fuskarshi yana kara nuna min yadda ranshi yake kara baci.

“Kodai mai napep din ne bai kai musu ba, saboda Nana ta fada min ya zo karba, kuma ta ba shi”

Ina kokarin dakko wayata na ce “Bari in kira shi to”

Tun da wayar ta shiga na sanya ta a speaker.

Tana gab da yankewa ya daga, Sai da ya fara ba ni hak’uri na jinkirin dagawar da ya yi, ya fada min yana kokarin yin parking ne.

Na amsa mishi da ba komai, sannan na ce “Dazu, kai ne ka kai wa yara abinci”

Cikin girmamawa ya ce “A’a Hajiya, ai na zo amsar abincin Hajiya karama ta ce min Alhaji ya kai musu”

Na mayar da kallona kan Bashir wanda attention din Shi kaf yake kanmu. Wayar na yanke ina fadin “Ka ji ko”

Komai bai ce ba ya mike rai bace, ya fita daga dakin

Da kallo na bi shi har ya fice, kafin na tabe bakina, a bayyane na ce “Ku shawo ta can, an cewa Dan daudu magriba ta yi, ya ce ku shawo ta can”

Ai yadda na ji a zuciyata ina son ta ji ita ma. Idan plan dina ya tafi daidai, to saura marin da ta yi wa Khalil ya rage in rama mishi.

Sai na ji kirjina sakayau, na ji kuma kamar in je in musu labe in ji yadda za ta kaya, sai dai ba dama, amma kam ina matukar son jin abin da zai faru.

Da safe bayan na sallami su Affan, customers dina suka fara shigowa karbar kaya, wasu kuma ganin kayan , haka suka shigowa group-group. Ina lura da yadda sarai ke ta kunci, ni dai addu’ata Allah Ya sa Bashir ne ya zazzage mata buhun rashin mutunci, daga cikin buhunan shi.

Ina sallahr la’asar wasu customers din suka kara shigowa, yanzu kam har da Maman Aiman, shigowarta ta biyu kenan, saboda da safe ma ta shigo, yanzu kuma wasu yan cikin unguwa ta rako.

 wajen biyar na mike don yi musu rakiya, bayan sun zabi kayan da suke so.

Mun zo daidai saitin kofar Sarai ta bude kofar hade watso dabzar aya saman jikin Maman Aiman, da yake ita ce ta farko a daidai saitin kofar, daga nan kuma sai ni.

Duk muka aje poster hade da juyawa inda take, Sai dai har ta koma ciki, hade da rufe kofarta.

Hijab din Maman Aiman na kama ina kakkabe mata dabzar ayar lokaci daya kuma Ina ba ta hak’uri.

Komai dai ba ta ce min ba, taya ni kakkabewar da take yi. Sauran ma basu yi magana ba.

A haka na raka su gate na dawo raina bace, kamar in kwankwasa kofarta, Sai kuma na wuce kofata kawai zuciyata tana yi min zafi.

Misalin karfe shidda saura su Maama suka dawo school, a lokacin kuma Sarai ce zaune a entrance din ta tana wanki, ta kuma shanya wasu  kayan a tsakiyar gida, kasancewar babu wurin daura igiyar mai kyau shiyasa shanyar ta yi kasa-kasa

Maama kam ta rugo da, gudu tana kiran sunana, dalilin da ya sanya ni yaye labulen windowna ina kallon yadda take gudu cike da zumudi.

Daidai lokacin ne kuma kanta ya janyo farin under wears din Sarai da ta shanya kan igiya. Yadda ya lulllube mata fuska ne ya sa bayan ya kai kasa, ta kuma taka shi.

Ta zaburo caraf hade da rike ta, daga inda nake zaune ina jin yadda cikin tsawa ta ce mata “Uban waye ya ce ki janyo min kaya, kuma ki taka min”

Tsuru-tsuru Maama ta yi cike da tsoro.

Ta kuma maimaita mata tambayar cikin tsawa, Khalil ya shiga kokarin kwace hannun Maama daga hannun Sarai yana fadin “ba ta gani ba ai, ki daina tsorata ta”

“Na tsoratata din, uwar waye ya ce ta yar min da kaya kasa” har zuwa lokacin ba ta saki Maama ba

Khalil ya duka hade da dakko siket din a kasa ya ce “Sakarta ni zan wanke miki”

Maimakon ta sake tan Sai ta kai yatsanta kan goshin Maama tana fadin “Idan kika kuma janyo min ka…” ba ta karasa ba, saboda yadda Affan ya buge hannunta da ta rike Maama da shi, lokaci daya kuma ya janye Maaman a fusace, sannan ya fisge siket din ta da ke hannun Khalil ya jefa mata kan jikinta yana fadin “Ba a wankewa”

Ta kawo mishi duka,  ya tale irin su daku din nan. Duk abin da suke yi ina kallon su ta windown falona.

Da na ga Sarai na matsawa jikin Affan da zummar dukanshi, shi ma kuma yana daɗa talewa alamar yana jiran ta iso. Ya kawo mata bugu.

A hankali na fito kan entrance dina na bude murya kadan na ce “Affan!”

Ya dakata da shirin bugun da yake niyyar kaiwa mata yana kallo na.

Da ido na yi mishi alamar ya zo, ko second uku bai ƙara ba ya nufo ni, sauran ma suka rufa mishi baya

“Allah Ya hada mu da jaraba” na fada cikin zuciyata hade da sauke ajiyar zuciya.

Ban tsaya tambayarsu ba’asi ba, saboda duk na ga abin da ya faru, kuma ban ce musu komai ba a kan rashin kunyar da suka yi wa Sarai. Ban san me ya sa ba na iya magana ba, idan na ga sun yi mata rashin kunya.

Na dauka da Bashir ya shigo da dare zai yi min maganar abun da ya faru, amma na ji ya yi shiru, ni din ma sai na fasa cewa komai, na dai hada mishi tsaraba na ce ya tafi wa da Sarai ita.

Da safe bayan na sallami yara, na gama gyaran part dina fes ina zaune cikin saukakkar kwalliya ina break, Haidar zaune a cikin kekenshi Assidiq kuma yana taya shi wasa.

Daidai lokacin Bashir ya shigo cikin kwalliyar boyel fari kal mai mai shara-shara, don har kana iya hango fara kal din vest din shi. Kanshi kuma sanye da bakar dara, kamshinshi mai dadi ya cika falon. Irin hadaddun matasan dattawan nan, da ilmi gami da gogewar zamani ya ratsa.

Haidar ya fara dauka da yake ta mika mishi hannu hade da kissing din goshinshi, kafin ya ce “Madam kina jin dadi fa, irin wannan break fast haka”

Na kalli gurasar gabana wacce ta sha kuli da mai, gami da cabbage, tumatur cocumber da albasa. Sai baƙi empty tea da ya Sha kayan kamshi.

Murmushi na yi kafin na ce “Good morning Sir!”

“Morning Ma!” ya amsa daidai yana zama kusa da ni, ya dauki yankar gurasar daya ya kai baki.

Haka muka rika cin gurasar tare muna hira.

Bayan da ya kammala ne, yana goge hannunshi da tissue ya ce “Khadija kina son in ajiye aikina ne, in dawo gida in zauna, in rika kula da yadda za ku zauna?”

A zuciyata na ce “Dama na san za a rina, wai an saci zanen mahaukaciya, ta ce kar a runa ma, a ga idan zai dauru.” a zahiri kuma  na ce “Wani abu ya faru ne?”

Ido ya zuba min, yadda yake kallona ne ya sanya ni dauke kaina ina murmushi.

“Ban hana makota shigowa gidan nan ba?”

Na ce “Ka hana, amma ba ka hana su zuwa siyan abu ba” .

<< Hasashena 37Hasashena 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×