Skip to content
Part 39 of 39 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Amma hakan ba ya nufin su rika cin zarafin matata” ya yi maganar da alamun rashin jin dadi

“Me suka yi mata?” na tambaye shi a hankali.

“Me ya za su rika ce mata yar ƙauye wacce ba ta yi karatu ba. Wai ba ina sane na auro ta haka ba? , ina ruwansu”

Na ce “Gaskiya kam, idan ba shiga uku ba”

Bata rai ya yi sosai kafin ya ce “I’m not kidding Khadija”

“Amma ai gaskiya na fada ko?”

Ya kara hade rai sosai kafin ya ce “Ba a kan sayen abu ne suke zuwa gidan ba, to daga yau na hana ki siyar da komai.” ya yi maganar hade da nufar ɗakin da nake tara kayan sana’a ta, ya rika kwaso su, yana kaiwa part din da ke facing din na Sarai, tun da ya fara kwashe kayan, Sarai ta fito kan entrance din ta tana kallo.

Sai da ya gama kwashe kayan tas, sannan ya bar gidan.

A lokacin na sauke ajiyar zuciya mai nauyi, hade da lumshe idanuna na bude cike da bacin rai. Tabbas ba zan bar sana’a ta ba, Sai dai idan auran na shi zan bari.

Na mike zuwa waje, ba tare da na san abin da zan yi ba, Sarai tsaye tana kwashe kayan da ta wanke, gani na ya sa ta fara waka

“_faɗa da aljani ba dadi… Uh-uh-uh. Fads da aljani fada da makami ne, uh-uh-uh fada da aljani ba dadi…_” Haka ta yi ta wakarta har ta kwashe kayan saman igiyar ta kai daki, ta kuma fitowa tana fadin “Mu kowa ya ci tuwo damu miya ya sha wlh, ni har an isa a hada ni da miji, abinci ne kuma ban kai ba, kuma na hana a kai”

Na sauka a hankali daga kan entrance dina hade da tunkarar ta…

Kasancewar duƙe take kuma ta juya baya tana tattare sharar munafurci, ba ta san na taho ba, har sai da ta ta ga inuwata a bayan ta, sannan ta yi saurin mikewa hade da juyowa, wannan ya sa tsakaninmu bai fi taku biyu ba. Muka zubawa juna ido muna kallon-kallo, kamar kajin da suka gaji da fada.

Da yatsa na nunata kafin na ce “Ke karamar yar’iska, idan ba ki san babbarki ba, to ni ce nan” Na juyo da yatsana zuwa kan kirjina kafin, na ci gaba da cewa) duk abin da kike yi ina sane da ke, amma kar ki bari in juyo kanki, idan na juyo da kafafunki za ki bar gidan nan ba tare da kin shirya ba. Ba kin hadani da shi kan sana’a ta kina murna ba, saboda tsabar hassada, to da an jima da kanshi zai maido da kayan nan dakina, har ma ya kara min da wani jarin, kuma ki saka ido ki yi kallo. “

Na karasa maganar ina kallon cikin idonta, ta dan ja baya kadan kafin ta ce” Ko yanzu na ci riba, saboda na fadi abu ya aikata, kuma abun ya taba miki zuciya. “

” Amma kuma za a dora min riba, ni da ke waye a kasa kenan? “

Shiru ta yi ba ta ce komai ba, sannan na ce” Ina kara gargadinki a kan shiga harkar yarana, ki fita a idonsu. Sannan har yanzu akwai bashin marin Khaleel a kan kuncinki, idan mijinki bai sanar miki ba, ni yau na fada miki da babbar murya, zan rama mishi marinshi, koda kuwa a kan gawarki ne”

“Gara da kika ce a kan gawata, amma ido bude kin yi kadan ki daga hannu ki mare ni”

Na kara matsawa kusa da ita sosai na ce “Allah ko!”

Komai ba ta ce ba, na ce “ki kara cewa ban isa ba, ki ga isar”

“Idan an ce me za ki yi?”

Na ce “Rama mishi zan yi yan…” buga kofar da aka yi ne ya dakatar da ni, ni da ita duk muka juya muna kallon gate din.

Ni ce na je wurin, bayan na bude muka gaisa da matar da ke tsaye a kofar sannan ta tambaye ni wani street, na kwatanta mata, kafin na mayar da kofar na rufe.

Zuwa lokacin kuma Sarai ta wuce kofarta. Daki na koma, na dauki wayata hade da kiran layin Inna. Bayan mun gaisa na labarta mata abun da ya faru

Cike da bacin rai ta ce “Shi Bashir din?”

Kamar tana gabana na daga kai, Sai kuma na ce “Eh Inna”

“Shi kenan, ki yi hak’uri zan kira shi”

Kamar zan yi kuka na ce”kuma masu sayen kaya, da wadanda na karbi kudinsu a kan zan kawo musu sai kirana suke yi, wasu ma sun fara fada min magana, wai ko na cinye musu kudi ne”

Ta ce “Subhnallah! Bari in kira shi yanzu, ya zo ya fito miki da kayan.”

Na amsa da to, sannan na dora mata da godiya.

Bayan kamar awa daya da yin wayar tamu sai ga Bashir ya dawo, Sai kawai na haye sama, ina jin shi ya rika shigo da kayan zuwa falona, har ya gama shigo da su kaf, sannan ya kuma ficewa.

Ajiyar zuciya na sauke, hade da janyo mirror na, na fito da kudin cinikina, na tattara sauran kudin dakin na hada su wuri daya, sannan na nufi dakin Sarai.

Bugu uku na yi wa kofar ta bude, sororo ta yi tana kallona, na fito da hannuna dana boye a bayana kafin na ce “Kin ga ribar da na samu, idan kina so zan iya ba ki ki ƙirga”

Kofar ta rufe da karfi, ni kuma na juya zuwa nawa ɗakin zuciyata fes.

Sai bayan na koma daki na rika jin abin da na yi ba daidai ba ne, lallai na yi karya, abun da ban taba yi ba tsawon zamana.

Wani sashin sai yana fada min in je in fada mata karya nake yi, wani sashen yana hanani, tare da tabbatar min ko na fada ba za ta yarda.

“_Astagfirullah!”_ na fada a bayyane, Sai kuma kalmar ta zauna a bakina, kadan-kadan in ambace ta.

Washegari Bashir ya dawo dakina, da fushinshi ya dawo, na share shi, saboda na san waye shi.

Da yamma na shirya abincin da ya fiso, ni ma kuma na sha kwalliyar tarbarshi, amma har 9pm bai shigo ba. Na san duk cikin salon ya bata min ne, ni kuma na ki yarda in yi fushin. Saboda lokacin da ya dawo zaune ya same ni falo ina kallo, yara kuma duk sun shige dakinsu, irin su Khalil, Malama da, Assidiq ma akwai wahala basu yi bacci ba, saboda kamar kaji suke.

Haidar ma ya yi bacci, “Sannu da zuwa yallaboi!” na fada idanuna a kanshi

Maimakon ya amsa min, Sai ya raba gefena da zummar wucewa, hannunshi na rike, hakan ya bamu damar jerawa tare. Muka shiga haura steps din, har zuwa cikin dakinshi.

Hannu ya zare ba tare da ya ce min komai. Ina kallon shi ya zare kayan jikinshi ya shiga wanka, ni kuma lokacin ne na sauka kasa don dakko mishi abincinshi.

Sai da tattara duk wani abu da na san zai bukata cikin falon, sannan na zauna kan sofa Ina kallon yadda yake shafa mai a hankali.

Bayan ya kammala ne na shimfida sallaya kusa da abincin da na jera, plate na dauka hade da zuba mishi, kafin na kamo hannunshi ina fadin “Ba a zuciya da abinci Rabin jikina, musamman irin wannan da kake.”ganin ya ki tasowa ne ya sanya ni dakko abincin na zauna kusa da shi hade da yin amfani da hannuna na debi zuwa bakinshi, ban yi tsammanin zai bude bakin ba, Sai na ga ya bude, ni kuma na tura hannuna ciki.

Na saki yar kara saboda yadda ya rike hannun nawa a bakin shi. Ba tare da ya saki ba, ya zuba min ido, ni kuma na langabe ina yar kara tare da kokarin kwace hannun nawa amma ya ki saki.

Sai ma ya kara datse shi da dan karfi, wannan ya sa na zame kasa ina yar kara, tare da rokon ya sakarmin hannun, Sai da ya mula don kanshi, sannan ya saki ba tare da ya yi magana ba.

Da ido ya yi min nunin in ci gaba da ba shi abincin, ni kuma na makale kafada ina kallon shi.

Ya zamo daga saman gadon zuwa inda nake tsugunne, ya saita fuskarmu ya hada hancinshi na gogar nawa ya ce “Ba kya ji ko? Inna ba ta son laifinki, yaranki ma basu jin maganar kowa sai ta ki. Abin da kike so kenan ko dama? Gida ya koma naki ko? Ya zama ke ce kike commanding, to kin samu”

Baya na ja kadan ina tura baki, ya ce “Na yi karya ne?”

Fuska na narke kamar zan yi kuka, sannan na ce “Ni ban yi komai don in bata maka rai ba”

Saman gadon ya koma, yana fadin “Zo ki ba ni abincin”

Na mike daga zaunen zuwa inda na tashi, na shiga dibar abincin ina ba shi a baki. Yana amsa, har ya koshi, daga nan na kwashe tarkacen zuwa kitchen, ɗaki na wuce don shirin bacci, sannan na kuma dawowa dakin nashi.

Zuwa lokacin har ya yi na shi shirin bacci. Bayan shi na kwanta lamo, kafin a hankali na ce “Don Allah ka yi hakuri”

Kamar ba zai tanka ba, Sai kuma ya ce “ki rika kiyayewa, kar ki kai ni karshe”

Kai na jinjina a hankali lokaci daya kuma Ina tuna wane karshen kenan, sannan me zan kiyaye.

Cikin son bugun cikin shi na ce “Da za ka yarda, da ka mayar da ni Ruma”

Da sauri ya juyo ya ce “Me ya sa?”

“kila idan muna different wurare za ka fi samun kwanciyar hankali”

Shiru ya yi, sai kuma ya shiga girgiza kai daga kwanciyar rigingine da yake sannan ya ce “Akwai abubuwa da yawa da zasu hana yin hakan. Kawai ki zama kamar Sakeena, kawar da kai da dattako, shi kika rasa”

Ni din ma shiru na yi, komai ban ce ba, ina tunanin yadda zan zama kamar Sakeena, bayan Sarai ba kamar Ni take ba. Kila da ace har yanzu Sakeena na raye, duk hak’urinta sai ta tanka Sarai watarana.

Da haka dai bacci ya dauke ni.

Da safe kuma kasancewar Friday ce, Bashir ya ce Ruma zai je, saboda yana son a yi mishi sharar gonakinshi, kuma a ranar za a kawo kudin auran Jamila kanwarshi.

Lokacin da zai ta fi ya nannaga min ya fi kafa saba’in a kan kar ya dawo ya ji wani abu ya faru na ɓacin rai. Yadda ya nuna damuwa da hakan ne ya sa na ji cewa zan yi hak’uri da halin Sarai har ya dawo.

Tun da ya tafi na shiga sabgogina, na kasuwancina da kuma hidimar gida.

Kwatsam Sai ga Uwani mai taya ni aiki, sosai na ji dadin zuwanta, aiko tare muka yi aikin, a nan take sanar min wai layin ta rufe shi aka yi, kuma sai ta tafi Niger dangin mijinta, ta kai musu yara suka gani, shekaranjiya ta dawo.

Na ce haba “shi ya sa ba na saminki, kullum waya a kashe. Ya Niger din?”

Ta ce “Alhamdulillah”

Ni ma na ce “Na ga alama a jikinki sosai kin yi kyau”

Ta yi murmushin jin dadi kafin ta ce “Suna da kirki, ni dangin mijina kamar dangina suke, ina jin dadin zama cikinsu suna yi min komai ba kyashi kamar ƴan’uwan miji ba”

Na ji wani irin dadi a ƙasan zuciyata, sannan na ce “Ma Sha Allah! Hakan yana da kyau, Allah Ya saka musu da mafificin alkairi”

Ta ce “Amin” ta dora da “Auntynmu zuwa fa na yi in fada miki aurena rana irin ta yau”

Baki bude na ce “Kai Uwani!”

Ta dan yi kasa da kanta lokacin da take yanka min aleyahu ta ce “Da gaske”

Da alamun mamaki a muryata na ce “Ikon Allah! Haka fa rayuwa ko? Yanzu bayan mutuwar mijinki har kin kara jin son wani ko. Ji yadda kike ba ni labarin irin son da yake miki, da kyautata mi kin da yake yi” na karasa maganar hannuna kan habata alamun mamaki

Damuwa ta bayyana a kan fuskarta kafin ta ce “To yana iya, shi ma yana sona wannan din”

Kai na jinjina alamar gamsuwa, sannan na ce “Allah Ya tabbatar mana da alkairi, ya nuna mana lokacin”

Ta amsa da amin a hankali, har zuwa lokacin akwai damuwa a kan fuskarta. Albasar da na yanka, na kwashe zuwa cikin kullun masata, zuciyata tana tuna irin son da Bashir yake yi wa Sakina, da tashin hankalin da ya shiga bayan mutuwarta. Kamar ba zai iya kallon ko wace mace ba, Sai ga shi ya auro wacce ma ba ta kai ta komai ba, ya jeho min ita ta hana mu sakat daga ni har yara.

Lokacin da su Affan suka dawo, suka iske Uwani ba karamin murna suka yi ba, sun tambaye ni sama da kafa dari “Auntynmu Baba Uwani ta dawo ne?” kawai sai dai in yi musu dariya. A haka suka yi shirin masallaci suka tafi.

 yamma lis Uwani ta tafi, inda na yi mata alkawarin in Sha Allah zan zo bikin.

Safiyar Asabar misalin 8am yara suka fito cikin shirin makarantar Islamiya, kasancewar ina ba Haidar nono shi ya sa ban samu na yi rakiyarsu ba,   fitarsu ko minti biyu basu yi ba,   Khalil ya shigo rike da hannu Assidiq wanda yake kuka”Yadda na gan shi futu-futu ne ya sa na ce “Fadowa ya yi daga cikin napep din?” Da shi ke an sanya shi Islamiya, amma ba a sanya shi boko ba. Sai first term.

Shiru Khalil bai amsa min ba, sai dai kayan Assidiq da ya shiga cirewa.  ya cire mishi tas, ya kai shi toilet din dakin su ya dauraye mishi fuska, har zuwa lokacin Assidiq kuka yake yi.

Ya fito hannunshi rike da wasu kayan na Assidiq.

Sai da ya gama canja mishi kayan ne ya ce min “Waccan matar ce ta watsa mishi shara”

Na rika kallon Assidiq wanda idanunshi suka yi ja saboda kuka. Dama shi Ogan kuka ne, aka yi tusar banza ma bare an ci wake.

Har suka fice komai ban ce ba, saboda ban san me zan ce din ba.

Amma tabbas ina jin takaicin yadda Sarai ke tsokanata da fada, ko yi min abin da ta san dole sai ya taba zuciyata.

<< Hasashena 38

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×