Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Duk yadda na kumbura fam ina jiran shi, lokacin da ya shigo sai na ka sa aiwatar da komai, idan ka dauke zumbure-zumburen baki da na rika yi. Kila shi ya sa komai bai ce ba, ya nemi makwancinsa. Hakan kuma ba karamin kara bata min rai ya yi ba. Shi ya na yi kuka mai yawa kafin bacci ya yi awon gaba da ni.

Da safe ma haka nan nai ta ayyuka rai babu dadi, ya kuma lura da hakan sai dai sam bai tambaye ni ba, ni ma kuma na shareshi

A haka muka gama kwanakinmu biyu tare da shi, ya koma dakin gimbiyarsa.

Ranar da ya koma ɗakinta, zaune nake a gaban TV da misalin karfe biyar na yamma , Sai dai hankalina sam baya gurin TV din.

Shawarar yadda zan bullo wa matsalata nake yi.

Kila wani zai ga ba abun damuwa ba ne, amma ni gaskiya ni yana ci min rai,, kamar kashin wuya haka ya tsaya min.

Yau da yake a dakinta yake, tun 10am da ya leko ni bana jin ma ya yi 10mns masu kyau ya fita har yanzu ko keyarsa ban kara gani ba. Kila ko don ya ga ina fushi ne oho. Idan ma haka ne ai kamata ya yi ya lallashe ni, ba wai ya yi banza da ni ba.

“Mtswww!” na ja dogon tsoki, lokacin da na tuna yadda yake sintiri ɗakinta, idan har yana dakina ne to ka’ida ne ya ziyarci matarshi sau uku a rana koma fiye.

Amma ni yau sau daya na samu ya leko ni.

“Gaskiya dole in yi mishi magana tun kafin matsalar ta girmama”

Na fada a zuciyata  hade da gyara zamana. Lokaci daya kuma wayata na janyo hade da kiran Badiyya. Cikin sa a kuwa ta daga. Muka gaisa, sannan na shiga kora mata abun da ke damuna. Cikin rashin jin dadi na ce “Kawata kar ki ce na faye korafi, amma wlh auran nan ya fita a kaina. Haka auran mai mata yake ne? Daga wannan problems din sai wannan?”

Cikin salon kwantar da hankali Badiyya ta ce “Haka zaman aure ya gada Khadija, musamman mu masu abokiyar zama, don haka hakuri za ki yi, wadanda suke su kadai ma haka suke fama. Kuma na sha fada miki hakan ai.”

Cikin dacin zuciya na ce “Nawa ya zo daban Badiyya, abin da na sani Amarya mai irin kwanakina bai kamata ace ta fara fuskantar irin abin da nake fuskanta ba, kiri-kiri fa yake nuna son matarshi a gabana. Ni na ma rasa dalilin da ya sa ya auro ni”

Yanzu kam gajeruwar dariya ta yi hade da fadin “Kauna mana ta sa ya auro ki”

“Gaskiya ban yarda ba, shi dai kawai ya auro ni don ya rika bata min rai” na ba ta amsa.

Kafin ta ce wani abu na kuma na cewa “Wai kin ga matarshi kuwa Badiyya, wlh kyakkyawa, wayayya ta sha boko ta koshi, Sai kin ganta komai na ta a can-a can”

Wata dariya ta kuma yi kafin ta ce “To da ya kike son ganin ta? Wata mummuna kucaka?”

“Ni dai abin da na dauka kawai shi ne amarya dole ta fi uwargida da wasu abubuwan, kuma miji ya fi son ta. Ba haka muke karantawa a littafi ba. Uwargida mai baƙin hali, Sai a auro amarya ta kwace gida?”

Yanzu kam dariya ta yi sosai, kafin ta ce “Khadija tawa, au dama haka shi ne HASASHEN KI? to bari ki ji, rayuwar auran novel daban, ta zahiri ma daban, sau nawa za ki ga uwargida mummuna ko mai bakin hali, amma kuma mijinta sonta yake ba ya son laifin ta, sau nawa kuma uwargida ke korar amarya? Ke dai sa a dai kawai.”

Buga kofar ne ya dakatar da ni ba Badiyya amsa, na ce mata” Yi hakuri ina zuwa.” na yi maganar hade da yanke kiran.

Lokaci daya kuma shiga bedroom da sauri,    soson powder na dauka hade da shafawa  a fuskata na kara fesa turare sannan na fito.

Khalil na gani tsaye a lokacin da na bude kofar

Wani haushi gami da takaici suka tokare min wuya  duk zatona Babanshi ne.

“Momyna ce ta ce ki zo”  ya fada tun kafin in tambayeshi

Kamar ba zan ce komai ba, Sai kuma na ce na ce ‘jira ni, ina zuwa”na kai karshen maganar hade da komawa cikin daki, na dora ƙaramin farin Hijab a kan bakar rigar da ke jikina.

Hannunshi  a cikin nawa muka shiga falon hade da sallama.

Kishingide yake cikin kaya kamar na sports masu kalar light blue , wandon ya dan wuce gwiwa kadan, sai riga mai yankakken hannu.

Ita kuma gimbiyar bakin wando ne dogo har kasa, kasan wandon ya dan bude kadan, can saman wandon daidai kwankoso duwatsu ne masu kyau aka yi ma wandon kwalliya dasu.

Sai farar rigar  T- shirt mai budadden gaba. Wanda rabin kirjinta duk a waje yake.

Ko hasadun iza hasadun ba zai ce ba ta yi kyau ba. Kishin ta sosai ya kama ni,  wannan zukekiyar mace a gaban mijina, to ni me zan nuna mishi?

Don kayan sun karbeta sosai, sun fito mata da surar jikinta, musamman manyan hips nata masu daukar hankali.

Ramla na dauka hade da neman guri na zauna, bayan na gaishesu.

A zuciyata kuma cewa nake “Ko me ya sa suka kira ni?, wani lokaci sai in ga kamar da gayya suke min abubuwa”

“Dama zamu fita ne idan babu abin da kike yi” Ta yi maganar hankalinta a kaina

Na dakata da yi wa Ramla wasa “Zuwa ina?”

“Store. Kin san bikin kanen Baban Khalil sati biyu masu zuwa ne, ya kamata mu je siyayya kafin lokaci ya kure”

Kamar in ce ba zan je ba na ji, don da alama sai da suka gama tsara komai sannan aka neme ni, ni dai na zama yar kallo ko me sai dai in ji ana yi, ko in gani.

“Wai haka auran mai mata yake?” na yi tambayar a zuciyata

Amma a zahiri  sai na nuna kamar dama na san da maganar bikin, ba a bakinta ne na fara ji ba. Na ga alamar ni ma sai na fara dagewa

“Je ki shirya to, ni ma bari in shirya kafin ki fito”

“To” na fada lokacin da na mike hade da aje Ramla a kan cikin Babanta, da yake kishingide yana jin maganarmu. Kamar bai san damu ba, saboda ko sau daya bai sanya mana baki ba

Tsawon minti uku na rasa kayan da zan sanya, daga karshe dai zabina ya fada a kan doguwar rigar shadda mai ruwan toka (light ash)  ta sha aiki daga sama har kasa

Ni kaina bayan na saka rigar dana kalli kaina a madubi sai da na ba kaina maki mai yawan gaske.

Musamman daurin dankwalina ture ka  ga tsiya da ya zauna das a kan goshina, jelar kitsona daya na zaro na saketa a kan dogon wuyana

Na dora sarkata ash mai tafe da agogo da zobe, farin mayafi da takalmi na yi amfani dasu, sai farar karamar jaka mai doguwar igiya.

Humrah kawai na shafa, na nufi bangaren Maman Khalil

Ita ma cikin riga da siket take na Lace mai kalar coffee, ta nada daurin dankwali na zamani, wuyanta, sanye da wata tafkekiyar sarka mai hade da yan hannu da zobuna.

Gaskiya ta yi kyau, sai na ga ma kamar ta fi ni, kasancewar ita kayan sun fitar mata da dirinta sosai.

Ni kuwa a sama ne kawai rigar ta dan kama ni.

Hotuna yake mata, wani ita da Ramla da yaran, wani kuma ita kadai.

Ganina ne ya sanya shi juyowa yana fadin

“Wow! Wow!! Wow!!!  Wannan amaryar tawa ta yi kyau Maman Khalil, ba ta taba yin kyau ma irin na yau ba, kalleta ki gani”

Juyowa ta yi tana dariya sosai, babu alamar damuwa a kan fuskarta ta ce,

“Lallai Abban  Khalil, wallahi ka yi na kudinka. Wato ba ta taba kyau ba irin na yau, me kake nufi to?”

“Nufina ba kwa kwalliya sai zaku fita”

“Kenan duk kwalliyar da nake a baya ba kwalliya ba ce, kuma ban yi kyau ba, haka nan yake cewa na yi kyau” zancen zuci daga gare ni kenan, a, zahiri kuma yaƙe nake yi, gani nake kamar ya ci kin fuska a gabanta

Ita kuma Ido ta zaro hade da kallona kafin ta ce

“Kin ji me ya fada kuwa?”

Ban yi magana ba illa murmushi kawai da na yi.

“Kana nufin har ni?” ta tambayeshi cikin sigar shagwaba

“Ban da ke” Ya yi maganar da muryar rada.

Tuni kishi ya kasheni a inda nake zaune.

Dalilin da ya sa kenan na Mike tare da nufar kofa.

“Ina kuma za ki je?” Ya yi saurin dakatar da ni

“Guri zan ba ku, ku yi soyayyarku da kyau” Na yi maganar a zuciyata

Amma a zahiri tsayawa na yi ina kallonshi

Da alama ya harbo jirgina, don haka sai ya share yana fadin “Zo in yi maku hoto mana kafin ku tafi”

Ban yi gardama ba, na je ya yi ta mana hoton kala-kala wani da yara, wani ni da ita, wani kuma ni kadai.

“Alhamdulillahi! Allah na gode maka da ka ba ni ahli kyawawa masu lafiya” Haka yake ta fada a lokacin  da yake mana hoton.

Ni ce na dauki Ramla lokacin da zamu fita, kuma har a cikin store din ni ce nake rike da ita.

Yayin da Sakeena ke zabar kaya masu kyau da tsada

Lace kala biyu, shadda biyu sai atamfa kala daya.

Gyale kala biyu, hijab daya sai takalma da sarkoki, dukkansu iri daya ne.

Sannan ta koma bangaren kayan yara, nan ma ta zabi masu kyau da tsada.

A ka yi total ta biya, sannan aka rako mu dasu har mota.

Ni dai mamaki nake yi hade da tambayar kaina “Dama haka ake yi ne? Kudin ma ba za a ba ni nawa ba in sayi abun da nake so sai dai a ba wata, ya suke son mayar da ni kamar wacce ba ta da ra’ayi ne?”

Har muka isa gida magana kawai nake, amma hankalina baya tare da ni, ni ma so nake  ya zama ina cin gashin kaina, bawai gashin wata ba, ya kamata kuma in magantu a kan hakan.

Muna isa gida bangarena na wuce, ko kyalle ban dauka ba, kuma ban tayata shigarwa ba, tun da dai ta ce ta ji ta gani, ai shigarwar ma ba zai gagareta ba.

Wanshekare misalin bakwai da rabi na ji buga kofa.

Ita ce na gani tsaye da ledar kayan da muka siyo jiya.

“Zan tafi gurin aiki ne, na yi magana da tela zai zo ya karbi kayan nan ya dinka, sai ki ba shi measurements naki.”

“OK.” Na fada hade da amasar kayan, lokaci guda kuma ina gaisheta.

 Wata leda ta miko min “Ga sauran kayanki nan”

“OK to na gode”

Ta kuma zuge karamar jakar da ke hannunta, kudi ta zaro hade da kirgawa.

“Yauwa! Wannan ragowar canjinki ne  na siyayyar da muka yi jiya”

Na kuma sanya hannu na karba, tare da fadin “na gode”

Aje kayan na yi hade da kara bude su ina kallonsu daya bayan daya, sun yi kyau kam sosai musamman lace din, ta iya zabe.

Kudin da ta ba ni ne na kirga, dubu tara da dari da hamsin.

Wani lokaci na kan rasa kan matar nan, kamar dai tana zaune da ni tsakaninta da Allah da  kuma zuciya daya. Wani lokaci kuma in ga kamar munafurci ne irin na mata.

Koma dai menene na kusa fashe kwan in ga zahirinshi.

<< Hasashena 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×