Skip to content
Part 40 of 42 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Asabar da yamma Affan ya wanke musu uniform tas ya shanya a backyard.

Bayan sun dawo sallahr asuba Khaleel ya zagaya don dakko na Assidiq ya goge, saboda dukkansu 2set gare su, kuma na Assidiq duk biyun sun baci, saboda sharar da Sarai ta watsa mishi jiya.

Kamar 5mns ya same ni kitchen, wai bai ga uniform din ba.

Ba tare da na kawo komai ba, na ce “tambayi Affan ko ya kwashe”

Ya juya zuwa kofar fita, kamar 3mns ya dawo ya ce min “Ya ce bai kwashe ba”

Na dakata da jera musu yamball din da nake yi a cikin lunch box na ce “To ko Maama ta kwashe ne, ka san halin ta da iya kwashe shanya ko basu bushe ba”

“Ita ma ta ce ba ta kwashe ba”

Yanzu kam mikewa tsaye na yi ina fadin “Mu je backyard din Khalil in gani”

Muka zagaya amma igiya fayau ba komai, cike da mamaki nake kallon Khalil, kafin na daga kai zuwa doguwar katangar gidan, wacce ke zagaye da waya kafin na ce “Khalil to ko ɓarawo ne dai ya shigo gidan”

Ya ce min “Amma Auntynmu ya rasa abun dauka sai uniform, me zai yi da su?”

Ji na yi maganar ta kama hankalina na ce “Kuma fa haka ne. To ko iska ce ta kwashe su?”

Yanzu kam da mamaki yake kallo na, kafin ya ce “To ta kai su ina?”

Na ce “baya mana, zagaya ka gani ko suna can”

Dariya ya yi kafin ya ce “Kai Auntynmu”

“Ni dai zagaya ka gani” ya juya zuwa hanyar da za ta fitar da shi yana dariya.

S bayan shi na bi,  tsaye na yi a tsakar gida har ya dawo, hannu babu komai

“Ba ka gansu ba?” na yi saurin tambaya

Cikin dariya ya ce “to wai dama ya za a yi a gan su”

Muka juya a tare, zuciyata cike da mamakin inda kayan suka shiga, wannan abu akwai mamaki.

A falo muka ci karo da Affan hannunshi rike da na Assidiq, an sanya mishi boxer da vest.

“Ka goge uniform din?” Cewar Affan yana kallon Khaleel

Da dariya a muryar Khalil ya ce “Sun bace”

Mamaki ya bayyana a fuskar Affan ya ce “Kamar ya?”

Yanzu kam Khalil dariya yake yi sosai yana kallon yadda na yi sororo sannan ya ce “Wlh ba a gan su ba”

Ya juya da kallon shi kaina alamun son karin bayani, kafin ya ce “Wai haka Auntynmu?”

Komai ban ce ba na wuce kitchen, na ci gaba da hada musu abin da za su tafi da shi makaranta. Zuciyata cike da mamakin abin da yake faruwa.

Sai ga su dukkansu cikin kitchen din, Affan ya ce “Kenan Assidiq ba zai je makaranta ba?”

Ba tare da na dago kai ba na ce “Eh. To da me zai je, ba a ga uniform din Shi ba”

Assidiq ya fadi kasa ya shiga kuka jin an ce ba zai je school ba.

Affan ya daga shi dakyar yana lallashinshi kafin ya ce “to ko muma mu fasa zuwa ne?”

Kai na girgiza alamar a’a, kafin na ce “ku tafi abin ku, an jima kadan zan je kasuwa in sawo wani yadin sai a kara dinka muku, wanda ya dauka kuma don kanshi”

Daidai lokacin Maama ta shigo, sanye cikin nata uniform din ta ce “Auntynmu uniform din fa suna wurin waccan matar, ita ce ta kwashe mana”

Mu duka muka kalli Maama, sai kuma suka dawo da kallon su kaina, suka kuma juyawa kan Maama, Khalil ya ce”aje a karbo? “

Kai na girgiza alamar a’a, Affan ya ce” To kyale mata za a yi, me za ta yi dasu? “

Na ce” Kawai don Maama ta fadi abu sai ku yarda, me ya sa za ta kwashe muku uniform Affan? Think very well “

Ya dan yi shiru, kafin Khalil ya ce” Maama ba za ta yi karya ba Auntynmu, tun da ta ce ta ga uniform din a wurin ta, to da gaske take yi, ta gan su”

 Maama ta yi caraf ta ce “Wlh Auntynmu na gani a wurin ta har ta yi min haka (sai ta juya idanunta alamun hara. Abin da duk ya sanya mu dariya mu dukkanmu)”

Affan ya ce “You see, da gaske ta ganta Auntynmu, bari in je in karbo”

“kar ka je Affan!” na yi saurin dakatar da shi

Duk suka zuba min ido, ni kuma na fito rike da basket din su Ina fadin “Ku zo ku karya”

Rai bace Khalil ya ce “Shi kenan yanzu ba zai je makarantar ba.”

Na juyo ina dan hade fuska sannan na ce “It’s OK Khalil, ba na son kara jin wannan maganar. Makarantar ai yau ne kawai ba zai je ba, na ce an jima zan shiga in yanko mishi wani yadin”

“To yanzu da ba ki da kudin fa?” cewar Affan

Na ce “Alhamdulillah, Allah Ya sa ina da su,  so please discard everything”

Duk suka yi shiru, amma ba don ransu ya so ba, shi ya sa ko abincin kirki basu ci ba. Suka tafi school din rai bace, yayin da Assidiq ke ta min rigima. Kuma dama na san za a yi haka.

Around 10am, na gama kintsa part dina tsaf, na shirya Assidiq muka fita zuwa gidan Maman Aiman, saboda a can nake son ajiye shi. Kamar in yi wa Saratu magana a kan na fita, Sai kuma na fasa, na fice abu na. Duk da na kira Bashir ban samu ba, hakan bai hana ni fitar b, tun da idan abu emergency ne ya yarje a fita.

Baki bude Maman Aiman take kallon mu alamun mamaki, a lokacin da ta bude mana gate Kafin ta ce “Ba shi da lafiya ne bai je school ba?”

Na kara sa shiga cikin gidan sosai kafin na ce “Uniform din Shi ya ne ya bace”

“Ban gane ba, kamar ya?” ta yi saurin tara ta

“To! Jiya dai yayanshi ya wanke su, ya shanya su a backyard, da asubar nan ba mu gani ba, na kuma sanya Khalil ya zagaya baya, ko iska ta kwashe amma bai gansu ba”

Wani kallo Maman Aiman ke min kafin ta ce “Wace irin iska ce za ta kwashe uniform gabadaya kamar an Aiko ta?”

“To ikon ya fi da haka Maman Aiman” na ba ta amsa cike da sarewa

Baki ta tabe kafin ta ce “To yanzu ina za ki je da safe?”

Goyon Haidar na gyara kafin na ce “Assidiq zai zauna nan, ni kuma zan je kasuwa in yanko musu wasu sabbin uniform din”

Komai ba ta ce ba, da alama ta gama cika da haushi, Sai da na juya da zummar fita ta ce min “Allah Ya kiyaye hanya, a dawo lafiya”

Na amsa da amin.

Bayan na yanki uniform din, wajen tellansu na wuce na ba shi, sannan na jaddada mishi ko bai din na sauran yau ba, to ya dinka na Assidiq.

Sai 12 na dawo gida, maimakon in shiga gidan Maman Aiman kai tsaye sai na nufi kofar gidana. Niyyata in je in yi blending kayan miya in dora, in ya so sai in dawo in tafi da Assidiq, koda na zauna dai, na san na rage aiki.

Hannu na saka hade da zare sakatar kasa, sannan na tura, na ji kofa gam.

Take gabana ya fadi, saboda na san Saratu ba za ta bude min ba, to shi kenan ni kuma ba damar in fita lokacin da nake in dawo lokacin da nake so?

Na shiga bubbuga kofar amma ba ta bude ba, har aka fara kiran sallahr azhur, masu kira 12:35pm ina tsaye a kofar, kuma ba ta bude min ba.

Duk yadda nake kokarin hana kaina jin zafin abun, na kasa yin hakan, don haka zuciyata wani daci take yi, ga takaicin safe ban gama da shi ba, an kara min na rana.

Haka na juya zuwa gidan Maman Aiman zuciyata babu dadi, time da na shiga Assidiq bacci yake, ita kuma tana hidimar abincin rana.

Yadda ta ganni ne ya sa ta ce “Me ya faru, ko ba ki samu kalar uniform din ba ne?”

Kai na girgiza alamar a’a, hade da zama saman kujera, ina sauke ajiyar zuciya.

“,Me ya faru wai? Ko kin yada kudin ne?”

Na kuma girgiza kai alamar a’a

“To menene?” ta yi tambayar cike da zaƙuwa

“Ta rufe kofar, tun dazu na dawo, na yi ta bugawa ba ta bude ba” na yi maganar raina yana kara baci

Shiru Maman Aiman ta yi kafin ta ce “Kai! Subhnallah! To yanzu ya za a yi? Kin san yanzu ba kowa ne, zai yarda ya dira ya bude miki ba, duba da abun da ya faru”

Hijab din jikina na zare, saboda ji nake kamar na lulluba duniya, kafin na ce “Bari in huta in kara zuwa in buga ko za ta bude”

Har 1:30pm ina gidan Maman Aiman, tana ta kara ba ni hak’uri, Sai da na yi sallah, kafin na dauki Haidar, muka fita tare da ita zuwa kofar gidan, saboda har zuwa lokacin Assidiq bacci yake yi.

Sama da 30mns,muna buga kofar amma ba ta bude ba, zuwa lokacin raina ya kai kololuwa wurin baci, Saratu ta raina ni sosai, kila sai na fara mayar da martani sannan.

Wayata na ciro cikin jaka ta, na kira Bashir, bayan mun gaisa na ce “Ka kira matarka ta bude min kofa, sama da awa biyu ina kofar gida ina bugawa amma ba ta bude min ba”

“Ke ina kika je?” ya tambaye ni

A hankali na ce “Na je kasuwa ne, yankowa su Khalil uniform”

“Wane irin uniform Kuma, me ya samu nasu?”

Na kuma cewa “Jiya Affan ya wanke su ya shanya, yau kuma bamu gani ba”

Da alamun mamaki a muryarshi yace “Gidan nawa boarding school ya zama da za a wanke uniform su ɓata”

Shiru na yi, komai ban ce ba, shi ma sai ya yanke kiran. After like 3mns Saratu ta bude min gate, Har da wani yamutse fuska irin daga baccin nan ta tashi.

Ni kam na wuce ta fuuuu, ko sallama ban yi wa Maman Aiman ba.

Rai babu dadi na shiga kitchen, haka na kasance har su Khalil suka dawo, can misalin karfe takwas kuma sai ga mai dinki, ya kawo min.

Safe dukkansu suka shirya zuwa makaranta, misalin 10am,Maman Aiman ta shigo, nan muka shantake hira, har wajen 12pm kafin ta mike don tafiya gida, sai dai me, babu takalminta guda daya sai daya.

Mu ka shiga nema, kitchen, garden, backyard, neman Kamar zamu daga interlock, amma ba mu ga takalmin ba.

Kofar Sarai na nufa hade da kwankwasawa, ta gama yangarta ta bude min, “Don Allah ko kin ga takalmin Maman Aiman guda daya?” na karasa maganar ina daga mata dayan takalmin da yake hannuna, na kara da fadin “Irin wannan nan ne?”

Kallo ta kare mana ni da takalmin kafin ta ce “Ni maigadi ce?”

Ban amsa mata tambayarta ba, ta ce “To ban gani ba. Ina ruwana da wani takalmin bakuwarki, ko bakuwar ma ba ruwana da ita bare takalminta. Ke kanki ma ina ruwana da ke” kai karshen maganar tata ya yi daidai da horn din Baban Khaleel, ni da ita muka zubawa gate din ido, har ya bude ya shigo.

Kawai yarinyar nan  ta kwala kuka tana fadin “Gara da Allah Ya kawo ka, satar takalmi suka makalama min, ni me zan yi da takalminsu daya…” ta ci gaba da kuka

Ba ni kadai ce na aje poster ba, har da shi kanshi Bashir din, Maman Aiman kam ta samu ta saɓe, ko dayan takalminta ba ta saurara ba

Sarai ta ci gaba da kara sautin kukanta tana fadin” Me zan yi da ɗayan takalmi don Allah, in rasa abun dauka sai silifas, kuma guda daya”

Ya karaso inda muke tsaye, idanunshi a kaina kafin ya ce “Me ya faru?”

Na rasa abin da zan ce, Sai kawai na juya zuwa bangarena, hannuna rike da takalmin Maman Aiman guda daya.

Sarai kuma ta ci gaba da kuka yana ba ta hak’uri, ita kuma tana nuna irin zafin da take ji, na dora mata satar da mu ka yi.

Tsaye na yi jikin window, ina, kallon yadda yake kokarin kira a wayar shi, addu’ata kar ya kira Ummata, ya fi min ya kira Innar Ruma, sabanin haka sai na ji yana cewa “Eh, dama na san ba ka gida shi ya sa na kira”

Ban san abin da aka fada ba a can bangaren na ji ya kuma cewa “Wato kwanaki can baya, na gargadi iyalinka a kan shigowa gidana saboda abubuwan da suke faruwa sakamakon shigowar tata, amma ba ta bari ba, yanzu ta zo gidana, abun babu dadi, wai matata ta dauke mata takalmi daya” ya yi shiru da alama magana ake yi a daya bangaren.

Ya dora da “To ka gani. Shi ya sa na kira ka, idan ba ka sani ba yau ka sani, ina jin kunyar ka”

Ya kuma yin shiru, can kuma ya ce “Babu komai, na gode da ka fahimta”

Sauke wayar tashi, ta yi daidai da zamana saman kujera jabar, kamar an zare min kashi an bar min tsoka.

Tausayin Maman Aiman ya kama ni, mijinta yana da zafi sosai, Allah kadai ya san tijarar da zai yi mata yau ba a kan laifin ta ba. Maman Aiman ba ta taba zuga ni ko sau daya ba a kan Saratu, kullum sai dai ta ce in yi hakuri, yanzu ga shi na jawo mata tijara da ɓacin rai.

Daidai lokacin ya shigo cikin falo a rai bace yana jefa kafar shi.

<< Hasashena 39Hasashena 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×