“Wato Khadija ni ban isa ki yi min abin da nake so ba ko? Kin rantse dai sai kin bata min gida ko? Ke ce babba amma kina abu kamar ke ce yarinyar? Kullum kina kirkiro min fitina. Me Nana za ta yi da warin takalmi silifas? Kuma sau nawa ina fada miki ba na son kowa yana shigowa gidana? Wato na fada ya shiga ta nan, ya, kuma fita ta nan (ya yi maganar hade da nuna min kunnuwanshi guda biyu) “
Shiru na yi ko motsi ban yi ba, ya kuma ɗorawa daga dawowa ta ko hutawa ban yi zan fara da bacin rai, to kun kyauta, haka, ake so.
Amma ki saurare ni da kyau ki ji, ina daga miki kafa ne don yaran nan, amma zan rufe idona muddin ba ki daina tada min fitina ba. Wlh ba zan daina kukan mutuwar Sakeena ba, na yi rashin mata ta kwarai. “
” Sai ka tafi lahirar ai ka dawo da ita”na fada cike da takaicin da yake damuna.
Takowa ya kuma yi kusa da kafin ya ce ” Abin da kika fi kwarewa a kai kenan rashin kunya, kuma kin san da ana dawo da mutum da na yi hakan, ba sai kin fada min ba zan yi. Mara kunya kawai, ina fada kina fada, ita wacce kuka raina din kuna ce mata yar kauye ba ta daga muryarta a kan tawa, Sai ke, wai sunan kin yi karatu, kuma yar gari, amma gara ya kauyen da ke.” ya, kai karshen maganar yana ficewa daga falon.
Idanuna na runtse kam, ina son hawaye su zubo, da karfin tsiya na rika matso su, statement din Shi na karshe na kara kartar min zuciya, ringing din wayata ya sanya ni bude idanuna, ganin Maman Aiman ce sai na daga, cikin kuka ta ce “Maman Maama kin san abin da ya faru kuwa? Maigidanki ya kira Baban Aiman wai ina shiga gidanshi ina hada fitina, kin san dai halin Baban Aiman, tijara babu irin wacce bai yi min ba, har da ce min shaidadiya” ta karasa maganar cikin kuka.
Ni ma cikin kukan na ce “ki yi hak’uri Maaman Aiman ni ce na jawo miki, Allah Ya sani ba ki taba zuga ni in yi wani abu ba daidai ba, ga shi na janyo miki bacin rai don Allah ki yi hak’uri”
Cikin kuka ta ce “Na san ba laifinki ba ne, na yi hak’uri, kuma ya ce idan na kara shigowa gidanki Allah Ya isa”
Hawayena na dauke kafin na ce “Zaman auran nan ya ishe ni Maman Aiman, musamman yau din nan, yarinyar nan tun da ta shigo ban huta ba, ni ban sa ba da irin wannan makircin ba. Zuciyata na fada min kawai in yi tafiya ta”
“Ki tafi ina!” ta yi saurin tara ta, kafin in yi magana ta ce “ki tafi ki bar mata yaranki, kenan ta kore ki, ta samu, abun da take?”
Sabbin hawaye suka zubo min, kafin na ce “to ya zan yi? Ni na gaji.”
Ta ce “Ki yi hak’uri don Allah! Kar ki tafi Khadija, ki kara hakuri”
Kawai sai na yanke wayar hade da rushewa da kuka. Wani irin kunci nake ji, a duk lokacin da na tuna da statement din Bashir na karshe.
Ban yi aune ba sai ga kiran sallahr azhur, haka na tashi na yi sallah sannan na shiga kitchen, ina girki ina kuka, har na gama na watsa ruwa hade da yin sallahr la’asar, na kwanta kan sallahyar hawaye na zirarar min, duk lokacin da na tuna ” abin da kika fi iya wa kenan rashin kunya… Da kuma sunan wai kin yi karatu, wacce ba ta yi karatun ba, kuma take kauyen ma ta fi ki…” sai in ji sabbin hawaye na kara sakko min.
Dakyar na yunkura na tashi, saboda jin ana buga min kofa, na rika sakkowa saman steps din kamar maijego sabuwar haihuwar da aka yi wa dinki, Sai da na goge fuskanta sannan na bude kofar. Sarai ce tsaye, hannunta rike da ledoji guda biyu, ta ce “Tsarabarki ce ke da yara” ta yi maganar babu yabo fallasa.
Komai ban ce mata ba, na mayar da kofata na rufe.
A ka’ida ba dakinta yake ba, kwananshi daya a dakina ya tafi Ruma, a ka’ida kuma namiji baya jefar da kwana.
Cikin falon na zauna, in yi kuka in kuma rarrashi kaina haka na yi ta yi har su Khaleel suka dawo.
Na yi ta kokarin boye damuwata don kar su gani, amma sai da Affan ya ce “Auntynmu lafiya?”
Cike da basarwa na ce “Me ka gani?”
“Na ganki da alamun damuwa” Khaleel ya cafe da fadin “Ina son tambaya ka riga ni”
“Kaina ke ciwo, dakyar na yi muku abinci ma” na yi musu karya
Duk sai jikinsu ya weak, suka shiga yi min sannu, ni kuma ina amsawa har sai da suka tafi masallaci.
Abinci dai ban iya ci ba a wannan ranar, kuma tun daga sallar isha’i ban sakko kasa ba, Khalil kuma ya hana su Maama su zo wurina.
Ina kwance lamo zuciyata na zafi Bashir ya shigo, ko dago kai ban yi ba, bare ya sanya ran zan kalle shi, na dai amsa mishi sallamarshi a ciki. Ya yi tsaye a kaina kafin ya ce “me kika ce da aka kawo miki tsaraba?” na yi shiru abu na. Ya kuma maimaita tambayar a karo na biyu, na kuma yin shiru, da ya kara maimaita a karo na uku, Sai na juya bayana, ba tare da na ce komai ba. Hannu ya sanya hade da birkitoni kafin ya ce “Khadija kada ki kure hak’urina fa” kwace kaina na yi, sannan na ce “Don Allah ka fitar min daki, duk abin da matarka ta fada ma shi na fada. Ai da maganarta kake amfani ko?”
Idanu ya zuba min yana kallon yadda nake ta huci, ba tare da ya kara cewa komai ba ya fita.
Ciwon kan da nake kirawa kaina, da shi na tashi kuwa, na yi sallahr dakyar kafin na shiga kitchen, su Khaleel kuma suka shiga shirin makaranta around 7:30am suka fice, na dakko wayata na hau WhatsApp hankalina na kan Maman Aiman, na san halin mijinta sosai, sallama na yi mata, Sai ko ta amsa min na ce “Ya ya ina fatan babu matsala?”
Sai da ta ajiye emojin dariya kafin ta ce “Ai ya sakko, na yi mishi bayani, kuma ya fahimta, ya ce dai kar in kara shiga gidan”
A fili na sauke ajiyar zuciya sannan na ce “Alhamdulillah. Gaskiya na ji dadi, sosai da abun na yi bacci”
Ta kuma aje emojin dariya sannan ta ce “Alhamdulillah komai ya wuce” muka ci gaba da tattauna matsalar har 10am,sannan na yi break hade da shan magani, na dan kwanta don in yi dan rage nauyin idanuna
Bayan na tashi kuma na shiga kitchen.
Ranar Talata Bashir ya dawo dakina, babu mai tankawa kowa, ga shi bikin Uwani Friday ne kuma Ina son zuwa.
Ranar Laraba da dare na tura mishi sako a kan ina son zuwa.
Sai safiyar Alhamis ya turo min da sako kamar haka _”Ban amince ba_”
Na jima ina kallon screen din wayar kafin na dauke idanuna. A WhatsApp na fadawa Maman Aiman, ta ce in sanarwa da Uwanin kawai.
Ina sauka WhatsApp na kira Uwani hade da shaida mata abin da ya faru, ta ce babu damuwa, sosai ta fahimce ni, sannan na kara da rokonta a kan ta yi squeezing ta zo.
Sai ko ga ta da bayan magriba, ta sha kunshi da gyaran kai ta yi fes, kamar ba ita ba.
Bayan mun gaisa na kuma tsokane ta, sannan na dakko turarurruka na jiki da na daki na ba ta, hade da 20k gudunmuwata. Ta yi ta godiya kamar na ba ta duniya, har gate na yi mata rakiya ta tafi.
A ranar Bashir ya koma ɗakin Sarai, har zuwa lokacin kuma bamu shirya ba.
Juma’a da yamma kasancewar babu makaranta, su Affan ne ke wasan ball a tsakar gida, amma na bangarena. Ni kuma ina falo ina hada turaren wuta, Sarai kuma na entrance din ta zaune tana kallon su.
Haka nan jikina bai ba ni ba, shi ya sa lokaci zuwa lokaci nake daga labulena, in leka su, har dai aikina ya dauke min hankali daga kansu.
Assidiq ne ya shigo da gudu, ya ce “Auntynmu, ana fada da Ya Affan da waccan matar(haka suke kiran ta, ni kuma ban taba hana su ba)” na mike da sauri ina dora Haidar saman kujera saboda kada ya yi min barna, sannan na fice. Sai ko na same su ita da Affan suna ta kokawa, so take ta kwace kwallon da ke hannunshi amma ya hana, Sai ma ya jefawa Khalil ita, yayin da kokawar ta koma babu ball, duk da kasancewarshi yaro sai neman kada ta yake, ga kuma naushin da yake kai mata. Da kyar na janye shi gefe ina hakki, saboda ni din ma na ci wuya, kamar da ni ake fadan.
Na kalli Khalil tare da fadin “Menene ya faru?”
“Ita ce muna ball din mu ta dauke mana, wai za ta yanka mana”
Na juya bangaren Sarai da take ta mayar da numfashi sannan na ce “Me ya sa za ki yanka musu ball”
Sai cewa ta yi wai buge ta suka yi. Yaran suka hau rantsuwa a kan Ball din ko kan entrance nata ba ta hau ba.
Na juya kanta ina fadin “Idan haka ne gaskiya ba ki kyauta ba, sannan kin zubar da girman ki, yanzu Affan ne abokin kokawar ki Sarai?”
Cikin masifa ta ce “Dama ai na san bayansu za ki goya, kuma duk dan’iskan yaron da ya kara bugo min kwallo sai na ci ubanshi, kuma na yanka ta, dan’iska haihuwar asara”
Na yi saurin cewa “To ya ishe ki haka, daina aibata min yara, duk cikinsu babu dan’iska, kuma gida gidan ubansu ne, ke ba ki isa ki hana su yin yadda suka ga dama ba wlh.”
Ta ce “Na isa, kuma za ki gani, wlh, Sai yaran nan sun daina buga ball a cikin gidan nan”
Ni ma na yi caraf na ce “To za mu gani, ni da ke waye da gidan, amma yanzu suka fara buga ball wlh”
Ta juya kan Affan cikin bala’i ta ce “Wlh sai na ci uwarka kai kuma, dukkanku sai na ci uwarku, za ku san da ni kuke labari”
“Kar ki kara zaginsu!” na yi mata maganar da alamar warning
Ta ce “An zaga, na ce duk kutu**r ubansu…” ta shiga mulmulo ashar tana ajiyewa, Sai kawai na kama hannun yarana na shige daki na kyale ta, tana ta ruwan bala’i, kai Allah Ya hadamu da yar tujara.
Komai ban ce ma yara ba, ban san me ya sa ko suke da laifi tsakaninsu da Sarai ba na yi musu fada ba, kila ko don na tsane ta ne oho.
Su Khalil na shirin tafiya masallacin magriba sai ga Bashir, yana wurga kafar nan, fuska cike da masifa, komai bai ce min ba ya nufi ɗakinsu Affan, da sauri na bi bayan shi, don haka tare muka isa, ya kai hannu hade da fisgo Affan, ya cire hannu da niyyar zabga mishi mari, na rike hannun gam, ina fadin “Wlh ba za ka doke shi ba, Sai ya yi amfani da dayar kafar shi mai lafiyar ya kai mishi hauri, cikin sa a kuma ya same shi. Sai na sake hannun na shi daya na tura Affan waje, ina fadin” Ku wuce masallacinku”
Fisgoni ya yi da karfi, don har sai da na fada jikinshi, sannan ya dago ni lokaci daya kuma hannunshi ya nufi kuncina, na yi saurin rike wa cike da mamaki na ce “Bashir dukana za ka yi?”
Ya ce “Kin fi karfin dukan ne, ni za ki wulakanta, ku taru ku dokar min mata, am ba ni amana kullum kina cikin gallaza mata”
Ba tare da na saki hannun ba na ce “Ita ce ta ce ma mun yi mata duka? To mun yi mata, kuma mun doki banza wlh. Babu wanda ya isa ya rama mata wannan dukan. Ya ishe ni haka Bashir, tun da yarinyar nan ta shigo gidan nan daga ni har yaran nan hankalinmu ba kwance ba, yau ta ce wannan gobe ta ce wannan. To bari ka ji, su Khaleel nan gidansu ne, gidan ubansu ne, dole kuma su sake. Har yanzu ba a haifi wacce za ta hana yaran nan yin rawar gaban hantsi a gidan ubansu ba” na kai karshen maganar hade da sake hannun na shi, na nufi kofar fita.
Da sauri ya maido ni, kafin ya ce “Bari in tuna miki wani abu, Khalil da Affan ƴaƴana ne, ba ke ce kika haifa min su ba, lokacin da na haife su ma ba ki sani ba. To daga yanzu na kwace su daga hannun ki, na sake su a tsakar gida, su din na kowa ne, ba za ki bata min tarbiyyar yara ba”
Wani abu mai daci ya tsaya min wuya kamar ba zan ba shi amsa ba, Sai kuma na ce “Dadin abun na haifa, don haka ba za ka yi min gori ba…”
Ya yi saurin tara ta da “Amma ke ai kin iya yi ma wani ko”
Na ce “Wanda na yi ma wa ya zo ya rama da kanshi, ba kai ne za ka rama mishi ba”
Haka muka rika fadi-fada kowa zuciyarshi na kara baci, ban san ko sau nawa ya yi attempting na buguna ina kaucewa ba, sannan ya fice.