Tun daga wannan lokacin zaman gidan ya kara rashin dadi, abu kyas sai bala’i, ba Bashir din ba, ba ni ba, bare kuma Sarai da take kamar karya. Kadan za ta kama haushi.
Kuma bai kara kwana a dakina ba sai a dakin ta, ni kuma na zuba mishi ido, ko ta kanshi ban bi, ita kuma sai kauɗi da habaici miji na kwana a dakinta baya kwana a nawa. Har ranar Juma’a da ta kama sati daya.
Da yamma bayan su Khalil sun dawo masallaci sallahr la’asar suka fito da ball, kuma ni ban hana su ba. Ita ma oganiyyar sai ta fito ta zauna, tana jiran masifa.
Can kam na ji bala’i ya tashi, wai ashe da wuka ta fito don neman masifa, kwallon na yo wa wajen ta, ta soke ta da wuka.
Lokacin da na fito kwallon na hannunta, yaran kuma na tsaye suna kallon yadda ta sanya hannu a cikin inda ta yankan tana kara yagawa.
Ina isowa na fisge kwallon, hade da dauke da mari, kafin ta dawo cikin hankalinta na kuma dauke ta da wani marin.
Ba zato ta kawo min yanka da wukar da ke hannunta, na yi saurin kaucewa dalilin da ya sa ta samu kirjina, Sai dai na ji tayau, don ma yankan bai shiga ba wata farar tsoka ta fito.
Ta kuma kawo min wani yankan na goce, Sai mu ka hau kokawa, cikin minti daya na kai ta kasa, na kuma fisge wukar da karfi tsiya na yi jifa da ita. Khalil ya dauke ta da sauri, ni kuma na ci gaba da jibgarta, Sai da na tabbatar ta jibgu sannan na daga ta, tana mikewa ta shig aiko min da zagi na rashin mutunci har da jifa. Ko a jikina, na wuce dakina.
Bayan shiga ta daki saman kujera na zauna ina mayar da numfashi, jin abun nake yi kamar mafarki, amma kuma zuciyata ta dan yi sanyi, saboda yau dai bugun ƴa da Uwa na yi wa Sarai.
Affan ya kai hannu kan kirjina inda jini ke tsattsafowa ya ce “Auntynmu jini na fitowa fa, ki zo mu je Chemist” kai na shiga girgizawa alamar a’a, kafin in yi magana na ji horn da bude kofar gate, ba Sai an fada min ba, na san Sarai ce ta kira Bashir ta kuma fada mishi karya da gaskiya.
Sai ko ga shi ya shigo ɗakin hannunshi cikin nata, yana janta kamar ya siyo akuya.
Burki ya ci gabana, sannan ya ce “Khadija! kalli fuskar Sarai fa, amana fa iyayenta suka ba ni, shi ne za ki yi mata wannan bugun haka”
Na mike hade da nuna mishi kirjina na ce “Ni ba uwa ce ta haife ni ba? Ko daga sama na fado? Ashe saboda ita din amana ce a wurin ka, Sai kuma in zauna ta kashe ni, kalli fa inda ta yanke ni da wuka”
Da alama jikinshi ya yi sanyi, saboda kallon na shi ya mayar kan Sarai sannan ya ce “Da gaske ke ce kika yanke ta haka?”
Cikin kukan munafurci ta ce “Ni ban gani ba, saboda da kokawa ta kama ni, kuma dama wukar na hannuna…”
“Ba wani wlh, ita ce ta fito da wuka ta yanka mana ball, sannan kuma ta yanke Auntynmu” cewar Affan
Sai ko Bashir ya dauke shi da mari, marin da ya sanya shi faduwa saman kujera sumamme.
Da sauri ni da Khalil muka nufi inda ya fadi din, na shiga girgiza shi, amma babu alamar numfashi a tare da shi.
A firgice na mike tsaye ina kallon Bashir kafin na ce “Ba dai mutuwa ya yi ba? Wayyyo Allahna!” na fada cike da tashin hankali, kafin na kara komawa kan Affan, na kuma girgiza shi, amma shiru.
Na juya da zummar kara yi ma Bashir magana, na ga fito daga kitchen hannun shi rike da gorar ruwa.
Ni kuma caraf na rike Sarai na shiga jibgarta ta ko ina, ina ihun ta sanya an kashe min yaro. Ita ma ta shiga ramawa.
Bashir na isowa ya shiga watsawa Affan ruwan, ba tare da ya bi ta kanmu ba, after some minutes ya ja dogon numfashi hade da bude ido. Sai ya sake gorar ya dawo kanmu. Ni ya fara fisgewa daga shakar da na yi wa Sarai, sannan ya janye hannun Saran suka fice, tana ta aiko min da manyan ashar da muguwar fata
Wurin Affan na isa, lokaci daya kuma ina dauke hawayen da ke zubo min, a zuciyata na ce “Ya Allah idan ka kaddarawa Bashir auran Sarai ne don in gane kuskuren Hasashena wlh na gane, Allah ka yafe min, ka kawo min karshen wannan bala’i”
Na shiga shafa Affan ina tambayarshi ko akwai abin da yake ji
Cikin kuka ya ce “Auntynmu kunnena daya ba na ji”
Kwakkwalo ido na yi na ce “Da gaske?”
Cikin wani kukan ya ce “Eh, wani dummm nake ji”
Da sauri na mikar da shi zaune, hade d kanga bakina saitin kunnen shi da ya ce baya ji din na dan hura. Sai ya yi maza ya janye kunnen yana fadin “Akwai zafi”
Ido na zuba mishi cike da damuwa sannan na ce “mu jira zuwa gobe kila ya warware, don Allah ka daina saka bakinka a abin da bai shafe ka ba, ka yi laifi kam, kuma kada ka sake”
Bi na kawai yake da ido kafin ya ce “Me kika ce?”
Kama shi na yi hade da kwantar da shi na ce “Cewa na yi ka kwanta ka huta” yanzu kam da dan karfi na yi maganar.
Daga Assidiq sai Khaleel ne suka je masallaci, Affan kam a gida ya yi sallahr magriba da isha’i.
Lokacin da asuba ta yi na tambayi Affan maganar kunnenshi, ce min ya yi har zuwa lokacin baya ji da shi, Sai guda daya.
A haka suka tafi makaranta tun da ba ciwo yake mishi ba.
Gida kam yana nan jiya I yau, kowa rai bace, hatta kayan miya da kayan amfani na kitchen Bashir bai sawo mana ba.
Ni ce nake saye, wannan duk bai dame ni ba, irin yadda Affan har lokacin baya ji da kunnen shi daya. Ina son faɗawa Bashir to baya kwana dakina. Ranar Sunday da dare haka nan na tura mishi text din matsalar Affan. Sai ya maido min da reply kamar haka “Yanzu yaranki ne ba nawa ba, babu abin da ya dame ni da su, tun da sun raina ni ba sa jin magana ta sai ta ki, ki kai shi asibitin ai kina da kudi”
Na dade ina karanta sakon, kafin na yanke shawarar kai Affan asibiti don ganin likitan kunne a gobe monday.
Safiyar Monday bayan su Khaleel sun tafi school, muma babban asibiti muka wuce, bayan cike-cike na samu ganin likitan kunne, haka aka shiga yiwa Affan gwaje-gwaje da hotuna.
Daga karshe dai wai ear drum din Shi ce ta samu matsala, don haka sai an yi aiki.
Wato tashin hankali da na tsinci kaina ba kadan ba, na kara jin tsanar Sarai, ta dalilinta yarona zai rasa kunnen sa daya. Haka na yi ta daurewa ban nuna tashin hankalina ba, saboda Affan kar ya tsoro ta
Wani babban takaicin na iske Sarai ta rufe kofa, na yi ta bugawa a banza.
Affan ya ce”Auntynmu ki samo min ladder, Sai in hau, Sai ki dago min ladder in kara sauke ta a cikin gidan, in taka in sauka”
Wannan shawara ta Affan ta ja hankalina, don haka na shiga makota na samo ladder, na jingina mishi ya hau, bayan ya hau kan katangar ya mike tsaye na taimaka mishi, muka daga ladder zuwa cikin gida, ya fara takawa kenan zai sauka Sarai ta zo wai za ta janye ladder, ga shi Ni ina waje, hayaniyarsu kawai nake ji, har zuwa lokacin da na ji dirar kafafun Affan a kasa, Sai kuma na ji takun gudunsu a farfajiyar gidan, kafin Affan ya shiga bude min gate, ita Kuma ina jin yadda take jibgarshi
A waje safa da marwa kawai nake yi, ban san ko sau nawa na kama katanga da zummar dirawa ba, Sai in ga ban iyawa. Don haka yana bude min kofa na banka cikin gidan da zafina, na cakume ta ina fadin “Kashe min dan za ki yi, yaron da ba lafiya yake da ita ba, yanzun nan muka dawo asibiti, shi ne za ki kama min shi da duka, dama ta sanadiyyarki yake niyyar kurumcewa”
Na rika aika mata da bugu ko ta ina, Sam na manta da goyon Haidar, Sai da na ji Affan na kwance shi yana fadin “Auntynmu tana bugun Haidar za ta kashe shi”
Zanen goyon na shiga kwance mishi da hannuna daya, wannan ya ba ta damar kwacewa daga rikon da na yi mata, wani shebur ta dakko ta yi kaina da shi, aiko na goce, haka muka rika artabu da ita, tana bi na da gudu wai sai ta kwaɗa min.
Affan ya sauke Haidar, ya bi bayanta hade da sanya mata kafa, ta fadi, shebur din ya yi wajen shi da Affan ya dauke. ta yi kan Affan din hade da cakume shi tana bugu.
Ganin haka ya sa na yi kanta, na janye da karfin tsiya, fadan ya kuma dawowa kaina. Muka dora daga inda muka tsaya. Zanen da ke jikinta ya balle daga ita sai buje. Zuwa lokacin ne mutane suka fara taruwa, saboda gate a bude yake duk wanda zai wuce yana kallon mu.
Aka shiga raba mu, amma da an janye Sarai sai ta kuma rarumo abun duka ta yo kaina, ko kan Affan, har da su duwatsu, ko kuma ta shammaci mutane ta kawo min duka, fadan ya kuma komawa sabo, a haka har muka fito kan center, mutane suka taru, su Maman Aiman sai janye ni ake ana ba ni hak’uri.
Amma tsabar jaraba da bala’i irin na Sarai ko na hak’ura din sai ta kawo min duka, ko ta auna min zagin da dole na je inda take mu koma sabuwar kokawa, kamar yanzu din ma wani zagin ta auno min.
Aiko ban san lokacin da na zabura zuwa wajen ta ba, muka ka came sabuwar kokawa.
A haka kuma Bashir ya taras damu, sakamakon kiran da aka yi mishi.
Da wata irin murya ya ce “Khadija!”
Na yi saurin sakin Sarai ina waiwaya wa, wani irin bacin rai na gani a fuskarshi wanda ban taba gani ba.
Komai bai ce ba, ya shige gida. Mutane suka shiga fadin albarkacin bakinsu, kowa da abin da yake fada. Ni din ma sai na ji ban kyauta ba, to amma yana iya, ba zan zauna Sarai ta nakasa ni, ko ta nakasa Affan ba.
Jiki ba kwari na shiga cikin gidan, Sarai ta biyo bayana tana kukan munafurci daga ita sai buje. A farfajiyar gidan ta rika tsintar kayanta da suka watse.
Daidai lokacin Bashir ya fito daga part dina idanunshi a kaina ya ce “Wato to dai sai da kuka tona min asiri ko Khadija. Yau matana ne a tsakar gari suke kokawa daga su sai buje. Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Wannan ya ce irin rana ce? Kun muzanta ni, kun zubar min da mutumci, kun watsa min kasa a ido. Kun nunawa duniya ni din ban isa da gidana ba, dukkanku na gode muku”
Sarai cikin kuka ta ce “Wlh, taron dangi suka yi min ita da Affan…”
Murya cike da bacin rai ya katse ta da fadin “Quite my friend! A dakinki suka same ki, me ya sa ba ki kirani ba, Sai ki ka dauki matakin ramawa da kanki, dukkanku ba zan karbi uzurin kowa ba. Wannan shi ne na karshe, na gaji da halayenku, and I mean it, I’m I’m very tired”
Ya karasa maganar kamar zai rufe mu da duka.
Sai da ya dan nisa tukun, kamar mai jin tsoron maganar da zai fada a hankali ya ce “Dukkanku na sake ku saki daya, duk ku fice min daga gida ba na son ganinku”
Gabana ya yi wata irin faduwa, na ji kamar sama ce ta ruguzo min a kai, na ji kamar ban ji abin da ya fada daidai ba. Kwakwalwata ta rika maimaita kalmar “Dukkanku na sake ku saki daya, duk ku fice min daga gida”
Daga inda nake tsaye nake kallon shi cikin ido ina son kara tabbatarwa,. “An sake ni” na fada a zuciyata, a zahiri kuma wasu hawaye masu dumi ne suka rika min zarya a kan kuncina, na juya ina kallon Affan wanda yake rike da Haidar, sai tausayinshi ya kama ni, saboda rashin lafiyar da ta same shi.
Sarai kam ihu ta fasa ta nufi Bashir tana fadin “Ni ka saka, wlh ba ka isa ba, Sai dai ka sake ta, duka wata nawa da auran namu, ko fa shekera ban yi ba, shi ne za ka ce ka, sake ni.”
“Ko yau na aure ki na sake ki”
Cikin kururuwa ta ce “Aiko Allah Ya isa tsakanina da kai, in Sha Allah ba za ka gama da duniya lafiya ba, mayaudari Azzalumi macuci”
Ya nufe ta a harzuƙe, da gudu ta je wurin shebur din nan na dazu, ta rike shi a hannu, cike da bushewar ido ta ce “Idan ka matso kusa da ni sai na karasa maka wannan makalallar kafa, kuma ka matso ka gani”
Aiko bai ji gargadin da ta yi mar ba ya nufe ta a zafafe, cike da rashin tsoro ta daga shebur din hade da kwaɗa mishi.
Affan ya fasa ihu hade da nufar mahaifinshi. Bashir ya ja baya, Sai ta biyo shi a guje, tana kai mishi duka da shebur din, shi kuma gudun ba iyawa yake yi ba, saboda kafarshi. Affan ne ya kuma sanya mata kafa ta fadi, ni kuma da hanzari na zo na kwace shebur din
Cike da mamaki gami da tsoro nake kallon bushewar idon Sarai, yau kam na gasgata Sarai yar bala’i ce. Yadda take aunawa Bashir zagi ka dauka igiyar aure ba ta taba shiga tsakaninsu ba. Cikin bacin rai gami da baƙin ciki ya ce “Na karasa miki saki biyun, ki fita ki bar min gida”
Ta kara saka kururuwa, ta shiga dukan glasses din windows, duk wanda ta samu sai ta maka mishi dutse, tana yi tana bala’i.
Kafin Bashir ya rike ta tuni ta farfasa kaso biyu bisa ukkun windows din.
Yanzu kam Allah Ya ba shi sa a ya rike gam hade da kwashe ta da mari, nan da nan suka kacame kokawa, ina kallon yadda ta kama gabanshi ta murɗe, Sai ga shi yana neman faduwa. To ba lafiyar kafa ne da shi ba
Haidar na ajiye hade da taimaka mishi ya kwaci kanshi, aiko ta dawo kaina. Ni dama mun saba, don haka muka dora daga inda muka tsaya.
Gate Bashir ya bude, ya ja ta karfin tsiya ya fitar waje, ya mayar da kofar ya rufe. Yayin da yake ta mayar da numfashi.
Ta rika auno zagin rashin mutunci daga wajen, wannan ya kara jawo hankalin ƴan’unguwa. Suka fara taruwa, daga cikin gidan ina jin hayaniyarsu. Daga karshe kuma na ji tsit, har aune-aune zagin babu.
Sai a lokacin ne kuma Bashir ya samu damar barin gidan. Ko kofar bai rufe mana ba. Sai Affan ne ya rufe, saboda ni kamar zane haka na zama.