Skip to content
Part 43 of 66 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Na gaji da tsayuwa a tsakar gidan na cewa Affan mu shiga gidan Maman Aiman, saboda dama sai kirana take yi.

Ina shiga kam na same ta a tsakar cike da rashin jin dadi ta ce “Haba Maman Maama, me ya ja miki, me ya sa kika biye ma?”

Kan entrance din ta na karasa hade da zama na ce “To zan zauna ta kashe ni ko ta kashe min yaro ne Maman Aiman?”

Kafin ta ce wani abu na kuma dorawa da “Affan fa ta kama da bugu, yaron da ba shi da lafiya, daga asibiti muke ma aka ce aiki za a yi mishi… (na ci gaba da ba ta labarin abin da ya faru na rufe da) Allah Ya isa tsakanina da Sarai, cikin watanni kadan ta bata min gida, har ta jawo min saki.”na karasa maganar cikin kuka

A matukar rude Maman Aiman ta ce” Saki! Saki kuma? “

Na shiga jinjina kai alamar eh, ina fadin” Ya, sake ni, abun da ban taba tunani ba. Lallai kishiya ba ta da kadan, ko ki zo a farko ko a ta biyu duk abu daya ne, Sai dai fatan samun ta gari. Ga shi dan hakin da na raina, bai tsaya a tsone min ido kadai ba, cire idon ya yi gabadaya Maman Aiman…” kuka ya sarke ni

Murya a sanyaye ta ce” Ki yi hak’uri kin ga Affan ma kuka yake yi. “

Na juya inda Affan yake, Sai na ji duk babu dadi, komai ya faru a gaban idonshi, ko bai ji wani ba saboda lalurarshi zai ji wani.

Idanuna na janye hade da mayar da su kan Maman Aiman na ce” Ta ya zan fara zuwa gida in ce sake ni Maman Aiman? “

Nisawa ta yi a hankali kafin ta ce” Babu inda za ki je, wadannan yaran fa ina za ki kai su? Gidanki za ki koma, tun da saki daya ne zai mayar da ke.”

” Ko zai mayar da ni Maman Aiman ai dole dai sai na tafi gida. Wlh Allah Ya isa tsakanina da Sarai. “na kuma karasa maganar cikin sabon kuka ina jin wani iri a kirjina.

Dama haka mutum ya ke ji idan an sake shi, musamman idan ba shi kuma yana da yara. Yau kam na yi lissafi ya fi dubu

Maman Aiman ta katse ni da fadin” Ko in kira Dadyn Aiman ya zo ne ya saka baki”

Kai na shiga girgizawa a hankali kafin na ce “Inna kawai za ta yi wannan aikin, ni, kuma ba zan iya kiran ta ba”

Maman Aiman ta ce “Ni sai in kira ta”

Na ɗan yi murmushin yaƙe kafin na ce “Ba cinya ba kafar baya, ai dai da wayata kika kira”

Ta kuma cewa “sai in kira da tawa wayar”

Na ɗan yi shiru kafin na ce “Bar shi kawai Maman Aiman, zan tafi gidan, yanzu damuwata yaran nan”

Kamar za ta yi kuka ta ce “Allah babu inda za ki je Maman Maama, ke da Bashir mutuwa ce za ta raba, in Sha Allah sai kun koma auranku”

Ta yi maganar hade da bude jakata ta dakko wayata ta fara scrolling

“Me za ki yi ne wai?” na tambaye ta hade da mika hannuna da zummar fisge wayar

Da sauri ta mike tsaye tana fadin “Babu ruwan ki, ni na san abin da zan yi”

Na ce “Don Allah Maman Aiman kar ki zubar min da aji, kin san an ce matar shige ba ta daraja. Idan har Bashir zai manta duk wani alkairi nawa ya sake ni, ba bukatar in roki alfarma don ya dawo da ni”

Ta ce “Na ji, kawai ki saurare ni ki ji ko zan zubar da ajin naki”

Na yi shiru ina jin yadda wayar da ta kira take ringing, a hands dree ta saka, wannan ya sa na ji muryar Yaya Habi ta bayyana.

Suka gaisa sannan Maman Aiman ta ce “Yaya Habi ce ko ta Ruma?”

Daga can bangaren Yaya Habi ta amsa da “Eh ni ce, wacece?”

Maman Aiman ta ce “Makociyar Khadija ce, nan Katsina, wlh wani abu ne ya faru, abun dai babu dadi, yanzu haka dai maigidan ya sake su dukkansu.”

Ina jin yadda Yaya Habi ke kwaɗa sallallami tana sallamewa, Maman Aiman ta dora da “Tun dazu nake fama da Khadija a kan ta kira ku amma ta ki, yanzu haka ma ta bar wayarta a gidana, ta tafi hado kayanta na samu na dauki lambarki na kira. Ban sani ba ko da abin da za ku yi, kafin abun ya yi nisa, tun da saki daya ne”

Yaya Habi ta kuma doka sallallami kafin ta ce “Shi Bashir din hauka yake yi, ya rasa wacce zai saka sai Khadija, yarinyar da ta rike mishi ƴaƴanshi babu hantara. Don Allah baiwar Allah kar ki bar ta tafi, yanzun nan zan taho Katsinar”

Daga haka ta yanke wayar, Maman Aiman ta kalle ni, Sai kuma ta yi murmushi ta ce “Wlh karyarshi sai mayar da ke”

Na ce “Ba lallai in yi daraja ba”

Ta ce “Za ki yi…”

Ta yi saurin yanke maganar jin wayata na vibration, ta Daga min wayar na ga sunan Inna yana yawo a kan Screen din wayar. Sai ta yi dan murmushi kafin ta daga kiran.

Cike da tashin hankali Inna ta ce “Ina me wayar?”

Maman Aiman ta ce “Ba ta kusa”

Inna ta kuma cewa “Ke ce kika kira yayarsu yanzu”

Ta amsa ta da “Eh”

“Yawwa don Allah me ya faru”

Maman Aiman ta kwashe duk abin da na fada mata ta fadawa Inna, har da marin da Bashir ya yi wa Affan, da abin da ya biyo bayan marin. Inna doka sallallami kawai take yi, sai da Maman Aiman ta kai aya ne ta ce “Babu yadda ban yi da yaron nan a kan kar ya auri yarinyar nan ba amma ya ki, yanzu wannan tashin hankali da me ya yi kama? Don Allah yarinya kar ki bar Khadija ta tafi, yanzun nan zan saka Bashir din ya dawo gidan ya mayar da ita gidanta kafin Yayarsu ta iso, kila ma tare zamu, taho”

Maman Aiman ta ce “To sai dai fa ya yi sauri, saboda na san tana dawowa daga hado kayanta za ta ce tafiya za ta yi, kuma ban isa in hana ta ba, tun da tun dazu nake rokonta.”

Abu kamar wasa sai ga shi, ƴan’uwan Baban Khaleel masu fada a ji suna ta kira a waya, wasu su kira layin Maman Aiman wasu layina.

Sai na rika jin wani irin dadi, ashe duk suna sona, ashe haka nake da matsayi a wurinsu? Ashe na yi nisa a cikin danginshi ban sani ba? Ashe har muhimmancina ya kai haka? Ashe duk sun damu da ni?

Hawayen dadi suka shiga sakko min, kamar 30mns sai ga kiran Bashir a wayata

Maman Aiman ta fasa wani ihu ta ce “Wayyyo dadi, ga mai gayya mai aiki na kira Maman Maama, ta shi maza je ki gidanki, ki fara hada kayan ki”

Kiran ta daga hade da sanya shi a hands-free, suka gaisa a nutse ina jin shi, sannan ya ce “Ina Khadijan?”

Ta ce “Tana gida”

“OK” ya fada hade da yanke kiran.

Ita kuma ta shiga jana, har zuwa gate, fadi take “Matsa Maman Maama ki je ki wargaza gidan nan don Allah”

Haka na shiga gidan na bude part dina na shiga, Sai na rasa abin da zan fara dauka, komai zaune cikin tsari. Kitchen na wuce nan ma komai fes, kuma babu abin da na saya da kudina. Ai da kunya in dauki wani abu. Don haka na fito na haura sama, na shiga zaro kayan da ke cikin closets dina na jibgesu saman gado. Kafin na shiga shiryasu cikin akwati.

Cikin kankanen lokaci dakin ya birkice.

Ina tsaka da loda kayan ne na rika jin takun mutum, gabana ya shiga faduwa, saboda daga yadda ake haurowa na san Bashir.

A kofar dakina ya dogare yana kallon yadda nake ta zuba kayan sanyawa ta cikin akwati.

“Me ya sa za ki kira su Inna?”

Na mike fuskata na nuna reaction din rashin fahimtar furucinci na ce “Inna kuma? Ni ban kira ta ba, in kira ta to in ce mata me?”

“Ki fada mata abin da ya faru mana”

Rai na bata sosai kafin na ce “Don Allah fita ka ba ni wuri, za ka ɓata min lokaci”

Kai karshen maganar tawa ya yi daidai da dukawata na ci gaba da abin da nake yi.

“Inna ta ce in mayar da ke, kuma na mayar da ke din, don haka ki mayar da wadannan kayan inda suke”

Bai jira cewa ta ba ya juya zuwa waje.

Kayan da ke hannuna na sake yaraf, hade da zama gefen gado, zuciyata ita ba farin ciki ba, ita ba bakin ciki ba. Kamar 5mns na ji takun shigowar Maman Aiman a guje.

Da wani irin karfi take hawan steps har ta iso dakina. Saman gadon ta fada tare da fadin “Wayyyo Allahna dadi, kai Alhamdulillah, Allah na gode ma” sai kuma ta mike zaune ta ce “Mijinki wai don Allah in zo in taya ki mayar da kaya, kuma in zauna da ke kafin su Inna su iso, kar ki tafi”

Ta kai karshen maganar hade da mikewa tana taka rawa. Yadda take rawar ne ya sanya ni murmushi duk da zuciyata babu dadi, wai yau ni aka saki, ikon Allah, ban da an daidaita da shi kenan zan koma gida in dasa zawarci.

Ajiyar zuciya na sauke ina kallon Maman Aiman da ke mayar da kaya cikin closet, har sai da ta gama sannan ta zauna gefena tana fadin “Maman Maama, zuwa yanzu kin kara fahimtar wace kishiya ko? To ki yi addu’a Allah Ya kawo miki ta gari kawai”

“Ba na fata Maman Aiman, Allah Ya rufe idon Bashir da ganin ko wace mace ma, na sha wuya cikin watanni kadan komai nawa ya birkice, ta raba ni da mutanen arzikina, ta hada ni da mijina, ta hana zuciyata sakat, wannan wace irin jarabawa ce?”

Ta ce “Haka na sha fama da tawa, wlh yadda ki ka ganku kan centern nan kuna dakuwa haka mu ka yi da tawa, sharri fa ta yi min wai na je wurin malami karbar magani ya yi zina da ni. Kuma mutane suka yarda, suka fara zundena cikin layi, har magana ta komawa mijina, shi kuma ya fada min, har da saki, aiko yana fita na je har dakinta na janyo ta na yi mata shegen duka. Iyayena kuma suka yi karar ta, shi ma malamin da ta ce na je wurinshi da yake dan cikin unguwa ne ya yi kararta. Abu fa ya rikice, da kanta ta ce sharri duk ta yi mana, aiko aka sasanta na dawo ita kuma ya sake ta”

Rike baki na yi cike da mamakin wannan makirci , Sarai ma tsab za ta iya irin wannan makircin babu Allah a ranta Sam!

Kasancewar duk kofofin gidan a bude suke, Sai dai na ji sallamar Yaya Habi da Inna, daga ni har Maman Aiman muka sauka kasa.

Rike da Haba Yaya Habi ke kallo na kafin ta ce “Har da yan daba kuka yi fadan ne, na ga gilasan gidan duk a farfashe?”

Murmushi na yi kafin na duka har kasa na gaishe da Inna, da ita ma take nata mamakin, ta amsa min tana fadin “Bashir din?”

Maman Aiman ce ta ce “Ya fita”

“To yaran fa?” Ya Habi ta tambaya

Yanzu na Maman Aiman din ce ta ce “Haidar dai da Affan suna gidana, su Khalil Kuma suna makaranta”

Ta kai karshen maganar tana yin hanyar fita. Har a lokacin kuma ban daga daga tsugunnawar da na yi ba.

Zama Inna ta yi tana fadin “Abu bai yi dadi ba Sam, me ya sa za ki biye mata ke? Ina yi miki kallon mai hankali.”

Shiru na yi ban ce komai ba, Yaya Habi ce ta ce “Wai Inna kin manta bala’in Sarai ne, wani abun ai dole ka biyewa mutum”.

<< Hasashena 42Hasashena 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×