Skip to content
Part 44 of 66 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

A lokacin ne na basu labarin abin da ya faru. Bayan na diga aya Inna ta ce “Ai a bar hali a ci me? Kuma nono guba, daman idan Sarai ba ta yi masifa ba me za ta yi? Na nunawa Bashir illar auran nan ya ce ba haka ba, wai wancan mijin nata yaro ne, shi kuma da hankalinshi zai biye mata ne. To ga shi nan ba aje ko ina ba ta nuna mishi iyakarta, yanzu wannan barnar da ta yi mishi nawa zai kashe ya gyarata, ga yaronshi da ta sanya ya nakasa… “

Yaya Habi ta tare ta da fadin” Ni addu’ata Allah Ya sa ba ta da ciki, mugun iri ai bai yi ba”

Inna ta amsa da “Amin dai. Ni ma addu’a ta kenan wlh”

Salloli muka tashi daga ni har su mu ka yi, ni kam ba azhur, ga shi an kira la’asar. Bayan mun fito ne na shiga kitchen, Yaya Habi kuma ta cire hijabi ta shiga gyara tsakar gida, saboda ko ina kananan glass ne.

Da Affan ya shigo ne ya shiga taya ta. Inna na tsokanarshi da ɗankurma. Yaya Habi na tare mishi.

Komai da nake yi karfin hali nake yi, amma sakin nan ya doki kirjina, ji nake kamar an kwashe kafafuna ta kasa na fadi. Ji nake duk ba ni da wata daraja da kima, ji nake kamar ba ni da sauran katabus.

Lokacin da yara suka dawo school haka suka dame ni da tambayoyi “Auntynmu ba ki da lafiya ne? Ko jikin Affan din ne? Auntynmu bara yi ne suka shigo gidanmu mu ka ga an fasa glasses? Auntynmu lafiya su Inna suka zo?

Wasu, tambayoyin in amsa wasu kuma in yi banza da su.

Da kyar na yi sallahr isha’i, saboda sosai zazzabi nake ji, ga jikina ko ina ciwo yake yi, shi ya sa na gyarawa su Inna wurin kwana tun bayan da na gama aikin abinci.

Lokacin da Bashir ya dawo tare suka hawo sama zuwa dakina. Yaya Habi ce ta fara cewa “Lafiya ko Khadija?”

Yunkurawa na yi dakyar na tashi zaune sannan na ce “Zazzabi ne ke damuna”

Inna ta ce “Ai dole, hayaniya ce ba ki saba ba, sannu Allah Ya sawake”

“Amin” na amsa a hankali, yayin da Bashir ke gaishe su.

Bayan sun gama amsawa ne Inna ta ce “Ban ji dadin abun da ya faru ba Bashir, da hankalinka, da mutumcinka ka aikata wannan abun”

Da alamun bacin rai a muryarshi ya ce “Inna ina mutumcin da girman, bayan sun zubar min da shi. A waje fa na same su suna kokawa mutane sun zagaye su”

Cikin rashin jin dadin maganar Inna ta ce “Shi ne kuma ba bin ba’asi sai ka yanke wannan danyen hukuncin”

Tsugunnonshi ya gyara sannan ya ce “Inna dukkansu ba ni da daraja a idonsu. Tun ba Khadija ba, ta canja sosai, ban isa in sa ta ba, kuma ban isa in hana ta ba. Yaran nan ma ko girmana basu gani..”

“Subhnallah!” Inna ta yi sauri tarar shi kafin ta ce “Wace irin magana ce kuma wannan?”

Da yatsa ya nuna ni kafin ya ce “Ai ga ta nan zaune idan karya na yi mata”

Inna ta dago kai tana kallo na kafin ta ce “Me ya sa haka Khadija?”

Kaina na dafe da yake min wani irin ciwo, a sanyaye na shiga labarta mata irin zaman da muke yi da Sarai, da yadda take nema na da bala’i, yadda ta takura ma yara, na kuma buda mata zargina da yake, sannan na dire a kan abin da ya rika haddasa mana tashin hankali cikin satin nan har zuwa yau da aka yi uwar watsi. Na kulle da “Duk abin da na fada a nan babu karya, idan kuma na yi mata sharri saboda ba na ganin idonta Allah Ya saka mata”

Yaya Habi ta ce “Sarai da za ta yi fiye da haka, wannan yarinyar wa take gani da mutumci, kuma shi din ma ai ya gani da idanunshi. Kalli rashin mutunci da ta yi ma a cikin gida, ai ni sosai na ji dadin abun da ya faru. Ko ba komai yanzu za ka yarda da kalubalen da mu ka kawo ma ka lokacin da za ka aure ta”

Inna ta cafe da “Ban da abun ka ma, Khadijan yau kake zaune da ita, da ko wane lokaci za ka rika yarda da abin da matarka ta fada a kanta. A aikin banza ka je ka nakasa yaranka. Yanzu ita ba ta tafi ta bar ka ba.  Ina amfanin irin wannan ta yi shiru har zuwa lokacin akwai bacin rai sosai a muryarta, bayan ta nisa ne ta dora “Ko me Khadija za ta yi a gidan nan babu saki a tsakaninku ko da raina ko babu raina ka ji na fada ma. Ita din tafi karfin saki. Kai yanzu akwai macen da za ta yi ma gatan da Khadija ta yi maka, ta rike maka yara ba su san kukan rashin uwa ba. Yanzu da Sarai din ce a tunaninka za ta rike ma yara haka? To ba ni boka ba ni Malam ba za ta iya ba. Saboda sonsomin hauka tsidda yawu, juma’ar da za ta yi kyau daga Laraba ake gane ta”

Babu wanda ya yi ko tari a cikin mu, ita ce ta kuma cewa “Saboda shashanci irin naka ana fada matsalar yaronka kana yin banza, wannan ai ba abu ne da za a yi wasa da shi ba, ga shi nan an ce sai an yi wa yaron aiki, saboda kwata-kwata baya ji kunnen na shi guda daya”

Wata irin zabura ya yi da alama abun ya taba shi “Affan din?” ya tambaya da alamar kaduwa

Inna ta ce “Shi din fa”

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!” “ya ambata cike da tashin hankali, Sai kuma ya dube ni ya ce” Haka likitan ya ce Khadija? “

Kai kawai na daga mishi, shi ma darajar su Inna suna wurin.

Ya kuma maimaita kalmar” Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un”

Shiru ya ratsa dakin, a hankali ya ce “Affan ba ya ji da kunnenshi daya. Ya salam! Oh my God” cike da tashin hankali yake maganar.

Sai kuma ya mike yana fadin “Wane asibiti kika kai shi dazu?”

A hankali na fada mishi, Ya dubi Inna yana fadin “Bari in je da shi wani private hospital, Idan ta kama a fita da shi waje, zan kira Rahma su bincika min likitan kunne a can inda suke, Sai mu kai shi can” yadda ya nuna damuwa da tashin hankali abun har mamaki ya ba ni.

Innan ce ta kuma cewa “To ku tafi da Khadijan ita ma ta ga likita, ka ga ba ta da lafiya”

“To” ya amsa hade da mikewa ya fice. Yaya Habi kuma ta taimaka min na kintsa kaina, ta kama ni har farfajiyar gidan, inda Bashir ke jiranmu

Duk yaran suna baya, shi ya sa na zauna a gaba. Ina jin Yaya Habi na fadin “Wai duk da yaran za ka tafi?”

“Sun ce za su raka mu” ya, yi maganar kamar ba ya so

Daga yadda yake tukin na fahimci yana cikin damuwa, saboda wani irin lallabawa yake kamar yana jin tsoron hanyar.

Ni da kwantar da kaina na yi jikin kujera ina sauraron su Khalil da suke ba Affan labarin abin da ya faru a school yau da bai je ba. Idan yana son ji sosai, sai dai ya juya daya kunnen wajen bakinsu, a hakan ma wani lokaci sai ya ce “Me kuka ce?” sai su kara maimaita mishi. Na fahimci hakan na kara taba Bashir.

A haka muka isa wani private hospital mai kyan gaske. Shi ne ya riƙewa Affan hannu, ni kuma ina biye da shi da sauran yaran

A reception ya bar mu ya shiga ciki, kamar 30mns da shigar shi, wata nurse ta ce ni da Affan mu shiga. Khaleel na fadamawa ya kula da su Assidiq, da shi ke na baro Haidar gida yana bacci.

Bayan mun yi sallama muka gaishe da likitan, ya amsa idanunshi a kan Affan. Sai kuma ya jawo shi kusa da shi, ya shiga yi mishi tambayoyi.

Daga bisani kuma suka ta fi da shi dakin aune-aune. Wannan ya sa na dawo wurin yarana na zauna. Sai after 9pm suka fito. Kuma likitan ya tabbatar mana da tabbas Affan na bukatar aiki cikin gaggawa.

Cike da damuwa Bashir ya ce”Za a iya aikin a nan successfully ko mu fita da shi waje? “

Shiru likitan ya yi kafin ya ce” Tabbas za a iya aikin a nan cikin nasara in Sha Allah, Sai dai kuma idan ka fi bukatar fita wajen, za ka iya fita da shi din”

“Shi kenan, za mu je gida mu yi shawara, daga nan zuwa gobe idan Allah ya kai mu. Sai kuma ya yi mishi maganar zazzabina. Still ni ma lab din aka tura Ni, a ka debi jinina, after some minutes result ya fito, bayan malaria Ina dauke da ƙaramin ciki dan wata biyu.

Sosai na kara shiga damuwa da maganar cikin nan, shu kenan ni ba ni da wani aiki sai na haihuwa, a wannan karon sha Allah allura zan yi ko in sanya roba, in Sha Allah sai na huta.

Har muka dawo gida su Inna basu yi bacci ba, a nan mu ka sanar musu da abin da ke faruwa.

Jikinsu ya kara sanyi, dakin ya tsit, Inna ce ta fara cewa “Duk inda mutum yake sauki na Allah ne, ina jin a yi wa yaron nan aikin nan a nan, Sai mu yi addu’ar dacewa, tun da an ce da gaggawa ake bukatar aikin”

Yaya Habi ta ce “Gaskiya, ni fa ba na son a dauki mara lafiya zuwa wajen nan, Sai in ga kamar ya tafi kenan”

Bashir ya ce “A can akwai kwararrun likitoci da kayan aiki ne”

Inna ta kuma cewa “Allah shi ne kayan aiki Bashir, a yi wa yaron nan aiki a nan, yana kusa damu muna ganin shi.”

Ya ce “To shi kenan, Allah Ya sa a yi cikin nasara”

Duk muka amsa da “Amin”

Na san wannan ranar ba ni kadai ce ban yi bacci ba, kila ma duk gidan babu wanda ya yi bacci, abubuwa sun yi wa kowa yawa a kai, ni dai ga damuwar sakin da aka yi min, duk da an mayar da ni, ji na dai nake kamar a saken nake. Ga ciwon Affan, ga tashin hankali da mu ka sha, ji nake kamar mafarki. Ga maganar ciki kuma,sosai ban so wannan cikin yanzu ba.

Asuba na ji Bashir na ta waya da mutane, duk a kan maganar aikin Affan. Har da su Rahma ya yi waya, su kam da ma na san ba za su so a taba kunnen Affan a Katsina ba. Saboda sai ga kiran Rahma tana rokona, ko iya Affan ne mu sako a jirgi za su zo su dauke shi, kuma za su dauki nauyin aikin.

Na ce ta kira Inna. Haka dai wannan rana aka yi ta waya, musamman da Rahma da kuma mijinta. Har suka shawo kan Inna a kan gobe za a wuce da Affan zuwa Indiya, shi da Babanshi.

Yadda ake ta cuku-cukun da cike-ciken tafiya shi ya mantar wani zazzabi nawa, a maimakon tafiya ranar Laraba kamar yadda aka tsara, Sai da tafiyar ta kai Asabar, saboda yan cike-ciken da aka rinka yi.

Lokacin da mu ka yi ma su rakiya zuwa airport don hawa jirgi zuwa Abuja, Sai na ji kamar ina yi musu bankwana ne, duk yadda na so daurewa sai gani rungume da Affan ina kuka, Khaleel dama ku san kullum cikin damuwa yake, idan na tambaye shi sai ya fara min kuka. Yau din ma sai ga shi da kuka kamar Affan din ya rasu. Kuka yake yi sosai. Wannan ya kara daga hankalin Bashir ya rika rarrashin Khaleel da fada mishi maganganu masu dadi, an dai samu ya, yi hak’uri a airport din, amma muna dawowa gida ta, dasa, su Yaya, Habi su kai ta lallashi, saboda ni ma lallashin kaina nake yi. Haka gidan ya kasance kamar an yi mutuwa, hatta abinci babu mai sauraron shi.

Misalin karfe uku na dare a Nigeria Bashir ya kira ni sun sauka, Sai a lokacin hankalina ya kwanta.

Kwanansu daya Affan ya ga likita.

Ina hawa online na ga, sakon Bashir _”Mun ga likita yau, sun yi aune-aune, likitan ya tabbatar mana da gaske eardrum din Affan ta samu matsala, kuma ko an yi mishi aiki sai ya hada da hearing aids domin ya taimaka mishi wajen jin magana_”

Wayar na saki ina furta “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un abu kamar wasa yana neman zama babba”

Reply na yi mishi da addu’ar samun sauki wa Affan din. Kafin na kama bakina na kulle, ban ba wa Inna da Yaya Habi labari ba.

Komai da yake faruwa Bashir da Rahma suna sanar min, ni kuma sai in sanarwar da su Inna abin da na san ba zai daga musu hankali ba.

Ranar Laraba ita ce ranar da aka ware don yi wa Affan aiki, darenta daga ni har su Inna ba mu yi bacci ba, salloli da karatun alkur’ani kawai muke yi, hatta Khalil sai gaf asuba ya yi bacci.

Misalin karfe biyu agogon nigeria Bashir ya sanar min za a shiga da Affan theater room. Hr cikina Sai da ya katsa, marata ta rike gam, a haka na shiga mikawa Allah kukana.

Wajen biyar na yamma Bashir ya turo min hotunan Affan sanye cikin kayan asibitin, wajen kala goma duk a cikin theater room din. Na kasa jurewa na kira shi voice call, ko gaishe shi ban yi ba na ce “Affan din ya farka?”

Ya ce “Eh babu jimawa”

“To ya jikin na shi?”

Ya amsa min “Alhamdulillah! Muna fatan a yi nasara”

Na ce “Allah Ya sa.

Kiran na juya zuwa video call na ce ya nuna min Affan, Sai ko ga shi kwance, kunnen shi nade da bandage. Ya yi min kuri da ido, Sai kuma ya yi murmushi hade da daga min hannu.

Kiran na yanke hawaye na zuba min, ba tare da na share su ba na ce “Allah ka ba yaron nan lafiya, ka tashi kafadunshi”

Haka kullum muke kiran video call muna ganin Affan, wani lokaci ya yi mana magana, wani lokaci kuma ya yi shiru sai dai ya yi ta murmushi, wani lokacin kuma ya yi kuka.

Kwanan Aunty Habi goma ta koma Ruma ta, bar mu da Inna, hakan kuma ya yi min dadi, tana debe min kewa Sosai.

Saboda zaman jinya muke yi sosai kamar Affan na tare damu. Sati biyu da yin aikin ya samu lafiya, amma da taimakon hearing aids yake Ji sosai da kunnen, yanzu kam sosai muke waya kuma yana ji ko a, hankali mutum ya yi magana, wannan abu shi ya dawo da walwala hade da farin ciki a gidanmu, saboda yanzu ƙirga kwanakin dawowarsu mu ke yi.

Sai dai me Bashir ya zo min da batun Rahma fa tana ta rokon shi a bar mata Affan, tana son rike shi hade da daukar dawainiyarshi, wai hakan zai sanya ta ji ba ta watsar da amintar da ke tsakaninsu da aminiyarta ba, kuma hakan zai sa ta ji kamar aminiyar tata ba ta yi musu nisa ba. Ya rika bayyana min yadda take rokonshi wai har da kukan ta.

<< Hasashena 43Hasashena 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×