Shiru na yi hade da nazarin maganganun na shi, yanzu da ba Affan a gidan ji nake kamar ba kowa, ga shi duk mun dokanta da son ganin shi, Sai kuma kawai Bashir din ya dawo mana hannu na dukan cinya.
A hankali na ce “Ta yi hak’uri mana ya dawo mu gan shi, in ya so sai ya koma daga baya”
Ya dan yi shiru kamar ba zai ce komai ba, Sai kuma ya ce “Ko hakan na yi sai in ji kamar na nunawa Rahma iyakarta, ba tun yanzu take kulafuci a kan yaran nan ba, kuma za ta ga dai kamar hana ta zan yi”
Kai na jinjina a hankali ina fadin “Gaskiya ne kam, Rahma na son yaran nan, amma mu ma muna son ganin Affan din ai” kamar zan yi kuka na yi maganar
“Khadija kin san duk abin da zai sanya ni rabuwa da Affan musamman yanzu da yake dauke da lalurin da ni ne sala, kin san abun ba karami ba ne. Zan duba maganar ki, amma kar ki fadawa Inna, saboda na san ba za ta yarda ba”
“In Sha Allah” na yi maganar jiki a mace. Daga haka muka yanke wayar, amma da abun na wani, duk lokacin da na kalli Khalil yana murnar dawowar dan’uwamshi na kuma tuna abin da ke shirin faruwa sai in ji komai ba ya min dadi.
Bashir ya sanya ranar dawowa, amma Sam ba na farin ciki ni, saboda ya shaida min ya bar wa Rahma Affan ba zai dawo da shi ba. Dadi daya idan muna video call sai in rinka ganin shi cikin walwala, wannan ya sa na ji bai damu sosai da zaman na shi a India ba. Amma ana I gobe Babanshi zai taho da mu ka yi video call na karanci damuwa sosai a kan fuskar shi.
Babu wanda ya je airport taro Bashir, kuma ban fadawa yara exactly ranar dawowarshi ba. Shi ya sa ma na ce su tafi school. Time da ya iso ba su nan sai Inna, tun ya shigo take fadin “Ina maigidan nawa na ganka kai kadai, ko ciwon ne ya dawo kuma”
Murya ya kwantar ya ce “Inna Affan ya warware, ai ke ma kin gani da idonki, zai ga likita ne nan da sati biyu, ni kuma ana nema na a wurin aiki, shi ya sa na taho”
Ta dan rage damuwar fuskarta kafin ta ce “To Ma Sha Allah, har hankalina ya tashi”
Ni dai duk maganganun da suke yi ban ce komai ba. Sai ma na fita daga dakin na koma nawa, after kamar 1hr sai ga shi ya shigo.
Daga zaunen da nake ya rungomoni hannunshi a kan cikina ya ce “I missed you and my baby”
A zuciyata na ce “da ba a mayar da auran ba fa” a zahiri kuma murmushi na yi ba tare da na ce komai ba. Saboda ba ya son maganar sakin nan, ina son bacin ranshi to in yi mishi maganar ya sake ni
Ba tare da ya raba jikinshi da nawa ba ya ce “Na san kin damu sosai, ki yi hak’uri komai zai wuce, har ki saba kin ji ko. Ba fa mutuwa ya yi ba, kuma yana wurin da ba zai yi kukan rashin komai ba. Just pray for him”
Kai na jinjina alamar to, yayin da ya shiga laluba ta, dalilin da ya sa na ce “Ba wanka za ka fara yi ba?”
Cikin muryar da ta yi nisa a abin da yake yi ya ce “zan hada gabadaya in yi. Na ce miki na yi missing din ki”
Dole na ba shi hadin kai, bayan komai ya kammala ne ya gyara jikinshi ya yi sallahr azhur da la’asar, sannan ya sauka kasa don cin abinci.
Yana kan dining din yara suka dawo, wayyyo Allah murna, take suka cika gidan da ihu, Sai kuma suka shiga laluben Affan. Cikin kwantar musu da hankali ya ce “Ku yi hak’uri Affan bai gama ganin likita ba, ni kuma ana nema na wurin aiki, amma sha Allah zan shirya mana tafiya don zuwa mu duba shi.” sauran yaran suka yi ta murna ban da Khaleel. Haka nai ta kwantar mishi da hankali har da ya dan warware.
Tun da Bashir ya dawo Inna ke maganar za ta koma gida kuma, shi kuma yana yin shiru, ni kaina ba na son tafiyar Inna, ina jin dadin zama da ita.
Satin Bashir daya da dawowa yake sanar min ya yi waya da ƴan’uwan Sarai a kan mutum biyu su zo gobe, saboda zai bayar da mota a kwashe mata kayan ta zuwa gida.
A zuciyata na ce “Barkanmu, Allah Ya raba mu da jaraba.”
Washegari kam sai ga yan’uwan Sarai sun zo kwasar kaya, haka suka rika fito da kayayyakin nata zuwa cikin mota ana lodawa.
Abun mamaki kuwa sai ga Uniform din su Assidiq an fito da su. Na ce ba zan karba ba a kai mata, ace mata in ji ni ta sanya ta koma makaranta.
Kai tsaye na fadi maganar, kuma basu ba ni amsar maganar ba.
Bayan na gama abinci na sanya musu, kuma suka karba, na dauka za, su ce sun koshi. Sai wajen karfe uku suka, bar gidan. Inna kamar ta bi su Bashir ya hana ya ce zai mayar da ita da kanshi.
Kullum Inna cikin lissafin dawowar Affan take haka ma Khalil, musamman idan mun yi video call da Affan din sai soyayyar ta shi ta dawo sabuwa a zukatanmu
Watan Inna biyu a Katsina ta koma Ruma, shi ma saboda bikin autarta Jamila.
Ranar ina zaune Khalil ya shigo dakina, bayan ya zauna gefena ya ce “Auntynmu ina son a kai ni boarding school”
Na kalle shi sosai kafin na ce “Me ya sa?”
“Ni dai ina son zuwa ne, tun da ba Affan, ranar da mu ka yi video call da shi ya ce min Momy ta sanya shi a makaranta”
Wani tausayinshi ya kama ni na ce “Wace school din kake so Khalil, Idan dai ana Nigerian nan take za a kai ka”
Har zuwa lokacin fuskarshi ba ta warware ba ya ce “Airforce comprehensive school Abuja”
Da dan murmushi a fuska ta na ce “Soja kake son zama ne?”
Yanzu kam shi ma ya yi dariya sannan ya ce “Mai tuka jirgi ba, kin ga sai in rika daukar mutane zuwa India, daga nan in ga Affan”
Jikina na jawo shi, ina murmushi sannan na ce “Ma Sha Allah. Allah Ya amince”
Ya ce “Amin”
Na kuma cewa “zan shaidawa Abbanku”
Kai ya jinjina alamar ya fahimta, daga haka ya fice daga dakin.
Shiru na yi ina nazarin abin da Khalil ya zo da shi, kila kadaici ne ya dame shi, saboda wasa-wasa Affan yana cikin wata na hudu, ko labarin dawowarshi ba a yi. Bangarena dai har na fara sabawa da rashin shi. Khalil din ne dai har zuwa yanzu bai saba ba. Duk ya rage kuzari.
Da dare na shigar da bukatar Khalil a wurin Bashir. Ya yi shiru na tsawon lokaci kafin ya ce “Abuja ta yi nisa Khadija”
Marairacewa na yi kafin na ce “Can ya ce yana so yallaboi”
“Ya canja ko zuwa nan Kaduna ne”
“Don Allah ka kai shi Abujan tun da can yake so, me kake tsaro ne? Abujan ma fa kamar Katsina ne, akwai abokan arzikin ka da yawa a can”
“Kenan sai in dora musu dawainiya?”
Kai na girgiza alamar a’a kafin na ce “Dawainiyar me za ka dora musu, abu da boarding ce Kuma ka san ba zuwa ma suke yi da abinci ba, a can ake basu”
“Shi kenan zan duba lamarin kafin hutunsu na JSCE din ya kare.”
“To don Allah ka duba mishi, kaɗaici ne ke damun Khalil ni kaina ina son a kai shi inda zai warware”
Kai ya jinjina min alamar fahimta.
A cikin satin na yaye Haidar, saboda cikina ya shiga wata bakwai, ga kuma hidimar bikin Jamila da muke ta yi.
Komai na bikin da ni ake shawara, har gajiya nake da, wasu hidimomin, saboda ko su kayan garar amarya a gidana aka yi, Maman Aiman ta gayyato min wasu suka taya mu.
Ana sauran sati daya muka tafi Ruma, gidanmu muka sauka, sosai an gyara gidan, babu wani datti, kaya kawai mu ka sauke hade da yin sallah mu ka runguda cikin gidan.
Inda muka shiga gaisawa da mutane, sai magriba na ware da Murja, a nan ne kuma take fada min wai Sarai ta bi gari tana fadin ni da yarana mu ka yi mata duka har mu ka zubar mata da ciki.
“Haka ta ce?” na yi tambayar hannuna kan habata alamun mamaki
Ta ce “Wlh haka ta ce, wai kin yi ma miji asiri bai jin maganar kowa sai ta ki, duk wata shawara da ke yake yi, kin sanya yara sun raina ta, kuma Ƴayanmu babu abin da yake iya yi.”
“Ikon Allah!” na fada da muryar mamaki, sannan na ce “Wato har da sharri ta bi mu da shi?”
Cikin dariya Murja ta ce “Ta ce tana nan tana jiran zuwanki Ruma, wai sai ta yi miki dukan tsiya”
Yanzu kam dariya na yi mai sauti kafin na ce “Ai gani nan na zo, Bismillahnta”
Duk mu ka yi dariya kafin mu ka shiga hirar biki, sannan ta koma tsokanata a kan wai ba na hutawa, inda ba na goyo to ina da ciki
Dariya kawai na yi, saboda ni kaina na gaji. Ina son in dan huta.
An saura kwana uku daurin aure aka fara shagalin biki, da kauyawa day amare suka fara, sannan aka yi wunin uwar Ƴa, Yaya Habi ce uwar ya nan fa mu ka sha kidin ƙwarya. Ana gobe daurin aure aka yi walima, ranar Friday kuma muka fara karbar baki yan daurin aure. Har da abokan Abban Khalil ƴan Abuja.
Zuwa 12pm kam mun kammala duk wani abinci da za a ci wurin bikin, gida ya cika makil haka ma kofar gida, dakyar na samu na yi wanka na shirya cikin doguwar rigar lace da ya sha dinki bubu na manya mata. Sosai na yi kyau, ya kuma boye min cikina, duk da dama a wannan karon cikin bai yi girma sosai ba.
Misalin karfe biyu Bashir ya shigo da wata bakuwa, da kallo daya za ka yi mata ka fahimci akwai tarin ilmi na zamani gami da wayewa a tare da ita.
Sanye ta ke cikin wani blue black din boyel na mata mai kyalli dinki doguwar riga, ba wani shirme aka yi a dinkin ba, amma kallo daya za ka yi wa dinkin ka fahimci telan ya kware, jan veil ta yi amfani da shi wajen nade fuskarta. Hannunta kuma rike da jaka fara haka ma kafarta sanye da flat shoe fari mai kyau.
A tsakar gidan na same su, bayan da ya sanya aka lalubo ni.
“Ga bakuwata nan Khadija, a bata wuri ta yi sallah, a ba ta abinci ta ci sannan ta huta, daga Kaduna take”
Idanuna na dora kan matar sai ta yi min murmushi, ni din ma na mayar mata, shi kuma ya dora da “She is my wife Khadija, mother of five kid, Khalil, Affan, Maama, Assidiq and Haidar” ya kai karshen maganar yana kallon ta
Baki bude ta ce “Duk ita kadai, gaskiya ta yi kokari, ga jikinta bai nuna ba, she is still young”
Ƴa kalle ni sannan ya ce “Kin ji wai you’re still young” murmushi Kawai na yi, shi kuma ya ce “Zarah za kina son kara hurewa Khadija kunne, yara goma nake son ta haifa min, ke kuma kina zuga ta wai ta yi kokari, daga yin guda biyar”
Ni da ita mu ka yi dariya mai sauti kafin ta ce “Na fadi gaskiya dai, ka ga ni that 2kid Ma’aruf and Salman is ok for me. Sun isa Allah Ya raya min su”
Da wani kallo ya bi ta wanda na kasa fahimta sannan ya ce min “Take her in mai kayan kamshi” murmushi na yi kafin na cewa Zarah ta wuce mu je.
Dakin Murja na kai ta, na gabatar mata duk wani abu da za ta bukata, sannan na dan ba ta wuri saboda ta sake.