Skip to content
Part 47 of 49 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ni dai na zuba ido in ga inda alakar nan za ta kai su, idan ma auran juna za su yi maraba da zuwanta, ni dai permanent sit gare Ni, Kuma na daina daga hankalina a kan kishiya, bare yanzu da ba ni kadai ba ce.

Suna isa ya kira ni ya haɗa ni da Zahra, mu ka gaisa cike da fara’ar nan tata ta wayayyun mata. Ta kara sanar min da sha Allah gobe za ta kai Khaleel school Abuja. Cikin tsokana na ce “To amana dai na ba ki, idan kin ga akwai wahala kawai ki dawo min da shi gida”

Cikin dariya ta ce “Ba a samun abu mai kyau da muhimmanci cikin sauki ai, matukin jirgi fa yake son zama” ni ma na yi dariya hade da yi mata godiya.

Bayan mun yanke kiran ne na koma kan kujera na zauna, karon farko da na shiga media don sanin wacece Zarah  Dikko , haka dai Bashir ya ce min sunanta.

Da Facebook na fara, suka watso min Zarori da yawa masu kalar sunanta, na rika bin su har na gano nata, tana da tarin followers sosai. Na shiga shafin don ganin abin da ya kunsa.

Da Biography nata na fara, wanda ta dora a kan Facebook din, na rika bin su dakki-dakki ina mamaki, abun da na fahimta secondary ce kawai ta yi a nigeria, amma degreenta na daya da na biyu duk a kasashen waje ta yi, ga tarin courses da ta yi, wanda kaf a bangaren law ne, sannan ita din member ce a kungiyoyi masu yawa, na gwamnati da masu zaman kansu.

Cikin pages din sosai na shiga, Sai na fahimci ita ma tana da kungiya tata ta kanta, wacce take taimakawa jama’a.

Comment section na shiga, kowa da albarkacin bakinshi a kanta, wasu su ce ta ki aure kuma tana hurewa mata kunne kar su yi, wasu su ce ita din yar aiken Yahudawa ce, wasu su ce tana fada da musulunci, wasu kuma su yaba ta hade da ba ta kwarin gwiwa.

Haka na yi ta nutsawa cikin shafin nata ina ganin yadda take cudanya da manyan mutane har da turawa, da yadda take fita kasashen waje. Har na kai kan hotunan yaranta biyu maza, da alama ranar graduation din su ne. Sai kuma wani da aka yi shi a airport. Iyakar hotunan da ta dora kenan na yaran.

A zuciyata na ce “Abban Khaleel da shiga kamar sartse, ina ya samo matar nan wai?”

Maganar Murja na tuno da ta ce ta fi karfin shi.

A bayyane na ce “Gaskiya fa kamar ta fi karfin na shi, wannan matar ga ta nan ido a bude, ina za ta da gurgu?” na karashe maganar ina shiga shafin Instagram, nan dai kamar Facebook din, na fita zuwa TikTok, still dai kamar Facebook din, gajiya na yi na mike don karasa ayyukan gidana

Bashir bai shigo bai sai wajen goma na dare, a zuciyata na ce” An je an tsinki fure”

Safiyar Monday misalin karfe goma na safe na bude data, Sai ga TikTok suna sanar min Zarah Dikko ta yi adding post.

Aiko da gudu na tafi, Khalil na gani sanye cikin kananan kaya farin wando jeans, kafarshi ma farin sneakers din takalmi ne, jikinshi bakar shirt, bayanshi goye da jakar yan gayu ta matafiya. Hannunshi cikin na Zahra suna taka matakalar jirgi.

Na yi ta maimaita kallon videon ina ganin kamar ba Khaleel ba. Sai kuma na ajiye wayar hade da ɗan bubbuga kaina, alamar in farka daga baccin mana. Cikin sauri na mike tsaye ina fadin “Khadija kar ki zama wawiya mana?”

Daidai lokacin na ji takun Bashir yana sakkowa, ido na zuba mishi ina kallon shi, har zuwa lokacin da ya karaso wurina. “Ya dai Madam?” ya yi tambayar daidai yana daura agogon hannun shi.

“Me yasa Zahra za ta kai Khaleel school ba kai ba?”

Murmusawa ya yi kadan kafin ya ce “Amma a, gabanki aka fara maganar makarantar nan, kuma ta ce da kanta za ta nemo mishi, ta turo form a gabanki na cike na mayar mata. Jiya na kai shi Kaduna ta ce min in dawo gida za ta kai shi interview da kanta, idan Khaleel ya dawo ki tambaye shi yadda na rika kokarin hana ta amma ta ƙi”

Cikin nuna alamar rashin gamsuwa da bayanin na shi na ce “To me ya sa duk za ta yi wannan?”

Baki ya tabe tare da fadin “I don’t know gaskiya”

Na ce “Ni na sani”

Kunnenshi ya kade alamun yana sauraro.

Kai tsaye “Na ce sonka take yi”

Murmushi ya yi kafin ya ce “Dyja tawa, ina sonki sosai fa. A zauna shiru ba a rigima, kina gaba da hakan”ya karasa maganar cikin dariya, Sai kuma ya janyo ni jikinshi yana shafa cikina ya ce” Tana sona, ni kuma ina sonki”

Na ɗan ture shi kadan kafin na ce “Kai ma kana sonta”

Ya ce “Amma ba kamar yadda nake sonki ba, ke fa kin mamaye ko ina a kirjina”

Baki na tabe, sannan na ce “Kuma ai da yanzu ina gida, kila ma na yi wani auran”

Fuska ya bata kafin ya ce “Ke abu baya wucewa a wurin ki ko? To ki ci gaba” daga haka ya fice daga falon

Raina yay ta yi min babu dadi, idan har da gaske Zahrah son Bashir take yi, akwai aiki a gabana ba karami ba, ina zan iya da ita, ga wayewa ga ilmi, ga kudi, ka kyawu ga iya kwalliya. tabbb ina ganin rayuwa. Haka na yi ta sake-sake har zuwa lokacin da kiran Bashir ya shigo wayata, na daga ba tare da na ce komai ba. Shi ne ya ce “Ki je online na turawa Zarah lambarki Khalil na son ganin ki”

Darajar Khaleel ta ci na tafi online din, ina zuwa kuwa kiran ta na shigowa. Dole na warware fuskata musamman yadda na ga tata fuskar cike da fara’a

Cikin dariya ta ce “Da alama yaron ki ya fasa zama matukin jirgin saman sojoji, Sai dai ya dawo gida Ruma ki bude mai yar container a nan kofar gidan su Inna ya rika cajin waya da turawa ƴanmata fina-finai”

Sosai maganar tata ta ba ni dariya, don haka na tuntsire da dariya ita ma ta shiga taya ni, bayan na tsagaita da dariyar ne na ce “Me ya faru?”

Ta juya camerar kan Khalil wanda ya yi laushi ta ce “Kalle shi ki gani, tun da na ce zan tafi ya yi kamar zai yi kuka, karshe ma ya kama kuka wai a kira mishi ke”

Na ji babu dadi a kirjina, Allah Ya sani ina son yaran, har gobe ban daina kewar Affan ba, duk lokacin da mu ka yi waya sai in ji Ina ma yana kusa da ni.

Tunanina na katse da fadin “Khalil me ya faru kuma?”

“Ba komai” ya yi maganar kamar zai yi kuka

Murmushi na yi kafin na ce “Haba big bros, Kamar ba namiji ba, abu da nan da kwana biyu za ka dawo. To idan ka ci jarabawar kuma ashe ba za ka zo makarantar ba?”

Ya yi saurin cewa “Zan zo”

“To shi ne kuma tun yanzu za ka fara kuka, kar ka sake Abbanku ya gani, daman ka san dai ba son nesa din yake ba, yasin ya ce ka dawo gida”

Kai ya jinjina min alamar to, kafin na kara cewa “Ka ji dai abin da na fada ma da za taho ko, ban da wasa da sallah Khalil”

Kai ya kuma jinjinawa hade da dauke hawayen da yake ta makalewa tun dazu. Ni ma sai na yanke kiran ina kara jin babu dadi.

Sai da su Mama suka dawo na dan rage damuwa. Bashir kam da ya dawo kamar komai bai faru ba da zai fita dazu, ni ma sai na warware mu ka ci gaba da harkokinmu.

Ranar Laraba da yamma na bude status din Zahrah, Sai na ganta cikin familynta suna ta Nishadi, ta yi caption din videon da “Home is sweet”

Da sauri na rubuta mata “Ba dai kina Katsina ba?”

Ta yi reply da “Dazu na shigo da rana”

Emojin nan mai zaro ido na aje mata kafin na ce “To yarona fa?”

Ita kuma Emojin nan mai rike baki ta ajiye min kafin ta ce “Yana can na siyar da shi”

Na yi dariya kafin na ce “Ba haka nake nufi ba, na san yau za su yi exam, ke kuma kin taho, shi kuma yana can, ga shi ban ji Abbanshi ya ce zai je ba” na rufe maganar da hada mata Emoji na kuka

Sai ta yi dariya ta ce “Amma duk da haka ai kin yi min kara”

Emoji mai rufe fuska alamar kunya na tura mata sannan na ce “I’m sorry”

“Tsakanin ke da Khalil din ban san wa ya fi damuwa da wani, komai zai ce Auntynmu. Kar ki damu, na yi mishi booking din jirgi, In Sha Allah karfe uku na rana na kawo miki shi har gida” ta rufe maganar da emojin dariya

Ni ma dariyar na yi kafin na shiga yi mata godiya.

Bayan Bashir ya dawo na fada mishi yadda mu ka yi da Zahrah, Sai cewa ya yi shi bai san ma tana Katsina ba. A zuciyata na ce “Ba wani nan, da wannan kauɗi naka”

Tun daren nake tunanin abincin da za tarbi Zahrah da shi, in tuna wannan in tuna waccan, karshe dai na tsaya a kan masa, saboda na ga ranar da ta je Ruma ita kadai ta ce, ta ce wai ita ce bakuwarta

Don haka Alhamis bayan yara sun tafi school na shiga gyaran gida, zuwa 11 na gama tsab, Sai, kuma na markada shinkafar da na jika, na, hada masa, na kai waje, na dawo na shiga hada miyar egusi, da ta ji Ice fish, Wanda na wanke da lemon tsami saboda karni.

Bayan na hada miya, Sai kuma na yi mata pepechicken.

Sai da na yi sallahr azhur na shiga siya masar, bayan na kammala na gyara kitchen din tsab kafin na shiga wanka, zuwa lokacin kam ba a maganar gajiya, dama ga nauyin ciki.

Rigar rubber material na sanya mara nauyi, wacce kuma ta ba ni damar sakewa babu takura.

Na dawo falo na zauna ina kallon agogo, can kuwa sai ga kiran Zahrah, bayan na daga ta ce “Alhamdulillah yaronki ya sauka ƙalau”

Ina dariya na ce “To Alhamdulillah” ita dariyar ta yi kafin ta yanke kiran.

Ta shi na yi hade da kara turare gidan, ban jima da gama turare gidan ba kiranta ya kara shigowa ta ce “Muna street din ku yanzu”

Ai da sauri na fita hade da wangale masu gate, tun da ta shigo ta sauke glass din side din tana min dariya. Ni din ma dariyar nake yi, tana gama parking Khaleel ya fito a guje ya fada jikina, na ko rungume tsam kamar zan mayar da shi ciki, sai murna muke yi kamar mun yi shekaru ba ma tare.

Da kanta ta je ta rufe gate, kafin ta fitar da jakar Khaleel da wasu manyan ledoji wadanda na tabbatar tsaraba ce, Khaleel na manne da ni ya dauki jakarshi da leda daya, na kai hannu zan dauki ɗayar ta ce “Ki samu ki sauke wannan kayan na gabanki tukun”

Dariya na yi ina fadin “Wannan ai babu nauyi”

Haka muka jera har zuwa part dina, idanunta ta lumshe hade da warware gyalenta ta zauna kan kujera tana fadin “Wash Allah! Ka ji wata ni’ima mai dadi, ga wani kamshi mai dadi”

Dariya na yi hade da zama ina fadin “Sannu da zuwa, an gode da dawainiya Allah Ya saka da alkairi”

Ba tare da ta kula da magana ta ba ta ce “Za ki yi min recommending turaren nan, Gaskiya yana da dadin kamshi”

Dariya na kara yi sannan na ce “Kar ki damu gidan kika zo”

Da sauri ta ce “Ke ce ke siyarwa ?”

Kai na jinjina alamar eh sannan na ce “Da kaina nake haɗawa”

“Ma Sha Allah! Gaskiya ina so, kuma zan kawo miki customers”

“Na gode” na fada kafin na ce “Bismillah ga abinci fa.”

Bangaren dining din ta kalla, kafin ta ce “Bari in yi sallah, kar in ci in kasa yi”

Samana na kai ta ta yi sallah, Sai yaba komai take yi, wai ina da tsabta sosai, ga ciki amma bai hana ni yin komai ba. Ni dai da murmushi nake bin ta.

Bayan ta sakko ne, na shiga kokarin zuba mata abinci, saboda shi Khaleel har ya zuba ya fara ci.

Fara cin abincinta babu jimawa su Maama suka dawo, tun da suka shigo idanunsu ya fada a kan Khaleel ai sai ihu murna, shi din ma haka, ni da Zahra kam bakinmu ya ki rufuwa, Sai washe shi muke yi.

Cikin dariya ta ce “Wai haka kuke son shi?”

Dariya kawai na yi ba tare da na ce komai ba, ita ce ta kuma cewa “Sai na ji yara da yawa na burgeni, amma gaskiya yanzu commitment dina ba za su bar ni in yi ciki in haihu ba”

Na ce “Haba, ba dai ki yi auran ba.”

Tana shan kunun ayar da na hada ta ce “I’m telling you Auntynmu, ba zan iya haihuwa ba yanzu. Auran ma ba ya gabana”

Dariya na yi, kafin in ce wani abu ta ce “Maganar gaskiya za a yi min take away din Masar nan, da kunun ayar, da ginger drinks din Nan, da pepechicken, ya kamata wadanda zan ba labarin dadin da na ci, su gani su kuma dandana, ko ba saura sai an yi min wani”

Dukkannu mu ka yi dariya kafin na ce “Akwai ma”

Sannan na ji akwai bukatar in daki juju don in ji kukan gwazarma, saboda haka na ce “Kin ce babu aure a gaban ki, kenan mu yaudararmu kike yi?”

Tana goge bakinta da tissue ta ce “Wai Oganki? So I don’t know, Sai abun da Allah Ya yi” yadda ta yi maganar kai tsaye babu wani shakku, ko nuku-nuku ya kara tabbatar min lallai ita din A ce.

Zuciyata ta rika harbawa, amma a haka na ce “Don Allah a bamu dama mu aje record”

Siririyar dariya ta yi hade da fadin “Auntynmu ni yanzu ba zan iya da tension din maza ba, kin san dai zaman aure, yau da dadi gobe babu. Ba zan iya ba” ta karashe maganar hade da girgiza kai tana tabe baki

Na ce “kodai don kin ganshi gurgu, kina ganin abun kunya ne yadda kika ficen nan ace kin auri gurgu”

Baki ta bude alamun mamaki kafin ta ce “Kun hada baki da shi ne, shi ma haka yake fada min”

Gabana ya fadi, wato namiji munafuki ne, ashe yana can yana lallabata ta aure shi, ni kuma yana fada min ita ce ke son shi.

Na kawar da wannan tunanin gefe sannan na ce “Ko daya, wlh bamu hada baki ba”

Ta ce “Zan iya auran Bashir ba ruwana, mutane basu fahimce ni ba ne, ba wai ina yabon kaina ba, amma ina da sauki kai sosai, sai da wasu suna ganin baki aure ne sai mai kudi, na ki aure ne saboda ina adawa da shi, ina kuma zuge wasu kar su yi, wasu ma cewa suke wai wuya na sha wurin mijina shi ya sa yanzu ba na son aure”ta karashe maganar da wani murmushi mai nuna rashin jin dadi.

<< Hasashena 46Hasashena 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×