Skip to content
Part 48 of 49 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Komai ban ce ba, saboda yadda ta fada din, hakan ake ce mata, ni dai da yake ba tu’ammali nake da social media ba, ban santa ba, Sai lokacin da suka fara alaka da Bashir, amma daga lokacin nake bibiyar duk wasu shafukanta, a nan na fahimci irin power ta,da yadda ta yi ƙaurin suna. Na kuma ga irin zarge-zargen da mutane suke yi a kanta. Amma yanzu da nake mu’amala da ita, Sai na fahimci macece mai saukin kai, iya mu’amala, taimako, da son ganin kowa ya samu cikar burinshi, tana da Juriyar kalubale.

Tunani ta katse min da fadin “Wai kin san me ya sa na ki yin aure?”

Kai na girgiza alamar a’a

“Saboda ina son in tashi da mijina a aljanna, jikina yana ba ni shi din dan aljanna ne, saboda ayyukan alkairinshi, ba na son in yi aure, in tashi ranar lahira ba da mijina ba” ta yi maganar hade da dauke hawayenta. Sannan cikin sansanyar murya ta ce “Shi ya sa tsawon shekaru sha biyar na rike kaina, wlh ban taba aikata zina ko madigo ba, kamar yadda mutane ke zargina. Na rikewa mijina kaina, na tsaya na ba yaranmu tarbiya da ilmi kamar yadda kullum yake fatan ya ga ya yi Allah bai ba shi iko ba. Salman yana karantar medicine, Baffana kuma likitan zuciya, saboda heart attack ne ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinsu”

Kai na jinjina cike da jin tausayinta, mutuwar miji akwai tashin hankali, wacce mijinta ya rasu ne kawai za ta fahimci hakan, musamman idan ya kasance akwai kyautatawa a tsakaninsu.

Duk muka juya muna kallon kofa yayin da Bashir ya shigo yana fadin “Ah-ah-ah-ah! Surprised! Yau Barrister Zahrah ce a gidanmu?”

Yadda ya ga fuskokinmu ne ya sanya shi rike fara’arshi, tare da saurin karasowa wurin mu ya zauna kujerar da zai iya kallon fuskokinmu duka ya ce “What is going on here? Anything wrong?”

Zahrah ce ta fara dauke hawayenta ta mike tsaye hade da fadin “Auntynmu a yi min take away dina”

Komai ban ce ba na mike jiki babu kwari na shiga kitchen domin hada mata abubuwan da take so.

Lokacin da na fito zaune na same ta, kanta a kasa da alama kuka take yi, yayin da Bashir ke magana kasa-kasa. Kan dinning na aje basket din na Kuma haurawa don hado mata turarenta, a can kuma na samu su Khalil suna rashin jin su.

Ban fada mishi Babanshi ya dawo ba, kawai na yi abin da ya kai ni na fito.

Yanzu kuma a tsaye na same su, kafadarta sagale da gyalenta, hannunta kuma rike da hand bag din tag. Bashir kuma yana rike da basket, ganina ya sa suka nufi kofar fita, na karasa saukowa daga sama steps din ina fadin “Ba dai tafiya za ki yi ba, ba ki yi sallama da yaron naki ba”

Bashir ne ya ce “No leave him she is not in the mood”

Bayansu na biyo hade da aje mata Ledar hannuna a back seat Kamar yadda na ga Bashir ya yi mata. Sannan na zagayo inda take tsaye ina fadin “Babu kalmar, ko wace kalma ta yi kadan wajen nuna godiyarmu gare ki, Allah Ya saka miki da alkairi, ya biya bukatun ki na alkairi, ya raya mana yaran mu, ya tsare su a duk inda suke, ya jikan mahaifinsu”

Murmushi ta yi tana fadin “Thank you so much, na gode”

Ba su wuri na yi, saboda na fahimci suna bukatar hakan, Sai ko ga shi duk sun shiga cikin motar.

A can lallashin kaina nake yi, ga tausayin Zahrah ga kuma kishin mijina, haka nai ta kai kawo, har sai da na ji tashin motar Zahrah sannan na samu nutsuwa. Zuwa can kam sai ga Bashir ya shigo.

Na bi shi da kallon tuhuma, kawai sai ya share ni, ya haura sama wajen yaran shi. Sai da lokacin sallar magriba ya yi suka fito.

Yadda ya share ni bai  yi min maganar Zahra ba, haka ni ma. Mu ka ci gaba da jan zaren mu

Bayan sati biyu da dawowar Khalil, Zahrah ta kira wai ya samu admission, Wai Allah murna, kila ranar bai yi bacci ba. Ta turo min da list din abin da school din ke bukata da kuma dokokinsu, uniform dai a can ake bayarwa.

Haka Bashir ya shiga hidimar haɗawa Khalil kayan tafiya. Khaleel kuma damuwarshi in haihu kafin ya tafi, kullum sai ya yi maganar, “Auntynmu Allah Ya sa ki haihu kafin in tafi” sai dai in yi mishi murmushi kawai, saboda na, san cikin bai isa haihuwa ba.

Ana gobe zai tafi ya ce in kira mishi Momyn Farhan ya gaisa da su Affan, tun da ya san gobe time da zai tafi su kuma suna school. Na kira su kam, bayan mun gaisa da Rahma da sauran yaran sai na ba Khaleel, haka suka yi hirarsu har sai da ya gaji don kan shi, sannan ya kawo min wayar.

Da safe kam da za su wuce, duk yadda na so daurewa kar in yi kuka sai da na yi, na yi mai isa ta bayan sun tafi, gidan ya koma min kamar ba kowa.

Da yamma sai ga status din Zahrah a school din su Khaleel, wannan ya tabbatar min tare suka je.

Duk yadda na so danne kishin, Sai da na ji wani ya soki zuciyata, amma na son dole in yi hak’uri hade da kawar da kai Zahrah ta yi nisa a zuciyar Bashir, ni har na fi son ma su yi auran a kan su yi ta tarayya babu auran.

Ranar Juma’ar da ta kama Lahadi visiting din Khaleel na haihu Baby girl.

Alhamdulillah kawai zan ce amma Sam ban so haihuwar nan ba, na so ace  na gama hada kayan visiting din sannan na haihu. Duk da ba wani abu ake kai musu ba, da ya wuce abin da za su ci a wurin,  dan snack kadan, wanda suke tafiya da shi hostel da drinks, amma duk da haka na so ace ni ce na yi, visiting din Khalil na farko, ba wai iya in yi abinci ba, har zuwa ma na so in yi saboda na yi  missing din shi.

Cikin kankani lokaci maganar haihuwa ta ta zagaye dangi, ai kam  kira  ke shigowa wani kan wani. Affan kam kullum zai  kira video call sau ba adadi ya ga Baby, kullum ya ce “Auntynmu kamar in taho. Don dai ba a yi hutu ba da na zo” na kan yi mishi dariya kawai ganin yadda ya damu da wannan haihuwa.

Maman Aiman na roka alfarma ta yi wa Khalil cincin, cake, dambun nama da kifi, ta yi mishi pepechicken, safiyar Lahadi kam dole na shiga kitchen na yi mishi chips da eggs in egg.

Dama Zahra ta kira ni, wai ba sai na yi abinci ba, ta bayar da oda a Abuja, wannan ya tabbatar min za ta je kenan.

Jirgin karfe tara Bashir ya hau, misalin karfe 11am kuwa ya kira ni wai in je online ga Khalil mu gaisa. Ai da gudu na tafi, na kira video call din, Khaleel baki ya ki rufuwa, tun kafin mu gaisa ya ce “Auntynmu, Abbanmu ya ce kin haihu”

Ni sai na ji ma duk kunya ta kama ni, yaran nan fa zuwa yanzu, sun san hanyar da ake bi a samu ciki, amma Bashir da kwarin gwiwarshi yake basu labarin na haihu.

Maimakon in amsa mishi tambayar sai na juya camerar kan Baby da ke sanya cikin overall pink color masu taushi, ai tuni ya hau ihun “Auntynmu dago min ita sosai”

Hannu na sanya na dago ta, ya ce “Auntynmu da Affan take kama, kamar dai Maama” yadda ya yi maganar ya sa na yi dariya, Bashir kuma ya ce “kar ka damu next time twins za ta haiho duk masu kama da kai” sai ko ga shi yana murna, a raina na ce,”Ai an yi kenan auran wata da wani, ba yaji babu ganin gida, yara na ta girma ni ina ta faman haihuwa, idan shi ba ya jin kunya ni ina ji”

Khaleel ya katse min tunani da fadin “Auntynmu a sanya mata sunaRamla”

Na ce “An yi an gama babban yaya”  baki ya washe sannan mu ka ci gaba da gaisawa da tambayarshi school. Mun jima muna hira sannan Zahra ta iso, ita ma muka gaisa, sannan na yanke kiran saboda in basu damar gaisawa.

Arround five ya kuma kirana wai za mu yi sallama da Khalil, bayan ya mikawa Khalil din, ya shiga jero min godiyar kayan visiting, sannan kuma ya lissafo min abin da yake so a zo mishi da shi next time, sannan mu ka yi sallama.

Sai washegari Bashir ya dawo gida, na kuma tabbata yana tare da Zarah, amma ban nuna mishi komai ba, mu ka shiga hidimar bikin suna.

Ranar Alhamis  yan Kano da ƴan Ruma suka iso, safiyar juma’a aka yi suna, yarinya ta ci sunan Ramla. Wata irin kauna da soyayya nake yi mata, fiye da sauran yarana, ji nake kamar waccan Ramlan musamman da ya kasance suna kama sosai. An sha shagalin suna, kamar ranar aka fara yi wa Bashir haihuwa, har da irin maza masu kidan gangan nan  suka zo.

Safiyar Asaw kuma aka fara watsewa, su Yusrah dai sai Lahadi suka tafi.

Bashir ya samo min tsohuwa mai dora min ruwan wanka safe da yamma.

Asabar da rana muna tsaka da cin abinci sai ga Zahra, yara suka gaishe ta, sannan suka bamu wuri, muka shiga gaisawa, bayan mun gaisa ne ta ce “Ba mu zo barka ba sai yau”

Dariya na yi kafin na ce “Ai kina kokari sosai, kullum kina cikin commitments”

Gyalenta ta warware kafin ta ce “Ki bari kawai, wlh mun shiga court ne wata shari’a”

Ina mika mata Babyn na ce “Eyyah! Allah Ya taimaka”

“Amin” ta amsa kafin ta ce “Ma Sha Allah, fine baby, Kamar ki ba ni”

Tana dire maganar na ce “Na ba ki”

Duk mu ka yi dariya kafin ta ce “Kamar gaske”

Na mike zuwa kitchen don zubo mata abinci ina fadin “Gaske ne mana”

Abincin na jera a gabanta, kadan ta ci abincin ta ce ta koshi, sannan mu ka shiga hirar duniya, Sai da ta yi sallahr la’asar sannan na yi mata rakiya, ina yi mata godiyar abun arzikin da ta kawo min.

Bayan ta tafi ne, na shiga bude ledojin, kayan baby latest, kaf babu mai karamin kudi, har da takalma, socks, huluna, tarkace dai kaca-kaca.

Ni kuma atamfa ce turmi biyu, da lace kala biyu ta kawo min, ko wanne dauke da gyale, takalmi da jaka, da kuma mayafin da ya dace da su.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ina jego na, Bashir na shan soyayyarshi da Zarah, soyayyar da bai iya boye ta, ka’ida ne duk sati zai   je Kaduna.

Zahra ba ta taba canja min fuska ba, ko yi min kallo a matsayina na matar bazawarinta, ko maganar Bashir ba ta hada mu da ita. Kuma ku san kullum sai mun yi magana, a chat ko a waya. Ni din ma haka na rika daurewa ba na nuna mata komai. Ina dai yawan faɗawa Bashir don Allah idan auranta zai yi kawai ya aure ta, amma wannan alakar ta isa haka nan. Kai tsaye ya ce wai in lallaba mishi ita, ta ƙi amincewa ya auretan

Ranar ban yi bacci ba, na rika jin me ya kai ni ma yin wannan zancen, ga shi dai na janyo kunne na ya ji abun da bai yi tsammani ba. Na rika hasaso kaina muna kishi da Zahra, lallai sai dai in yi zaman ƴaƴa.

Ba mu yi arba’in visiting ya kuma zagayowa, duk yadda na so zuwa Bashir hanawa ya yi, wai ba zan daukarwa Baby iska ba, kuma ai an kusa hutu ma, Khaleel din ya dawo. Haka na kuma hada kayan visiting ya tafi, a wannan karon ma tare suka je da Zahra, saboda ita ce ma ta kira ni video call wai mu gaisa da Khaleel. Ni har mamakinta nake yi, kai tsaye take abun ta, ita ko irin ta hasaso ina jin haushintan nan ba ta yi. Ina ruwan kemudugus.

Wannan karon ma tare suka dawo, don misalin karfe takwas na dare jirginsu ya yi landing, kuma da motarta aka kawo Bashir gida. Tsabar bushewar ido ma da bakinshi ya ce min direban Barrister ne ya kawo ni, haka yake kiran ta.

Haka na zuba ido ina kallon Ikon Allah, kullum alakar Zahra da Bashir kara karfi take yi, ga shi sun ki auran juna, kuma ta cika min idon da ba zan iya bude wuta a kan alakar tasu ba, dole nake zuba ma wani abun ido, wani kuma in tsawatar.

An yi visiting da sati uku aka yi wa su Khaleel hutu, wannan karon ma Zahra ce ta biya mishi kudin jirgi, saboda karfe 11 na safe ya iso gida, yara sai ihu, ga babban yaya ya dawo, ni kaina murna nake yi mara misultuwa, shi kam hankalinshi kaf a kan Ramla, tun da ya iso ita ya fara raruma, Sai kallon ta yake yi, yana murmushi.

Abin da na fahimta idan ka dade ba ka ga mutum ba, lokacin da za ka gan shi abu biyu sai ya faru, kodai ya girma ko ya lalace, Khaleel kam wani girma na ga ya yi min, ga muryarshi ta bude, wani gwangwaran, abin da ke nuna girma ya zo.

“Auntynmu!” ya kira sunana. Na dago ina daga barewa Haidar chocolate din da nake yi ina kallon shi. A hankali ya ce “Wannan Ramlan kamar waccan Ramla din, sosai suna kama”

Murmushi na yi kafin na ce “Kowa yana fadin haka Khaleel” sai kuma muka shiga hirar waccan Ramlan, wani lokaci mu yi jimami, wani lokaci kuma mu yi dariya. Su Maama kam sai tambaya suke yi, wacece Ramla, a ina take.

<< Hasashena 47Hasashena 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×