Wunin ranar nan gidan kowa cike da farin ciki saboda dawowar Khaleel. Haka ma Bashir bakinshi ya ki rufuwa ya ga yaron shi ya fara zama saurayi.
Don sosai Khalil ya yi girma, Maman Aiman har tsokanarashi ta yi, wai kodai baya koshi a nan gida ne, irin wannan ƙiba haka, kamar jira yake ya tafi, wai ana zuwa makaranta a yo rama, shi ya dawo a cike.
Da dare bayan na yi shirin bacci ina sanyawa Ramla pampers Bashir ya shiga sanye da jallabiya, gefen gadon ya zauna yana kallo na, har na gama shirya Ramla, cikin overall na bacci, kasancewar ba baccin take yi ba, ya dauke ta yana yi mata wasa, ita kuma tana wangale mishi baki. Kan cinyarsa ya kwantar da ita kafin ya ce “Da ace wancan Ramlan tana nan, kuma a lokacin da kika haifi Maama wannan kika haifa, to babu wanda zai ce ba identical twins ba ne”
Na ce “Abin da Khaleel ya fada kenan dazu”
“Shi ma ya ga kamar kenan?”
Na ɗan yi murmushi kafin na ce “Ya gani, Affan ma kullum sai ya fada”
Zaman shi ya gyara yana fadin “Tun da na ce mishi Khaleel na hanya ya damu, shi ma zai zo gida”
“Ni ma nan haka yake damuna, ai ya yi kokari, ku san shekera daya fa”
“Da bari na yi sai yi SSCE kin ga sai ya zo mana hutu kafin result ya fito”
Na ce “To Allah Ya kai mu”
“Amin” ya amsa kafin ya ce “Finally dai Zahra ta amince da ni”
Gabana ya yi wata irin faduwa dam, zuciyata ta rika harbawa da sauri, jikina ya mutu likis, kwakwalwata kuma ta yi dummm…
Da kyar na daidaita nutsuwata ina fadin “Ma Sha Allah, Allah Ya tabbatar da alkairi”
Ya amsa da amin, daga nan kuma sai dakin ya yi shiru, saboda ni dai ban san me zan kara cewa ba kuma ba. Can kasan zuciyata ma wani irin tukuki nake ji hade da fargaba, zaman da mu ka yi da Sarai ya fado min, zama mai cike da tashin hankali, duk Zahra ba ta yi kama da haka ba, amma kuma ai ban san irin salon nata makircin ba, musamman yadda take a wayen nan, ga shi Bashir na yi mata wani irin so, fiye da yadda yake yi wa Sarai, a lokacin da yake neman ta.
“Khadija!” ya kira sunana a hankali. Na juyo a sanyaye ina kallon shi, ba tare da na amsa ba
Yadda yake kallona ne ya sanya ni saurin sauke idanuna kasa, Ramla ya aje, ya maye gurbin inda ya dauke ta da ni. A hankali ya ce “Wlh Khadija ba ina aure ba ne don ba na sonki, ko don kasawarki, ko daya. Kawai dai akwai wannan Ɗabi’ar a jikin namiji, komai son da yake wa mace hakan kuma ba ya hana shi hango wata. Amma ko kusa, a yanzu babu macen da ta cika zuciyata kamar ke, na san ba lallai ki yarda ba, amma kuma wannan shi ne gaskiya “
Ya dan tsagaita da maganar sannan ya dora da” Akwai abubuwa da yawa suka cancanta a soki don su, wanda ba ni kaɗai ba kowa ma zai iya son ki don su. Misali, yadda kika rike min yara, kina da hak’uri hade da kawar da kai, ba kya da yawan ba ni-ba ni, kin san maza mun tsani ba ni – ba ni. Kina da tsafta, kin iya abinci, kina da ilmi, kin iya mu’amala da mutane, sannan kin iya gyaran shimfida “ya kai karshen maganar hade da dago fuskata yana murmushi, ni kuma na yi saurin sunne kaina a kirjinshi ina murmushi.
Cikin murmushin ya ce” Ban taba tunanin za ki iya juya ni a gado ba a farkon auranmu, saboda kunyarki, amma zuwa yanzu kin karyata hasashena”har zuwa lokacin murmushi yake yi.
Kafin ya ce “Akwai kuma abin da personally ni ne nake son a wurin mace. Ina son mace me ƴar rigima time-time not always, kuma kin iya wannan, ke din rigimammace. Mace sai da ɗan bori, amma shiru ba borin nan sai ki ga macen kamar namiji.” muka dan yi murmushi a tare kafin ya ce” Kina da fada sometimes, ba kya ɗaukar raini, wannan yana burgeni, duk da wani lokaci ya kan bata min rai, amma daga baya idan na huce sai in rinka murmushi ni kadai idan na tuna. Ina son mace mai yanayin jikinki, waye zai kalle ki ya ce kin haihu hudu, komai cas-cas”ya kuma dago fuskata yana kallo na.
Na yi saurin duka da kaina, shi kuma ya ci gaba da fadin “Wadannan dalilan ya sa kika yi nisa a zuciyata. Ko lokacin da na furta miki kalmar saki, Sai da na fi ki cutuwa, ba na son in fada ne kawai ki ga lago na” yanzu kam ni ce na dago ina kallon shi, ya ce “Yes! I’m telling you na shiga tashin hankali, da ace lokacin hankali kwance yake za ki lura da yadda gaban motata ya mole, wata bishiya na daka, ban da Allah Ya kiyaye da sai dai a kira a ce ki je asibiti kodai ki taras da gawata ko kuma dai jikin babu yadda yake. Ji na yi kamar raina ya fita a gangar jikina, ban da ina tsoron kar ki ga na fado, da ko gidan nan ba zan fita ba zan ce na mayar da ke. Ina son kiran Inna a lokacin ina kuma jin tsoro, ban san me zan fada mata ba, cikin ikon Allah ma sai ga kiran ta, na fi ki farin ciki da umarnin da ta ba ni, saboda ina pillar dama zan jingina wajen mayar da ke ban samu ba. “
Ya kuma nisawa a hankali kafin ya ce” Ba zan ce miki komai a kan Zahra ba, ni dai kawai zan aure ta da kyakkyawar niyya, in hada ku da kyakkyawar niyya, kuma Ina yi mata kyakkyawan zato, amma a wannan karon na daukar miki alkawarin abin da ya faru lokacin Saratu ba zai faru lokacin Zahra ba. Da zarar kin ga wani abu da bai gamshe ki ba gami da ita, just tell me, ni kuma na yi miki alkawarin aikata abin da duk kike so. Wannan alkawari “ya karasa maganar yana miko min hannun shi na dama alamar in riƙa.
Ban mika nawa hannun ba, Sai kallon shi da nake yi, da kai ya yi min alamar in saka hannuna, kamar mara wayau haka na saka hannun nawa cikin na shi, ya damtse da dan karfi yana fadin” Deal!”
Idanuna na lumshe a lokacin da nake zare hannuna cikin na shi, lokaci daya kuma zuciyata na tattauna maganganun da ya fada min, wani bangaren yana yarda da su, wani kuma yana fatali da su.
A wannan daren har tsoro ya ba ni, saboda yadda Bashir ya tafiyar da ni, Sai ga ni da safe da shan maganin ciwon jiki, har da su zazzabi. Su Khaleel ne da Bashir din suka yi ta hidimar gidan.
Ranar Monday iyayen Bashir suka zo nemawa Bashir auran Zahra, Sai da suka gama komai a can, aka yi baiko hade da sanya ranar daurin aure kafin suka biyo gidana, cikin sa a na gama abinci, aka bude musu dayan part din, Khaleel ya kai musu abinci, kafin na je na gaishe su, Sai wajen karfe uku suka tafi, a lokacin ne kuma Bashir ke sanar min, dauri aure sai nan da wata biyu masu zuwa. Na yi addu’a da fatan alkairi. Amma deep down kam ba na jin dadi, tsoro da fargaba ke damuna, wannan karon ba kishi nake yi ba sosai, tsoro ne ke damuna.
Misalin 6:15pm Khaleel ya dawo ball, yana zaune sama kujera yana zare socks din kafar Shi ya ce “Auntynmu na ji dazu su Baffa suna ta yi wa Abbanmu Allah Ya sanya alkairi, har da Allah ya kai mu lokacin, wai me ya same shi ne?”
Na juya wurin su Maama da suka yi min ratai da ido suna jiran amsar da zan ba Khalil, murmushi na yi a zuciyata a fili kuma na ce” Aure zai yi”
Khaleel ya waro ido alamun mamaki, Maama kuma a zabure da mike zaune with shock ta ce “Aure kuma!” yadda ta yi maganar da yanayin reaction dinta Sai na ga kamar ba yar primary five ba. Na kalle ta da kyau kafin na ce “An hana ne?”
Warware fuskar ta ya daga alamun mamaki zuwa alamun damuwa ba tare da ta ce komai ba. Khaleel ne ya ce “Wa zai aura kuma?”
“Zahra. Barrister, ta Kadunan nan” na ba shi amsa
Ya dan yi shiru, kafin ya tabe baki, hade da daga kafadu sama ya ce “Ba laifi tana da kirki”
Daga haka ya mike zuwa dakinshi.
Na juya kan Maama wacce ta kara hade fuska, ganin mun hada ido, Sai ta turo baki kafin ta koma ta kwanta
Assidiq ya ce “Nan za ta dawo Auntynmu?”
Kai na jinjina alamar eh, ya kuma cewa “Dakin wannan matar da ta tashi?”
“Eh” na amsa mishi. Ya kuma cewa “Amma ita ba ta rika hana mu shan fruit ba ko, da yanka mana ball, da yin fada da su Ya Khaleel da Ya Affan idan ya dawo?”
Da mamaki nake kallon Assidiq wato kaf wannan abubuwan bai manta ba, lallai ba shi da mantuwa.
Haidar ya ce “Dukanku take yi?”
Assidiq ya ce “Eh mana, har fada suka yi da Auntynmu yaro, Auntynmu ta kada ta ta yi ta dukanta”
Cike da jin dadin labarin Haidar ya ce “Yauwa Auntynmu ashe kina da karfi, da ina nan zan rika naushinta haka (ya shiga gwada yadda zai naushetan a jikin fillon kujera”
Cikin tsawa Maama ta ce “Dalla can ni kun dame ni, mutum yana fama da abin da yake damunshi?”
Da mamaki na ce “Me ke damunki Maama?”
Komai ba ta ce min ba, na kuma maimaita tambayata, Sai kawai ta fashe da kuka, daidai lokacin kuma Khaleel ya fito cikin dakinsu, ya zuba mata ido kafin ya ce “Me aka yi mata?”
Na ce “Oho” Maama kuka take yi sosai, ni dai komai ban ce ba, Khaleel ne ya ja ta zuwa dakinsu, ni kam ma sai na haye sama don shirin yin sallahr magriba.
Na fito daga bayi bayan na yi alwalar magriba, Khaleel ya shigo dakin yana dariya, ya ce “Auntynmu bari in ba ki update mai zafi kafin in tafi masallaci, kin san kukan me Maama take yi” kai na girgiza alamar a’a
Ya ce “Wai Abbanmu zai yi aure, wai a kan me zai yi aure” Tare muka fashe da dariya, yana kokarin fita saboda an fara kiran sallah ya ce “Allah sai na fadawa Abbanmu, ni ma fa ban son auran nan Haba don Allah” ya karasa maganar kamar zan yi kuka. Ni dai hijab din sallahta na shiga nema, lokaci daya kuma Ina dariyar abun, kila shi ya sa ban ji kishi ba, ashe an raba mana ne ni da wasu.
Na idar da sallah Maama ta shigo fuska a hade ta zauna gefen gadona, ba tare da ta ce komai ba, kamar minti biyu da shigowarta na ce “Ya aka yi wai?”
” Ya Affan za ki kira min”
“Me za ki yi mishi?” shi ru ta yi ba ta amsa ba, bayan na kara maimaita tambayar ne ta ce “Magana zan yi mishi”
“Wace irin magana”
Kuka ta fashe da shi kafin ta ce “Ni dai don Allah ki kira min shi”
Murmushi na yi a zuciyata a zahiri kuma
Baki na saki ina yi mata kallon mamaki, sannan na ce “ciro ga wayar can a wurin caji”
Bayan ta miko min ne na kira Rahma, mu ka gaisa, sannan na ce ta hada ni da Affan Maama na son yin magana da shi. Na karashe maganar ina kallon Maama da take dauke hawayenta.
Kunna recording na yi, sannan na mika mata, ita kuma ta fice. Like 10mns ta shigo hade da mika wayar, har zuwa lokacin Affan na kan call din. “Auntynmu da gaske Abbanmu aure zai yi?”
Rike haba na yi kafin na ce “Wai ina ruwanku da auranshi ne, yau na ga ikon Allah, nawa ne gudunmuwarku a ciki”
Fuska ya kuma batawa sannan ya ce “Auntynmu kalli fa abin da ya faru lokacin wannan matar, shi ne Abba zai kuma auro wata, kuma ga shi ni da Khalil ba ma nan, balle ma idan ta yi wa su Maama abu mu tare mu su”
Murya na kwantar sannan na ce “Affan ba fa duk aka taru aka zama daya ba, a ko ina akwai mutanen kirki, ku rika kyautatawa mutum zato”.