Misalin karfe goma na safe kuwa sai ga telan ya iso, tape ya ba ni, na rika auna duk inda yake son na auna, yana rubutawa sannan ya tafi.
Gidan ya kasance shiru sai ni kadai da bacin raina, saboda ko yau da safe Abban Khalil ya shigo bai ba ni fuskar da zan yi mishi korafi ba. Ya dai dan yi romancing nawa sama-sama ya fice, saboda ana ta kiranshi a waya, alamar ana jiranshi.
Maman Khalil kam sai 2pm ta dawo kamar, kullum tun da ta shige part din ta da yaranta kuma ban kara jin duriyarsu ba.
Abban Khalil kuma sai gab magriba ya dawo, shi ya sa bai shigo dakina ba sai 9pm, yadda na hade fuska ya sanya bai jima ba ya fice. Haka zaman ya ci gaba da gudana, ni da shi sama-sama, yayin da Maman Khalil ke ta shirin biki. Atoh ta ke shiri mana, ni shirin me zan yi, ban san kowa ba, kowa kuma bai sanni ba.
Ni ko waya ba ma yi dasu, ita kam kullum suna kan waya, idan ma ba ta kira ba, su kam za su kira. Ni kuma sai idan Abban Khalil ya kira su, aka yi sa a muna tare ya ba ni mu gaisa.
Ranar Alhamis muka isa garin Ruma da misalin karfe biyar na yamma.
Gidanmu na Ruman muka fara sauka, komai a gyare.
Flat dinmun a jere yake ba kamar na Abuja ba da ya kasance kowa da bangarenshi.
Babu wani tarkace a cikin dakin, idan ka dauke kayan amfani da mutum zai bukata a ko wane lokaci.
Babu aikin da mu ka yi lokacin da muka isa, idan ka dauke wanka da cin abinci, Sai kuma jefi-jefi da mutane ke shigowa suna mana sannu da zuwa. Da yawansu kuma ƴan’uwanta ne, da kuma ƴan’uwan Abban Khalil da suke danyen ganye.
Karfe takwas na dare ta yi min maganar zuwa cikin gida (Gidan iyayen Bashir)
Na gaji sosai, kamar in ce ta je, amma tsoron baki ya sa na bi ta. Saboda tun da muka zo din ma ba hutawa mu ka yi ba, wannan ya fita wannan ya shiga.
Don ma ni ba mu saba sosai ba, iyakata dasu gaisuwa sai su wuce wajen Maman Khalil.
Koda muka shiga cikin gidan ma dai gaisuwar ce kawai, ita kuwa tun da ta aje ni dakin mamar mijinmu ta yi cikin gida kasancewar babban gida ne, ban sake ganinta ba sai da na sanya aka nemota saboda baccin da ke ci na.
Da kyar na isa gida, dama mijin ba nawa ba ne, don haka baccin gajiya kawai na hau yi.
Safiyar juma’a aka tashi da aikace-aikace kasancewar za a yi walima da yamma.
Maman Khalil kam ba zama, komai ita ce a kan gaba, duk wani abu da ake so ko shawara da ita ake yi, duk abin da ake nema to ita ake tambaya, idan ma yi za a yi sai ta bayar da izni.
Ni kuwa kallonta kawai nake yadda take ta kaiwa da komawa ba tare da gajiwa ko kosawa ba.
Kamar ba ita ce matar Bashir Balarabe Ruma ba, matar nan mai tsantsar tsabta kula da kanta da kuma yaranta
Matar nan da take zaune a daki mai A. C da fankacecen gado mai dauke da lumtsumemiyar katifa ba.
Matar nan mai hawa mota da daura zannuwa masu tsada.
Matar da idan ka yi mata kallo daya sai ka ga kamar ba za ta iya kwana rufin kasa ba. Ko mu’amala da ƴan kauye ba, irin haka ba
Amma ta manta duk wadancan abubuwan ta zage da ita ake ta dorawa ana saukewa babu wani girman kai.
Duk da dai asalinta yar garin ce hakan ba zai hana ta bambanta kanta da wasu ba da wata ce.
Abin da na fahimta shi ne sosai take da fada a dangin mijin nan, abu ne mai matukar wahala kafin in samu fada kamar tata balle ma in wuce ta.
Idan kuwa har na kasa samun hakan, to gaskiya a bazance zasu rika kallona. Sannan ba zan yi wani tasiri ba. Saboda ko yanzu din ma iyakaci na da su gaisuwa, amma wata shewa da tattaunawa duk da Maman Khalil ne
“Kai!” Na fada hade da dafe kaina.
Sosai akwai aiki a gaba, ta ina ma zan fara ne?
Kokarin janyo hankalin mijina
Karbar ‘yancina ta yadda zan rika cin gashin kaina
Kafa fadata a zuciyar mijina ta yadda ni ma kominshi zan rika sani, haka komai zai yi in sani ya kuma yi shawara da ni
Ko Neman fada a wajen dangin mijina.
“Cikin wadannan da wanne zan fara ne?”
Na yi maganar a hankali ina kallon mutanen cikin gidan da suke ta sabgoginsu cikin farin ciki da annashuwa.
“Wallahi duk macen da ta yi aure, kuma ba ta da kishiya to kamar tana kan gadon mamanta ne a kwance”
Na kuma fada a zahiri.
Ai tarin kalubale yana ga macen da ta auri mai mata, ni ban san haka abun yake ba, ai da ban je fa kaina a ciki ba, sai in samu saurayina mai dan rufin asiri in aura mu je mu zauna hankali kwance, duk inda yake me yake hankalinshi na kaina. Kodai ya dakko wata daga baya na san zuwa lokacin na yi mata fintinkau, kamar yadda Maman Khalil ta yi min.
Misalin karfe biyar na yamma duk an hallara a farfajiyar gidanmu, a can za a yi walimar
Rumfuna ne manya guda shida, jere da kujeru gwanin sha’awa.
Kowa ka kalla fuskarshi cike da annuri, da yawan mutanen da ke gurin hijabai ne manya a jikinsu wasu ma har da nikab.
Ina jin dalilin da ya sa kenan Maman Khalil ta siya mana hijabai.
Zaune nake kusa da Maman Khalil kominmu irin daya, Ramla na kan cinyata su Khalil kuwa suna gurin Babansu.
Karewa jama’ar gurin kallo nake yi
Maganar gaskiya mutanen garin sun burgeni, akwai su da kara iya mu’amala da rikon addini, son zumunci, uwa uba ilmi zamani dana addini.
Ashe al’adarsu ce hakan shi ya sa Maman Khalil ita ma duk ta hadasu.
Babu abin da ke burgeni irin yadda kowannensu maza da mata, yaro da babba fuskarsa ke dauke da zanen biyu-biyu (11-11) a gefen kunensu, wasu kuma a kan kumatunsu . Sai na ji kamar ni ma in je in zauna a yi min, in shiga layinsu, na rika ji na daban, kamar wata gayyar sodi.
Zanen ba ƙaramin karbinsu ya yi ba, kamar ma shi ne ke kara masu kyau, don gaskiya jama’ar garin Ruma kyawawa ne, ni tun da na zo ban ga wani, wanda muninshi ya kai muni ba Tubarakhallah.
Mun sha wa’azi kam da nasiha a kan zaman aure masu ratsa zuciya.
In da aka zayyano hakkin namiji a kan matarsa da hakkin mata a kan mijinta.
Darajar aure da kuma bambanci da ke tsakanin ibadar matar aure da wacce ba ta da aure.
Ana kiran sallahr magriba aka tashi daga walimar wasu ma duk a gidanmu suka yi sallah.
Bamu samu damar komawa cikin gida ba, saboda gajiya ga kuma baki har da wadanda zasu kwana a gidanmu.
Hatta Amaryar ma da tawagar kawayenta a gidanmu zasu kwana.
Kila shi ya sa Abbansu bai samu damar kebewa da ni ba, kasancewar ni ce mai girki. Ni ma na ji dadin hakan, ko ba komai na dan huta.
Gari na wayewa Maman Khalil, ta kuma ja na zuwa cikin gida, maganar gaskiya na gaji, kan dole na bi ta. Ni kam ba zan iya wannan zirga-zirgar ba. Sam ban saba ba.
Yadda na ga ana ta hada-hada ina raɓe kamar kareriya ya sanya ni kutsa kai cikin su, ni ce daka kayan miya wanke-wanke, yan kananun aiki dai sai in karbe in yi.
Kuma sai na ga hakan yana masu dadi. Har wasu sun fara sakin jiki da ni. A zuciyata na ce “ashe haka abun yake, to ai shi kenan, za mu ci gaba da jarabawa”
Shawara ce dai ba da ni ake yi ba, sai dai Maman Khalil.
“Ko yaushe ni ma za a fara shawarar da ni oho? Ko yaushe zan zama kamar ita?”
Wadannan duk tambayoyi ne da ni ba ni da amsarsu. Ban san kuma ranar samun amsar tasu ba
Haka muka ci gaba da hidimar biki cikin farin ciki da annushuwa, ranar Juma’a aka daura aure, misalin karfe hudu na yamma aka raka amare dakin su, daga can kuma aka wuce dinner, bamu dawo gida ba dai sai kar 11pm na dare. Safiyar Asabar kuma Maman Khalil ta ja nigidansu mu ka wuni, don gobe Sunday za ta wuce abuja.
Na ga karamci kam, na yarda Katsinawa na kara, saboda na ganta da idona ba labari ba. Mahaifiyar Sakeena zam Sakeena, da alama halayenta kaf ta dakko, akwai karamci da kawaici, duk abin da ta ba Maman Khaleel ni ma sai da ta ba ni. Haka mu ka wuni gwanin daɗi cikin ƴan’uwanta, babu kyara ko kallon banza.
Ban taba tsammanin haka daga gare su ba, saboda tun ban saki jiki da su ba, har sai da suka sanya na saki jikin dasu. Abin da na fahimta tana da kyakkyawar alaka da kowa. Sam ba ta da girman kai.
Sai da aka yi sallahr magriba muka dawo, bayan mun yi sallahr isha’i, na taya ta hada kayanta, Sai, wajen 10pm ɗai muka kwanta. Asubar fari kuma Abban Khalil ya kai ta Katsina, daga can ta hau motor Abuja.
Sai kuma na ji gidan shiru babu dadi, kaɗaici ya yi min yawa, in kwanta in tashi, ban warware ba sai da Abban Khalil ya dawo gida.
Tun ina jin rashin dadi gami da tafiyarta, har na warware, na rika cin duniya ta da tsinke.
Ji nake kamar kar mu koma Abuja mu yi zamanmu a nan, sosai yake ba ni kulawa da yin duk wani abu da nake so.
Duk da dai a rana sai ya yi waya da matarshi da yaranshi ya kai sau goma, tana fada mishi wai sun yi kewarshi, shi din ma haka yake fada masu.
Ni kuma ga kishi sai zuciyata duk ta baci, daurewa kawai nake yi, wani lokaci kuma na kasa daurewa har sai ya gane a fuskata amma baya nuna ya gane.
Haka dai muka kwashe sati biyu a Ruma kafin muka fara shirin komawa gida Abuja.
Tarkace masu yawa maman mijina ta ba ni wai in kaiwa Maman Khalil abin da take so ne, haka ma daga gidansu aka aiko da sako wai in kai mata.
Ya na iya, haka na runguma mu ka yi sallama da su na dakko hanyar kano ni da mijina, inda zamu kwana a kanon da safe mu bi jirgin karfe hudu zuwa Abuja.
Shi ɗaki ya kama a hotel, yayin da ni kuma na nufi gidanmu, wanda shi ne karon farko na zuwana bayan aurena.
Na sha tarba kam, kowa murnar ganina yake, sannan kowa cewa yake na canza jikina ya yi kyau duk da dai ban yi wata kiba ba. Ni kam sai baki na washewa, sincerely speaking na ji dadin zuwa gida, wani irin farin ciki nake ji mara misultuwa.
Ban samu damar keɓewa da Ummata ba sai karfe goma na dare.
Hira muke sosai, da yawan hirar kuma a kan zamantakewar yau da kullum ce. Cikin nuna kulawa ta ce
“To ya zamanku a Abujan, in ce dai ba wata matsala ko?”
Matsalolina da nake fuskanta suka rika yawo a cikin kwakwalwata, ina tantance wadanda suka cancanta in fada. Da wadanda bai kamata in fada ba. Wata zuciyara gargadina take yi da kar in fada, aure wata uku kacal ace na fara kawo matsala gida
“Ya ya dai?” Ta katse min tunani na
“Ba komai ” na amsa a hankali saboda har zuwa lokacin ban yankewa kaina hukunci ba
“Fada min gaskiya, ba a boye matsala karama, domin daga karamar ne take zama babba”
Na kai hannu hade da shafa fuskata, lokaci daya kuma na gyara zamana. Ina fuskanta, hade da tace maganarta, gaskiya ne matsala daga karama take farawa, kafin ta zama babba
“Ni ban san me zan ce ba, yadda za ki fahimta” Na yi maganar hade da rufe bakina dalilin hammar da na yi.
“Ki fada min komai zan fahimta.” ta amsa ni
Na ɗan ja siririn tsaki “Ni lafiya lau muke zaune da ita, tsawon wata uku da mu ka yi tare ko mugun kallo ba ta taɓa yi min ba.”
“To shi fa mijin naki?” Umma ta yi saurin tambaya
“Shi ma haka”
Na ba ta amsa
“To me ye damuwarki?” Ta yi tambayar hankalinta a kaina
“Umma dama haka auran mai mata yake?” ni ma na tambayeta ina kallonta
Ita ma kallona take, ba ta yi alamar magana ba, wanda hakan ya nuna min tana neman karin bayani a gurina ne
“Ki gode Allah da ba ki auri mai mata ba Umma wallahi duk yadda kike ganin kina da matsaloli a gidan auranki ke kadai to basu kai ace kina da kishiya ba. Ni kam na yi danasanin auran mai mata “
“Ni ki fada min matsalar, ba zagaye-zagaye ba”
“Umma sam ba ni da ƴancinkaina, sai abin da matarsa ta ce, ba a shawara da ni sai dai in ga ana yi, ke ko wani abu zai min sai ya biyo ta hannun matarsa, yana tare da ni amma hankalinsa na gurin matarsa da yaransa, ke kam dai na zama kamar wata tunkiya a garken awaki. Ko dama haka ake yi? ” Na rufe maganar da tambayar ta, lokaci daya kuma ina tabe bakina.