Kara bata rai ya yi kafin ya ce ” Thank God ma ba na nan za a yi bikin, kuma ni komai kirkinta babu ruwana da ita” daga haka ya yanke wayar, da alama babu Rahma a wurin na tabbata da sai ta kara kira.
Misalin karfe takwas Bashir ya shigo gidan shi da Khaleel, tun da ya shigo kuma yake tambaya ta ina Maama. Da alama Khaleel ya labarta mishi abin da ta yi. Na ce “Tana dakinsu Khaleel”
Zuwa can sai ga shi sun fito hannunta daya cikin na shi, ɗayan kuma tana share hawaye. Cike da mamaki na ce” wai har yau kukan take yi? Aiko zan ci kaniyarta yanzun nan”
Bashir ya yi saurin fadin “Babu ruwan ki, ke fa ake tayawa kishi ma. Maama, ba kya so in kara auran?” ya yi mata tambayar daidai yana dora ta kan cinyarsa
Kai ta jinjina alamar eh, ya kwantar da kanta a kan kirjinsa ya ce “Me ya sa?” sai da ya kara maimaita tambayar sannan cikin muryar da ta gaji da kuka ta ce “Abin da idan ta zo bugunmu za ta rika yi, ta hana su Ya Khaleel da Assidiq yin ball, ta hana mu shan fruit, ta rika yi min tsawa, sannan ta rika fada da Auntynmu tana zaginta” ta karashe maganar cikin kuka.
Shiru ya ratsa falon, sosai jikin Bashir ya saki, ya kwantar da kanshi a kan kujera hade da lumshe idanunshi. Ya dauki tsawon lokaci a haka, yayin da Maama ke ta share hawayenta. A hankali ya ce “Maama I promise you hakan ba zai faru, if ya faru kuma, please let me know, za ki ga matakin da zan dauka, zan kore ta kamar yadda na kori waccan I promise you that. Kin ji ko?”
Kai ta jinjina alamar eh, sannan ya ce “Mu je to ki ci abinci, ki sha magani kar kan ki ya yi ciwo”
Haka yay ta kirkirar abin da zai mantar da yaran abin da ya faru yanzu, har ya samu suka dan saki jiki. Ni kam ma tashi na yi zuwa dakina, na ji kamar Maama ma ta fi ni hankali, idan har yarinya karama kamar Maama za ta shiga tashin hankali saboda tana jin tsoron abin da ya faru baya ya sake faruwa yanzu, me ya sa ni ban damu sosai ba, Anya kuwa haka abun ya kamata ya kasance.
“To ya zan yi?” na tambayi kaina da kaina. Zan ta tayar da hankali ne in jawo ma kaina raini tun kafin amaryar ta zo, abu daya zan yi, shi ne in zuba ido, har Zahra ta shigo, in ga nata kamun ludayin.
Shigowar Bashir ce ta sanya ni dago kai ina kallon shi, har ya zauna gefen gadon, jikinshi a sanyaye ya ce “Gidan babu dadi, da a ce na san yaran nan za su shiga damuwa haka, da ban yi auran nan ba”
A zuciyata na ce “Ji son kai, bai son yaran shi su damu, amma yarinyar wani ta damu, ba don damuwata zai fasa auran ba, Sai don damuwar yaranshi” a fili kuma komai ban ce ba.
Shi ne ya kuma cewa “Affan ma ya kira ni, yana fadin The same abin da Maama ta fada, kina jin Assidiq ma abin da ya fada kenan. Khadija ko dai kin sanya musu a baki ne? “
Fuska na hade sosai kafin na ce” Za ka fara ko? A kan me zan sanya musu a baki, me hakan zai amfanar min? A wancan karon ma fa haka ka yi min, komai laifina ne da sanya hannuna a ciki. A wannan karon fa ba zan yarda ba, gara tun yanzu ka san abun yi. Ni wlh babu yaron da na tsara ma wani abu”rai a bace na karashe maganar.
Hannuna ya rike na dama yana murzawa a hankali kafin ya ce “I’m sorry, I’m just asking Gimbiya”
Na kuma hade fuska sosai kafin na ce “And now you know your answer”
Duk mu ka yi shiru kafin ya ce “Ban san haka Saratu ta yi treating din yaran nan da ke ba, har Assidiq ma ya kasa manta wasu abubuwa har yanzu”
Baki na taɓe kafin na ce “Nana ai ba ta laifi a wurin ka, mune dai kullum masu yi mata laifi yar gold din”
Kallo na yake yi har na idar da maganar, kafin ya janyo jikinshi a hankali yake fadin “I’m very sorry Khadija, wlh ban san irin zaman da kuka rika yi kenan ba, zuciyata tana yi min wani irin zafi, amma a wannan karon ba zan zama dolo ba, zan sanya ido sosai, ta yadda dayanku ba zai cutu ba. Cikin fa kuka Maama ke sanar min wai zan kawo wacce za ta rika hana su wasa, tana yi mata tsawa, tana dukansu, tana hana su shan fruit. Can you imagine Khadija Kamar wasu ƴaƴan riko, saboda su wa nake nemowa ba don su ba. Affan ya ce min wai har kitchen take rufewa sai dai ki bayar da kudi a siyo maku abinci ki dafa masu. Kuma Khalil ya tabbatar min da haka ne”
Wani abu mara dadi ya tokare min a wuya, ina jin kamar yanzu abun ke faruwa, dole sai da hawaye suka zubo min kafin na samu ya wuce.
Jin ban ce komai ba ya ce “Don ku yafe min, Sha Allah a wannan karon zan sanya ido sosai, duk da ba na jin Zahra za ta kasance kamar Saratu”
Ni dai ban ce komai ba, shi ne ya cika ni da alkawura kala-kala har mu ka yi bacci.
A hankali maganar auran Bashir ta zagaye dangi, da yawansu ba su so, wai ya rasa wacce zai aura sai mace mai budadden ido, ta zo ta watsa mishi gida, kowa da abin da yake fada, ni dai addu’a kawai nake yi, Ummata ma haka ta ce min in dage da addu’a Allah Ya tsare ni da dukkan sharrinta, Ya canja min shirin ta mara kyau a kaina zuwa mai kyau. Haka ma Yusrah da Rahma suka ce min. Ga Maman Aiman a gefena da kullum take kara ba ni kwarin gwiwa. Duk wannan bai hana ni damuwa ba, Sai dai damuwar ba kamar lokacin bikin Saratu ba. Saboda yanzu kasuwancina ya tafi da rabin damuwar, abokan arziki suka raba rabin uku suka dauke daya, yarana kuma suka dauke kashi dayar, yar guntuwar damuwar da ta rage ma, muna raba ta da Bashir ne, saboda sosai jikinshi a mace yake da auransu da Zahra, kowa nuna mishi rashin dacewar hakan yake yi, wai idonta a bude yake, ba zai iya juya ta ba, ba za ta yi mishi biyayya ba. Kuma ba zai hana ta yawace-yawacenta ba. Kuma idan ta fita ya san abin da take aikatawa. Wai duk ga mata nan na kirki zai dakko feminist.
Wani lokaci ma ni ce ke ba shi kwarin gwiwa a kan auran. Idan kuma kishina yana ka, in yi banza da shi.
Zahra kam daga lokacin da aka tabbatar da auransu da Bashir na ja baya sosai da ita, da kullum muna chat, ina bude status din ta. Muna waya amma yanzu duk sai na kulle wannan, ita din ma tun da aka sanya ranar auran yanzu ku san sati ba ta yi min magana ba.
Na ce “Oh Allah! Mata kenan, wato dama wancan faran-faran din wayon a ci ne, wai an kori kare gindin dinya”
Kwana daya da wannan batun nawa, ina hawa online sai ga kiranta a WhatsApp. Kamar ba zan dauka ba, Sai kuma na dauka, fuskarta kamar ko wane lokaci cikin fara’a mu ka gaisa, sannan ta ce min “Surprise!”
Cikin dariya na ce “What?”
“Guess what” ita ma ta fada cikin dariya. Iyakar tunanina ban tuna abin da za ta yi surprising nawa da shi ba. Don haka na ce na ba ta gari.
Cikin dariya ta juya camerar a kan Affan, ban san lokacin da na yi zumbur na mike zaune sosai ba ina fadin “Oh my God what a good surprise. Thank you so much” ta shiga dariya, ni ma dariyar nake yi, Affan kuma ya gaishe ni, na amsa cike da farin ciki gami da kewarshi. Ji nake Ina ma ni ce yau gani ga Affan. I’m very eager in ga wannan rana. Na ɗan bata fuska ina fadin “Gaskiya ba ki kyauta min ba, why not ƙi fada min, in dan aiko mishi da wani abu daga nan.”
Tana murmushi ta ce “Fara? (sai ta daga farin transferred din bokiti, wanda soyayyar fara take a ciki gwanin sha’awa, sannan ta ce) ga ta nan na soyo mishi, akwai tuwon ruwa ma(sai ta dago wani bokitin tuwon ruwa zaune a ciki gwanin sha’awa, ta kuma cewa) ga goruba, magarya da kuma aduwa”
Ina dariya na ce “lallai duk abin da yake so ne, an gode Allah Ya saka da alkairi”
Ta ce “Ba komai, wlh tafiyar ce ta kama ni a gaggauce, ai da na taho mishi da Maama, to kin san rigimar yaran nan, dole na taho”
“Ba komai a gaba da yawa, an gode sosai”
Ita ma ta ce “Haba babu komai yi wa kai ne ai.”
Daga nan mu ka ci gaba da gaisawa da Affan, ya tambaye ni Khaleel, na ce yana ball. Fuska ya bata kamar zai yi kuka ya ce “Auntynmu I missed all those moments. How I wish I’m there. Please Auntynmu Don Allah ki sanya baki, idan na yi jsce in taho gida hutu.”
Na ce “Zan duba yiwuwar hakan sha Allah Affan, muma a nan muna kewarka. Inna Ruma tun tana fada har ta gaji ta hak’ura da jiranka ta canja sabon miji”
Ya yi dariya kafin ya ce “Su Maama fa?”
Na ce “Suna gidan Maman Aiman”
Ya ce “Har da little Ramla”
Kai na jinjina mishi alamar eh, kafin ya ci gaba da fada min yadda yake kewar gida, kasancewar Rahma tana can tare da Zahra, kuma Zahra fitowa ta yi waje, saboda kar in gane inda take, na ci gaba da kwantar mishi da hankali, sannan ya koma ciki ya hada ni da Rahma da sauran yaran.
Washegar da safe misalin 11am sai ga wani kiran Zahran, bayan mun gaisa ne ta ce min ta zo wurin yaranta ne Salman da kuma Ma’aruf (Baffa) shi ne take son mu gaisa. Na yi murmushin da ke nuna farin cikina a fili na ce “Ma Sha Allah, gaskiya kin kyauta min, ba ni su”
“Za ki ga fuskarsu a hade, ba haka suke ba, wai suna fushi ne zan yi aure”
Baki na bude alamar mamaki, Sai kuma na rufe ina murmushi tare da fadin “Allah sarki, su yi hakuri , ba ke ce kika tsarawa kanki ba, haka Allah Ya so. Mu da su duk ba mu isa hana hakan faruwa ba” komai ba ta ce ba, ta juya camerar kan Salman wanda shi ne kuma babba. Da gaske kuwa fuskar tashi a haden, damuwa kwance a kai. Besides that, yaron be very handsome kyakkyawa, shi ba fari ba, kuma ba baki ba, amma Zahra ta fi shi haske sosai. Sai dai bayan wannan rashin haske Salman ba shi da wata makusa, jikinshi a cike gwanin sha’awa wanda ke nuna yana samun duk abin da yake so. Madaidaiciyar sumar kanshi bakikkirin ta sha gyara.
Ko kallona mai kyau bai yi ba ya ce “Ina kwana”
Na ce “Lafiya kalau, ya karatu?”
Har yanzu dakyar ya amsa min da “Alhamdulillah”
Na ɗan yi murmushi kafin na ce “Yau dai a zahiri Allah Ya nuna min mai fushi da Mahaliccinshi” karon farko da ya dago kai ya kalle ni, Sai kuma ya yi saurin janye idanun. Cikin alamar rarrashi na ce “Haba Salman, ka manta da kaddara, ka duba tsawon lokacin da Mamarku ta dauka babu aure, ka ga da tana da niyya da tun a wancan lokacin ta yi, sai dai kuma kwatsam ga shi yanzu ya fado mata. A yanzu ma ba ita ce ta zabi hakan ba, Allah ne ya zaba mata, don haka don Allah ku yi hak’uri, kar ku yi jayayya da ubangijinku, ku yi addu’a Allah Ya sa haka shi ne ma fi alkairinta”
Komai bai ce ba, sai dai har zuwa lokacin fuskarshi babu annuri, a haka ta juya camerar kan Baffa, shi din ma dai kamanninsu daya da Salman din, kawai dai ya fi shi haske, kuma jikinshi bai kai cikar na Salman ba. Haka shi ma fuska babu walwala mu ka gaisa, na tunatar da shi kamar yadda na yi wa Salman, kafin na tuna da wani abu, don haka na ce a ba Salman wayar. Ya karba ba tare da ya ce komai ba. Ni ce na ce “Kar ka sake ka auro yar Indiya, ka dawo nan gida za mu yi maka auran India din, ni zan biya sadaki, in aura ma Maama”
Sai ko ya yi murmushi har haƙoranshi suka bayyana. Ina jin sautin murmushi sauran ma. Ni ma na yi murmushi tare da fadin, “Babu abin da yan indiyan nan za su nuna mata. Bari ka gan ta. Na daga murya ina kwadawa Maama kira, wacce take dakinsu Khalil suna wasansu.
Ta amsa hade da fitowa a guje, ganina da waya ina video call sai ta kara azama, ni kuma na mayar da camerar kanta, Salman kuma yana kallon ta tun daga can take fadin “Auntynmu Ya Affan ne?” jin muryarta ya sanya Baffa tasowa shi ma ya leko cikin videon yana murmushi , lokacin da ta karaso ta ga bakuwar fuska sai ta yi turus, karsashinta ya bace, alamar rashin fahimta ya bayyana a kan fuskarta, a haka ta juyo da kallon ta kaina, tana wasa da jelar kitson kalabar da ke kanta, komai ba ta ce min ba, ta kuma juyawa da kallon nata a kan su Salman da suke kallon ta, da murmushi a kan fuskarsu, ta kuma maido kallon ta kaina,
Duk muka fashe da dariyar yadda take ta raba ido a tsakaninmu.