Ita kuma kwantawa ta yi a kan kafadata a hankali ta ce “Su waye wadannan”
Cikin dariya na ce ” yaran Momy Zahra ne, ki gaishe su” ta dago daga kan kafada ta ce musu “Ina wuni” Baffa ne cikin daiya ya ce “Wuni kuma?” sai ta yi dariya hade da boye fuskarta a kan jikina kafin ta ce “Ina kwananku?”
Suna amsawa ne su Haidar suka fito, irin reaction din da Maama ta yi, su ma shi suka yi, wannan ya kara sanya mu yin dariya, haka suka gaisa babu karkasashi. Muna ta dariyar abun Khaleel ya fito, shi kam lafiya lau suka gaisa, wai ya sansu, suna gaisawa idan Zahra ta je mishi visiting a school.
Don haka sai na mikawa Khalil wayar na tashi Ina dariyar abin da ya faru. A can kasan zuciyata kuma na ji dadin yadda suka warware. Ina jin su suna tambayar sunan yaran daya bayan daya, amma da aka zo kan Maama kin magana ta yi, sai ma ta boye a bayan Khalil tana murmushi, kafin daga bisani ta bar wurin a guje.
Bayan sun gama gaisawa ne Zahra ta karbi wayar, Khaleel kuma ya kawo min, sosai take godiyar yadda na sanya su Salman suka warware.
Sannan ta ce “Zan fadawa Abban Khalil kin kyautar mai da ƴa” duk mu ka yi dariya sannan mu ka yanke kiran.
Kawai sai nai ta ji na cikin Nishadi, duk da wani lokaci maganganun Affan na son zuwa gida su kan fado min, sosai nake son ya ga ƴan’uwanshi a zahiri, kodai ya zo kuma mu mu je. In Sha Allah za a yi daya cikin abubuwa biyun nan.
Bari dai a gama bikin nan, saboda na san yanzu Bashir hankalinshi kaf a kan bikin ne.
Rayuwa ta ci gaba da shurawa daga sakanni zuwa mintoci, daga mintoci awanni, awanni su rikide zuwa kwanaki, kwanaki zuwa makonni, makonni zuwa watanni, watanni zuwa shekaru.
A haka hutun Khali ya kare, ya koma zuwa makaranta, lokacin kuma bikin Zahra saura sati biyar ya rage. Babu wani abu na canji da na gani daga bangaren Bashir ko ita. Idan ka dauke yawan maganar da mu ka rage. Don idan ba ita ta yi min ba, ni dai ban yi mata. Ita kuma commitment dinta basu ba ta damar yin chat any how.
Kuma abin da na fahimta a media babu wanda ya san da zancen aure, Sai makusantanta, su din kuma basu fasa maganar kowa ya ji ba.
Ya rage saura sati biyu biki aka fara shirye-shirye both side. Zahra ɗai ɗaya bangaren ta zaba, ba bangaren da Saratu ta zauna ba. Nan Bashir ya kira kwararrun engineers aka kara mata renovating din Shi, ya kuma fitowa daidai da zamani. Ni kaina sai ya burgeni.
Bangarena, Bashir ya sanya an kwashe komai na falon a ka zuba wasu, hatta labulaye da dinning Sai da aka canja, kitchen ma an kara zuba sabbin na’urori, haka dakin yara ma an kara gyara masu shi da abubuwan bukata na yara. Aka canjawa gidan fenti zuwa fari, volt din tsakar gida ma aka canja wasu masu kyau da daukar hankali. Ko daga nesa ka hango gidan sai ka ji ya burge ka bare ka shigo. Maman Aiman har cewa ta yi, idan har Baban Aiman zai gyara mata gida da dakinta haka, ita kam ya auro mata uku ma, su cike hudu. Dariya kawai na yi. Kishiya daban, ko me za a yi ma sai ka ji wannan kishin.
Ranar da yamma ina zaune ni kadai cikin falona, Ramla na kan keken zamanta, ni kuma ina chat da Maman Hana, da shi ke ba ta kasar an tura wani course a England, kiran Salman ya shigo wayata.
Ba yau ne karon farko da ya fara kirana ba, duk lokacin da ya so ya kan kira ni mu gaisa, sannan ya ce in nuna mishi matarshi.
Abin da na fahimta yana da wasa da dariya da sakin fuska, kamar dai mahaifiyarshi.
Na daga kiran ina murmushi, na ce “Surukina” da yake haka nake kiran shi, idan ina jin nishadi. Shi ma dariya ya yi mai sauti, kafin ya gaishe ni, bayan na amsa ya ce “Ina first lady?”
“Suna makaranta basu taso ba” na ba shi amsa
Ya yi dariya kafin ya ce “Magana za mu yi Auntynmu”
Yadda na ga ya yi serious, ni ma sai na tattara hankalina kaf kanshi, cikin rashin walwala ya ce “Don Allah Auntynmu kar ki bari Momynmu ta yi komai na shagalin biki, kawai a daura aure, shi kenan. Ba na son dinner ko wani free weeding pictures Irin yadda kawayenta ke yi idan za su yi aure”
Murmushi mai sauti na yi kafin na ce “Haka kake so mu yi bikin lami kamar an yi mutuwa Salman?”
Ya kuma narkewa yana fadin “Please Auntynmu don Allah, I’m very serious Ni ba na so. Kawai sai a ga Mamanmu da wani wai za ta yi aure. Haba don Allah”
Yanzu kam dariya na yi mai sauti kafin na ce “Wlh yaran nan kun raina mu, wane irin abu ne haka wai? Duk kun hana mu rawar gaban hantsi. Nan ma fa first ladyn ta ka har da kukanta a kan Abbanta zai yi aure. To wai don an haife ku shi kenan kuma sai mu ja ma komai layi? Kun mayar da mu tsaffin dole”
“Kuka ta yi first ladyn?” cike da mamaki ya yi tambayar
Na ce “Har da kin cin abinci”
Ya dan yi dariya kafin ya ce “Is she jealous?”
“I don’t know” duk mu ka yi dariya ni da shi. Kafin ya dora “Please Auntynmu don Allah ki yi min wannan favor din”
“Kar ka damu, I will talk to both of them.”
“Yauwa thank you.” Daidai lokacin Maama suka shigo
Tana turo kofa ta ce “Auntynmu Ya Affan ne?”
Na shiga girgiza mata kai hade da juya camerar yadda za ta ga fuskar waye. Ta yi murmushi tana fadin “Ya Salman in wuni?”
Na mika mata wayar daidai lokacin da yake “Fadin my first lady kin dawo school din?”
Ni dai kaya na shiga cirewa su Haidar, ina kuma tattauna maganar da mu ka yi da Salman a zuciyata.
Sai dare na kira Zahra, saboda na san a lokacin ne take free, bayan mun gaisa na isar mata da sakon Salman. Murmushi ta yi kafin ta ce” Salman, yana da rigima sosai “
Dariya na yi kafin na ce” Ni dai a taimaka min da wannan “
Ta ce” Bangarena babu problem, Sai ki tuntubi Oganki “
Na ce an gama, daga nan mu ka shiga hira, kafin daga bisani mu ka yi sallama
Da safe da nake sanar da Bashir bukatar Salman, shi ma murmushi kawai ya yi, kafin ya ce” Wato wannan shi ne alamar mun haihu fa. Allah Ya raya mana su, yadda suke so haka za a yi. “
Shirin visiting din Khaleel mu ka shiga yi, karon farko da zan je mishi visiting.
Ranar Asabar da ta kama saura sati daya bikin Bashir ranar muka tafi visiting din Khaleel mu duka gidan ba a bar kowa ba. Tun da muka fara shiga Abuja memories din abubuwa da dama suka shiga dawo min, duk da ba zan iya gane hanyar gidanmu ba yanzu, hakan bai hana ni tuno zaman Abujan ba. Na shiga jerawa Maman Khaleel addu’a ita da Ramla. Idanuna na lumshe ina jin kewarsu musamman Ramla, Sai kuma na bude idon ina kallon Ramlan da ke hannuna. Marabarsu da waccan Ramlan gashi ne kawai, amma kamar photocopyn waccan Ramlan aka yi. Ina ta compare and contrast tsakanin Ramlan Sakeena da tawa Ramlan mu ka shigo makarantar su Khaleel.
Ai tun da Khalil ya dora idonshi a kaina ya kwaso a guje, ya rukunkume ni kamar wani mace. Murnar da yake yi har sai da Abbanshi ya ce “Ashe Khaleel kara kawai da kawaici kake mana lokacin da muke zuwar maka visiting, ba mu kake son gani ba”
Mu ka yi ta dariya, na kira mishi Affan kamar yadda ake mishi kulle, wannan karon kam Affan har da kukanshi, shi zai taho gida, ganinmu ringis a gaban Khaleel ya tayar mishi da tsumin son ganinmu, don har sai da Rahma ta kira wai za ta hana mu waya da yaronta, muna tayar mishi da hankali.
Bayan mun gama wayar da Rahma ne da sauran yaran na ce “Abban Khaleel ya fa kamata a duba lamarin yaron nan Affan. Ba tun yanzu yake fada min yana son zuwa gida ba. Ka ga har ya fara kuka”
Shiru ya yi kafin ya ce “To ni ya zan yi? Kin san dai ba zan iya kiran Rahma in ce Affan ya zo ba. Har sai idan ita ce da kanta ta ce zai zo gida. Kuma ta fada min cewa so take ya gama secondary school. Kin ga nan da 3 years kenan. Tun da baya suka maido shi. Da ace dai ba su mayar da shi baya ba, da yanzu shi ma yana ss1 din ai”
“Yanzu shi kenan mu ba za mu je ba, shi ba zai zo ba har sai 3 years?” na tambaye shi da yar damuwa.
Ya ce “Ni zan je in duba shi”
Hararar wasa na yi mishi kafin na ce “Ban gane kai za ka ba, kai kawai yake son gani. Mu duk yake son gani”
Su Khaleel suka yi dariya, shi kuma ya ce “Ina laifi idan ya ganni ni kadai din, abin da ya sa ba na son zuwa, kar Dr da Rahma su rika jin don Affan yana can shi ya sa nake ta zarya”
“Sai ka bar mu, mu mu je, amma gaskiya Affan ba kai yake son gani ba”
Yanzu kam baki ya rike da mamaki ya ce “Ashe haka ku ka yi da shi?”
Yanzu ma su Khalil dariya suka yi Maama ta ce “gaskiya Abbanmu mu za mu je”
“Ina na ga kudin jirgin biya muku ku daya (ya shiga kirgamu har ya dire kaina sannan ya ce) ku shidda fa”
“Ko mu goma ne kana da kudin biyan jirgi, ai ba magana kudin ke yi ba.”
Murmushi ya yi sannan ya ce “Shi kenan, zan duba yiwuwar hakan in Sha Allah”
Su Maama suka shiga murna. Sai 4pm muka baro garin Abuja cike da kewa, around 10pm muka iso Katsina, take away Bashir ya yo mana, kowa yana ci sai baccin gajiya.
Daga nan aka shiga hidimar biki, Salman ya kira ni a kan maganar dinner da pre weeding pictures ban san iyaka ba, yana kara nannaga min kar in bari a yi don Allah.
Ranar Laraba masu jere suka zo, dukkansu maza ne daga company suke, da alama aikinsu kenan. Suna hidimarsu ina yin tawa, bayan na gama abincin rana na kai musu, a kan entrance na ajiye musu na juyo
Sai wajen biyar na yamma suka gama, daya ya kwankwasa min kofa, bayan na bude ya ce “Hajiya ga key din kofar mun gama”
Ban amsa ba na ce “Haka aka ce ku ba ni?”
Kai ya jinjina alamar eh, jiki a sanyaye na karbi key din hade da juyawa ciki, ina mamakin dalilin da ya sa aka ba ni key din, ban san ana yin haka ba ni.
Shi ya sa da Bashir ya dawo da dare na mika mishi key din
“Na menene?” ya tambaye ni ba tare da ya karba ba
Na ce “Na part din Barrister ne”
Still bai karba ba ya ce “Haka ta ce a ba ni? Ni me zan yi da key? Ki samu wuri ki adana shi.”
Komai ban kara cewa ba, na adana din, ranar Alhamis kuma sai ga akwatunan lefe guda ashirin da hudu cif, komansu iri daya, kala kawai ta bambanta, wannan light pink, dayan kuma white, wai in zaba. Sai na dauki pink din. Sannan ya ba ni kudin hidimar bikin yara.
Juma’a mu ka fara saukar baki daga Ruma, ranar Asabar kuma da ta kama daurin aure bakina na Kano suka iso, dandanan gida ya cika, a wannan karon ma sai da Maman Aiman ta dakko mana mai Asharalle, ai kam misalin 4pm ya fara wasanshi, gidan ya kara kacamewa, manyan mata suka fara watsa kudi. A daidai lokacin Salman ya kira ni video call, kasancewar ina online, bayan na daga ne ya bude baki alamar mamaki, saboda yadda ya ji kida na tashi. Dalilin da ya sanya ni dariya hade da mikewa na koma wurin da babu hayaniya sosai.
“Amma Auntynmu kin yi min alkawari fa” kamar zai yi kuka ya yi maganar
Dariya na kuma yi kafin na ce “Ba dinner ba, ba kuma pre weeding pictures ba Salman. Wadannan tawaga ta ce suke taya ni dannar kirji”
Sai ya dan yi murmushi, sannan ya ce “A tashi lafiya” na ce “Allah Ya sa” da haka mu ka yi sallama
Misalin karfe shidda na yamma amarya ta shigo, tare da rakiyar manyan motoci na gani na fada, ban yi mamaki, don ko a jirgi aka dakko Zahra matsayinta ya kai.
Dangin amarya suka fada cikinmu aka shiga cashewa, tun da a can ko cokali ba a buga ba, Zahra ta ki yarda. Su Maman Aiman suka kai mu su abinci, amma ba su bi ta kanshi ba, Sai da aka tsayar da kidan don yin sallahr magriba da kuma isha’i, sannan suka koma kan abincin, ni ma da tawa tawagar mu ka nemi namu abincin.
Tun da Zahra ta shigo ba ta ga keya ta ba, ni ban ma tuna in ganta ba, kuma har zuwa lokacin ban san ya jerenta yake ba, mutane dai na ta yabawa, wai falon ya yi kyau sosai.