Misalin karfe takwas na dare mai’asharalle ya mayar da kida, Sai 10pm sannan aka tashi, a lokacin ne kuma yan rakiyar amarya suka fara watsewa, ina jin suna surutun ba a kai amarya sashen uwargida ba fa za ku tafi, amma ina hankalin ko wace mace ya koma gida, ina jin wata tana cewa “Ta kai kanta, abun da ba bakin juna ba ne”
A haka dai aka samu wasu a gurguje suka kawo ta, hade da yi mana fada a takaice sannan suka mayar da ita.
Zuwa 11pm dai part din Amarya ba kowa, Sai part dina ne dayan part din ake ta hayaniya, da shi ke ƴan Ruma da Kano duk suna nan.
Ina zaune cikin ƴan’uwa kiran Zahra ya shigo, Sai da ya kusan katsewa sannan na daga, ta ce “Auntynmu ki zo don Allah” daga haka ta yanke kiran.
Na mike tare da sanar da Yusrah ina zuwa.
Ina murza kofar ta bude, “Ma Sha Allah!” na fada a hankali, saboda karon da na ci da falon Zahra. Komai unique, babu hayaniya, babu takarce, TV plasma katuwa ce kawai manne a jikin bango, Sai wasu irin kujeru masu shegen kyau, wadanda suke single babu wani tarkace, center tables mai ɗan fadi a tsakiyarsu. Sai labulaye masu kyau da suka dace da falon, bangaren dinning ma komai cool. Sai na ji kamar ta fita ta bar min falon, saboda duk wanda ya shigo falon sai ya ji wata nutsuwa ta ziyarce shi.
A hankali na karasa cikin bedroom tana zaune a gefen fankacecen gadonta, har zuwa lokacin da lullubi a kanta, yadda na ganta ta yi wani zumuu, ya sa na tuntsire da dariya, a zuciyata na ce “Wato shi aure daban yake, duk girmanka, duk wayewarka duk shekarunka, duk isarka, muddin aka ce ga shi yau an kawo ki gidan wani da sunan zaman aure dole sai kin yi wannan fargabar. Kalli Zahra mace da take fitowa cikin dubun maza ta bayar da points a saurare ta, macen da take shiga cikin turawa su fada ta fada. Kalle ta yau kamar wata gata, duk ta zama kalar tausayi “
Bayan na zauna gefenta ne na ce” Kar dai ki ce min kuka kika yi Barrister, wai kin gan ki duk kin yi wani laushi kamar wata karamar yarinya “na karasa maganar cikin dariya, don sosai dariya take ba ni
” Tun da na zo ban ga kin shigo part din nan ba, kar dai fushi kike yi? “
Wata siririyar dariyar na yi kafin na ce” Wane irin fushi kuma, kawai mutane sun yi yawa “
Ta kuma cewa” Har yaran nan babu wanda na gani fa”
Da mamaki a muryata na ce “Don Allah fa, to wlh ban san ma basu shigo ba, amma na san za su shigo.” kafin ta kara cewa wani abu na ce “Don Allah ki sake jikinki, duk kin yi wani iri, yau ko dan murmushin ma babu”
Wahalallen murmushi ta yi kafin ta ce “Danasanin auran nan nake yi Auntynmu, ji nake me ma ya kai ni na yi shi. Ina zaman-zamana. Wani iri nake ji, ji nake kamar na yi zunubi, zan kwana da wani na miji ba Dadyn Salman ba. Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Kai!! Kai mutuwa!”
Ta karashe maganar cikin kuka, mai taɓa zuciya…
Jikina ya yi sanyi ƙalau, tausayinta ya kama ni, damuwa karara ta bayyana a kan fuskata.
Shiru ya ratsa dakin, idan ban da sautin kukan Zahrah da yake fita a hankali. A hankalin ni ma na ce “Haba Barrister don Allah, mun fara abu cikin dadin rai, kuma za ki rufe shi da wata magana ta daban, Allah Ya kaddara sai kin auri Bashir, ki duba haduwarku mana, kila shi ya sanki, amma ke na tabbata ba ki san shi ba. Allah Ya jarabci ɗanmu da lalura, saboda ta hanyar kai shi asibiti za ki hadu da Bashir. Sai kuwa ga shi kun hadu, zumunci ya rika shiga tsakaninmu a hankali, har zuwa yanzu da kike zaune a gidanshi a matsayin mata. Ban san yadda kike ji ba, amma tabbas na san kina jin abun kamar mafarki, kuma kamar gaske. Kina jin kamar ba ki kyautawa mijinki na baya ba. Amma babu yadda kika iya, Allah Ya ri ga da ya kaddaro Bashir a cikin mazajenki na duniya, fatanmu ya sa shi ne na karshe. Bashir Ruma mutumin kirki, za ki ji dadin zama da shi don Allah ki ba shi dama “
Hawayenta take daukewa a hankali ba tare da ta ce komai ba, daidai lokacin Bashir ya shigo, ni kaina ban ji takunshi ba, Sai dai na gan shi tsaye jikin kofar shigowa. Idanu ya zuba mana kafin ya ce” Akwai matsala ne? “kai na girgiza alamar a’a
Ya kuma cewa” Na kira wayarki ba ki dauka ba”
“Ba na tare da ita” ya kara so cikin dakin sosai ya ce “Da kika taho nan din, wa kika bari ya rako ni? Kodayake ke ce babbar kawar amaryar” na dan yi murmushi, Zahrah dai komai ba ta ce ba. Ya ɗan kalle ta, ya kalle ni sai kuma ya ce “Barrister yau ba ta magana ne?”
Kallon ta na yi ina dariya, sannan na ce “Sai ka sayi baki”
Shi ma dariyar ya yi ya ce “Nawa ne bakin?”
“Da tsada sosai”
“ba fa tsaya min za ta yi a shari’a ba”
Dariya na yi hade da mikewa, na nufi kofa ya ce “Zo daukar maku Ledar nan daya ke da yara, na ga duk sun yi bacci”
Na duka hade da daukar ledar ina yi mishi godiya.
Koda na koma sashena sai na kasa bacci, ina ta imagining yadda Bashir zai lallashi Zahra har ya mayar da yawunshi da ya jima yana hadiye a kanta, haka na yi ta juyi bacci ya ki zuwa, ga zuciyata sai azalzalata take yi da imagination marasa dadi. Sai 3am bacci ya fara dauka ta, ba jimawa kuma na ji su Yusrah na ɓuruntu a kitchen. Dole na tashi na shiga kitchen din, mu ka ci gaba da aiki tare, amma fa raina babu dadi, kowa da komai haushi yake ba ni, har 9am Bashir bai fito ba, ƴan Ruma da ƴan Kano duk suna ta shirin tafiya gida, Sai wajen 10am ya fito, ya sallame su, ni kam ko hada ido ba na son yi da shi. Kuma na fahimci ya gane hakan, saboda sai lalubar kwayar idona yake yi ina zamewa. Duk wadanda za su tafi sai sun shiga wurin Zahrah sun yi mata sallama, kuma sai ta haɗasu da kayan biki, haka mu ka yi ta sallamar bakin har wajen 12pm da mu ka yi wa bakin karshe rakiya, da sauri na dawo bangarena, Sai dai ina kokarin tura kofar ɗakina Bashir na shigowa, dole na hak’ura, ya shigo, ya kuma sanyawa kofar key da kanshi. Ya karbe Ramla da ke hannuna, ya kwantar da ita saman gado ya ce “Zo mu samo mata kanai yau din nan, watanta bakwai fa, ya kamata ace yanzu kin fara laulayi”
Na shiga kokawar kwatar kaina ina fadin “Me ya haka don Allah, ba fa mu kadai ba ne a gidan” ganin ba zan iya kwacewar ba, na shiga rokon shi a kan ya kyale ni don Allah ba kwanana ba ne, an ce ba kyau. Amma ko kadan bai saurare ni ba, Sai da bukatar shi ta biya, ya yi wanka sannan ya haye gado ya soma bacci. Lokacin da na fito daga bayi na ce “Me za ka yi wai? Bacci? Wlh ba a nan ba, tashi ka fita, ni babu ruwana” haka na rika jan shi, har ya, sakko daga saman gadon, na bude kofa hade da tura shi waje ina fadin “Ni ba, za ka daura min jakar tsaba ba, ka hada ni da kaji”
Sallahr azhur na fara yi, kasancewar lokacin ta ya yi, sannan na kwanta ina fatan Allah Ya sa bacci ya dauke ni, cikin cikin ikon Allah addu’ata ta karɓu, , na yi baccin sosai , saboda sai hudu da wani abu na tashi, na kara yin wanka hade da yin sallahr la’asar sannan na sakko kasa.
Nan Maama ke sanar min Momy ta shigo sun ce mata ina bacci, sannan suka nuna min take away din da aka yo musu, Assidiq ya dauko min nawa. Na zauna Ina ci a hankali hade da kallon TV. Daidai lokacin Zahrah ta kuma shigowa. Mu ka yi wa juna murmushi sannan ta ce “Kin tashi kenan?”
Na ce “Da kyar!”
Mu ka kuma yin dariya sannan ta ce “Sannu da kokari, ai kin sha hidima” haka muka shiga hira, har na gama cin abincin mu ka shiga kitchen tare a nan take shaida min rabon ta da ta shiga kitchen ta yi abinci tun Babansu Salman na da rai, ko tea ta kan yi sama da wata daya ba ta hada ba, Sai dai yan aiki su hada mata. A zuciyata na ce “Akwai aiki ashe”
Haka mu ka gama girkin abinci gwanin dadi, a zuciyata nake jin idan har hakan ne zai ci gaba da faruwa lallai gidan zai yi dadin zama.
Sai magriba ta koma part din ta, daga nan kuma sai da mijinta ya dawo, suka taho cin abinci, basu bar part dina ba sai 10pm.
Yau ma kamar jiya haka na kasa bacci, Sai na rika jin kamar gara Sarai, saboda ita dama ba ta shiga harkarta ba, amma ita wannan ta shiga jikina sosai, duk time da ta ware da mijina sai in ji Ina jin zafin abun, saboda ta san sirrina yanzu. Kai wayyo Allahna kishi. Ni gani ba sunana Aisha bare in ce ko kishi ya bi jini, an ce ko a tarihi Nana Aisha tana da kishi. Dakyar bacci ya dauke ni, haka suka gama kwanakin ukunsu ya dawo ɗakina, yadda ya yi min kamar ba daga wurin mace yake ba.
A kwana a tashi Zahra ta kwashe wata daya a gidanmu, zamanmu lafiya kalau, komai muna yi a tare ne. Abincin safe ne na ce zan rika yi, ba sai ta tashi ba, amma abincin rana da na dare duk tare mu ke yi. Wani lokaci kuma sai ta ce wai mun gaji, oder za a yi, aiko haka za mu huta daga rana har dare, ba ta jin kyashi take yo mana oder abinci masu rai da motsi mu ci.
A satin da za ta koma aiki, a kuma satin ne za mu je wa Khaleel visiting Don haka tare muka runguda makarantar, daga nan kuma mu ka dawo Kaduna gidanta. Lallai ana karyar zama, wai danfulani ya shiga birni bai ga rumbu ba, ya ce ana karyar zama a nan.
Gidan Zahra kamar a Turai, na yadda kam ba ta girki, saboda tun da mu ka zo komai yi mana ake yi. Da safe mu ka dau hanyar komawa Katsina ita kuma mu ka bar ta a nan.
Tun daga wannan lokacin Zahrah ta kan yi sati biyu a Kaduna, wani lokaci kuma duk weekends take zuwa, ko kuma shi Ogan ya zo. Wani lokacin ma sai ta yi wata daya a Kaduna, ta zo Katsina ta yi sati daya. Sai nake jin kamar ba ni da kishiya. Wakar Sarai ta ce “Allah ya ba ni kishiya mai yawo, kafin ta dawo na ci duniya” ai ko na yarda da wannan wakar tata, saboda idan Zahrah ta tafi hidimominta sai mu yi sama da wata daya da Abban Khalil a gida.
Yaranta kam kullum kara shakuwa mu ke yi, duk wani abu da ya shafe su, Abban Khaleel ya kan yi musu shi kamar yaranshi. Yarana ma Zahra ta ja su jikinta sosai, musamman Ramla da Maama. Don idan har ta zo, to Maama na wajen ta sai ta tafi.
A haka rayuwa ta rika mikawa, komai sai Alhamdulillah, muna samun ci gaba sosai, saboda Khaleel ya gama makaranta, saura kuma University, Inda shi ma Zahra ta dage a kai shi India su hadu da su Salman.
Bashir kuma ya amince, don haka, aka shiga nema mishi admission. Time din Maama na Jss 2 haka ma Assidiq. Haidar ne ke primary 5.
Ramla kuma na yaye ta, ina hutawa wata abuna, karon farko da na yi yaye ba ciki, kuma cikin bai samu da wuri ba.