Bashir kam Zahra ta daure mishi kwankwaso ya fada harkar siyasa, har yana neman chairman din Batsari. Ni dai nawa ido, ban san komai a harkar siyasa ba, suke hidimarsu, ita ta san manya a Abuja kuma ta iya shiga da fita, ni kuwa babu abin da na sani a nan bangaren, na fi gane kasuwancina. Saboda ni ma har an bude min shago na zuba yara, kuma Ina samu sosai Alhamdulillah.
Yau Zahrah na gida Katsina, don haka duk yaran suna bangarenta, ni kuma ina zaune a falo ina duba hoton wasu shaddoji da aka turo min. Suka shigo har da Zarah. Na bi su da kallo, saboda yadda na ga fuskarsu cike da annashuwa.
Khaleel ne ya fara cewa “Auntynmu don Allah ki ce ni za ki biya mawa”
“Me zan biya ma?” na yi saurin tambaya
Zahra ta ce “Umrah”
Da sauri na bude baki, kafin na rufe ina fadin “Umrah kuma ni jikanyar Adamu, wace irin umrah wai? Wacce ake hawan jirgi aje Saudiyya a yi?”
Cikin dariya Zahra ta ce “Ita fa” na yi shiru ina dariya, hakan ya sa su ma suka shiga kyakyatawa. “Amma dai tsokanata kuke yi ko?”
Maama ta ce “Allah Auntynmu da gaske mu ke yi, Abbanmu za mu je mu yi wa addu’a”
Baki na rike alamar mamaki sannan na ce “sai kun dawo, ni ba ni da kudi, idan kun je ku roka min Allah kudi su zo ni ma in je”
Zahra ta ce “Allah kina da su, yar kasuwar kamar wata sarauniya kenan, a rana daya miliyan nawa kike kamawa?”
Wata dariyar na yi cike da Nishadi ba tare da na ce komai ba.
Ita ce ta kuma cewa “Ba wasa mu ke ba fa, ni zan biyawa Maama da Ramla”
Wata dariyar na yi cike da Nishadi na ce “Manya kaurin gayya”
Ita ma dariya ta yi, kafin Khaleel ya ce “Auntynmu don Allah”
Na ce “Kai Khalil, ni fa ƴar Kano ce na san zakin kudi”
Duk suka kuma kwashewa da dariya, kafin Zahra ta ce “Bari ki ji, Oganki ya biya miki ke da Inna Ruma da kuma Umma”
Yadda nake kallon ta ne ya sa ta ce “Allah ba wasa nake yi ba, ce mishi na yi, don Allah Ya bari in yi miki albishir”
“Wai don Allah gaske ko wasa?” yaran suka shiga rantse min, ai sai na mike bayan na yi sujada na shiga taka rawa, yaran na taya ni. Ana ta dariya. Na juyo wurin Khaleel na ce “Khaleel na biya maka kai ma”
Haba sai ihu ya cika falon, Sai kuma na dakata na ce “To Affan fa?”
Zahra ta ce “Ai duk zamu hadu da su a can”
Cike da mamaki na ce “Wai duk yaushe aka yi wannan plan din?”
Cikin dariya ta ce “Kina can kina lissafin kasuwancinki”
Na yi dariya sosai, kafin na kira Umma na yi mata albishir, na kira Yusrah da sauran ƴan’uwa.
Sai da na gama kiran duk wanda ya kamata sannan na ce “To wai Assidiq da Haidar fa?”
Maama ta ce “Abbanmu ya biya musu su ma”
Na rika washe baki, kamar ban iya rufewa ba, video calls Kam Sai da aka kira magriba na yanke.
Daga wannan lokacin mu ka shiga shirin tafiya Umrah. Ji nake kamar mafarki, ba gaskiya ba.
Su Rahma sun riga mu isa Saudiyya ita da su Salman, mu sai bayan sun isa da kwana biyu muka tafi. Muna cikin motar da za ta kai mu masauki, mu ka shiga tattauna yadda Affan zai yi idan ya gan mu, sannan mu ka ce za mu ga wa zai fara tara, duk wanda ya fara rungumewa to shi ya fi missing.
Bayan mun fito daga mota Bashir ya kwantantawa Dr mijin Rahma inda muke, can kuwa sai gasu nan zuwa su dukkansu. Rahma da yan mazanta hudu , ga kuma Affan, Sai kuma Ma’aruf da Salman.
Ai tun da Affan ya hango mu ya kwaso da gudu cike da murna, duk s muka mike mu ka shiga layi, muna jiran mu ga wanda zai fara runguma.
Addu’a nake yi Allah Ya sanya ni, cikin ikon Allah kuwa kai tsaye ya nufo ni hade fadawa jikina, ban damu da irin girman da ya yi ba, na rungume shi tsam, ina jin kaunarshi na bin ko wane bangare na jikina, after some seconds Kuma, ya rungume Maama, wacce dama ta kosa, Sai tsalle take yi ita kadai, daga nan kuma ya rungume Khaleel, sannan ya nufi Bashir aiko muka fashe da dariya, bayan ya rungume Bashir ne ya nufi Inna, ta ture shi cikin wasa ta ce, “na sake ka yau, kullum ina tunaninka, amma ni ce ta karshen wacce za ka runguma don gidanku”
Mu ka kuma fashewa da dariya, daidai lokacin sauran suka iso, mu ka shiga gaisawa sannan mu ka runguda masauki.
Ranar dai ba bacci, hira kawai, yaran suna ɗakinsu suna ta su, mu kuma nan muna tamu.
Haka mu ka rika gudanar da ibada a nutse, wata irin nutsuwa ce take ratsa ni, wani shauki da soyayyar addinina ke kara shiga ta, wata irin nutsuwa a kan addinina ta kara kama ni. Tsoron ubangijina ya kuma shiga ta, soyayyar fiyayyen halitta da ahlinsa ta rika ratsa sassan jikina. Mun zagaya wurare da yawa na tarihi, Sai na ji Ina son zuwa aikin Hajji kuma, tun daga lokacin na daura niyyar sha Allah sai na dawo aikin Hajj.
Na yi wa Sakeena da mahaifina addu’a, na yi wa Baban Khalil a kan kujerar da yake nema. Yarana da sauran musulmi ba ki daya, kawai nake jin kwarin gwiwa a kan duk abin da na roka an amsa min.
Yau da yamma bayan mun dawo masallacin sallahr la’asar ina zaune ni da Rahma da kuma Barrister , da yake mu uku masaukinmu daban, haka Inna da Umma ma nasu masaukin daban, yara maza ma haka, haka su Abban Khalil ba.
Wasu zannuwan gado nake dubawa, hade da turawa customers dina, idan suna so sai in siyo.
Barrister ce ta leko wayar tana fadin “Yar kasuwa, ana kasuwancin ne?”
Dariya na yi ba tare da na ce komai ba, Rahma ta ce “Ban san lokacin da Auntyn Ramla ta rikice neman kudi haka ba, dama kin iya kasuwa haka?”
“Momyn Farhan, ni fa ƴar Kano ce, akwai mutumin Kano da bai iya kasuwanci ba?” na ba ta amsar ina dariya
Suka hada baki wajen fadin “Gaskiya kam, mutanen Kano akwai neman kudi”
Daidai lokacin su Abban Khalil suka shigo. Dr ya dauki Ramla da ke wasanta a kan katifa, Bashir kuma ya ce “Yau Khadija a dakin nan, hala su Umma basu dawo daga masallaci ba?”
Barrister ce ta ba shi amsa da fadin “kamar ko ka sani, can mu ka baro su”
Ya ce “Na sani mana, ai ita kam kamar ta fi kowa sanin dadin uwa”
Ni dai shiru na yi, saboda na san a kan abin da yake magana, so ya yi ya ja ni zuwa wani hotel din ni kuma na ki, saboda ni ce yar daɗi miji, ga yara da suruka sai mu rika zuwa hotel, duka fa 2weeks za mu yi, ga shi ma 2wks din ya kusa karewa.
Jin ban ce komai ba, ya juya hirar kan Barrister ya ce “Baffa ya ce kin hana su zuwa gida Barrister”
Yanayin fuskarta ta canja kafin ta ce “Ai ba haka mu ka yi dasu ba, nawa za a kashe su tafi Nigeria, kuma nawa za a kuma kashewa su koma India din”
Dr ya ce “Tun da suna son zuwa don Allah ki bar su, ga Affan nan ma yana son zuwa, Sai su dawo tare”
Furucin Dr ya yi min wani irin sanyi a zuciyata, Rahma ta ce “Ni ma ina son zuwa wlh”
Duk mu ka yi dariya, Bashir ne ya ce “Ai duk sai mu tafi, in ya so ku dawo a tare”
Ta juya idanunta a kan Dr tana mishi wani irin kallo. Ya ce “Allah Ya kiyaye hanya”
Duk mu ka yi dariya. Shi kenan akalar tafiya ta juya zuwa Nigeria, Dr ne kawai zai wuce India.
Mun yi ibada sosai daga mu har yaran, kafin mu ka dan tsinci tsaraba, ni kam kayayyaki na sawo sosai.
Ranar da mu ka bar Makka zuwa Jidda sai na ji duk babu dadi, Makka da Madina garuruwa ne da duk musulmin da ya je, Sai ya ji ba ya son tahowa.
Abuja muka sauka, nan mu ka bar Rahma da iyalanta, mu kuma mu ka yo Katsina, Umma ce kawai ta bi jirgi zuwa Kano, na ji kamar in bi ta, idan na ga saukarta sai in dawo gida. Amma su Yusrah suna can suna jiranta.
Time da mu ka iso gida an gyare shi tsaf, wannan kuma aikin Maman Aiman ne, part din Sarai aka gyarawa su Salman aka zuba masu komai da matashi ke bukata.
Sai da Inna ta yi sati daya sannan aka mayar da ita Ruma. Kuma zuwa lokacin yan sannu da zuwa sun dan rage, duk da saboda siyasar da Abban Khaleel ya shiga, kullum gidan cikin baki yake, maza da mata.
A cikin satin Zahra ta koma kd wurin aikinta, aka bar mu mu kadai, sosai gida ya yi albarka yan maza na shida, ga Salman, Baffa, Khalil, Assidiq, Affan da kuma Haidar. Sai Maama da Ramla.
Duk lokacin da Bashir zai fita wani taro na siyasa, ya kan kwashesu su raka shi, har campaign da su yake fita.
Kamar yau ma da misalin karfe biyu na rana suka dawo, kwanansu biyu rabonsu da gida, dukkansu sun yi wujiga-wujiga, kar ma Baffa ya ji labari, shi dama bai yi kalar jure wahala ba, yana nan yalolo da shi babu jiki, tun da suka shigo Maama ke dariya, ni din ma dai na kasa danne dariyar tawa, na shiga yinta ina kallon su daya bayan daya.
Salman dan gayu, amma sumar nan futu-futu da kura ta yamutse, Da yake Khalil farar shadda ya sanya da zai tafi, ta koma milk, babu abin da babu a jikinta. Baffa bakin wando ya sanya da jar shirt, wandon nan duk ya yi futu-futu. Affan ma haka, Assidiq kam fes da shi, wai wurin Inna ya tsaya bai bi su ba.
Na tsayar da idanuna a kan Salman na ce “Wai mutanen kauyen a saman kanka suka taru?”
Gorar ruwan hannunshi ya dire hade da shafa kan yana murmushi sannan ya ce “An ci wuya ne kawai Auntynmu. Mu yi ta zagin ƴan siyasar nan, muna cewa sun shige cikin A.C Yen-yen-yen ashe su ma suna cin wuya kafin su shiga A.c,Auntynmu irin wannan wahalar, ko ni sai na cika aljihu na taf, na warware wahalar da na sha kafin zan waiwayi wani”
Duk mu ka yi dariya kafin na ce “Allah ba ruwanshi da waccan wahalar da ka sha Salman, dama nema ka fita, kuma ya ba ka dole ne kuma ka sauke nauyin jama’a da ke kanka”
Baffa da ke kwance saman doguwar kujera alamun gajiya duk sun bayyana a tare da shi ya ce “Maganar gaskiya to ni ba zan nemi wani mukami a siyasa ba, wannan bakar wahalar ba da ni ba, kuma a haka ma ana iya yin zaben ba ka ci ba, aiko sai zuciyata ta buga”
Mu ka kuma yin dariya kafin Khaleel ya ce “Idan kuma ka ci, ranar lahira a kaika gaban Allah a daddaure aikin da ka yi ya kwance ka”
Baffa ya juyo yana kallo na, tare da fadin “Kin ji kuma ko Auntynmu, abun dai babu sauki”
Affan ya ce “Ni hayaniyar ce ma ba na so, kunnena ma ciwo yake yi tun a can, ban dai fadawa Abbanmu ba ne. Amma kida nan gam-gam, can yekuwa Yen-yen-yen, Haba wa zai iya wannan wahalar don Allah”
Na ce “Aiko ba za ka kara zuwa ba gaskiya”
Khalil ma ya ce “Ni dama ban so ya bi mu ba”
Salman ya gyara zama yana kallon Affan cike da kulawa ya ce “Ko mu je hospital ne?”
“Mu dan jira zuwa gobe mu gani” cewar Affan yana dan taba kunnen. Baffa ya yunkura dakyar ya tashi, yana fadin “Wane gobe, kawai Malam tashi ka yi wanka ka ci abinci aje hospital”
Da haka duk suka mike zuwa part din su, Maama kuma ta shiga hada masu abinci.
Sai a lokacin Bashir ya shigo gidan, shi ma da alamun gajiya a tare da shi, don haka na mike na bi bayan shi. Bayan na yi mishi duk abin da ya dace na sakko kasa don daukar mishi na shi abincin. A nan na ga yan samarin nawa fes, kamar ba su ne dazu busu-busu ba. Cike da tsokana na ce “Inye! Kun Sha kyau, waye zai kalle ku yanzu, ya ce kune na dazu din nan.(Na kalli Maama da ke kamawa Ramla kai da band na ce) Maama ya kika ga Excellency yanzu?”
Kai ta dago tana kallon Salman hade da dariya, shi ma dariyar yake tare shafa sumarshi da take fitar da kamshi maya-mayai kala-kala ya ce” kuma kin san dazu cewa ta yi wai tsami mu ke yi, muna shigowa wai temperature din falonki ta canja”
Sauran suka yi dariya, khaleel ya dauki filon kujera ya kai mata jifa yana fadin “Au! Haka kika ce, yasin don ban ji ba, amma yadda nake a gajiyancen da na sauke miki nauyi”
Mu kuma yin dariya, sannan na ce “Asibitin za ku je?”
Baffa ya ce “Eh, gara mu je likita ya duba shi”
Ya yi maganar yana daukar key din motar Zahra, wanda yake ajiye a wurin sauran keys din gidan
Na ce “Amma Abbanku ya ce ku daina daukar mata mota ko? Ga mota can ya ba ku, ya ce duk time da za ku fita ku rika dauka.”
Salman ya dauki key din motar da nake magana kafin ya ce “kin san shi ya fi iya tuka Auto, motar mata”
Ya kai karshen maganar yana nufar kofa
Na daga murya ina fadin “Don Allah ban da tukin ganganci”
Maama kuma ta ce “Ya Affan zan bi ku”
Ba ja ya ce “Taso mu tafi”
Khaleel ya yi saurin tare kofar yana fadin “Where? Cewa ta yi fa muna wari. Babu inda za ta bi mu”
Kallona na juya kanta, ta marairaice tana magiya, Baffa da Khaleel sun dage a kan ba ta bin su.
Salman ya dawo yana fadin “First lady fito mu tafi, idan ba haka ba, su din ma ba za su je ba, Sai mu tafi daga ni sai Affan da kuma ke. Ai ni kika fadamawa ina tsami ba su ba. Ko da su kike?”
Kai ta girgiza alamar a’a
Ya kalle su hade da watsa hannuwa yana fadin “You see! Da ni take. Ni da ita kuma 5&6 ne, don haka dakko hijab din ki mu tafi”
Ya kai karshen maganar hade da juyawa, ita kuma ta dakko hijab, da ta zo wucewa Khaleel da Baffa suka yi mata dundu, a haka ta fice tana dariya, su ma suka bi bayan ta.
Daidai lokacin da Bashir ya sakko yana fadin “Khadija babu abincin ne hala?”
“Yi hakuri, na tsaya sallamar yaran nan ne”
“Ina za su je? Daga dawowarsu ko hutawa ba su yi ba. Kin san fa ba na son yawon nan”
Kamar in fada mishi inda za su je, Sai kuma na fasa, saboda su dukkansu rokana suka yi wai kar a sanar mishi kada tension ya yi mishi yawa. Shi ya sa na basu kudi, ba tare da na tambaye shi ba
Ina hada mishi kayan abincin na ce “Low-cost za su je wurin Hajiya (kanwar karkarsu ta wajen uwa, da yake mahaifan Zarah kaf sun rasu
Zama ya yi tare fadin” Ba na son suna fita any how, za a iya amfani da su wajen ganin an kai ni kasa”
Cikin alamun kwantar da hankali na ce “In Sha Allah babu abin da zai same su”
Yana cin abincin ya ce “Ba na jin zan kara fita da su ma, wannan karon sun sha wahala, tun ba Affan ba, kin san ba lafiyar kunne ne da shi ba, kuma ga kara da hayaniya ya yi yawa a wurin. Ina tunanin ma ya dan je ya ga likita”
“In Sha Allah babu matsala” na yi maganar ina ba Ramla abinci, haka mu ka ci gaba da tattauna different issues har su Salman suka dawo. Daga nan kuma suka shiga alwala don tafiya sallahr magriba.