Skip to content
Part 54 of 58 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

A satin kuma sai ga ƴan mazan Rahma su ma sun zo, Adnan, Yusuf, Faruk da kuma Farhan. Wanda shi ne sa’ar Affan

Gidan sai ya kara cika, ko ina duk maza, Maama da Ramla ne kawai yan mata, lokacin da Zahra ta zo weekend ta iske gidan a cike,  cewa ta yi “Lallai Auntynmu kin sha aiki, kuma kina shan aiki. Sau nawa kike dafa abinci, gaskiya ba zan iya ba, guduwa zan kuma yi” kwananta biyu kam ta gudu, kin zama ta yi, Sam Zahra ba ta son shiga kitchen.

Sai da aka kammala komai na makarantar Khalil, sannan suka fara shirin tafiya, daga Katsina Kaduna suka sauka, Zahra ta kwashe zuwa Abuja, daga can kuma Rahma ta dauka zuwa India.

Shi kenan gidan ya kara komawa shiru, ban san Khalil ya yi nisa a zuciyata ba sai da ya tafi,  na rika ji na shiru, musamman idan Maama sun tafi makaranta, ga Zahra ba zama take yi ba. Shi ma Abban Khaleel din baya zama, duk da an gama yawon campaign amma kullum suna cikin commitments, idan ya fita tun safe sai dare.

A haka har satin zabe, aiko Zahra ta baro Kaduna ta dawo Katsina, tare da ita suke ta hidimarsu, wani lokaci ya riga ta fita, wani lokaci su fita tare, iyakcina idan sun dawo suna tattauna wata kitimurmurar  abun ya yi ta ba ni mamaki, in ce siyasa mugun wasa.

Saura kwana biyu zabe mu ka kwashe zuwa Ruma, amma still Zahra da Abban Khaleel suna Katsina, Sai ana gobe zabe Abban Khalil ya iso, Zahra kam sai ranar zaben ma ta iso.

Bayan na dawo daga kaɗa kuri’a ta na zauna ina zaman jiran tsammani, ni ma sai na ji ba na son Bashir ya fadi, da kam ban damu ba, amma yanzu  na damu sosai, ina fatan ya yi wining, ko don struggle din da ya yi, ga shi ba lafiyar kafa ne da shi ba, amma haka yake ta struggle.

Zahra da ita aka raka akwatuna zabe, da ta tawagar lauyoyi  da kungiyoyin masu zaman kansu da ta kwaso.

Yadda a can ba su yi bacci ba, haka a nan ma ban yi bacci ba, saboda fargaba me zai je ya zo. Musamman yadda aka sha artabu a wajen zaben, Sai da aka kira ƴansanda. Su Khaleel ma haka su ka yi ta kirana har cikin dare suna tambayar ya ake ciki, sai dai in ce musu su yi addu’a, ni din ma ita nake yi.

Ranar Sunday shiru ba a fadi sakamako ba,  ranar Monday da yamma aka fadi cewa wai an yi cancel din zaben wasu mazabun sai an canja, kuma rumfunan da Abban Khaleel ke da kuri’u masu yawa aka yi cancel. Sam abun bai yi mana dadi ba, su Khaleel ma da na fada  masu haka na ga duk jikinsu ya yi sanyi ransu ya baci, ni ce na rika kwantar masu da hankali. Don makarantar yara kawai na koma Katsina, amma zaman Ruman ya yi min dadi, ranar Sunday na isa da yamma, Zahra kuma ta tafi Kaduna Monday da safe.

Tun daga lokacin da aka yi cancel din zaben nan ban kara samun kan Abban Khaleel ba, wani lokaci idan ya fita tun safe sai karfe biyun dare yake dawowa, yau yana LGA gobe yana state secretaria, jibi yana inec office, citta yana collation center, haka dai kullum.

Har abun ya fara damuna, kai da miji kun zama baƙin juna, Sai na ji Ina ma bai shiga siyasar nan ba, mun yi zamanmu irin baya, ya fita 9am ya dawo 6pm hankalinmu kwance, babu wata fargaba ka damuwa a tare da mu.

Amma yanzu hankalinshi bai kwanta ba, nawa bai kwanta ba, na yara bai kwanta ba, na ƴan’uwa bai kwanta ba. Kullum jininmu a kan kumba.

Yau ma  misalin karfe biyu na dareya shigo gidan, dama idona biyu ban yi bacci ba, don haka tun daga bude gate din Shi, da shigowa part dina duk ina ji. Sai da ya turo kofa ne ya shigo bedroom na tashi zaune ina kallon yadda yake  jan kafarshi mara lafiyar a matukar gajiye.

Babbar rigarshi ya fara cirewa, kafin ya zauna gefen gadon yana fadin “Wash Allahna!”

“Sannu” na furta cike da tausayi

Ya ce “Yauwa, ba ki yi bacci ba?”

“Ina zan yi bacci kana waje, kai ma ka san ba zan iya ba”

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “Komai ya kusa zuwa karshe ai, ranar Asabar za a canja zaben”

Ni ma nisawa na yi a hankali kafin na ce “Abban Khlil kodai za ka janye ne, ni wannan tashin hankalin ya ishe ni, daga lokacin da ka tsoma hannunka cikin siyasa shi kenan bamu da kwanciyar hankali, kai ba ka huta ba, mu ba mu huta, yanzu ko lokacinmu ma ba ka da shi. Ni gaskiya idan haka harkar siyasar nan take ta fita a kaina, matan gwamnoni da shugaban kasa suna hak’uri, ni gaskiya rayuwarmu ta baya ta fi min daɗi “

Ya ɗan murmusa kadan kafin ya ce” Kin san aski idan ya zo gaban goshi ya zafi, ki yi hak’uri. Komai zai wuce. Kuma batun in janye Khadija ai ba shi, idan na yi haka tamkar na ji tsoro ne, kuma dama abin da abokan adawa suke so kenan, don haka duk lokacin da na yunkura, za su danne ni, gara in nuna musu a shiryena nake ko a mutu ko a yi rai, tun da jama’a suna yi na”

“Amma ba za a bar su su zabe ka ba. Tun da ga shi sun zaben kan, an yi cancel”

Da damuwa a fuskarshi ya ce “Wannan shi ne yake yi min zafi, ni in rasa kujerar baya damuna, da ace ba su zabe ni ba, na fadi, to zan karbi faduwar, amma yana min zafi ace mutanen nan su bar ayyukansu, su fito cikin rana su yi zabe, amma a hana su abin da suka zaba”

Shiru na yi ina taya shi jin zafin, kafin ya katse mana shirun da fadin “Akwai kitimurmura a siyasar Kasar nan Khadija, wanda yake ciki ne kawai ya sani. Allah dai ya bamu ikon yin adalci idan mun samu abin da muke nema”

Jiki a sanyaye na amsa da amin, sannan na kara da “Yaushe Barrister za ta zo kenan?”

Ya ce “Laraba ko Alhamis in Sha Allah”

Kai na jinjina ina fadin “Mace mai kamar maza kenan, Zahra ta yi nisa sosai gaskiya, yar gwagwarmaya ce”

Murmushi ya yi mai hade da shauki, lokaci daya kuma ya mike tsaye yana fadin “Ba ta da tsoro Sam”

Ni ma murmushin na yi, ba tare da na ce komai ba, shi kuma ya shiga toilet, kitchen na tafi don sama mishi abin da zai dace da lokacin da ya da ya dawo.

Ranar Laraba kam Zahra ta diro Katsina, tun daga lokacin da ta iso ba ta zauna ba, ni dai nawa ido, da fadin Allah Ya bada sa a, ko in ce Allah Ya sa a dawo lafiya.

A wannan karon shirin da jam’iyar su Abban Khalil ta yi ya fi na wancan lokacin, duk wasu kungiyoyi wadanda suke da alaka da zabe an tanade su.

Ranar Asabar kam tun safe su Salman ke kirana in basu situation report, bayan Ni ma ban san komai ba, to ko na kira Zahra ba ta dagawa bare Bashir.

Sai wajen karfe uku na rana Zarah ta kira ni, wai na kammala zaben ana ƙirga kuri’a, can wajen shida na yamma kuma ta kira ni cewa Bashir ne ya lashe zaben, amma za mu jira hukumar zabe ta sanar. Haka na sanarwa wa su Rahma da suke ta faman kirana.

Daga Bashir har Zahra babu wanda ya dawo gida, ni din ma kasa bacci na yi, safiyar Lahadi tun safe muke dakon hukuma ta sanar da na nasarar Abban Khalil Amma shiru, mutane sai kirana suke yi, daga Kano, kawaye da abokan arziki suna tambayata halin da ake ciki, dole na kashe wayata, na cewa Zahra any information ta kira ni da wayar Maman Aiman.

Haka na zauna tsumm, ko abinci na kasa ci, ga wani ciwon kai ɗan uban su, su kansu yaran duk sun nutsu babu hayaniya, a haka ma ban fito sak na fada masu abin da ke faruwa ba.

Misalin karfe uku, Maman Aiman ta shigo gidan, Maama ce ta bude mata kofa. Bayan mun gaisa ta ce “Su Abban Khaleel har yanzu shiru”

“Wlh kam” na amsa ta a takaice

Ta ce “Barrister wai a kawo miki waya, wayarki a kashe”

Gabana ya tsananta faduwa, ina kallon Maman Aiman da take kokarin kiran Barrister, ba jimawa ta miko min.

Jiki a sanyaye na ce “Ya ya?”

Ta yi dariya kafin ta ce “Ki kwantar da hankalinki, mijinki dai ya zama chairman, yanzu hukumar zabe ta tabbatar da hakan”

Wani sanyin dadi ya ratsa ni, na lumshe ido ina fadin “Alhamdulillah Ya Rabbb”

Sai kuma na yanke wayar hade da yin sujudur Shukar, kafin na dago na fesa wa su Maman Aiman abin da ya faru, suka kacame da murna ni kuma na dakko wayata na kunna, bayan komai ya zama daidai na kira Rahma na fesa mata ita da yara, suka hau ihun murna, haka na rika kiran mutane ina sanar musu da nasarar Abban Khaleel.

Misalin karfe biyar kuma sai ga kiran Murja, wai an sanyawa gidanmu na Ruma wuta.

A zuciyata na ce” kai Ya Allahna! Haka siyasar take ne, ashe tsugunne ba ta kare ba, an siyar da kare an sawo biri”

Sai isha’i Murja ta fada min an kashe wutar amma ta yi barna.

Barrister dai Monday da safe ta dawo, tana gama shan tea ta yi wanka sai bacci, babu wata hira doguwa da mu ka yi.

Kuma har zuwa lokacin ban kira Bashir ba, shi ma kuma bai kira ni ba, ban kuma yi fushi da hakan ba, na san yana cikin commitment. Ni din ma I’m so committed din, Ga aikin gida, ga mutanen da suke shigowa don taya mu murna.

Misalin karfe biyu ina zaune a falo ina cin abinci Zahra ta shigo, ta kara wani haske har da yar rama ta yi.

Har ta zauna ban dauke idanuna a kanta ba “Wai Allah! Sannu, kin ga yadda kika yi wata rama kuwa” na karasa maganar ina mika mata flask din abinci.

Ta shiga zuba abincin tana fadin “Ba dole ba, yaushe rabona da in zauna in ci abinci ya zauna min, kai Nigeria kasarmu ta gado. Gaskiya Nigeria ba za ta gyaru ba, na fitar da rai a garuruwarta, kawai dai mutum ya yi fighting a kan hakkinshi, ka nemi abin da za ka rayu shi kenan”

Na ce “Haba, ya kike fadin haka, ai sai ki kashe mana gwiwa”

Tana cin abincin ta ce “Aiko sai dai ta mutun, saboda ni na san abin da na gani, Auntynmu Nigeria ba za ta gyaru ba idan kuwa har za ta gyaru, Sai dai idan duk kashe mu za a yi, a yo sabbi”

“Subhnallah!” na fada ina yar dariya. Ita kuma ta shiga ba ni labarin shiga da fitar da su rika yi. Irin yadda aka rika tayar da jijiyoyin wuya da murza gashin baki.

Hannuna a kan haba nake kallon, kafin na ce “Tabbb! Let assume ba ki san Abban Khaleel bai sanki ba. Duk n Allah wane amfani zan yi mishi a nan?”

Ta dan yi murmushi tare da fadin “Addu’a mana, addu’ar mace a kan mijinta ai karbabbiya ce”

Kai na shiga girgizawa sannan na ce “Bayan addu’a akwai aiki ma a aikace. Taya zan zube hannu a gida ina addu’a wai mijina ya zama chairman bayan babu campaign, babu goyon bayan jama’a. Abu ne mawuyaci Barrister. Bayan irina da nake addu’a, yana kuma bukatar irin ki, da kika san komai”

Dariya ta yi kafin ta ce “Kamar kullum dai, abincin nan ya yi dadi”

Ni ma dariyar na yi kafin na ce “kin iya fada kam, amma ba za ki shiga a yi da ke ba”

Wata dariyar ta yi kafin ta ce “Da an jima ma zan gudu”

Ido na waro da sauri na ce “Ina?”

“Kaduna wurin aiki, ana bukatata da gaggawa”

“Kai wannan aiki, anya ba za ki ajiye shi ba, na dauka za ki jira angon ya dawo, ki dan ci amarci sannan”

“Aiki ai ba zai ajiyu ba, ina son aikina. Amarci kuma na bar miki ki  hada da nawa ki ci”

Kafin in yi magana ta ce”Ina son zuwa wurin yaran nan, kila next week, zan tafi da Maama da Ramla, tun da ai next week za su gama exam”

Na ce “Allah Ya kai mu”

Daga nan mu ka shiga hirar duniya, a nan ta yi sallahr la’asar, Sai 5pm ta ce za ta je ta shirya jirgin 6pm za ta bi.

Wannan karon kam har airport na yi mata rakiya, Zahra mutuniyar kirki ce, ni kaina na san ta fi ni kirki nesa ba kusa ba. Yarana kamar nata, ba ta wani kishi a kaina, ita auran ma kamar irin na je-ka-na-yi-ka din nan, sam ba shi ne a gabanta, sabgoginta ne a gaban ta. Kila shi ya sa nake jin dadin kishin da ita. Duk da wani lokaci shi gogan ya kan bi ta har Kaduna din, ko kuma ya matsa mata lallai ta zo. Amma don ita ko a jikinta.

Idan ma ta zo ta dade shi ne sati, wani lokaci na kan ce Bashir ya yi mata satin duk, amma sai ta ce ita wlh ba ta yarda ba, wai ba za ta iya ba, ita za a takura mata

Na kan ce mata in don abinci ne zan girka mata, tun da na san shi ne ya kashe kakarta, Sai ta yi tsalle ta dire, ta ce ita fa ba ta so. Kuma har cikin zuciyarta ba ta so din.

<< Hasashena 53Hasashena 56 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×