Skip to content
Part 56 of 58 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Misalin karfe goma na dare Bashir ya dawo tare da rakiyar mutanen da ban san yawansu ba.

Su Maama da suke jiran dawowarshi, suka tare shi da murna, haka shi din ma ya rika hugging din su cike da farin ciki.

Bayan mun kebe ne na ce “Sannu Honorable, Allah ubangiji Ya sanya alkairi ya ba ka ikon sauke nauyin da ya dora ma, haka siyasar ashe?”

Jikinshi ya janyo ni yana fadin “I missed so much my half, Ina can zuciyata tana nan, ya kike da Babies dina, ya yi maganar hade da shafa marata”

Hannunshi na janye kafin na ce “Za ka fara ko, ina dan hutawa za ka jawo min ciki, kuma na san tun da ka fara maganarshi yanzu zai samu”

Dariya ya yi kafin ya ce “Bare ma akwai, kawai dai karami ne, na so fada miki so I’m so committed. But Yanzu na fada miki, kuma twins nake hoping, Saboda ko a ka’aba su na roka miki”

“Ya kake dai yanzu, fatan komai lafiya, babu sauran wani tsugunne ta shi?” na canja mana topic.

“Alhamdulillah! Everything is OK now”

“Ma Sha Allah” na fada ina nuna farin cikina, kafin in ce wani abu ya ce “Barrister ta tafi ko?”

Na jinjina kai alamar eh

Ya yi murmushi yana fadin “Zahra trouble, wato ba ta jira ni din ba dai, I will follow her back tomorrow in Sha Allah”

Wani abu ya tsire ni, na yi saurin kawar da shi gefe ina fadin “Allah Ya kai mu”

Mun jima muna tattauna yadda abubuwa suka kasance, wanda da yawansu labari ne a kan rawar da Zahra ta taka mishi, yadda yake fadin jajircewarta a kan nasarar shi sai na ji ni ban yi komai ba, kamar kuma ban taba yi mishi komai ba.

Washegari misalin karfe tara ya daga Kaduna, duk yadda nake son dannewa sai da abun ya rika damuna, ko na warware ina harkokina sai in ji wani abu a kasan zuciyata yana damuna, can sai in tuno tafiyar Abban Khaleel ce.

Na idar da sallah Azhur ina zaune kan sallayar ban tashi ba, tafiyar Abban Khaleel ta fado min, na shiga yin bad imagination din nawa kamar yadda na saba.

A hankali na furta “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Ya Allah ka yaye min wannan kishi ko son kai.” Saboda yanzun gani nake kamar kaina nake so ba kishi ba. Idan ba haka ina laifin Zahra, mutuniyar harkokin gabanta ne kawai a gabanta. Ni ke ta miji, ita ba ta shi take yi ba. Irin dai yadda nake jin kishin shi ba na jin ita tana jin irin wannan. Tana dai ba duk wani abu da ya shafe shi muhimmanci, kuma ta kan yi bakin rai bakin fama. Misali samowa Khaleel makarantar Comprehensive Abuja, samo mishi a Indiya, tallafawa Bashir wajen takararshi. Biyawa su Maama Umrah, akwai dai tarin alkairanta wadanda ba ta duba kishi.

Bai kamata in rika damuwa don mijinta yana nuna kulawarshi a kanta ba. Bayan ma ni na fi ta morar shi, lallai wannan son kai ne.

Na kai karshen tunanin hade da mikewa zuwa kitchen don zuba abinci, ina zuba jallof sin Shinkafar cikin plate kamshinta ya doki hancina, Sai kawai amai ya taso min, dole na juya na yi shi a cikin sink. Ina dauraye sink din gabana na faduwa, saboda tuna maganar Abban Khaleel, kar dai da gaske ciki ne da ni.

A gajiye na koma falo na kwanta, abincin da ban ci ba kenan, Sai fura na yi oder aka kawo min.

Wasa-wasa sai ciwo, wannan ya tabbatar min ina da lallai ciki ne da ni, daga wannan ranar kullum fura ce abincina, har Abban Khaleel ya yi kwana uku, jikina ya rika ba ni, sai weekend zai dawo. Ba na son fada mishi ba ni da lafiya, kar ace ko kissa ce.

Ranar Friday haka na tashi da amai, na yi ta yi ba kakkautawa, Sai wajen 2pm na ji sauki, har bacci ya dauke ni. Maama ce ta yi komai na gidan ta dafa masu taliya. Ni dai ina ta baccin gajiya. A cikin baccin na ji Ina shakar kamshin Bashir, ido na bude a hankali hade da dora su a kanshi, Sai kuwa yunkura dakyar na tashi, ina fadin “Yaushe ka dawo?”

Kusa da ni ya zauna yana fadin “Yanzun nan, me ya sa kika ki fada min ba ki da lafiya?” ya kai karshen maganar hade da ba bata rai.

Na ce “Da sauki ai”

“Wane sauki, duka kwana nawa shi ne har kin zube haka”

Hawayena na dauke kafin na ce “Ina expecting da gaske ina da ciki”

Mamaki shimfide a fuskashi ya ce “To me ye? Ba ni ne mai shi ba? Addu’a fa na yi, kuma Allah Ya amsa min, ai ni na san kina da shi, kuma ke da shi duk ina son ku”

“To ni ba zan huta ba, Sai dai in yi ta haihuwa, idan ba ciki ba goyo, ni ma fa ina son ina dan huta”

Jikinshi ya janyo ni kafin ya ce “Khadija! Ina son yara sosai, duk lokacin da su Salman da su Adnan din Rahma suka taru a gidan nan sai in ji Ina ma ni ne mahaifinsu. Ni ban taɓa ƙin ki, ko kyamarki don kina goyo ba, ina kara sonki ne ma, saboda kina ba ni abin da nake so. Don Allah ki daina kallon wasu ko wata. Just give me my happiness. Tashi mu je asibiti “

Kai na girgiza a hankali na ce” Ni ba zan je ba”

Wayarshi ya dakko hade da kiran likita, bayan ya gama wayar ne ya ce “Doctor zai zo ya duba ki” ban amsa ba Zahra ta shigo, ganin ina dauke hawaye, Sai ta yi sororo jiki a mace ta ce “Wai duk ciwon ne?”

Bashir ne ya ce “Wai tana da ciki, shi ne take kula”

Baki ta bude alamun mamaki tana kallona, Sai kuma ta karasa shigowa dakin gabadaya, daidai lokacin wayar Abban Khaleel ta shiga vibration, don haka ya dauka ya fice daga dakin, ita kuma ta zauna wurin da ya tashi.

Shiru ya ratsa ɗakin kafin ta ce “Kukan dadi kike Auntynmu. Da can dai ba na sha’awar haihuwa, amma yanzu ina so, saboda Bashir yana so. Na san idan Bashir ya ganni da ciki, soyayyata za ta karu a zuciyarshi, amma ke kin samu kina kuka”

Dama tuni na dakata da kukan nake yi ina kallon ta. Nisawa ta yi a hankali kafin ta daga min rigarta tana fadin “What do you see?”

Na kurawa fatar cikinta ido wacce wani gefe ya yi tabo alamun dai an yi dinki a wurin. Bayan ta tabbatar na gani sai ta saki rigar tana fadin “Yanzu ba ni da mahaifa, an cire ta sakamakon fibroid. Da ace Ina da mahaifa da na haihu ko don Bashir da kuma surutun da mutane suke yi, a kan cewa ko na yi aure ba zan yarda in  haihu ba. Kin ga idan na haihu zan farantawa mijina, sannan zan ba masu cewa ba zan haihu ba kunya. Ki godewa Allah Khadija akwai mutane da yawa da suke jiran irin wannan ranar basu samu ba, tun da ke kin samu ki godewa Allah “

Kai na jinjina a hankali kafin na ce” Allah Ya raya miki wadanda kika samu, ya albarkace su, ɗa ɗaya gari ne idan Allah Ya raya shi. Ni ma ba wai ba na son haihuwar ba ne ina son dai ɗan huta “

” Kin huta ai, Ramla fa cikin shekara ta uku take. “

Kai na kuma jinjinawa a hankali, kafin na ce” Ba tun yanzu na fahimci kina son Maama ba, idan har da gaske kina da ra’ayin rike ta, wlh ni dai na bar miki, ko mutuwa na yi ta ki ce. “

Murmushi ta yi hade da kamo hannuna tana fadin” Ina son Maama, wlh, jin ta nake kamar ni na haife ta, abin da ya sa nake yin baya-baya da ita, ina jin tsoron me zai je ya zo, in kwallafa raina a kanta, kuma a zo a nuna min iyakata. Amma zuwa yanzu na samu kwarin gwiwar daukarta, na gode sosai Allah ubangiji ya sauke ki lafiya ya raya abin da za ki haifa.

Na amsa da amin, daga haka ku ka ci gaba da hira, tana kara ba ni kwarin gwiwa har Dr ya zo ya duba ni, ya sanya min drip.

Tun daga wannan lokacin rikon Maama ya koma hannun Zahra, dakinta da komanta ya koma can, ko Zahra ba ta nan to ita tana bangaren, wani lokaci har bacci a can take yin abin ta ba ta jin tsoro

Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya Alhamdulillah, ta ko wane bangare muna samun ci gaba, Bashir na daya daga ciyamomin da suke sauke nauyin da ya hau kansu dai gwargwado.

Tun cikina na wata biyar aka tabbatar min yan biyu ne, tun daga wannan lokacin kuwa Bashir da Zahra ke shirye-shirye tarbarsu.

Ni kam dai ina tantance ciki, nauyin ma da bambanci da sauran cikin da nake yi. Haka dai na yi ta lallabawa har Allah Ya sauke ni lafiya, na samu yan biyuna mace da namiji. Farin ciki wurin ƴan’uwa da abokan arziki ba a magana, yara kam kamar su yo tsuntsuwa su taho. Wannan karon ban so yin taron suna ba, to kun san mata da bidi’a ga ƴan’uwa na nesa sun zo, dole dai aka tara jama’a, ga shi har da baki maza mu ka yi masu kidan gargajiya. Zahrah kam ita da Yusrah sune suka yi ta hidima da baki. Har aka kammala suna, gida ya koma namu.

Daga Ruma Inna ta turo min da mai taya ni zaman wanka, don haka ba ni da matsala nan wajen, bangaren abinci kuwa Maama ke yin komai, saboda SS2 take a lokacin. Zahrah ma duk weekend tana gida. Shi ya sa Bashir ke samun kulawa, saboda idan dai kula da miji ne Zahrah ta iya, abu daya ne damuwarta shiga kitchen, kuma za ta yo odar abinci mai rai da motsi ta ba mijinta, har muma a kara mu.

Su Hassana na da wata hudu Su Khalil suka zo hutu, zuwa lokacin kuma ku san 2 years da hawan kujerar Abban Khaleel, yanzu ma kujerar majalisar yake hari, kuma yana samun goyon bayan jam’iya da mutanenshi.

Zuwan su Khaleel sai gidan ya kara cika, hidimarshi kuma ta kara yawa. Zahra ce da kanta ta samo mana yar aiki, Abban Khaleel kuma bai hana ba, da ni ce dai na samo, akwai wahala ya yarda, zai ce ina aikin yake. Amma ita ya yi shiru bai daga ba, sannan akwai mai shara da gyara fulowoyi, ita kuma kanta Zahra tana da tata yar aikin, wacce idan ta zo yarinyar ke zuwa.

Mu dai sunan tamu Rabi, amma yara suna kiran ta da Maman Usi, ita kuma yar aikin Zahra sunan Zaituna.

Zuwan Maman Usi ba karamin sauki na samu ba, tana da tsafta sosai, respect ga kai zuciya nesa, sam ba ta da hayaniya kuma ba ta da ƙiwa.

Yanzu ni babu abin da nake yi, illa bayar da umarni, zan zauna a kitchen ina kallon Maama da Maman Usi yadda suke girki, wani lokacin ma ko kitchen din ba na shiga, Sai dai Maama ta rika zuwa tana tambayata.

Su Hassana da Hussain kam bayar da nono ke hadamu sai bacci, basu hannun wannan basu hannun wancan.

Yanzu ma zaune nake a falo, ina ware wasu shaddoji, ƴan samarin kuma duk suna falo, kasancewar ko Zahra na nan, falona dai shi ne wurin zamansu.

Hassana zaune cikin kekenta a tsakiyar falon, lokaci zuwa lokaci su kan yi mata wasa. Yanzu ma Baffa ne ke yi mata wasa, tana wangale mishi baki, yadda yake mata  wasan ne ya sanya ni juyowa ina kallon shi. Ni ma kawai sai na ji Ina dariyar ya dage “kek-kek-kek, kamotanan-kamotanan, wacece wannan, wacece wannan” ita kuma sai ta wangale baki, shi ma sai ya kama dariyar. Kasancewar Salman ne a kusa da ni, shi ne ya ji sautin dariyata, ya dago yana kallona, Sai kuma ya mayar da kallon na shi kan Baffa, shi ma sai ya kama dariyar. Dalilin da ya sa Baffa dagowa yana kallonmu, lokaci daya kuma yana dariya ya ce “It seems like mad person Ko? Allah Sai yanzu na lura”

Dalilin da ya janyo hankalin sauran zuwa kanshi, ni kuma da Salman muna dariya. Na juya kan lissafin da nake yi ya ce “Auntynmu yarinyar nan ta ki, is very – very beautiful Allah, the only problem kawai ba ta da gashi” ya kai karshen maganar yana kara yi mata wani sabon wasan.

Cikin tsokana na ce “Haka nan kuma za ka jira ta girma ka aure ta, ga ku nan zaga-zaga ina za mu kai ƴanmatanmu, daya bayan daya zan haiho mu ku mata, har da su Adnan.”

Salman ya ce “Ni dai an haifi min tawa, ni ne farko, Sai ku dasa layi”

Cikin dariya Baffa ya ce “Waye zai zauna jira, Sai dai su zo a na biyu, yanzu ko wannan yarinyar ni ai ba zan iya jira ba”

Baki bude nake kallon shi, na ce “lallai Baffa, wato ba ko kunya”

Cikin dariya ya ce “Haba Auntynmu I’m 22 fa yanzu, don Allah in zauna jiran wannan yarinyar nan ta girma in aure ta, time din fa na kai 40 years”

Khaleel ya ce “To me ye? Har wani labarin aure kake, mtswww!” ya karasa maganar yana juyawa kan kallon da yake yi.

Na bi shi da kallo, seriously a fuskarshi auran baya gaban shi, kodayake dama bai isa fara wannan tunanin ba, duka shekerunshi 19,su ko su Salman next year suke hada degree din su na farko, the different is clear. Shi Ko goga Affan kamar ma baya falon.

Salman ya ce “Ni zan iya jiran first lady har zuwa wannan lokacin, to amma a taya ni barka ma ta girma”

Na juya kan Maama wacce ke silent murmushi kanta a kasa, Affan kuma na aika mata harara. Ya ce  “Ke dalla tashi ki fita ki ba mutane wuri, munafuka, ana magana kina wani kasa da kai kamar bakuwar jaɓa”

Duk suka mayar da kallon su kan Maama wacce ta bata fuska kamar za ta yi kuka, lokaci daya kuma ta mike ta nufi upstairs.

Khaleel ya bata rai yana kallon Affan kafin ya ce “Me ye haka da Allah?” komai Affan din bai ce ba. Khaleel ya juya kan kallon shi yana cewa “Kodayake ma kun fi kusa. An jima kadan zan gan ku tare”

Gaskiya Khaleel ya fada Maama da Affan akwai soyayya, shakuwa da kuma kauna ta musamman a tsakaninsu. Komin Maama Affan ne ke fara ji, daga nan Zahra, ni ce ta karshen ji, wani lokaci ma a bakin Affan din nake ji. Haka shi din ma komai ya samu na Maama ne.

Sai dai na fahimci yana masifar kishi a kan kannen shi mata, ba wai Maama ba, hatta Ramla Affan ya tsani ya ga mu’amala mai tsawo tana shiga tsakaninsu da samarin gidan wadanda ba muharramanta ba, yanzu zai kawo abin da zai yanke alakar.

Haka yake a kan Salman da Maama da zarar ya gansu tare, Sai ya san dalilin da ya raba tsakaninsu. Ko sun fahimci haka, ko ni kawai ce na fahimta oho. Salman dai ta shi ya yi, ya bi Maama, shi kuma Affan din ya raka su da harara.

<< Hasashena 56Hasashena 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×