BAYAN SHEKARU UKU
A cikin wadannan shekarun, abubuwa da yawa sun faru, masu dadi da akasinsu, duk da dai masu dadin su suka fi yawa.
A bangarena na dai na yaye su Hussain, kasuwancina ya ci gaba. Khaleel na shekarar karshe a makaranta, Affan saura shekera daya. Maama na school of nursing Katsina year 2 first semester. Assidiq na jami’ar Alkalam year 1 shi da Haidar, Hassana da Hussain suna nursery one.
Bangaren zamanmu da Zahra kam, Sai ala-san-barka. Ni ba ni da wani case da ita mai zafi, duk da kishi wani lokaci ya kan motsa, amma ina kokarin dannewa in ga cewa ban nuna ba, kamar yadda ita ma take danne nata a kaina. Saboda na tabbata tana jin abin da nake ji wani lokaci duk dauriyarta da kawar da kanta. Don haka ni a bangarena komai Alhamdulillah.
Bangaren Bashir ma hakan take, a kujerarshi ta chairman ya yi abubuwa da yawa masu kyau ga al’umma duk akwai kalubale sosai, kujerar jin ta ya fi ganinta, da yawan ayyukan da yake yi da kudinshi ne. Saboda yana noma, kuma kasuwancinshi duk bangaren noman ne, siyar da taki, maganin kwari na ruwa da na gari, sayar iri ko wane kala. Yanzu kuma da ake buga gangar siyasa, tuni ya jingine kujerar ciyaman din yana neman ta reps, don haka yanzu hankalinshi baya jikinshi, kaf yana kan kujerar reps din nan. A wannan karon ma dai shi da Zahra da wasu manya suke yi mishi susa. Zahra ta yi nisa fiye da tunanin mai tunani, ni kaina na san ita din ba sa a ta ba ce, ta ko wane bangare, ilmi, dukiya, sanayya wayewa ta ko wane bangare Zahra ta yi min fintinkau. Saboda har SA gwamnan Katsina ya ba ta. Shi ya sa na kwantar da kaina, na daina daga hankalina a kanta. Ba dalilin ya fada da wanda ya fi ka.
Bangaren Zahrahn ma kamar yadda na fada komai yana tafiyar mata daidai, kamar ita ce take cewa Allah haka nake so a yi min, kuma sai ya yi mata din. Ita din ƴar sa’a rayuwa ce, komai ta tasa a gaba sai ta yi achieving, duk da tana da jajircewa, tabbas Zahra jajirtaccen mace ce, a wurin ta na koyi abubuwa da yawa wadanda nake ganin sun fi karfina, amma na fi karfinsu a yanzu. Komai girman abu Zahra ba ta jin tsoro ko shakkar tunkararshi.
Mutane da yawa idan ana kallon comment din su a karkashin post idan ta yi, sai in rinka yin murmushi. Da yawansu suna fassarata da ba yadda take ba.
Wasu su ce mijinta ya zama mijin Hajiya, eh za a iya cewa hakan, amma tabbas Bashir ba mijin Hajiya ba ne, saboda ni na san yana ba ta umurni kuma tana bi. Tana kuma kiyaye duk wasu hakkokinshi. Don yadda nake fada yana fada ma, ita ba ta yin haka, har mamaki nake yi.
Kila suna hukuntata da yadda take fafutuka kuma kowa ya santa, wannan kuma ra’ayinta ne, sannan ta na yi ne don gobenta da inganta rayuwar yaranta. Saboda abin da na fahimta ita ke dawainiya da yaranta, ba ta jiran kowa a kansu, kuma ni ban taba ganin wanda ya kawo mata wani taimako a kan yaranta ba, bangaren mahaifinsu ko bangarenta.
Tabbas wannan na daya daga cikin abin da na koya a rayuwarta, ina jin a yanzu da Allah zai dauki rayuwar Bashir, ni din zan kula da yaranmu, ba sai na nemi taimakon kowa ba.
Zuwa yanzu kam Salman da Ma’aruf (Baffa) duk sun gama school, sun kuma dawo gida Katsina, dukkansu sai da ta nemar musu aiki a babban asibitin Katsina, ta siya musu mota a matsayin gifts din su, sannan ta kuma nema musu admission a Kasar Malesia, ni ban san ma wane irin karatun suke yi ba, ko degree na biyu suke yi oho.
Dukkansu suna da fili ana yi musu gini, a takaice dai ta gina yaranta, idan yanzu ta bar duniya suna da madafa. Na ji ma tana fadin asibiti za ta gina musu idan ta samu yadda take so.
Duk karshen semester suke zuwa hutu gida su rika zuwa aikin sun. Baffah na daya daga cikin likitocin zuciya da suke tashe, Salman kam idan dai maganar magani ce to Allah Ya ba shi wannan. Zai yi wahala ya rubuta maganin wata cuta ba ka ji sauki ba. Shi ya sa har private hospital renting din Shi suke yi Idan ya zo always he is busy.
Wannan abu ba karamin kyau yake yi min ba, yara da kananun shekeru kowa yana da abun yi. Ga hankali kamar ya zuba. Kullum ina addu’ar Allah Ya sa in ga su Affan haka. Duk da su ma sun dakko hanya. Amma dai yaran Zahra na burgeni sosai. Koman su cikin tsari da nasara.
Kamar wasa soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Maama da Salman, yanzu kam kowa ya san wannan, lokaci kawai mu ke jira, mu sha biki.
Adnan din Rahma kuma Ramla ce ta shi, duk da ni dai hankalina bai kwanta ba, ba na jin zan iya bayar da ƴan India, tun da a can yake aiki, ko su Rahma sun dawo gida shi ya na can.
Su kam tasu soyayyar ba ta yi fasuwar ta su Maama, saboda su dukkansu miskilai ne, kamar basu damu da juna ba. Ko maganar Adnan ake yi Ramla ba ta sanya baki, kamar ba ta san komai a kanshi ba. Shi ya sa ma ni har yanzu ban yarda akwai soyayyar ba, duk da Rahma kan jaddada soyayyar wani lokaci.
Dukkanmu muna rayuwa cike da farin ciki daidai gwargwado.
Kamar yau ma zaune nake gefen gado, ina sauraron vn din da yaron shagona ya turo min a kan wasu, kaya Zahra ta shigo.
Pause na danna Ina kallon ta, saboda yadda na ganta a fusace.
“Auntynmu wlh ina jin kunyar ku, na gaji da daga muku kafa, Allah zan yi wa yaron ki rashin mutunci”
Tun da ta yi maganar na san da Salman take, don haka cikin dariya na ce “Me mu ka yi?”
Da alamar bacin rai a muryarta ta ce,” kin ga yau ma ya je ya kara dauke Maama a makaranta, na je daukarta kawayenta suka ce Yayanta ya zo sun tafi, na kira wayarta a kashe, shi kuma na kira shi ya ki dagawa”
“Subhnallah!” na fada da alamun murmushi a muryarta.
Cike da takaici ta ce “Ban fada mishi ya daina bin yarinyar nan school ba, shi ya yi karatunshi lafiya ita yana son hana ta, kina gani fa ko a gida haka yake hana ta sakewa, in yi magana ya ce min karatu yake kiya mata, kuma Allah karya yake yi”
Yadda take maganar bilhakki ya sa na yi dariya ina fadin “Yanzu me ye laifi a ciki fisabilillahi Barrister, ya dakko ta daga school ya koya mata karatu, me ye laifin?”
Baki bude ta ce “Haka za ki ce? Ke kanki fa kin san Salman ba karatu yake koyawa Maama ba. Yana dai hana ta karatu kawai, kuma Allah zan ci ubanai”
“Yo ga wacce za ki ci ubantan nan yar ki, ita ta ba shi fuska ai” na yi saurin tarar ta
Ita din ma ta tare ni da fadin ” Auntynmu haka ne abun? Wlh zan dauke Maama daga Nigeria in kai ta waje ta yi karatunta, kuma cikin satin nan zan siya mata mota, na ga dalilin da zai kara kai shi makarantar…”
Shigowar Bashir ya sa mu ka mayar da hankalinmu kanshi, ya rika bin mu da kallo daya bayan daya, kafin ya ce” Anything? “
Zahra ce ta fara cewa” Salman yana hana min yarinya karatu Honorable, kullum sai ya je school ya dauke ta. A gida ma haka yake hana ta karatu”
Kafin Bashir ya ce wani abu na yi saurin cewa “Ya kike magana haka Barrister, kika ce wai kullum sai ya je ya dauke ta. (na juya kan Bashir tare da fadin) ba fa haka abun yake ba, Sai an tashi yake zuwa ya dauke ta.”
Still kafin ya kara magana Zahra ta ce “Ni dai to ba na so, ya bar ta ta yi karatunta, idan ba haka ba zan canja mata makaranta. Shi ba ya yi karatunshi ba, ga shi yana cin gajiyar abun ita sai ya hana ta”
“Sau nawa Maaman ta taba faduwa jarabawa dalilin Salman?” na yi tambayar ina kallon ta. Ban jira amsar ta ba na ce “Ita ta san yana guiding nata ai, ki tambaye ta ki ji”
Bashir da yake kallon mu ya ce “Please don Allah Ya ishe ni haka. Issue a kan Salman da Maaman nan ya fara yi min yawa. Yau ya kawo kara tana kula wani, jibi ki kawo karar tana mishi rashin kunya. Citta ke kuma ki kawo karar ai yana takura mata. Kullum cases nasu daban. Zahra (ya kira sunan ta hade da kallon ta) za mu kawo kudin auran Maama, a cikin satin nan, mu tsayar da ranar biki, kowa ma ya huta”
Ni ce na yi zaram da fadin “Wane irin biki kuma, yaushe Salman din ya shirya, ko fa gininshi bai kammala ba, ga karatu yana yi”
“Duk bai san da wannan din ba da, Sai ya yi kokari ya gama duka” shiru na yi Zahra ce ta ce “Wane irin aure wai? Yarinyar da a gida na ya hana ta karatu bare kum tana gidan shi”
Bashir ya ce “Shi kenan sai ta yi zaman aure, ta kama sana’a, dole sai ta yi karatun” daga haka ya fice.
Muka kalli juna da Zahra, cike da damuwa ta ce “Ba zai yiwu ba” ta yi saurin bin bayan Bashir. Ni ma sai na bi bayan ta.
A kofa suka yi kicibis da Salman, zai shigo ita kuma za ta fita
Don haka caraf ta rike kunnen shi
Maama kuma ta koma baya a guje. Na yi saurin sakkowa daga stairs din daidai tana cewa “Me na fada ma ka? Ban ce ka daina bin yarinyar nan makaranta ba? Wato ka rantse dai sai ka lalata mata karatu ko”
A shagwaɓe ya ce “Ni fa ban yi mata komai ba, kawai na zo school din ne, na yi musu wata lecture, kuma da aka tashi sai na wuce da ita”
“Ka kai ta ina?” ta yi saurin tambaya
“Asibiti na koma na dakko sauran kayana mu ka taho” ya amsa tambayar yana kallo na.
Har zuwa lokacin kuma ba ta sakar mishi ba, ta ce “Ina ruwan ka to da ita, tun da ka yi abin da ya kai ka, ka taho mana…”
Wurin na karaso, ina fadin “Yau na ji ikon Allah, wannan shi ne haƙilo fada ba gaskiya. Don Allah ki sake shi. Ki fadawa yarinyarki ta daina bin shi mana idan ya zo”
“Abu da zare mata ido yake yi sai ta bi shin”
Sosai maganarta ta ban dariya, shi ya sa na dara kadan ina fadin “To sakar shi dai”
Ɗiɗɗirka mishi dunduna ta shiga yi tana fadin “Idan ka kara zuwa makarantarsu, Sai na ba ka mamaki, ka yi karatunka lafiya kana son hana wata”
kwacewa ya shiga kicinyar yi, hade da kiran sunana. Na janye shi daga hannunta ina dariya, ta fice tare da fadin “Za ka sani ne”
Cikin falon ya shigo sosai yana dariya, ni ma dariyar nake yi, kafin na ce “Ba ka da zuciya Salman, kullum idan ka zo maganar kenan, kai kuma ka ki dai na shiga sabgar yarinyar nan”
Fuska ya narke zuwa shagwaɓa kafin ya ce “Ta ya kenan Auntynmu zan daina shiga harkar Maama?”
Na yi saurin cewa “To shi kenan na ji, ai ga shi nan yau dai Abbanku ya ce ya gaji, nan da sati daya za a kai kudin auranka” na kauda wancan zancen, don na san yanzu zai fara lissafo min irin yadda yake son Maama ko kunya ba ya ji
Da sauri ya ce “Kudin aurena kuma? Da wa?”
“Wa kake so?”
Ido waje ya ce “You mean Maama?”
Kai na daga alamar eh, with shock ya ce “Auntynmu da gaske, haka Abbanmu ya ce?”
“Na taba yi ma irin wannan wasan, ya ce cases din ku ya ishe shi kullum”
Cike da jin dadi ya ce “Wayyyo Allahna Auntynmu, labari mai dadi, oh my good God, Allah Ya ƙarawa Abbanmu lafiya da nisan kwana.”
Hannuna a kan haba na ce “Salman! Oh kana murna, har auran fa cewa ya yi bai zai wuce karshen semestern nan ba, shi ne kake murna”
Maimakon in ga ya yi la’asar kamar yadda na yi zato, Sai na ga farin cikinshi sun ninninka na baya.
Baki bude alamun mamaki nake kallon shi, kafin na rufe bakin da fadin “Dama Barrister tana ce min ba ka da hankali ina kin yarda, yau kam na yarda, wato kai ba ka tuna hidimar da ke gaban ka ko, ba ka gama gini ba, ga makaranta kana yi, sannan ga maganar aure ta taso, shi ne ko a jikinka”
Wata irin dariya ya yi mai nuna yana cikin farin ciki ya ce “Akwai ki, akwai Abbanmu ai, ke fa the big ƴar kasuwa ce Auntynmu. Don Allah kar ki kashe min jiki, ki hana ni farin ciki a wannan ranar da na dade ina jiran zuwanta.”
Baki na tabe, sannan na ce “Ga abinci can idan ka gama ɗokin”
“Bari in je wurin Momy Auntynmu kar ta ce za ta bugi first lady”
Ina haurawa sama na ce “Kai ma ka san ba za ta buge ka ba, da dai kai ne kam, da ta buga son ranta, amma waccan ai yar gold ce, Sai dai shafa”
Dariya ya yi yana kokarin fita lokaci daya kuma yana fadin “Let me go and gist them, especially Adnan, na yi gaba sai ya taho”
Kai na girgiza, kamar ba zan ce komai ba, Sai kuma na fadi abin da ke ci na “Salman ba ka da kunya wlh, wai wannan murnar don duk za ka yi aure ne, ikon Allah!” na kai karshen maganar hannuna a kan haba, alamun mamaki.
Cikin dariya ya fice daga falon, ni din ma sai na ci gaba da haurawa sama, zuciyata fari ƙal, hada zuriya da Zahra abun alfahari ne, sannan mace ta samu miji kamar Salman abun tinkahonta ne. Yaro ɗanye sharaf, ga kuruciya ga naira, ga ilmi ga kyawu, faran-faran da kowa. Maama ta dace miji, Sai dai in yi mata addu’ar Allah Ya raba ta da kishiya irin Sarai, kai Sarai ƴar bala’i ce, da ace na biye mata kullum sai mun daku.