Tun daga lokacin da Bashir ya yi magana a kan Maama da Salman bai sake ba. Hankalinshi kaf a kan zabe ne, daga shi har jarumar matar tashi. Kuma hankalinsu bai dawo jikinsu ba, sai da aka yi zabe, dakyar Bashir ya samu kujerarshi, a haka ma sai da aka je court. A court din ma Zahra ce ta yi ruwa ta yi tsaki, mu dai namu addu’a.
Ana cikin wannan rundunbar su Khaleel da Affan da kuma yaran Rahma su Adnan suka zo hutu, dama kuma sun saba, duk karshen shekara suke zo mana hutu.
Hankalinmu dai bai kwanta ba, Sai da kotu ta tabbatar wa da Bashir kujerarshi sannan, hankalin kowa ya koma jikinshi, mu ka shiga harkokinmu kamar kullum.
Misalin karfe shida na yamma Bashir ya shigo falona, wanda samarin gidan ke zaune su shadaya reras suna kallon ball, ni kuma ina dining ni da Maman Usi muna shirya abincin dare.
Daga inda nake na yi mishi sannu da zuwa, yaran ma suka shiga gaishe shi, yana amsawa cike da kulawa, kafin ya ce “Adnan, da kai da Khaleel, da kuma Baffa, za ku yi min rakiya gobe idan Allah Ya kai mu”
Duk suka amsa da to, cike da girmamawa, Salman ya ce “Ni fa Abba?”
“Ban da kai” ya amsa shi yana kokarin hawa stairs. Sai da ya je tsakiya ya juya yana kallon su, lokaci daya kuma ya daga murya alamun kashedi ya ce “Kar wanda ya sanya min kananun kaya.”
Bayan ya haye saman ne Farhan ya ce “To da Baffa ake, kai ne ba ka sanya manya kaya”
“Zan ari na Affan” cewar Baffa yana kallon Affan
“Ba zan bayar ba, ai kana da shaddoji, ka kai dinkinsu yanzu a yi ma express”
Yusuf ya ce “Akwai kaya na fita kunya a wurina, amma renting za ka yi, sannan akwai sharuda da ka’idoji”
Faruk ya cafke da “Ni ma ina da su, kuma zan yi ma sauki malam, kwasha-kwasha a buga a kwashe.”
“Ka dai ji kunya wlh, ace ba ka da kayan fita, unguwa” cewar Adnan cikin manyance, don shi boss ne
Baffa ya ce “Ya da haka Boss (sometimes Haka suke kiran shi) ina fa da kaya kai ka sani. Wandona daya zai iya sayen shadda masu tsada kala biyar”
Karin farko da na sanya baki a hirar tasu da fadin “kuma duk a banza, tun da ba za su biya ma wata bukatar ba”
Kamar zai yi kuka ya ce “Haba Auntynmu don Allah ki yi shiru mana”
“Na ƙi in yi shirun, Sai a ki fadin gaskiya, ace kullum kana yawo da ƴan bigilallun kaya, to ka rufawa kanka asiri ka dinka manyan kaya saboda shiga taro ko gidan surukai. Yanzu idan za ka je gidan surukanka sai ka tafi da wadannan kayan?”
“To su waye surukan nawa Auntynmu idan ba ke ba”
Duk falon suka yi dariya har da ni, sannan na ce “Ka yi wa Husaina tsufa ai a lokacin, ba zan yarda ta auri dan 40 years ba”
Ya juya kan Husaina da hankalinta kaf yake a kan cartoons ya ce “Wai haka 2nd lady”
Hassan ya ce “eh” duk suka yi dariya idan ban da Baffa da ya ce “Kai rufewa mutane baki, ba kai a ka tambaya ba”
Na ce “Ai da gaskiyarshi.”
Daga haka na haura sama, na ba bar su suna dragging din su.
Washegari misalin karfe 11am masu rakiyar Bashir suka shigo cikin shiri, ma Sha Allah duk sun yi kyau, na kalli Baffa da ya sanya kayan Yusuf na ce “Sosai kayan nan sun yi ma kyau Baffa kamar naka”
“Yanzu Auntynmu idan akwai mutane haka za ki yarfa ni?”
“To sai in ki fadin gaskiya, daga nan ba sai ka yi zuciya ka yi naka ba”
“Zan yi in Sha Allah, ina dawowa zan bayar da dinkunana a yi min. Ni ma na ga na yi kyau” ya kai karshen maganar yana baza babbar rigar
Adnan ya ce “Ni ban yi kyau ba kenan Auntynmu, Baffa kadai kika yaba”
Dariya na yi kafin na ce “Au wai kai ma kana so? Ban yi tunanin kana so ba”
Fuska ya shagwaɓe, sauran kuma suna yi mishi dariya. Daidai lokacin Zahra ta shigo, Adnan ta kalla kafin ta ce “Boss ya fuskarka Haka, bayan ka yi kyau kamar ango”
Baki ya washe sannan ya ce “Ina yin ki Momynmu, Auntynmu ta yaba kwalliyar kowa amma ba ta yabi tawa ba”
Cikin dariya Zahra ta ce “Ka yi kyau sosai, kamar ango”
Salman ya ce “Momy ki daina cewa kamar Angon nan, shi fa akwai sauran hawa”
Baki ta tabe sannan ta ce “Yi min shiru, mara kunya ai kai matarka na gida ka baro”
Ya yi dariya mai sauti kafin ya ce “Soon in Sha Allah”
Baki Zahra ta rike alamar mamaki, kafin ta juyo tana kallo na ta ce “Salman ba shi da kunya, in yi magana ki ce ba haka ba(sai kuma ta juya kan Baffa ta ce) kai kuma Ina ka samu kaya, suka amshe ka haka kamar naka?”
Ya gimtse dariyar da yake yana fadin “Momy!”
Ta ce “Ai na san ba naka ba ne”
Yusuf ya yi caraf da fadin “Na Oga Yusuf ne”
Baffa ya aika mishi da harara. Yusuf ya kuma cewa “Yasin za ka cire su yanzun nan, ba sai ka matsa daga nan ba.”
Daidai lokacin Bashir ya sakko cikin shigar farar shaddar da ta karbi jikinshi, hade da fito da kamalarshi. Bayan shi kuma Khalil ne biye da shi, shi ma sanye da farar shadda ƙal dinkin zamani, ya dora huta da ta dace da shaddar. Sosai ya yi girma a cikin kayan, kamanninshi da mahaifinshi suka kara bayyana.
Bashir ma sai da ya tsokani Baffa sannan suka wuce. Sauran matasan ma kowa sai ya kama gaban shi, muma mu ka shiga hidimar abincin rana, saboda Bashir ya ce a yi special.
Misalin karfe biyar na yamma kaf muna zaune a falona har da Zahra, wani Korean film muke kallo, hankalinmu na kanshi, duk da ni wani lokacin na kan tuna su Khaleel da suka fita tun safe, har yamma basu dawo in ji, kamar in kira sai kuma dai in daure, amma zuciyata da matsa min da son sanin ina suka je haka.
Daidai lokacin kuma na ji karar shigowar motar Abban Khalil shi da escorts din shi, Sai a lokacin ne hankalina ya kwanta.
Baffa ne ya fara shigowa bakin nan a washe, tun da na ga haka a zuciyata na ce “Akwai labari mai dadi kenan.”
Duk muka zuba mishi ido muna kallon yadda bakinshi ya ki rufuwa. Faruk ya ce “Fesa mana mutumina, kar dadi ya kashe ka”
Ya juyar da kallon shi kan Faruk sannan ya juyo kaina ya ce “Auntynmu, wlh mun girma”
“Ko?” na yi tambayar hade da dariyar yadda ya kasa rufe baki
Ya ce “Wlh, aure fa mu ka je nema, Ya Adnan ya mika kudin aure, kuma aka ce an bamu”
Tsakanin ni da Zarah ban san wa ya riga kallon wani ba, gabana ya shiga faduwa dam-dam, kar dai kuma wata macen Bashir zai sargafo mana, shi ya sa ya ki fada mana inda zai je, ya kwashi yara suka tafi.
Na mayar da kallona kan Maama da Ramla da kuma Affan wadanda na karanci fargabar da suke ciki a kan fuskarsu.
Daidai lokacin Khalil da Adnan suka shigo, suka dauki abincin mutanen da suke waje tare da Bashir
Yusuf ne ya yi karfin halin tambayar”Kudin auran wa?”
Cikin wani zallar farin cikin ya ce” love bird din gidan nan mana, kuma wlh an bamu “
Gabadaya kowa a falon ya kalli Salman saboda sune dai love bird a gidan, wanda reaction din shi ke nuna matukar kaduwa da jin maganar. Faruk ya ce” Da gaske wai ko wasa? “
” Na rantse muku da girman Allah da gaske nake yi, daga fa Ruma muke”
Affan ya ce “” “To da wa?”
“Ya ce yo su waye love bird din, akwai wasu ne? “
Yanzu kam gabadayanmu Maama muke kallo, wacce ta saki baki ita ma cikin rashin fahimta. Na yi karfin halin cewa “Baffa keep joke aside please, menene gaskiya?”
Kafin ya yi magana Khalil ya shigo, don haka ya ce “Khalil don Allah ba kudin aure mu ka kai ba, kuma an bamu”
Khaleel ma ya washe baki hade da cire hular kanshi ya ce “Auntynmu ashe haka ake kai kudin aure? (ya kuma washe baki sannan ya ce) yasin ji na nake duk na zama wani babba, kai yau Abbanmu ya girmamamu wlh, ji na nake kamar na girmi duniya”
Duk mu ka yi dariya har da shi sannan ya ce “Da gaske kudin aure mu ka kai Ruma, na Ya Salman da Maama, kuma Baba Rufa’i da Alhajin Runka suka karbi kudin, suka ce sun bayar. Kai yau na ga yadda ake hada aure” ya kuma rufe maganar cikin wani sabon farin cikin.
“Kar ku sanya ni in yi guda ƴaƴan nan don Allah” na fada cike da zallar farin ciki
Baffa ya ce “Wlh idan ma ƴan hayar gudar za ki dakko Auntynmu ki dakko, wannan zance daga nan har birnin Sin haka yake”
Na juya kan Salman wanda har zuwa lokacin yake cikin shock, Maama kam tuni ta gudu. Barrister cikin shock din take saboda tun da aka fara maganar komai ba ta ce ba, Sai ma ido da take ta bin kowa da shi. Karshe tashi ta yi hade da ficewa daga falon, ta bar mu nan muna ta hayaniyarmu cikin farin ciki, Salman ma jiki ba kwari ya fita, abun da ban yi tsammani ba, na dauka har rawa zai yi, amma sai ga shi duk ya yi la’asar, amma kam Baffa ai har da rawa, wai sun girma an je neman aure da su.
Gidan dai ranar har dare maganar kenan, Sai tsara yadda za su yi hidimar biki suke yi, kamar an ce gobe ne daurin auran.
Da dare Bashir ya shigo min sai da safe, a lokacin ne na ce “Sai na ji abu kwatsam”
“Wane kwatsam kuma, ba na fada maku ba tun kwana ki”
Murya na kwantar sannan na ce “Ai da na ga an dade da yin batun, na dauka maganar ta wuce”
Kai ya girgiza kafin ya ce “Ba ta wuce ba, zaben nan ne ya sa na ajiye ta gefe. Da Ramla ma ta isa auren da na hada da ita na sallame su na huta.”
A tausashe na ce “Amma Salman bai shirya ba fa, ko gini bai gama ba, ga kuma school”
Har na fitar da rai zai ce wani abu sai kuma ya ce “Khadija I planned everything Tun kafin in yanke hukunci, just watch.”
Hannayena biyu na daga sama tare da fadin “Allah Ya taimaki Honorable”
Murmusawa ya yi kadan kafin ya mike yana fadin “Bari in wurin Barrister, na tabbata tana can ta cika, kila ma ta fashe.”
Dariya na yi, saboda na san maganar da ya fada gaskiya ne, Barrister ba ta so a yi auran nan yanzu ba. Na san burinta a kan Maama, yanzu kam tana can kamar za ta yi a man wuta.
Har falo na rako shi, ina kokarin rufe kofa Salman ya fito daga dakinsu, kuma na san wurina zai zo, don haka na dakata har ya karaso, muka juya falon tare.
Bayan ya zauna ne na ce “Ka ci abinci kuwa? Ni kamar ban ganka a wurin cin abinci ba dazu”
Yana gyara zaman shi a kan kujerar ya ce “Na je hospital ne, Sai kuma na biya wani restaurant na ci abinci”
Kafin in yi magana ya ce “Auntynmu Momy ta kira ni, tana ta fada wai na yi sanadiyyar yanke karatun Maama, wai ta san ni na matsawa Abbanmu a kan lallai a yi bikin nan, tun da ya manta. Don Allah na sake yin maganar nan tun bayan da mu ka yi ta da ke?”
Murmushi na yi, a zuciyata kuma Ina tuna daman na tabbata kaf haushinta a kan Salman za ta dora shi, kuma ba zai fita ba a wurinta ba. Ya katse min tunanin da fadin” Ta ce wai lallai sai in fadawa Abbanmu sai Maama ta gama school za a yi bikin, idan ba haka ba komai ba ta yi min”
Kujerar da ke fuskantarshi na zauna, cikin sigar kwantar da hankali na ce “Fita batunta Salman, kar wannan ya tayar maka da hankali, can za su gama ita da mijinta, kar ka sake ka cewa Abbanku komai. Kuma kar ka tayar da hankalinka a kan hidimar biki, Sha Allah za a yi komai lafiya a gama lafiya. Don haka ka kwantar da hankalinka”
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, ba tare da ya ce komai ba. Wannan ya sa na ci gaba da kwantar mishi da hankali, har dai ya dan samu nutsuwa, sannan ya tafi, ni kuma na haura sama. Zuciyata fal farin ciki, don ni kam yau farin ciki nake yi sosai. Duk da wani lokacin ina jin ba dadi, ban san irin rayuwar da Maama za ta yi a gidan nata auran ba. Amma zan yi mata addu’a Allah ya shiga lamarinta, ya ba ta ikon daukar ko wacce irin jarabawa.
****