A ranar kuma Rahma ta diro ita da ta tawagarta, da ragowar akwatunan lefen guda shidda, wanda samarin ne suka hada kudi su ka yi, a matsayin gudunmuwarsu. Komai a akwatin babu na banza, haka mu ka gani hade da sanya albarka.
Masu hoto kam basu dawo ba, Sai yamma, zuwa lokacin Zahra ta yi fada har ta gaji, wai abu tun safe, da ta san haka za su ji ma wlh ba za su je ba, kawai a tsaya a yi hoto shi ne aka dade haka, ko zana su za a yi, with different style Ai ya kamata zuwa lokacin an gama. Shi ya sa da suka dawo Salman ya ki shigowa, Sai Maama ce ta shigo, aiko ta wanke hannu a kanta, tai ta fada, Rahma na bayar da hak’uri, ni dai bakina shiru, Salman ya kira ni, wai in duba WhatsApp ya tura min hotunan in gani kafin a saki din.
Hotunan na rika kallo cike da burgewa gami da tsafta, babu inda Salman ya rike hannun Maama kamar yadda babu inda ita ma ta taba jikinshi, kuma ba ta shigar banza ba. Ba ƙaramin kyau hotunan suka yi ba, ina kallon Maama kamar ba ni ce na haife ta ba, wai wannan budurwar ni ma tawa ce, “ikon Allah” na fada a bayyane, lokaci daya kuma Ina mikawa Rahma wayar, ta shiga yaba hotunan, tana fadin “Allah Ya nuna min na Ramla da Adnan ni ma, wlh ji nake ina ma haɗawa aka yi”
Dariya na yi ba tare da na ce komai ba, ita kuma ta mikawa Zahra wayar, Sai da ta gama shan kamshinta ta ce “Sun yi kyau, Allah Ya sanya alkairi” ni da Rahma mu ka amsa hade da dariyarta.
Cikin awa daya da approving hotunan sai ga shi sun fara zagaye kafafen sada zumunta, duk wani babban flat form sun dora, yan comment kowa na fadar albarkacin bakinshi.
Ana saura kwana biyar daurin aure su Rahma suk kai lefe Ruma wurin Inna, a kuma can suka baro lefen, Sai ranar Laraba su Yaya Habi suka taho da shi. Zuwa lokacin kam hidimar biki ta kankama, musamman anguna, saboda program masu yawa suka shirya, Zahra dai kullum warning ban da rashin kunya, tun tana sakayawa har ta fito fili ta ce “Wlh Salman na ga rungume-rungume rashin ɗa’ar nan sai ranka ya baci” shi dai komai bai ce ba, ya fice cikin kunya, ni da su Yaya Habi mu ka yi ta dariyar yadda ta gaji da zagaye-zagaye, ta fito fili.
Ƴan’uwana tun ranar Laraba wasu suka fara zuwa, wasu Alhamis wasu kuma juma’a, haka bangaren Bashir ma, har Inna sai da ta zo. Gida fa ya yi cikar kwari, musamman ranar daurin aure, don ma a Ruma aka dauro auran, amma hall din da ke cikin gidan a nan suka yi reception din su.
Su Maman Aiman iyayen bidi’a, Sai da suka dakko mai asharalle, aiko fa aka girgije hade da yin nishadi
Muna tsaka da rawa aka zo kirana, wai za a kai Maama gidan miji. Sai na ji abun wani banbarakwai, na ce “To me zan yi mata?”
Yaya Habi ta ce “Yau ga sakarcin banza, ba za ki ce mata komai ba”
Cikin dariya na ce “Wlh ban san abin da zan ce mata ba. Na san uwarta ma ta yi mata fada, ni dai ba sai na je ba”.
Ba tare da ta saurare ni ba, ta ja hannuna har zuwa part din Zahra.
Baki bude nake kallon su, Zahra zaune saman gado, Maama ta dora kanta saman cinyoyinta tana kuka.
Haɓa na rike kafin na ce “Haka ake fadan?”
Yusra da ke zaune jiki a sanyaye ta ce “Kowa ya yi na shi, ke ake jira”
Murmushi na yi kadan kafin na ce “To ni me zan ce? Ai duk abin da zan fada na san kun fada, Allah Ya bada sa a, Ya sa ace gara da aka yi”
Duk suka amsa da amin, suka kuma dorawa daga inda suka tsaya ni dai ina tsaye ina jin su, zuciyata tana yi min wani iri. Memoryn nawa auran ya dawo min, haka aka tasa ni ana yi min fada, kadan za a ce kin ga dai gidan kishiya za a kai ki. Sai kin yi kaza, kin bar kaza. Ajiyar zuciya na sauke ina kallon Yaya Habi da ta kama Maama, zuwa kofar fita, a hankali duk suka fice, ya rage daga ni sai Zahra da ke sharar hawaye, wurin da Yusra ta tashi na zauna kafin na ce “Wannan kuka Barrister kamar kina yin shi da biyu, aure fa aka ce Maama ta yi ba mutuwa ba, ni ban ga abun kuka har haka ba. Musamman da kullum za ki iya zuwa ki ganta ko ki ce ta zo”
Karon farko da ta yi min wani kallo mai kama da harara, wannan ya sa na dauke kai ina siririyar dariya. “Kamar gaske” ta fada lokacin da take fyace hancinta da tissue. Cikin dariya na ce “Ai na san za ki iya. Abbansu ya ce Allah Ya sa ki bar su ma su zauna auran”
Duk da fuskarta akwai damuwa, hakan bai hana ta murmusa ba, kafin ta ce “Haka yake fada min kullum, amma zan ba ku mamaki.”
“Allah Ya sa” na amsa ta ina kallon wayata da kiran Salman ke shigowa.
“Auntynmu ina jin yunwa” ya yi maganar bayan na daga kiran
“Ba lafiya, ango guda na jin yunwa, ba ka ci abinci ba ne?”
Daga can ya ce “Wlh ban samu na ci ba, hayaniyar mutane, yanzu kuma mutane sun rage sun fara tafiya wurin dinner, idan akwai abincin ni dai in zo in karba”
“Bari in dafa ma indomie dai, saboda duk abincin gidan nan ba za su yi ma dadin ci ba. Sun huce, idan an gama zan kira ka”
“To.” ya amsa min, na mayar da kiran kan layin Ramla, sosai tana cikin hayaniya, Sai da ta koma gefe na ce “Kina ina?”
“Ina waje za mu kai amarya”
“Yauwa to dawo ki dafawa Salman indomie”
Kamar za ta yi kuka ta ce “Auntynmu kai amaryar fa?”
Na hade fuska kamar tana gani na na ce “Kai amaryar wani kayan gabas ne? Waye bakon ki, amaryar ko gidan amaryar? Zo ki dafa mishi abu kin ji, daga baya kya je” Ban jira cewar ta ba, na yanke kiran.
Zahra da ke kallo na ta ce “Gaskiya ba a kyauta mata ba, shi din wane ango ne ma ke damuwa da abinci ranar auran shi. Ya je can ya samu abincin mana ya ci”
“kin fa san Salman, ba a ko ina yake cin abinci ba”
“Ai na san karya yake yi dama, ba rasa time din cin abinci ya yi ba, na bikin ne dai ba zai ci ba”
Komai ban ce mata ba na mike tsaye da zummar fita, hannun da ta rike min ne ya sa na juyo ina kallon ta. A hankali ta furta “Na gode Khadija, Allah Ya biya ki da gidan aljanna, yau ina cike da farin cikin da rabona in yi shi tun kafin Kabir ya rasu” nisawa ta yi kafin ta ci gaba “Na dauka ba zan iya ba, na dauka ba zan ga wannan ranar ba, ashe za ta zo. Na sha struggling a rayuwa, lokacin da mahaifin su Salman ya rasu duk suna kanana, ga shi ni kuma ina karatu, kuma shi ne mai daukar dawainiyar karatuna. Khadija ba sai na fada miki halin kunci, damuwar gami tashin hankalin da na shiga ba.
Ga mutuwar miji, ga nauyi ya hau kaina. Da farko dai Yayanshi kamar gaske ya dauki dawainiyar karatun yaran nan, ni kuma duk week yana ba ni 5k kudin abinci, a hankali komai ya fara canjawa, ya fara gajiya da dawainiyarmu, yara sai a koro su makaranta, wani lokaci har a yi exam basu koma ba. Ina da ƴan’uwa masu kudi, amma babu wanda zai tuna bari ya ba ka, wai sai ka bude baki ka tambaya, ga shi ni ban iya roko ba.
A haka na samu wata private school Ina zuwa, salaryna na makarantar yarana ne, karatuna kuwa deferring shekerar na yi dole. Abinci kuma watarana a koshi, watarana kuma sai a hankali. Ƴan’uwanshi na da hanyar samar min permanent aiki, amma da kyar suka samar min S power a ma’aikatar shari’a. Cikin hukuncin ubangiji ko wata biyu ban yi da fara aiki ba, aka ce mu je screening za a yi permanenting din mu. Bayan screening Ina ɗaya daga cikin wadanda suka yi nasara. To tun da na samu wannan aiki, kowa ya zare hannunshi a hidimar ya rana aka bar min kayana, ni ce komai din su. Inda Allah Ya taimake ni ma basu da yawa.
Watarana na ji kishin-kishin wasu kudi da za a ba mijina na mortgages sun fito.
Na rasa wa zan tunkara, don haka na yi ma wata matar kanen mijina maganar. Sai ta ce min wai ban sani ba dama, ai tuni suka fito, sun fi wata shida da fitowa.
Da na lissafa watanni, Sai na ga a lokacin muna cikin matsin rayuwa sosai, saboda ban fara aiki ba. Ba sai an fada min ba, na san wadannan kudin babu su. Don haka na zuba ido ina jiran Ikon Allah.
Kusan shekaru biyu da rasuwar Kabir aka kira mu screening a kan kudin fansho din shi. Bayan na je sai na ga account details din na Yayan Mijina ne mai bamu 5k din nan, wanda ya kasa ci gaba da daukar dawainiyar karatunsu Salman, kuma wadancan kudin ma da aka cinye ta hannunshi suka biyo. Aiko sai na bi wasu hanyoyin aka canja account details din zuwa nawa. Na dawo gida na yi shiru abuna.
Bayan sati sai ga kudi sun fado, na kira yara na nuna masu, duk da lokacin basu da hankali sosai, amma sun yi wayon da za su fahimci kudin da kuma yawansu, saboda time din suna jss 2.
Na shirya na tafi gidan mahaifiyarshi, time din ba ta rasu ba, na fada mata kudi sun shigo, kuma ga adadinsu. Ta ce to, ta kira yayan mijina ta fada mishi, da shi ke baya gari Abuja yake aiki.
Ina jin yadda yake ta fada, wai ya aka yi kudin suka shigo account dina, to a fada min kar in sake in taba su, a jira shi ya zo da weekend, zai karbe su a jujjuyawa wa su Baffa su.
A zuciyata na ce, lallai kam, idan ba sunana Zahra ba ko?
Ai ina barin gidan na tafi gidan wani babban Malami, na fada mishi matsalata, na kuma nuna mishi yawan kudin, na ce don haka ya raba min su gado, duk mai hakki a fitar mishi da hakkin shi.
Bayan ya kasafta min, na bayar da cigiyar gida a nan cikin Kaduna, na siyawa Baffa. Gidan da muke ciki kuma ya zama kason Salman . Na biya musu kudin school fees har su gama. Na siya mana kayan abinci. Na bude masu shago na zuba musu provision da manyan fridges na kara batteryn solar, yadda zai iya daukar fridges din.
Wadannan abubuwan fa, sun faru ne cikin kwanaki uku, kafin Yayan Mijina ya baro Abuja ya zo.
Bayan na kammala duk wani abu da nake ganin shi ne goben yarana, na zauna kuma jiran abin da zan fuskanta.
Ranar Asabar kuwa misalin goma na safe sai ga kiran waya, wai in kawo kudi gidan Goggo (surukata) na ce to
Yara duk jikinsu ya yi sanyi, wai idan na je to me zan ce. Na ce kar su damu.
Bayan na je aka gama gaishe-gaishe, Goggo wai in kawo kudi, na ce ni fa kudi tun a can na ce a samu malami ya fitarwa kowa na shi, na zaro takardar rabon da ke cikin jakata, na ce ga takardar nan, an raba komai.
Wai to in kawo kason su Salman a jujjuya masu. Na ce na riga na siya musu gida, na shiga lissafo masu abin da na yi.
Aiko su ka hau bala’i, lallai aje a siyar da gida in kawo kudin, ni kuma na ce ba zan siyar ba. Haka aka tashi baram-baram, suka rika kai karata wurin ƴan’uwana, duk wanda na ba labarin abin da ya faru sai ya ce na fi su gaskiya. Ke abu kamar wasa sai gamu a court. Wai an raba gadon yara na lalata na yara.
A lokacin karatun lawyer ya yi min rana, mu ka rufa shari’a, har da kudin mortgage na zakulo, aiko alkali ya ce basu da gaskiya, sannan ya ce a dawo da kudin mortgage a bamu kasonmu ni da yara. Ke wannan baram-baram din da aka yi ya sa kaf dangin uba na Salman, suka zare hannunsu a kan su. Wa kika ga ya kawo mana gundumuwa daga dangin Babanshi? “ta yi tambayar tana kallo na.
Shiru na yi ban ce komai ba, wannan ya sa ta dora” Tun daga lokacin nake fafutukar gina yarana, komai na nufa sai ki ga na yi achieving Allah kuma ya sanya albarka a ciki, na kara samun aiki da NGOs, na shiga kungiyoyi lauyoyi masu zaman kansu, ke haka nai ta kutsa kai, ina kara samun damar yin karatu, har Allah Ya kawo mu yau din nan.