Skip to content
Part 6 of 8 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Umma ta ɗan murmusa kadan, murmushi dana kasa gane dalilishi

Kafin ta ce “Ki yi duk yadda za ki iya ki zama kamar ita, sannan ki yi hakuri, ba da gaggawa ake taka matsayi mai girma ba, kafin ta zama haka sai da ta kwashe tsawon shekaru, kin ga kuwa ke da kike da kika zo jiya, ba ki isa ki zama kamar ita ba. Ki bi komai a hankali “

” Kin ga Umma hatta danginshi sai abin da ta ce, wurin bikin nan duk shawara da ita ake yi”

Ta kalle ni da alamun damuwa kafin ta ce “Duk wannan kar ya dame ki, a hankali za ki iya zuwa matakin da take, kila ma ki wuce ta. Abin da kike bukata kawai shi ne kyautatawa, girmama na gaba da ke. Sannan girmama kowa. Da tsayawa matsayinki, ba ruwanki da yawan tsegumi ko gulma. Babu girman kai, Sai girmama kai. “

Shiru na yi hade da nazarin maganganun Ummana, tabbas wadannan sune abubuwan da Maman Khalil ta rike, babu dadi babu kari. Saboda kowa bai raina ta ba, kuma ba ta raina kowa ba.

Haka muka rika tattaunawa, har bacci ya dauke ni.

Cikin bacci na rika jin hayaniya da karar taɓa abubuwa.

A hankali na bude idona, wanda bacci bai isa ba, kasancewar jiya bacci bai dauke ni ba sai wajen uku saura na dare.

Saboda hirar da mu ka rika yi da Umma. Ko bayan hakan ma na dade ina nazarin duk wasu maganganu da ta fada min

Duk abin da Hasashena ya ba ni, sabanin haka na taras, yayin da Umma ta kara tabbatar min da cewa Hasashen nawa gaibu ne, ba lallai abin da na Hasaso ya kasance gaskiya ba, kamar yanzu ma.

Ni abin da na dauka shi ne, a matsayina amarya, to zai kasance hankalin mijina yana kaina, zai tarairayeni, zai ji da ni, kamar dai yadda na sha fada tun farko.

Amma me ya sa ban samu wannan ba?

Kodai ni ce ban iya tarairayar miji ba?

“Wannan ba gaskiya ba ne.” na ba kaina amsa, hade da yunkurawa na tashi zaune a kan katifar.

“Me ye bana mishi? Ina mishi komai, bana barin kazanta ko datti a ko ina.

Ina kiyaye ganinshi da jin shi. Girki ma na dage sosai nake kokari, duk da dai ni kaina na san ban kamo kafar Maman Khalil ba a nan bangaren”

Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, a bayyane na fadi

“Mata ce kamar mayya, komai ta iya, ni ban taba ganin mace irinta ba”

Jin almar za a shigo dakin ne ya sa na yi saurin yunkurawa na daga net din ina kokarin fita.

Maryam ce kanwata

“Aunty ashe ma kin tashi, dama Ummanmu  ce wai in zo in tashe ki”

“Na tashi” na ba ta amsa, lokaci daya kuma muka fita tare

Bayan na idar da sallah, daukar tsintsiya na yi, na, share gidan fes, sannan na shiga kitchen inda Umma ke saka danwake

“Tsawon wata uku kenan ban ci danwake ba Umma ba” Na fada hade da janyo karamar kujera na zauna gefenta, tare da fara saka danwaken a cikin tukunya.

“To me ya sa, ba kwa yi ne?”

“Ni dai ban taba yi ba, ban sani ba ko Maman Khalil ta na yi”

“Oh kowa girkinsa yake yi”

Kai na jijjiga alamar Eh.

“Kina ji na?” Umma ta yi maganar hade da dakatawa daga saka danwaken alamar maganar na da muhimmanci.

“Allah ya hada ki da kishiya mai wayo, wacce ta san kanta”

Na yi saurin kallonta alamun ina neman karin bayani.

“Magana ta gaskiya,  shi ne akwai aiki a gabanki, kafin ki taka matsayin da kishiyarki take kai yanzu.”

Ta dan tsagaita, yayin da ni kuma nake bubbuga kumfar danwaken da ta taso.

“Natsuwa za ki yi, ki gano  a ina gazawarta take, sannan ban da kwaikwayo, ya zama ke ma kin zo da naki sabon salon  da zai zama bako a gurin mijinki. Wannan shi ne kawai”

“Me kike nufi da haka?” Na yi tambayar a lokacin da nake tsame danwaken

“To me kuma kike son in fada miki, komai sai an yi miki dalla-dalla ne?”

“Haka ya kamata a rika yi, musamman a kan macen da za a kai gidan kishiya.”

Na yi maganar a zuciyata, a zahiri kuma murmushi na yi, ina yaba alkunya irin ta iyayenmu, wato komai sai su bamu shi a dunkule, yayin da muka warware za mu samu abubuwa da yawa masu muhimmanci. Duk da wani lokaci mu kan warware abun ba daidai ba, ya fi ace an warware mana shi ta yadda za mu fahimta.

Ni na raba danwaken na sanyawa kowa, ni ma na ja na wa, ci nake amma kuma bitar maganar Umma nake yi.

Zuwa karfe takwas gidan shiru sai ni, kanwata Maryam da take zana min lalle, Sai kuma Umma da ke ta faman hada min tsaraba.

Hira muke da Maryam a hankali wacce da yawan hirar a kan kannenmu ne, Sai kuma Yusrah, daya kanwar tawa da take aure a Kaduna.

Ita kam ta jima da aure, saboda ta ma riga ni auran, tun mahaifinmu na da rai aka yi mata aure, ni kuma sai da na kammala NCE.

Zuwa karfe biyu, na fita shar da ni, kamar yau ne za a kai ni gidan miji, kunshina ya yi kyau, haka ma kitson da Umma ta yi min zanen kwance, ya fito da fuskata fayau.

Doguwar riga mai ruwan madara na saka, na zagaye fuskata da dankwalin rigar ina jiran zuwan Abbansu Khalil

Ba jimawa kuwa ya iso, bayan sun gaisa da Umma  ya yi mata ihsani, mu ka yi sallama, sai Airport.

Karon farko da na fara shiga jirgi a rayuwata, amma kuma ba na ɗoki, murna ko farin ciki. Hasali ma raina a bace yake, komai baya min dadi, ji nake kamar in ce a tsaya in sauka.

Shi kanshi na ga ya fahimci hakan, duk da komai bai ce ba, idan ka dauke hannuna da yake cikin na shi yana murzawa a hankali.

Duk bacin ran nawa, na san baya rasa nasaba da yadda nake tunanin yau Maman Khalil za ta amshe min miji, na san yau za ta fanshe duk wasu kwanaki da ya yi a wajena.

Gaskiyar Ummanmu ne, Maman Khalil mace ce mai matukar wayo, iya mu’amala da zaunawa a rai.

Ta san yadda ake tafiyar da miji, da yi mishi abin da zai tsaya mishi a kwakwalwa da zuciyarshi.

Sosai nake tausayin kaina, idan na tuna irin kalubalen da ke gabana.

“Tea or coffee?” Ma’aikaciyar jirgin ta yi min magana cikin wani irin turanci da take yi ma Tajweedi

Shiru na yi, na kasa gane me ta fada a kalmarta ta biyu, ta fari dai na san tea ne, kuma ai kullum ma sai na sha shi.

Don haka sai na yi saurin cewa “Coffee” da irin sallon da  ta furta.

Cikin yan dakikai, aka kawo mana abin da muka bukata

Tea mai kauri na ga an mikawa Abbansu Khalil,, yayin da ni kuma aka  mika min abu baki.

Na kurba a hankali, hade da kallon Abbansu Khalil, shi ma ni yake kallo, da alama yana son ganin reaction dina ne

Idanuna na dauke daga kan fuskarshi, zuwa wani bangaren, na rufe idanuna gam sannan na hidiye abin da na kurba.

Gudun kar in yi abun kunya  na rika sipping abun kamar magani.

Da kyar na sha rabi, na aje sauran. Ina danasanin rashin cewa a ba ni tea dan gida.

Misalin biyar muka sauka Abuja

Saukar mu ke da wuya na hango Maman Khalil sanye cikin wani hadadden leshi mai ruwan goro

Dinkin riga da siket ne, ya zauna jikinta das, ta sha sarka da yan kunne masu kyau da tsada.

Eye glass din da ta sanya ya kara mata kyau sosai, idan dai kwalliya ce to Maman Khalil kam ta iya sai madalla.

Yaran ma fes dasu cikinsu kaya masu kyau da tsada

Tun daga inda take tsaye take aikawa mijinta sakon murmushi.

Shi ma hankalinshi duk yana kanta, kamar ya ture mutanen da ke gabanmu ya isa gareta

Tuni kishi ya turnekeni, zuciyata ta yi kunci, raina ya dagule, ji nake kamar in dora hannu a kai, in yi ta zumduma ihu.

Gaskiya babu abin  tashin hankali  a gurin mata irin ka ga mijinka da wata, kuma ace mallakinsa ce,, musamman irin su Maman Khalil,, kishi da irinsu ma bala’i ne.

Yaransa ne suka fara isa gareshi a guje cike da tsantsar farin ciki, shi ma cikin farin ciki yake dagasu, hade da yi masu tambayoyi, har zuwa lokacin da ya isa gurin Maman Khalil da ke tsaye ta na murmushi.

Na yi tunanin zasu rungume juna, sabanin haka hannu ta mika mishi suka gaisa hade da fadin, bayan ya dauki Ramlah

“lale marhababika da bangon gida, kowa ya yi kewarka, Alhamdulillahi da ka iso lafiya jarumina”

Murmushi dauke a fuskarshi ya mayar mata da amsa

“Na yi kewarku sosai uwargidana ke da yara, na yi farin ciki da na same ku lafiya”

Na yi tsaye sororo da kaya a hannu, ina kallon yadda suke fadawa juna yanayin da suka shiga da ba sa tare

Kamar ma sun manta ina gurin, dalilin da ya sa kenan na mika hannu na karbi Ramla, don sai wangale min baki take yi, hade da daga hannuwa alamun tana son in dauketa.

Haka nan nake son yarinyar, ina jin kamar ‘yata ta cikina haka nake jin kaunarta.

Gaba ya zauna shi da matarsa, yayin da ni da yara muka zauna a baya.

Ita ce ke tukin cikin kwarewa, yayin da suke ta hirarsu cikin nishadi, da alama sun manta da ni, don kuwa ko sau daya ma basu saka ni a hirar ba, ni ma kuma ban shiga ba.

Ni da yara kawai muke tamu hirar.

Bayan mun iso gida, na nuna mata tsarabarta da aka ba ni in kawo mata, ni kuma na dauki  tawa na yi sashena.

Hade da ajiyar zuciya na zauna, kan kujerar, kaina ma har ya fara ciwo, saboda tsananin kishi.

Kwankwasa kofar ne ya sa na mike da sauri, na yi zaton Abbansu Khalil ne.

“Ga shi in ji Aunty a kawo miki.” Wata yarinya bakuwar fuska ta fada, shekarunta ba za su wuce sha uku, zuwa sha hudu ba.

“Na gode.” Na fada hade da mika hannu na karbi babban tiren.

Tuwon semo ne da miyar egusi da ta sha kifi da ganda, ga ganyen ugu, gaskiya a ido ma kawai akwai burgewa bare a baki.

Sosai na saki jiki na ci tuwon, na sha ruwa.

Sannan na mike na shiga kakkabe dakina saboda kurar da ya yi

Har sha biyun dare na kasa bacci, zuciyata saka min abubuwa marasa dadi kawai take yi

Tana hango min Abbansu Khalil da Maman Khalil cikin jin dadin da baya misultuwa.

“Mtswwww!” Na ja siririn tsaki, hade da mikewa zaune, ni dai yanzu da za a ce in koma budurwa, to gaskiya zan zabi auran miji mara mata, na yadda wata ta biyo bayana, amma dai ni in zo a farko.

Yanzu da ace ni ce farko, da ba ruwana wata ce zan bari cikin kalubale.

Yanzu ga shi tun da muka dawo ban kara ganinshi ba, ko a waya ma bai kira ni ba. Na so kiranshi, amma kuma ina tsoron kar ta ga kamar na shiga huruminta

“Kai jama’a! Kai da mijinka, amma kira a waya ma ya zama damuwa.” na yi maganar tare da mikewa na shiga toilet don rage marata

Wasa-wasa ban yi bacci ba sai biyu saura,  shi ma cike da mafarkai kala-kala.

Dalilin da ya sa kenan na tashi da matsanancin ciwon kai, har tashin zuciya nake ji.

Da kyar na dafa indomie da tea na sha, na koma na kwanta.

Cikin bacci na ji ana jan kafata.

Da alamun yanayin bacci na bude I danuwana hade da dorasu a kan fuskarshi.

Sanye yake ciki yadi  ruwan kasa mai laushi, dinkin manyan mutane, ga kamshinshi da na matarsa na fita a jikinsa.

Haushi yake ba ni sosai, ko kunya tun jiya yana manne da matarsa, ko leko ni ya kasa yi sai yanzu karfe sha daya na safe. Mayar da idona na yi hade da lumshesu, ina jin wani daci a zuciyata.

“Amaryata, ya gajiyarki, fatan kin tashi lafiya?” Ya yi maganar daidai yana zama saitin kaina.

“Ban tashi ba, ya dameka ne? Ba dai ka dawo wajen babbar masoyiyarka ba?” na yi maganar a zuciyata, a zahiri kuma ban ce komai ba.

Bargon ya yaye hade da kwantar da fuskarshi a kan kirjina “Ba kya ji ne?”

“Ina ji, na tashi lafiya” Na yi maganar tare da kokarin ture sa.

“Jikinki zafi”

“Eh bana jin dadi ne tun jiya”

“Ban sani ba, sannu,  kin samu magani ne?”

“Eh na sha paracetamol”

“Sannu to, gajiyar hanya ce kawai, na so leko ki jiya ai, ni ma na gaji ki yi hakuri”

“Amma gajiyar ai ba ta hanaka hawa gado ba” na kuma yin maganar a zuciyata

Amma a fili na ce “Ba komai.”

“Zan je wurin aiki”

“Allah ya kiyaye hanya”

“Amin”  ya fada a lokacin da yake kokarin tashi.

Sai da ya sumbaceni a wuya da hannuna sannan ya ja min kofar ya fice.

Na sauke ajiyar zuciya mai sauti

Allah ya sani ina son mijina, ina kuma son kasancewa da shi a ko wane lokaci

Amma kuma ba damar hakan, ya zama ma kamar ƴarmin ake yi.

Wunin ranar dai haka na yi shi da zazzabi, komai karfin hali kawai nake yi.

Maman Khalil kam har daki ta zo, ta kawo min tsarabar da aka ce in kawo mata, ni ma na kai mata tawa tsarabar.

Jin tsoron abin da zai faru da dare ne ya sa na kira Abbansu Khalil a kan ya taho min da maganin zazzabi.

Tun da ya shigo nake jiran ya kawo min maganin amma shiru, ga kuma zazzabin ya kara tsananta.

Har karfe goma bai shigo ba, ni kuma na ki kiransa.

Paracetamol na kuma sha na kwanta

Tun da na zo duniya, ban taba jin matsanancin zazzabi irin wanda na ji a daren nan ba , ban taba tunanin za a wayi gari da ni ba.

Kuma a daren  ne na fi yin nadamar auran mijin wata, da mijna ne ni kadai, da ko mutuwa zan yi, zan mutu ne a hannunshi, amma wannan kam sai dai  da safe su zo su samu gawata.

Jiya ma ko leke bai lekoni ba, bare a yi batun magani.

Hade da sallama ya turo kofar, kamshinsa ya daki hancina sai na ji zan yi amai.

“Morning Dear!” Ya fada a lokacin da yake matsa kafafuna.

Bakina cike yake da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji, hakan ya sa na yunkura, na mike zuwa toilet din bedroom nawa ba tare da na yi magana ba.

Bi na ya yi kamar bindi, har na zubar da yawun na koma cikin dakin hade da zama gefen gado.

“Har yanzu jikin ne?” ya tambaye ni hade da cire hijabin da ke jikina yana taba jikin

“Subhanallah! Sannu, wannan kam sai dai asibiti, bari in yi wa Maman Khalil magana ta sauke ki.”

Na bi bayanshi da kallo bayan ya fita, ni duk haushi yake ba ni, ina gidanmu ya yi ta yi min dadin baki ya auro ni, kamar a duniya babu sauran wanda yake so sai ni.

Amma ga shi tun da na shigo nake ganin bambanci, sannan baya ma nuna shi yana yin wani abu da bai dace ba.

Tare suka shigo da ita, tana sanye cikin doguwar riga ja, da adon fulawa fara, kamar kullum dai ta yi kyau, kamar ba ta da wata matsala.

“Sannu Auntyn Ramla, ya jikin?”

“Da sauki.” na amsa mata

“Bari in taimaka mata ta shirya sai mu je asibitin, ka je gurin aikinka ba damuwa ” Ta yi maganar hade da kallonsa.

“Ok, to ki kula.”

“zan kula, kar ka damu da wannan”

“Allah ya ba ki lafiya, sorry” ya yi maganar tare da kallona cikin yanayin tausayawa.

Ita ce ta taimaka min na shirya, sannan muka fita.

Duk wani zirga-zirga a asibitin ita ce ta yi, har sai da ya rage ganin doctor kawai zan yi, sannan ta wuce gurin aikin ta, bayan ta ba ni 10k  a hannuna.

Bayan gwaje-gwaje dai an gano ina dauke da ciki wata biyu, sai kuma malaria.

Ban baro asibitin ba sai karfe biyu, kasancewar dama bamu je da wuri ba.

Ganin motarta a harabar gidan ne ya tabbatar min da ta dawo.

Yarinyar da har yanzu ban san wacece ba, ita ce ta bude min kofar bayan na kwankwasa. Kasancewar maigadin baya nan.

<< Hasashena 5Hasashena 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×