Skip to content
Part 60 of 66 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bashir shi ne uba na biyu a wurinsu Salman, Sai yanzu suka san irin rawar da uba ke takawa, suka san ya uba yake, da ni ce ubansu ni ce uwar, kuma ni ce danginsu. Amma zuwa yanzu komai ya canja, akwai inda Salman ko Baffa zai kai kukanshi a share mishi hawaye ba tare da ni na sani ba. Wannan kadai Idan na tuna sai in ji wani dadi ya kama ni da farin ciki. Yau ga shi kamar mafarki wai Salman ya yi aure. Ko yanzu na mutu Khadija Alhamdulillah, na san yarana dai a hannunki ke da Bashir suna cikin aminci. Na gode da karamcinku gare mu, Allah Ya saka maku da mafificin alkairi. ” ta kai karshen maganar hade da sake hannuna tana dauke hawayen fuskarta.

Ajiyar zuciya na sauke, a zuciyata ina fadin” Mace mai kamar maza kenan. Irin mu aka bari to ni da yaran duka rayuwar sai ta zama abun tausayi, ba zan iya wannan gwagwarmayar ba.”

Gefen gadon na koma na zauna a sanyaye na ce” Allah Ya jikan Kabir”

“Amin” ta amsa a hankali, sannan na ce “Ke mutuniyar kirki ce, ba na yi miki kallon kishiya sai ƴar’uwa, da ace haka kishiyoyi suke babu macen da za ta ce ba son kishiya Zahra. Ni kaina a yau ina jin idan na mutu na bar yarana a hannun jajirtattar uwa. Shigowarki rayuwarmu, kin kawo mana abubuwa masu yawa, duk na ci gaba. Dama turawa sun ce “Behind any successful Man, there’s a woman” tabbas na yarda, ke din jajirtatta ce. Kin yi aiki tukuru don ganin kin in ganta rayuwarmu. Ni kaina babu abin da zan ce miki sai godiya, tarayya da ke na kara min ƙaimi, da karfafa min gwiwa. In Sha Allah za mu ci gaba da rayuwa cikin aminci. Shaidan ba zai samu nasara a kanmu ba”

“In Sha Allah” ta fada, lokaci daya kuma muna kallon kofa, Ralma ta shigo dauke da babban tire, wanda ta dora foodflask karami, plate da spoon da kuma ruwa. Fuskar nan a hade.

Bayan ta aje abincin na ce “Bari in kira Affan sai ya zo ya dauke ki”

Komai ba ta ce ba, Sai baki da take turawa.

“Affan kana ina?” na yi tambayar bayan ya daga kiran.

“Ga ni nan a event center ana decoration”

“Yi hakuri ka zo ka dauki Ramla, na dan tsayar da ita ne”

Ya amsa min da “Ga Ya Adnan nan za su zo gida daukar wasu kaya sai su dauke ta, bari in fada masu”

Na amsa da to, kafin na yanke kiran na kira Salman a kan maganar abincinshi.

Lokacin da na fita tsakar gidan duk mutane sun kwashe, ba kowa sai Innar Ruma, da wasu tsahhin sa’arta.

Ina kokarin shiga part dina Salman ya shigo, don haka na ce mishi, abincinshi yana part din Barrister, kai tsaye kuma ya wuce can din.

*****

Misalin karfe bakwai da rabi na dare ina kan sallaya, bayan na idar da sallahr isha’i Zahra ta shigo, hannunta dauke da wata leda, bayanta kuma wata yarinya ce dauke da wani ƙaramin akwati.

“Auntynmu ta shi a yi mana kwalliya gidan dinnern can za mu je” cewar Zahra tana aje kayan saman gadona

Murmushi na yi kafin na ce “Kaza kanki da motsi”

Dariya ta yi tana zama kusa da ni, yayin da yarinyar da suka shigo take bude akwatin hannunta.

Light make up aka yi mana, irin dai na nutsuwar nan, wani ubansu farin lace muko dora riga da zane, dinkin simple babu hayaniya. Dauri mai steps aka yi mana, wanda ya dauru kamar da computer. Daga wuyanmu zuwa hannayenmu duk gwala-gwalai ne. Da na dubi kaina a madubi, Sai na ganni kamar wata babbar kawar Maama, wannan ya sa na yi dariya, ina fadin wannan kwalliyar ita ce mai da tsohuwa yarinya.

Prosser golden da takalmi golden muka rike, Sai farin mayafi wanda ya fallasa asirin kwalliyar tamu saboda rashin kwalliyar shi.

Key din motar da zamu basu gift ta miko min, na dauki keyn Salman na mika mata na Maama. Ta sanya a cikin posser da muka shirya dalolin kudi a a ciki. Tana gaba ina bin ta a baya mu ka rika sauka daga stairs din, fada min dalilin da ya sa ta canja shawara take yi. Wai tana son ba dangin mijinta haushi ne, su kara fahimtar ta yi nisa, abun da suke yi mata fata, na ta zo tana rokonsu Allah bai karbi fatan tasu ba.

Zahra na taka stairs din karshe da zai kai ta falon Bashir ya shigo, ya rika bin mu da kallo, Sai kuma ya yi murmushi yana fadin “Hassana da Husainah ina za ku je”

“wurin dinner” Zahra ta ba shi amsa tana murmushi.

Fara’a kwance a fuskarshi ya ce “Alhamdulillah da Allah Ya ba ni ku a matsayin mata, kalle ku gwanin sha’awa son kowa kin wanda bai samu ba, kuma wai duk biyun nawa ne, akwai abokiyar gwagwarmaya a waje, akwai ta cikin gida. Allah Ya kare hade min ku, ya zaunar min da ku lafiya, Ya jikan Sakeena Ya haskaka kabarinta”

Dukkanmu mu ka amsa da “Amin”

Ya ce “Abuja zan tafi jirgin 9pm zan bi”

Dukkanmu mu ka ce “Lafiya ko?”

Ya amsa da “Zan je kan batun wasu ayyuka ne, da nake son yin signing din su. Kuma gobe za a tura su fadar shugaban kasa da karfe takwas na safe”

Duk muka jinjina kai alamar fahimta, kafin mu ka juya zuwa dakinshi, mu ka taya shi kintsawa, sannan mu ka fito tare.

Shi da securitynshi suka fara fita, mu ma da namu securityn muka dafa masu baya.

Tun daga wajen event din na fahimci an tara mutane, motoci ne parke a gefen event din, bayan drivernmu ya yi horn, maigadin ya wangale gate din, ta yadda muke iya hango yadda aka yi decorating wurin very nice.

Motarmu ta silala ciki, yayin da Mc ya shiga shelanta zuwanmu.

Motarmu na tsayawa yan mazan nan suka yo kanmu, har da ango da amaryar ba a bar kowa ba

Dukkansu cikin farar dakakkiyar shadda suke, dinkin babbar riga da ya sha aiki, su shadaya riingis. Adnan, Yusuf faruk da Farhan yaran Rahma. Salman da Baffa yaran Zahra. Sai nawa Khaleel, Affan, Assidiq, Haidar da Husain. Sai kuma ƴan matan Maama, Ramla, da kuma Hassana.

Yadda su ke yo ɗuuu zuwa kanmu sa Zahra ta ce “Wlh Auntynmu idan na ga dama ba zan taka kafata ba”

Cikin rashin fahimta na ce “Ban gane ba”

“Yo ba ki ga samudawan da muka tara ba, yasin sai dai a daga ni sama a kai ni filin taron”

Ina dariya na ce “Bismillah!” na yi maganar daidai ina bude kofa na fita. Affan ne na farkon da na fara rungumewa tsam, wani dadi gami da farin ciki yana cika min zuciya, sannan na rika bin su daya bayan daya ina basu side hug Wasu Kuma in shafa kansu, daga mu har su baki ya ki rufuwa. Khaleel ya ce “, Auntynmu kuka ce ba za ku zo ba, ba a tanadar maku wurin zama ba”

Ina murmushi na ce “kar ka damu Khaleel, ai ba dadewa za mu yi ba”

Zahra na rike da hannun Maama da sauran ƴanmatan, ni kuma tawagar mazan ne nawa. Haka muka shiga filin Mc na ta zabga kirarin iyayen amarya da na ango.

Khaleel ne ya zaunar da ni a kujerar zaman ango, Maama kuma ta zaunar da Zahra a kujerarta,  ta zauna a hannun kujerar, Salman ma ya zauna a nawa hannun kujerar, sauran mazan kuma duk suka tsaya bayanmu.

Duk wanda ya kalle mu ya san akwai tarin farin ciki a tare da mu, sannan akwai shakuwa, fahimtar juna soyayya da kuma kauna a tare da mu da yaranmu

Muna a wurin zaune sauran mutane suka rika zuwa ana gaisawa. Kafin Mc ya bukaci ganin amarya da ango a fili, amma fir suka ƙi fita. Kasancewar Salman na kusa da ni, haka na rika mishi inkiya amma ya ki fita, Sai da na kama hannunshi zuwa filin sannan, lokaci daya kuma na bude jakata na shiga yi mishi ruwa liki da daloli, Sai ga su Baffa sun kawo Maama, nan fa fili ya rikice, a kai ta nuna capacity na kudi. Rahma cewa take wani abu sai ma bikin Affan ita shi ne yaronta

Bayan komai ya lafa Mc ya ba ni microphone, Wai me zan iya cewa a kan amarya. Kila an fada mishi ni ce mahaifiyarta.

Bayan na amshi microphone din na ce “Ai ni ban san komai kan amarya ba. Sai dai in yi mata albishir da ta tsinci dami a kale, yarona one in town Ne” duk wurin aka dau tafi da shewa, sannan na dora da “Na tabbata za ta yi alfahari da samun shi a matsayin miji, shi din ya fi mijin novel. (filin ya kuma cika da ihu, na dora da) saboda duk wani abu da mace ke so a wurin namiji Salman ya tattara, kawai sai dai in yi musu addu’ar samun zama lafiya da zuriya dayyiba. Daga karshe ina son in ce, So, so ne, amma son kai ya fi don haka, ni yarona zan yi wa kyauta. A wannan rana mai albarka gami da dimbin tarihi a wurinshi, na yi mishi kyautar mota”na kai karshen maganar hade da daga key din da ke hannuna

Filin ya kuma sarkewa da sowa, bayan komai ya lafa na ce “Uban ango, kuma uban amarya Alhaji Bashir Balarabe Ruma, ya biyawa amarya da ango kudin kujerar hajji, domin su je su sauke farali”

A kuma daukar tafi sannan na mikawa Mc microphone din, bayan ya yi dogon sharhi, ya ba Zahra, ita din ma Maama ta yaba kamar dai yadda na yabi Salman, sannan ta danka mata kyautar key din nata motor. Sannan ta ce amarya ta zabi Kasar da take son don zuwa yawon shakatawa za ta biya kudin.

A ka shiga tafi raf-raf-raf, Mc ya karbi microphones din cikin ihun murna ya ce “Wannan shi ne ake kira da bikin ƴaƴan gata, uwaki Naira, ke din banza, kin zo inda aka tara ki buhu. Kun ji dai, ga sabbin motoci, ga kujerar Hajj, ga kyautar yawon shakatawa. Kai ku tafawa iyayen ango da amarya”

Wurin ya kuma cika da sowa ana tafi sannan ya ce “Wannan fa biki, dakan ɗaka shiƙar ɗaka ne, tankaɗen bakin gado, sannan tuwona maina. Ga wadanda basu gane ba, bari in yi masu dalla-dalla. Wato ita dai Hajiya Khadija, mamallakiyar Ramla clothing ventures, ita ce mahaifiyar amarya, amma marikiyar ango. Barrister Zahra shugabar kungiyar lauyoyin arewa, kuma senatornmu ta gobe in Sha Allah ita ce uwar ango marikiyar amarya. Wadannan matan guda biyu ba fa ƴan’uwa ba ne, kishiyoyi ne, amma don Allah ku kalli yadda suke zaune, ya kamata sauran mata ku yi koyi dasu, ko a samu ci gaba “

Aka dauki ihu da tafi, yayin da ya shiga zayyano kyakkyawar alakar da ke tsakanina da Zarah, daidai lokacin kuma tawagar Samarin ƴaƴanmu, su Yusrah, Rahma Maman Aiman da sauran na kusa damu, sosai suka tashi don yi mana rakiya zuwa wajen da mu ka aje motormu

Time da mu ka isa gida goma saura, sauran kuma basu dawo ba sai wajen 12. Kowa labarin yadda dinnern ta kayatar yake, ba iya nan ba, har a media, yayin da zamantakewata da Zahra ya zama topic a social media. Kowa da abun da yake fada, wasu su ce wai dama talauci ne ke kawo kishin, wasu kuma su ce miji ne muka mora, wasu su ce saboda duk muna da ilmi ne, kowa dai abin da yake fada.

Cikin kwana biyu da biki baki muka yi ta sallama, Rahma ta kwashe nata iyalan, Adnan, Yusuf, Faruk, Farhan, Baffa da kuma Khaleel suka wuce India. Baffa ma ya koma school. Salman kuma yana cin amarci.

Wajen kwana takwas da bikin ina zaune ni da su Ramla muna break Zahra, ta shigo kamar a rude, wannan ya sa na mayar da hankalina kanta. Ina fadin “Lafiya?”

“Maama ce ta kira ni, wai in je ba ta da lafiya sai kuka take yi”

Na ɗan yi shiru kafin na ce “Ba yau za ki koma Kaduna wurin aiki ba?”

“Ciwo Maama kuma ai girmi wannan Auntynmu, kin ji yadda na ji ta kuwa?”

“Ina, shi Salman din?”

Na tambaye ta

“Yo wannan kuma, yana can yana baccin shi” ta ba ni amsa cike da takaicinshi

Na ce “to gaskiya ba za ki je ba”

Baki bude take kallo na, na jinjina kai ina fadin “Eh ba za ki ba, ban ga dalilin zuwan ba, don ubanta haka za ta yi nata zaman auran, abu kadan ta ce wani ya je, idan da ba nan ta yi auran ba fa. Allah ba za ki je ba. Ta mutu don ubanta. Kuma sai na ci mata ma.”

“” Ina fada miki abu, kina min wata magana daban, kin fa san Salman da careless, kila ma ba tun yanzu ne ba ta da lafiyar ba. Ga mari ga tsinka jaka.”

Na yi saurin tasowa na rike ta ina fadin” Wlh! Wlh!! Wlh!!! Barrister ba za ki je ba, kuma ba za ki sanya ni kaffara ba”

Sosai ta bata rai kamar za ta yi kuka, ba tare da ta ce komai ba. Ni ce na ce “Ramla za ta je yanzu, shi kenan ko”

“Me Ramla za ta iya yi, sai dai idan ke ce za ki je”

“Ni kam ba zan je ba”

Daidai lokacin Bashir ya sakko cikin shirin fita office, daga inda yake ya ce “Lafiya? Ke ba yau kika ce za ki koma aiki ba?”

Kamar za ta yi kuka ta ce “Maama ta kira ni tana kuka ba ta da lafiya, Auntynmu ta hana ni zuwa”

Ya dan yi shiru kafin ya ce “Ta kyauta, babu inda za ki je, ki je ki shirya ki zo ki wuce wajen aikinki, babu wanda zai je, su koyi handling matsalolinsu da kansu, ai mun yi mai wuyar kuma”

Na sake ta ina rausayar da kai alamun jin dadin abun da ya fada.

Ita kuma ta fice, rai babu dadi.

Bayan na sallami Bashir ya fita ne na kira Maama a waya ta dauka, murya kasa-kasa alamun dai ta ci kuka ta gaji. A zuciyata na ce “Kin dauka auran abun wasa ne, ba ku soyayya ba, ai haka kowa ya ji”

“Me ya same ki?”

Na fara tambayarta, cikin kuka ta ce “Ba ni da lafiya ne?”

Na ce “Ai na sani, me ke miki ciwo?” shiru ta yi ba ta amsa ba, na kuma maimaita tambayar cikin tsawa, maimakon ta amsa min, Sai ta fashe min da kuka, kafin ta ce “idan Momy ba za ta zo ba, ke ki zo don Allah Auntynmu, ji nake kamar zan mutu”

Sai kuma na ji ta dan ba ni tausayi, na sassauta murya na ce “Ina Salman din?”

“Yana dakinshi” ta ba ni amsa cikin kuka.

Na ce “tun yaushe ne ba ki da lafiyar?”

Cikin wani sabon kukan ta ce “Tun jiya ne”

“kina ji na?” na yi mata tambayar, kafin ta amsa na ce “ki yi wanka, zan zo idan Abbanku ya fita”

“Ai ba zan iya tashi ba Auntynmu, ni dai don Allah ki zo yanzu”

Kamar tana gabana na rike haba a zuciyata na ce “Abu ba ya samu ma’iya, kukan aure da sallallami”

A zahiri kuma na kaurara muryata na ce “Ke ban son sakarci, ki tashi ki yi wanka don kaniyanki”

Ta kuma fashewa da kuka, tana fadin “Wlh ba zan iya ba”

“To taahi ki bude kofar, in kira Salman din ya zo, ya taimaka miki”

Tun kafin in dire maganar cikin daga murya ta ce “A’ah! A’a!! Ni ba na son ya zo, don Allah kar ki kira shi, ni dai kawai ki zo.”

Na sauke wayar ina fadin “Kai wannan yarinya da shegen raki take Haba da Allah. Kamar ba za ta haihu ba”

Daidai lokacin Zahra ta shigo cikin shiri, jiki a sanyaye, na kalle ta ina fadin “Har kin shirya?”

“Eh” ta amsa min, kafin ta marairaice tana fadin “Don Allah Auntynmu ki je wurin Maama don Allah na roke ki, wlh ina tunanin yaron nan haiƙe mata ya yi da karfin tsiya, kuma na kira shi ya ƙi dagawa, duka-duka yaushe aka yi auran fisabilillahi”

Na dauke idona daga kanta, kamar ba zan ce komai ba, Sai kuma na ce “Shi kenan zan je”

Ajiyar zuciya ta sauke tare fadin “Na gode, don Allah ki ci min kaniyar Salman, ko ki dakko Maama ta dawo gida, tun da shi ba shi da kunya”

Cike da kosawa da zancen na ce “Don Allah ki kyale ni. To zai yi ta kallon ta ne, yarinya sai shegen rakin tsiya, da rashin dauriya, akan ta aka fara aure ne? Kowa ki ji shi lukui cikin dakin babu wanda ke sanin abin da ya faru sai ita, Yen-yen-yen duk ta cika mutane, ai ta san dama hakan zai faru” na karashe maganar ina kokarin hawan stairs din da zai sada ni da dakina.

“Ni dai kar ki je, ki yi mata bala’i”

“Allah ya kiyaye hanya” na fada ba tare da na bi ta kan maganar tata ba.

<< Hasashena 59Hasashena 61 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×