Skip to content
Part 61 of 66 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bayan na kira driver na shaida mishi zan fita yanzu, sako na turawa Salman kamar haka “Salman ka fita a gidan nan Barrister na zuwa”

“Ok” ya yi min reply ba ko minti daya sakon nawa bai yi da sauka ba

Wannan ya sa na mike na shiga shiryawa, ba na son in same shi a gidan, na kuma san idan ya san ni ce zan je, ba lallai ya fita ba.

Ina kokarin saka hijab kiran Maama ya kuma shigowa, Sai da na gama saka hijab din sannan na daga “” Auntynmu za ki zo?”

” Eh. “na amsa mata

” Don Allah ki yi sauri “

” Na ji”na fada hade da yanke kiran ina jan tsoki.

30mns ya kai ni gidan, tun daga tsakar gida nake noticing din gidan, komai tsab har cikin falo.

Sama na haura inda dakinta yake na shiga kwankwasawa a waya, maimakon ta bude min, Sai ga kiran ta, na daga a hankali ta ce “Auntynmu ke ce ke buga kofa?”

Takaicinta ya kuma kama ni, a fusace na ce ” ki zo ki bude min ko in koma”

Na sauke wayar ina kallon kofar, jim kadan na ji fitar key, dalilin da ya sa na tura kofar, a kan gwiwoyinta na ganta, wannan ya tabbatar min da rarrafe ta zo wurin. Kamar in yi dariyar abun, Sai kuma na hade fuska na ce “Me ye haka? Ba kya iya mikewa ne?”

Ta shiga jinjina kai tana hawaye, baki na tabe kafin na ce “Kuma a haka kika kira Barrister wai ta zo saboda ba ki da kunya, Allah Ya kyauta”

Hawayenta kawai take daukewa, toilet din na shiga hade da cika mata kwamin wanka da ruwa mai zafi wanda ba zai cutar ba, sannan na fito har zuwa lokacin tana a inda na bar ta.

“To zo ki wuce toilet”

Da rarrafen ta taho, baki na saki ina fadin “Allah zan ci mutumcinki Maama, ke ba ki da Juriya ne, me ye haka kamar ba mace ba, haihuwa fa za ki yi wata rana” na karashe maganar ina daga ta, ban damu da karar da take yi ba. A haka muka shiga toilet din, na ce ta shiga ruwan zafin.

Kamar gaske ta saka kafafunta, Sai dai tana zama ta yanka ihu ta mike zumbur.

“Lallai borin namiji ne” na fada a zuciyata, a zahiri kuma da karfin tsiya na rika zaunar da ita cikin ruwan, hannuna rike da takalmi coge, idan ta yunkura za ta taso, Sai in daga alamar zan kwaɗa mata, dole ta koma ta zauna. A haka na gama kintsa mata jikinta, ta yi wankan tsarki a gabana ina gani, sannan na fito, a zaune ta yi sallah, ni sai mamakin wannan lanƙwai nata nake yi. Na san daren farko kam akwai azaba, amma Maama langaɓewarta ta yi yawa.

Bayan ta idar na kawo mata tea, da dankalin da na soya mata, na tsare ta sai da ta ci, na gyara dakin tsaf da toilet din, sannan na ce ta kwanta, saboda zuwa lokacin zazzabi sosai ya rufe ta.

Ina tsaye a kanta na ce “Kina ji na?” tana rawar sanyi ta jinjina min kai

Na ce “Ki bar kofa a bude Salman zai zo ya duba ki ya kawo miki magani” kan ta kuma jinjinawa alamar fahimta

Da alamun kashedi na ce “Maama, idan kika kara kiran wani kika daga mishi hankali a kan sirrin gidanki wlh zan ci mutumcinki. Don ubanki wannan sirrinki ne bai kamata kowa ya sani ba. Haka kika ga sauran mata na yi? Kuma ko wace mace ai sai da ta bi ta wannan hanyar”

Komai dai ba ta ce ba sai rawar sanyi da take ta yi, gefen gadon na zauna, na ci gaba da fadin “Don haka ki yi hak’uri, zafin nan na dan lokaci ne, komai zai wuce, kuma kar in sake in ji ta dalilin wannan kina yi wa Salman rashin kunya ko kin guje shi. Wlh dawowa zan yi in yi miki shegen duka. Kin ji ni?” ta kuma jinjina kai

“Sannan ki kasance mai Juriya, ba mai yawan raki ba. Abu na gaba ba na son ko wace matsala ki ce za ki fadawa Barrister, Sai idan wacce ta kama ta sani din ce, amma kar ki yawaita kai karar Salman don Allah. Kuma kar ki kara kiranta ki daga mata hankali. Har abada ba za ta canja ba, ita din mamar mijinki ce, ke yanzu saboda Allah da kuma rashin kunya, Sai ki kira ta, ta zo ta same ki a wannan yanayin Maama ba kya jin kunya? Kai Allah Ya kyauta “

Na karashe maganar ina mikewa tsaye hade da taɓe bakina. Ita kuma ta tura baki alamun ko a jikinta.

” Tafiya za ki yi Auntynmu? “

” To zama zan yi? “

” Amma za ki dawo an jima ko? “

Cike da haushi na ce” Nan zan dawo ku ba ni daki”

Na doshi kofar fita, bayan na rike handle din kofar ne na ce “Ina kara fada miki, wlh kada ki yi Salman shirme, saura ki ki shan maganin, kuma idan wannan abun ya faru mutum bai cin abinci mutuwa yake yi”

Ban jira cewarta ba na fice, Sai da na zauna cikin mota, na bude wayata da Zahra ta ishe ni da kira na kashe ta, text na turawa Salman kamar haka _”Ka je ka duba jikin nata yanzu, Sai ka samo mata maganin da ya dace da halin da take ciki “_

Sakon na sauka reply din shi ya shigo, kafin na kira Zahra, ta gama surutunta na kashe wayar.

Tun daga lokacin mu ka fara asalin surukata da Salman, bai zuwa gidan kuma bai kira, idan ma wani abu ne sai dai ya turo text. Sosai yake ban dariya, amma sai na share shi, satin Zahra biyu ta zo weekend, safiyar Asabar ta matsa min lallai sai mu je mu dubo Maama, saboda tun da na je sau daya ban kara komawa ba, ina dai aika musu da abinci. Misalin karfe 11 na safe kam mu ka shirya, mu kadai ban da yara

Un expected zuwa mu ka yi musu, wai irin shi iyaye ke yi wa ƴaƴa, a nan za ka gane yarinya na da tsabta ko a’a in ji Zahra.

Tun da aka bude gate na ga motor Salman na yi dariya tare da fadin “Yau dai ruwa ya karewa ɗan kada bai gama wanka ba”

“Me ya faru?” Zahra ta tambaya

“Salman mana, kin ga tun da abun nan ya faru, ba kira ba zowwa”

Tana fita daga cikin motar ta ce “Yo ai da kunya idan ya santa”

Mu ka yi dariya a tare, lokaci daya muna nufar entrance din.

Bugawa daya aka ce “Waye?” da alama dama akwai mutum a wurin kofa, duk mu ka yi shiru, Sai ma Zahra da ta kara kwankwasawa a hankali, daidai lokacin kuma kofar ta bude, Salman da sanye cikin kananan kaya ya yi saurin ja baya, yana yi mana kallon mamaki.

Cikin tsokana na ce “Biko na zo, tun da ka yada ni, Salman amana ba ta ce haka ba” na karasa ina dariya

Aiko kamar ya nutse kasa da kunya, Sai soshe-soshe yake yi, ni kam na basar na shiga falon wanda yake gyare tsaf yana fitar da kamshi mai dadi

Zahra ta ce “Ma Sha Allah, da alama yarinyata mai tsafta ce”

Daidai lokacin Maama ta sakko cikin dinkin doguwar rigar atamfa, kanta sanye da hula yayin da hannayenta ke rungume da littattafai, ganinmu Un expected ai Sai ta watsar da littafan ta nufo mu  a guje, na yi saurin kaucewa duk da dama ba ni ta nufo ba. Zahra ta mamutse kamar za ta kayar da ita, Salman kam har ya saɓe ya gudu.

Zahra lungu da sako na gidan Maama sai da ta leka, inda ta ga kuskure ta gyara, wani wurin kuma a yaba, ni dai ina biye da su. Bayan mun dawo falo ne Maama ta ce mu zauna a dora abinci na ce “Ai ko ni ba sakarya ba ce, da zan zauna har a gama abinci in ci.”

Duk suka yi dariya, Zahra ta ci gaba da nannaga wa Maama lallai ta koma makaranta, kar ta biyewa Salman.

Watan Maama hudu da aure ta fara rashin lafiya, ga kuma exam, kowa ma ya san ciki ne, kuma na wajen wata uku. Muna ganin langwai kam, wai an taba ƴan baka, kura ta saci kalangu, ba ita, ba uwar tata ba, kullum korafi, karshe ma Zahra dakko ta ta yi, wai jinya, kuma ita ba zama take ba, ni take bar ma wa in ta fama, yau ta ce alale, jibi dambu, citta tuwon dawa miyar kuka ba manja, haka dai kullum take sanya ni wahala.

A haka har ta gama exam, ta kuma kwashe wata daya a gida, wannan ya yi daidai da cikinta wata hudu aure kuma wata biyar.

Misalin karfe tara na dare Salman zaune kan dinning yana cin abinci, lokaci zuwa muna taba hira, a kan exam din da zai yi nan da wata biyu

Na ce “Zuwa Saudiyya dai sai a hakura sai next year, saboda lokacin tafiyar ita ma Maama tana exam din final year, yawon shakatawar ma duk ba aje ba, kun gama shakatawarku a gida”

Komai bai ce ba, Sai murmushi da ya yi yana sunkuyar da kai, na dora da “Atoh! Babu inda za ku je da waccan Umma Lagwai din, wahala za tai ta ba ka.”

Yanzu din ma bai yi magana ba, Bashir ya shigo, bayan sun gaisa ya kalle ni, ya ce “Me wannan yake yi har yanzu a nan?”

“To Zahra ta hana shi matarshi, maganar Allah ka sanya baki ta ba shi matarshi, exam din nan ta gama, shi kuma laulayi gama shi ba sai a hankali ba.”

Komai bai ce ba ya juya, kamar 10mns sai ga shi ya dawo, ya kalli Salman tare fadin “Tashi ka same ta ku wuce gida”

Ya kai karshen maganar hade da nufar stairs din da zai sada shi da dakinshi

“Thank you so much Auntynmu, amma zo ki raka ni, na san Momy na can na jirana”

Dariya na yi hade da mikewa na bi bayan shi. Ilai kuwa tana tsaye kan entrance din ta, ganinmu ya sa ta sakko, shi kuma ya ruga da gudu wurin parking space yana dariya, na rike ta ina fadin “Allah Barrister ina jin kunyar ki”

“Ni ce zan ce ina jin kunyar ki Auntynmu, Allah ba kwa yi min adalci, yarinyar nan tana tsaka da karatunta kuka matsa aka yi auran nan, ba aje ko ina ba sai ga ciki, kina kallon irin wahalar da take sha, dan hutawar da take kuma kin zuga Abbansu ya kore ta, yanzu idan ta koma ita ce girki, da dawainiya da Salman, kin san halin shi sarai da son iyawa”

“” To yi hak’uri, na san mun yi laifi, daga wannan ba za a sake ba”

Komai ba ta ce ba, Sai kallon Salman da yake ribas zai fita.

Haka rayuwa ta ci gaba, har zuwa karshen shekara, inda karshen shekarar ta zo mana da abubuwa masu yawa da dadi, ciki dai akwai gama karatun Affan da Khaleel. Baffa da Salman, Ramla, Farhan da faruk. Shi ya sa gidan namu ya cika, taf, kamar dai ko wace karshen shekara, Maama kam ciki ya yi girma haihuwa yau ko gobe, duk lokacin da na kalle ta, tana tura ciki sai in kara jinjinawa Ikon Allah, kamar jiya na haife ta ban sani ba, ta zo a lokacin da muke cikin tsananin tashin hankali, ta yi sati biyu ba a ba ta suna ba.

Kamar ba ita ce mai shegen rikicin nan ba, mai yawan kuka, wai yau ita ma ga ta dauke da nata cikin, addu’ata kullum shi ne Allah Ya raba su lafiya.

Tun da su Affan suka dawo, suke shirin hada party, wai na murnar gama makaranta, Zarah kam ta biye musu. Su ka yi ta shirye-shiryensu.

Ranar da za su yi partyn, suka kira masu decoration suka kara gyara hall din cikin gida, suka sha anko abun su, tun ina kin muhimmantar da abun har kuma ya fara kama hankalina. Zuwa karfe hudu mu ka shiga hall din ya Sha gyara, Sai ga shi abu ya kayatar makota duk sun shigo, haka ma abokansu Affan din. Salman sai nan-nan da Maama yake yi, don ma yana jin kunyarmu, ni dai ana kiran sallahr magriba na baro wurin, su kam sai da Bashir ya dawo masallacin sallahr isha’i ya ce su tashi haka nan.

Da safe na shirya mana break fast, kaf dinmu muna falona muna break Bashir ya ce “Idan Allah ya kai mu Hajji next year, dukkanku zan biya maku ku je ku sauke farali a matsayin gift dina, kun ga sai ku tafi da su Salman, hakan ya yi muku ko?”

Duk suka amsa da eh cike da farin ciki, ya juyo yana kallona ya ce “Auntynsu sai ki kira Umma a wannan karon ma su tafi ita da Inna su sauke farali, ke kuma da Barrister sai ku biyawa kanku ai kuna da kudi”

Barrister ta yi caraf da fadin “Yau na ga sonkai(ta juya kan yara tana fadin) don kaniyanku ku yi karo-karon kudi ku biya mana, kowa iyayenshi da ƴaƴanshi yake biya ma wa”

Adnan ya ce “Shakuruminki Momy soon, za ku fara sauke faraki each and every shekera in Sha Allah”

Duk mu ka amsa da amin, sannan mu ka shiga yi mishi godiya da kwaroro mishi addu’o’i, yana amsawa da amin.

Yana kallon Adnan ya ce “Adnanu kun daidaita kanku da Ramla ko, to duk wanda ya shirya ya kawo matar aure a cikinku, saboda ni na shirya.”

Duk suka kalle mu, cikin dariya na ce “Wato dai so kake ka sallami kowa”

“Ashe kin gane” ya yi maganar hade da mikewa yana fadin, zan je wani taro, samarin nan ku shirya ku raka ni”.

<< Hasashena 60Hasashena 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×