Da kaina na shirya zuwa, Kano don yi wa Ummata albashir, da kuma maganar bikin Maryam, Sai lokacin Allah Ya kawo nata mijin.
Ni da Hassana da Husaini na tafi, Umma kam ta ji dadin zuwana, ni kaina na ji dadin zuwan, saboda yanzu lokacin ziyarar wahala yake yi min, hidimomi sun karu, ga duk inda mutum zai je sometimes Sai da security, Amma a wannan karon daga ni sai direba mu ka taho.
Lokacin da na sanarwa da Umma albishir din da na kunso mata, ba karamin farin ciki ta yi ba, har da kuka, wai dama kullum tana addu’a Allah Ya kara mayar da ita. Na ce Allah ya amsa. Sai da mu ka raba dare muna hira, babu inda ba mu tabo ba, musamman Yusrah, wacce ita ma ake shirin auran First born dinta namiji, dama yaran biyu ne, daga nan haihuwar ta tsaya.
Da asuba dakyar na tashi na yi sallah, ina Azkhar kiran Zahra ya shigo, bayan mun gaisa ta ce “” Auntynmu Maama ta haihu da asubar nan”
Kamar tana gabana, wari ido na yi, cike da mamaki na ce “Kai Barrister?”
“Allah da gaske, an samu Baby girl, Sai kin ganta kyakkyawa, bari in tura miki hoton ta”
“Kin san Allah ni har yanzu ban yarda ba”
Cikin doki ta ce “Kashe in kira ki video call, wlh muna asibiti”
Na yanke kiran ina kallon Umma da ita din ma ni take kallo na ce “Wai kin ji Umma Maama ta haihu yanzu”
Mamaki ya bayyana a fuskar Umma ta ce “Haba dai?”
Na ce “Haka dai Barrister ta ce, ni ma ban yarda ba, ji nake kamar tsokanata take yi.” na karasa maganar ina bude data ta. Sai ko ga kiran Zahra
Bude baki na yi cike da mamaki ganin Maama kwance, ga baby a hannun Zahra, camerar na juyawa Umma ta ce “Ashe ko da gaske ne, kai barka alonƙosa ta haihu” Zahra ta yi dariya tana tarewa Maama tsokanar da Maama ke yi mata, wai ta san dai sai da aka daddaure ta. Kafin suka gaisa ta yi masu barka, Maama dai kin juyowa ma ta yi, miko min wayar Umma ta yi, ni ma na yi musu barka sannan na ce in Sha Allah zan taho yau. Bayan na yanke kiran Zahra ta turo min hoton Baby. Idanu na zuba mata ina mamaki, kamar mafarki, na haifi ƴa ita ma ta haihu, ikon Allah, kamar ba ni ce aka aurar ba, na je na yi ta shirme, ga shi na dauki jika, a kwana a tashi babu wuya wurin Allah.
Baby kam kyakkyawa, asalin kyau, to Zahra da ƴan’uwanta a wurin kyau ba baya ba, sosai Zahra kyakkyawa ce, fara tas, doguwa, gashi, diri ga kuma wayewa da iya tsara kwalliya, wannan ke kara bayyana kyawunta a kallo daya.
Haka ma Salman yake, kyakkyawa sosai duk da bai kai Zahra haske ba, kamar yadda bai kai Baffa ba, amma sosai Salman kyakkyawa ne.
Ita kanta Maaman ba daga baya ba a kyau, kowa ya san Rumawa, musamman na garin Ruma basu da munana sosai, ku san kowa mai kyau ne, to Maama ma ta dakko irin wannan gadon kyan, komai nata mai kyau ne.
Na faɗawa su Husaini Aunty Maama ta haihu, Haba sai murna wai mu tafi gida, haka sauran yaran suka rika kirana ana fada min Maama ta haihu, har da Salman, na ce “So ka zama Baba kuma Salman, Allah Ya ba ka ikon sauke nauyin da ke ta kara hawa kanka.” ya ce amin cikin doki.
Haka muma a nan mu ka rika sanar da ƴan’uwa, kowa kam sai murna, time da na kira Yusrah sai ta ce min Maama ta shaida mata a WhatsApp. Na ce wato mu ne take ji wa kunya kenan to mun gode.
Misalin karfe goma mu ka baro Kano, zuwa 1:30pm muna gida, kai tsaye kuma na wuce sashen Zahra inda mai jego take.
Ina tura kofar bedroom din muka hada ido da Maama, Sai ta yi kasa da kai tana dariya a hankali. Ni kaina dariyar nake tare da fadin “Shi kenan Maama an zama uwa, ikon Allah”
Barrister ta yi dariya ta ce “Kamar mafarki Auntynmu, Sai kin ga murna wurin Salman ba ko kunya”
“Rashin kunyarshi ce ta fito fili, ita ma ta gaban ki ai kiran mutane take yi, tana fada masu ta haihu”
Zahra ta juyar da kallon ta kan Maama tana fadin “Da gaske, wa ta kira? Ban ji ba”
“Tambayar ta ai ga ta nan” na yi maganar ina juna Maama da ta rufe fuska da hannayenta biyu, lokaci daya kuma Ina daukar Baby da take kwance saman gadon Zahra cikin overall mai kyau light pink, da farin showel”
Dungure Maama ta yi cikin wasa ta ce “Wato zama da Salman Maama ya ɓata ki, Allah Ya shirye ku”
Na amsa da amin, ina kara karewa Babyn kallo katuwa da ita kamar ba haihuwar fari ba, ga ta kyakkyawa fiye da a hoto. A hankali na furta “Barakhallah Ma Sha Allah, Allah Ya raya, ya bayar da lafiyar shayarwa, kin ga Baby zam Babanta?” na yi maganar ina kallon Zahra
Ta ce “Haka kowa yake cewa, su Adnan ma duk haka suka ce, shi kanshi uban yar yana daukarta sai ce min ya yi, Momy kamar ni ina jariri ko?”
Murmushi na yi ina fadin “Kai Allah Ya shiryi Salman, amma ya Maama da haihuwa kam, Allah Ya taimake ni ba na nan”
Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce “Yo ya fa, hak’uri ta yi”
Na kuma cewa “amma sai da ta rika shan mari ko?”
“Umm! Ba dai za ki ji ba” ta ba ni amsa, lokaci daya tana karbar abincin da Maman Usi ta kawo. Ni din ma mikewa na yi zuwa part dina. Babu wani datti tun da akwai Ramla
Da yamma haka samarin suka cika dakina sai labarin haihuwar Maama, hakan duk sai ya tayar musu da tsumi, wai su ma za su kawo matar nan soon, ni dai jin su nake yi, wani lokaci in sanya baki wani time kuma in yi shiru.
Da dare Bashir ya dawo, na je na dakko mishi sabuwar amaryashi, ido ya zuba mata cike shauƙi kafin ya ce “The first grandchild in Bashir Balarabe Ruma family. Alhamdulillah Ya Rabbb.” Kai ya dago yana kallo na, kafin ya ce “Su Khadija rikici an yi jika”
Dariya na yi, ba tare da na ce komai ba, ya yi mata addu’a, sannan mu ka shiga hirar baya, abubuwan da suka wuce, amma sam ya ƙi a yi hirar Sarai, ban san me ya sa ba ya so hirar Sarai ba. Idanunshi a kan Babyn Maama na ce “Wai Yallaboi me ya sa ba ka son hirar Sarai ne?”
Cikin rashin jin dadi ya ce “Saboda raina yana baci, duk lokacin da na tuna a sanadinta Affan ya rasa ji, Sai in ji wani irin bacin rai mara adadi. Yaron Sakeena, a bayan ranta ma na yi wasa da rayuwarsu saboda wata. Sakeena ba ta cancanci haka ba Khadija. Har gobe Ina jin mutuwar Sakeena, ina jin ina ma tana raye na kai wannan matsayin. “
A hankali na nisa memoryn rayuwarmu ta baya tana dawo min, yanayin murmushinta wanda ko wane lokaci yana kan fuskarta, musamman idan abu ya yi mata dadi. Kawaicinta, kwalliyarta, yadda take yin abu a nutse babu hayaniya. Idanu na lumshe a hankali ina fadin “Allah Ya jikanta Ya gafarta”
Ya amsa da amin, ya kuma cewa “Abu na biyu yadda ta sanya igiyar saki ta shiga tsakaninmu, yarinyar nan shaiɗaniya ce wlh.”
Ya karasa maganar cike da jin haushi
Kafin in yi magana ya ce, “ki tuhumi iyalanki, kowa ya fito min da mata, Adnan dai ga Ramla nan, saura Khaleel, Affan da kuma Baffa. Su Faruk kuma ban san me ye shirin mahaifinsu a kansu ba.”
Kai na jinjina alamar ina fahimta, ya dora da “Ba na jin akwai mai wata matsala a cikinsu, kin ga Khaleel da aikinshi a hannu ya fito, Affan ma Zahra ta nemar mishi aiki, a babban asibitin Abuja, ni kuma ina da plan din bude masu asibiti su ukun nan gaba”
Na yi saurin cewa “Tunani mai kyau Allah Ya taimaka”
Ya amsa min da amin, tare da fadin “Kai musu Babynsu”
Da safe kam ina daki Khaleel ya shigo, bayan mun gaisa ne yana niyyar futa na ce “”Dawo Khaleel ina son yin magana da kai”
Gefen gadon ya koma ya zauna, saboda ni dama Ina kan sofa ne a zaune
“” Yaushe za ka fara zuwa wurin aikin ne?
Ya ce “I don’t know yet, but I’m waiting in ji daga gare su”
Kai na jinjina sannan na ce “Madalla, Allah Ya taimaka Ya sa a fara a sa a, Ya tsare ka, Ya kare ka daga dukkan sharri”
Ya amsa da amin cike da jin dadin addu’ar tawa.
Bayan mun dan yi shiru na ce “Kwanaki Abbanku ya yi maganar ku kawo wacce kuke so, kai na ji ka shiru, ko ba ka samu ba ne?”
Shiru ya yi, har sai da na kara maimaita tambayar sannan ya ce “Ban san ya za ku karbi abun ba ne”
“Ya abun yake?” na yi tambayar ina mayar da hankalina a kanshi
Ya ce “Sunanta Preeta, a can kasar India din take”
Tun da ya fara maganar nake kallon shi, bayan ya idar ne na ce “Babbar magana!”
“Za Ta musulunta Auntynmu”
Kai na jinjina har zuwa lokacin ina nazarin maganganunshi, na dauki a lokaci kafin na ce “Tun yaushe kuke tare da ita?”
“Shekarata ta biyu a makaranta, ita tana karantar bangaren likitar mata ne”
Kai na kuma jinjinawa ina fadin “Khaleel ka yi tunani mai kyau fa, ma fi munin zabi a rayuwar nan, shi ne zabin abokin zama”
Cike da kwarin gwiwa ya ce “Preeta ba ta da matsala Auntynmu ki tambayi Affan ko Momyn Farhan ki ji, ai ta san ta”
Na ce ” to iyayenta fa, kana gani za su ba ka yarsu ka musuluntar da ita, ka aure ta, kuma ka rabo su da ita, wannan fa issue ne babba Khaleel”
“Mun rin ga mun tattauna wannan da ita, da kuma iyayenta, su suna ba yara dama su yi abun da suke so idan har sun balaga”
Na kuma yin shiru cikin dogon nazari, kafin na ce “Khaleel ina maraba da duk abin da kake so, amma a wannan karon hankalina ya kasa kwanciya da wannan magana. Gaskiya ba na son a yi abin da za a dawo ana dana sani”
Kamar zai yi kuka ya ce “Auntynmu ki tambayi Affan ki ji, Allah babu matsala”
Kamar hadin baki kuma sai ga Affan din ya shigo, da kallo ya bi mu kafin ya ce “Lafiya dai ko, na gan ku so cool”
“Gara ma da ka zo, Maryam din da kake ta sintirin zuwa wurinta auranta za ka yi, ko bata mata lokaci kake yi?”
Guntun murmushi ya yi kafin ya ce “Auntynmu bayan ita, na taba yin maganar wata a gidan nan? Da gaske auranta zan yi”
Kai na jinjina kafin na ce “To ka yi wa Hajiya magana za mu kawo kudin aure” kai ya daga alamar to, yana kallon Khaleel da ya yi la’asar, ya dan taba shi kafin ya ce “Hey man, what is wrong?”
Idanuna na sauke a kan Khaleel sannan na ce “Kar ka damu, zamu tattauna a kan batun ka.”
“A kan preeta ne ?” Affan ya tambaya
Da kai na amsa mishi, ya dora da “Tana da kirki ba ta da damuwa, kawai dai ta yi nisa ne, idan da zai samu wata a nan da ya fi”
Khaleel ya aika mishi da harara, daga ni har Affan din mu ka yi dariya, shi kuma ya mike zuwa kofar fita
Na kalli Affan na ce “Kana ganin abun nan zai yiwu kuwa Affan?”
Kafadunshi ya daga sama kafin ya ce “Ba na ce ba gaskiya, yana sonta sosai haka ita ma, kuma ta ce za ta musulunta, don haka a fara gwadawa, idan abun ya ci tura sai a hak’ura, amma tana son shi sosai, ga ta kyakkyawa Auntynmu, kila shi ya sa yake kara rudewa”
Murmushi na yi kafin na ce “Ba ka da kirki fa Affan”
Shi ma murmushin ya yi tare da fadin “Allah kyakkyawa ce, amma ba ta fi Maryam dita ba”
“To tashi ba ni wuri, na fahimci kai sai ka fi Salman rashin kunya”
Dariya ya yi hade da kwanciya saman gadon sosai, ya ce “Ba ta da kyau ne Auntynmu,+? tun fa ban san kyau ba, na san Maryam mai kyau ce”
“Tashi ka fitar min a daki na ce ma”
Kafafunshi ya mayar saman gadon sosai ya kwanta ya ce “Bacci zan yi, Allah gadonki akwai dadin bacci, ga dakin ki lokacin sanyi dumi, lokacin zafi kuma sanyi”
Kai na shiga girgizawa ina dariya.
Daidai Zahra ta shigo saɓe da Babyn Maama, Affan ta fara turewa, wannan ya sa ya koma tsakiyar gadon sosai ta ce “Kana nan ne, kai kam Allah Ya yafe ka, ka raina mata gado, Sai ka zo ka yi wani shekeke ko kunya ba ka ji”
Dariya ya yi, ni kuma na ce”Babu ruwan ki, mun fi kusa, idan ma nan ya ce zai dawo, ina maraba ya kwaso kayanshi. “
Ya ce” To kin ji. Wanda yake ganin bai ji dadin wannan magana ba, ya tafi kotu “
Filon gefenta ta dauka da zummar buga mishi, da sauri ya mike zaune ya ja baya sosai yana dariya. Ta dora mishi Babyn a kan cinyarshi tana fadin” Kai ne kawai ba ka dauke ta ba, shi ya sa na kawo ma”
Ido ya runtse kam hade da kankame jikin shi ya ce “Don Allah Momy ki dauke ta, wlh ba na iya daukar jariri”
Ganin ba za ta dauke ba, ya sa na taso na dauke Babyn daga jikinshi, ya sauke bayyanannar ajiyar zuciya, hade da dirowa daga saman gadon ya bar dakin a ɗari
Cikin dariya ta ce “Na samo maganin rashin kunyarka ai.”
Ni ma ina dariya na ce “Kin korar min yaro”
Wurin da ya tashi ta kwanta sannan ta ce “Haka kawai da girman shi da komai sai ya zo ya haye gado fisabilillahi ko kyau babu, wani goɗai-goɗai”
Na ce “Ke ce ke ganin girmanshi, ni wlh har gobe yaro nake kallon shi”
“Shi ya sa yake yadda yake so ai, Affan da girmanshi ba shi da lafiya wai sai ya zo ya tasa ki kamar karamin yaro yana kuka, ko ya kwaso gajiyar shi ya zo ya zube miki saman gado, baccin rana ma wai sai ya ce gadonki ya fi daɗi, ai daga yanzu da sabuwar Babyn nan zan rika korarshi”
“Ai ga shi nan, kin kore shi ke kin kwanta”
Dariya ta yi kafin ta ce “Allah gadonki dadin kwanciya katifarki laushi”
Na yi dariya ina fadin “Khaleel wai yarinyar da yake so a India “na yi maganar cike da jimami
Ba tare da ta nuna kaduwar zancen ba ta ce “Eh mun yi magana da Rahma kwanaki, shi ma Khaleel din mun taba maganar da shi”
“Kenan ni ce kuka ware?”
Dariya ta yi kafin ta ce “Yanzu ba ga shi kin ji ba”
“Haka ne, amma ya kike kallon abun?”
Ta ce “So simple, Idan yarinya ta amince tana so, iyayenta za su bamu shi kenan, mu bamu da matsala ai”
Da murmushi a fuskata na ce “Mara din ki baya kunya, dama na san haka za ki ce ai”
Duk mu ka yi dariya a tare.