Skip to content
Part 63 of 66 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Aje maganar Khaleel na yi, na mayar da hankalina kan taron sunan Maama, komai na gata Maama da Babynta sun samu, ta ko wane bangare.

Ana gobe suna muka fara amsar baki, ƴan’uwa na nesa. Misalin karfe takwas na dare ina daki ni da su Yusrah da Maryam, da sauran ƴan’uwana ƴan Kano da suka zo muna ta hirar zumunci, Khaleel da Affan suka shigo dauke da jakunkuna da za a rabawa ƴan suna.

Saman gadona suka aje jakar sannan Affan ya ce “Auntynmu Ya Salman ya riga mu yi miki takwara, sunan ki aka sanya”

Yusrah ta yi saurin daukar jaka guda daya tana karantawa, sannan ta ce “Ai kuwa sunanki aka sanya, amma wai Khariyya za a rika kiranta.”

Na ce “Na gode, Allah Ya raya ta bisa sunnah, ku kuma ai akwai sauran sunaye da yawa da suke bukatar takwara din ai”

Khaleel ya ce “Idan ana maimaita suna, to zan yi ta maimaita sunan Khadija, Sakeena wa yara na mata”

Affan ya cafe da “Ashe tunaninmu daya, Khadija A, B, C, har zuwa Z, haka ma Sakeena”

Su Yusrah da ke dariya suka ce “Allah Ya nuna mana lokacin dai”

Na amsa da amin cike da jin dadi, ina kuma alfahari da kaina, da ace mugun riko na yi musu, da komai sunana ba za su su ji an, ambata ba, bare su yi sha’awar sakawa yaransu.

Ranar suna kam gida ya yi cikar kwari, Maama an ci kwalliya kamar wata amarya, haka mu din ma mu ka ci kwalliya, su Ramla uwar ya ba a magana har gayya ta yi ta kawayenta, can ango ma da abokanshi haka, Rahma ce dai babu da su Adnan.

Da yamma kuma sai ga Maman Hana da Umaima unexpected, har da yaranta ƴanmatan. Sosai na ji dadin zuwanta, na rika ina aka saka ina aka aje da ita.

Cike da kunyarta na ce “Wlh ban san kin dawo ba”

Ta ce “Ai ban yi sati biyu da dawowa ba, Honarable bai fada miki ba?”

Kai na girgiza alamar a’a, sannan na ce “Wlh bai fada min ba, kin san abubuwan kanshi yawa ne dasu”

Ta ce “Gaskiya kam, ai shekeranjiya ya je, da Baban Hana ya zo, kuma sun dade tare”

“Shi ya sa ba zan ji maganar dawowar ta ki ba, ai shekaranjiya gidan akwai baki sosai”

Hira mu ka yi sosai ta yi min murnar abubuwan da suka faru da ba ta nan, ni ma na taya murnar ci gaban da take samu. Su Hana kam tuni Ramla ta janye su, shi ya sa ma ni ba zan iya tantance su, na san dai yan’matan sun kai biyar.

Sai yamma lis suka tafi, bayan na cika su da abubuwan suna. Ji nake komai na ba ta ya yi kadan, turare wuta na daki  na kaya da na jiki duk sai da na hada  musu.

Gajiya dai ba sai na bayar da labarin gajiyar da na yi ba, ban kuma samu na warwareta ba, Sai da gidan ya koma iya namu mu ka sallami kowa. Har Zahra ma ta koma wurin aikinta, Sai Maman Usi da ke kula da Maama da kuma ni din da nake taimaka mata.

Yau dai na shirya yi wa Bashir maganar Khaleel, tun da yanzu kowa hankalinshi ya dawo jikinshi. Maganar aikin Hajji ce kawai ta rage kuma akwai sauran lokaci.

Don haka bayan ya shigo, ya kammala duk wasu hidimominshi har da cin abinci, hankalina na tattara a kanshi na ce “Honor a kan batun Khalil”

Ya ce “Ina ji”

Zama na gyara hade da tattara duk wasu kalamaina da na san za su sanya ya gamsuwa na ce “Mun yi magana da shi, ya ce min akwai wata yarinya Preeta mai hankali da nutsuwa yar India, sun daidaita da juna har ma ta ce za ta musulunta, shi ne ya ce in fada ma”

Kallona kawai yake yi har na idar da maganar sannan ya ce “Ke da Zahra wani lokaci hankalinku da tunaninku a hannun riga yake, ku dai kawai abin da yara ke so, shi kuke bi. Ita Zahrar da ya fara turowa da maganar ai na fada mata ban amince ba, ni babu wanda zai dakko min wata yar India can, ba zan iya da tsare-tsarensu ba, don haka na yi magana da Mustapha Sandamu Khaleel ya je nemi Hana, hankalina ya fi kwanciya a nan bangaren. Na so fada miki ban samu lokaci ba ne”

Shiru na yi ina jin maganar kamar fadowar gini, wannan shi ne tsaka mai wuya, ba zan so kin hada zuriya da Maman Hana ba, kamar yadda ba zan so a yi Khaleel dole a kan abin da ba ya so ba. Sai na ji nauyi da kunyar tanka maganar koda Bashir din ma, don haka na ce “To Allah Ya sa haka ne ma fi alkairi”

Ya amsa da amin, kafin ya dora da “Ki ce mishi ya je a cikin satin nan”

Da to na amsa, na shiga wata hidimar zuciyata dai babu dadi.

Kwana biyu komai ban cewa Khaleel ba, musamman idan na ga yana ta walwalarshi cikin Nishadi, na tuna maganar da zan fada mishi za ta yanke waccan walwalar sai in yi shiru abuna.

Ranar da aka yi kwana hudu da yin maganar ne Bashir ya same ni daki lokacin da zai fita office rai bace ya ce “Khadija Khaleel ya je gidan Sandamu?”

Na shiga kame-kamen rashin gaskiya, fuska ya kuma hadewa sannan ya ce “Kar yarinyar nan ta koma Abuja bai je ya ganta ba, kar ku mayar da ni ƙaramin mutum mana, ranku zai baci gabadaya wlh” ya karasa maganar cike da zafi fiye da farkon fara maganar ta shi, bai jira cewa ta ba ya fice, shiru na yi cike da damuwa, no way out, hakan ya sa na mike zuwa sashen yaran, time da na fita, motocin Bashir da escorts din shi suna fita, Sai da na bari sun fi ce gabadaya kafin na nufi side din su.

Komai na part din tsab, ga motocinsu nan a jere, Khaleel Baffa, da Affan, Sai Assidiq shi da Haidar. Ganin ban ga motar Salman ba ya tabbatar min yau kodai ya kwana a gidanshi ko wurin aiki.

Dakin Khaleel na kwankwasa, ya bude kofar tare da fadin “Auntynmu!” yadda ya kira sunan da alamun fargaba ya sa na kara jin babu dadi.

Na rika bin dakin da kallo, komai a daidai, babu wata kazanta ko datti, gefen gadon ya nuna min yana fadin “Zauna, Allah Ya sa lafiya?”

Murmushi na kirkiro ina fadin “Inspection na zo yi”

Ya yi dariya mai sauti yana kallon dakin nashi sannan ya ce “Na san ma ni ne zan na daya”

Ina zama gefen gadon na ce “How are you sure?”

“I’m very sure” ya amsa min, duk mu ka yi dariya, sannan na amsa gaisuwar da yake min.

Na ce “Zauna magana za mu yi”

Kai karshen maganar tawa ya yi daidai da zamanshi a kan center carpet din da ke tsakiyar dakin.

Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce “Magana za mu yi Khaleel, ban san yadda za ta zo ma da yadda za ka dauke ta ba, amma koma dai menene ina son ka yi hakuri don Allah ka yi addu’ar neman zaɓin Allah ban so abun ya zo a haka ba”

Kanshi a kasa komai bai ce ba, wannan ya sa na dora “Mun yi magana da Abbanku a kan yarinyar da kake so, I’m sorry to say bai amince ba Khaleel, na iyakar bakin kokarina amma ya ki amincewa, har ma ya ce min lallai ka je ka ga Hana ku daidaita, saboda ya yi magana da mahaifinta”

Komai bai ce min ba, kamar yadda bai dago kanshi ba, a sanyaye na ce “Ka yi hakuri Khaleel, haka Allah Ya hukunta, Mustapha Sandamu na da nagartar da za a so haɗa zuriya da shi. In Sha Allah idan Allah Ya sa aka yi auran nan za ka yi alfahari da zabin mahaifinka”

Komai dai bai ce ba, wannan ya sa na shiga kwantar mishi da hankali, har zuwa lokacin da na mike da zummar tafiya, dakin Baffa na buga, bayan ya bude na ce “Ka je ka zauna da dan’uwanka”

A firgice ya ce “Ba shi da lafiya ne?”

“Eh to ku san haka, Abbanku ne bai karbi zaɓinshi ba, kuma ya kawo mishi na shi zaɓin”

Shiru Baffa ya yi ba tare da ya ce komai ba, ni kuma na juya zuwa nawa sashen.

Gidan sai ya zama wani iri duk babu dadi, da yake zuwa lokacin kowa ya ji abin da ya faru, walwalar kowa ta yi karanci.

Ni dai tun da na yi mishi maganar ban sake cewa komai ba, amma duk wanda ya san Khaleel a baya, ya kalle shi yanzu ya san akwai damuwa. Ba shi da walwala ko karsashi gabadaya.

Yau da misalin karfe 12pm Bashir ya shigo gida, da alama wani abu gaggawa ne ya taso, kuma yau kama kwana uku da na yi wa Khaleel maganar zuwa wurin Hana, na san bai je ba, kuma ban kara yi mishi magana a kan ya je din ba. Ina Kitchen ya haura sama, ina kokarin barin kitchen din sai ga shi, wannan ya sa na ja baya, Maman Usi kuma ta gaishe shi cike da girmamawa sannan ta raba ta fice daga kitchen din

Fuska a hade ya ce “Me ya samu dakin Khaleel da zai zo ya kwanta a dakinki?”

“Ba shi da lafiya” na amsa mishi a hankali.

Ya kafe ni idanunshi masu kwarjini, wannan ya sa na janye nawa gefe a hankali “Abin da na ce ya yi?” ya kuma tambaya ta.

“Ka yi hakuri, ya so zuwa tun shekaranjiya, amma ba shi da lafiya, in Sha Allah ya ji sauki zuwa gobe zai je”

Kitchen din ya shigo sosai sannan ya ce “Khadija yau nake son Khaleel ya je wurin Hana ba gobe ba, kar ya wuce yau bai je ba. Umarni nake ba ku ke da shi”

“In Sha Allah” na yi maganar with respect

Juyawa ya yi zai fita kitchen din, Sai kuma ya juyo yana kallo na “I’m going to Abuja right now, so come and prepare for me”

Kai na jinjina alamar to, sannan na bi bayan. Sai da na kintsa shi tsaf, na rako shi, sannan na dawo dakina inda Khalil ke bacci.

Gefen gadon na zauna ina kallon yadda yake sauke numfashi peacefully, da alama yana jin dadin baccin “Khaleel!” na kira sunanshi

Kamar dama ba baccin yake ba saboda tsakanin rufe bakina da bude idanunshi ban san wanda ya riga wani ba.

“Ba ka bacci da dare ne?” na jefa mishi tambayar idanuna cikin na shi.

Sai da ya yi mika sannan ya ce “Ba sosai ba”

Fuska na ɗan hade kafin na ce “Wato ka sanyawa kanka damuwa ko? Sai ka je ka jawowa kanka wani ciwon”

Daga kwancen da yake ya ce “Auntynmu is not easy kana tare da mutum ace ka bar shi fa”

“Na sani, amma ka rika sassautawa”

Komai bai ce ba, ni ce na kuma cewa “Yanzun nan Abbanku ya fita, yana ta fada ba ka je wurin Hana ba, don Allah ka rufa min asiri Khaleel ka je yau, kai dole ma ka je, saboda ya ce yau ba sai gobe ba yake son ka je, kuma ni da kai duk umarni yake bamu”

Idanunshi ya dauke daga kallona ba tare ya ce komai ba. Na kara cewa “Ka ji abin da na ce ai?”

“Eh.” ya amsa min dakyar, na mike da zummar fita, maganar shi ta dakatar da ni “Wai Auntynmu wacece wannan Hanar? Ni fa ban san ta ba ma, ban san ma gidansu ba. Fisabilillahi haka ake yi, Abbanmu ya bar kowa ya zabi matarshi da kanshi sai ni ne za a ce in je in auri wata yarinya, idan ma ba za a yarda da preeta din ba, a bar ni in nemo wata da kaina mana “

” Khaleel! “na kira sunan shi, kai ya dago yana kallona ba tare da ya amsa ba

Wannan ya sa na ce” Hana ita ce diyar matar da ta rika dawainiya da Abbanku a lokacin da aka kwantar da shi asibiti, tsawon sati biyu kullum sai an kawo mishi abinci sau uku daga gidanta. Kuma ita ce wacce ta ba ni wurin kwana a lokacin da nake jinyar mahaifinku, ban taba kukan komai a gidanta ba. Kuma ita ce wacce lokacin da kuka zo duba Abbanku a asibiti ku kwana a gidanta. Maman Hana da mijinta mutanen kirki ne”

“To yanzu rama mata abin da ta yi mana aka yi, da tursasa ni in auri ƴarta?”

“Khaleel!” na kuma kiran sunanshi da alamun warning

Ya yi kasa da kanshi, wannan ya sa na ce “Ka je ka ga Hana yau din nan.period!”

Daga haka na fice daga dakin na bar shi, shi ma ba jimawa ya dakko don zuwa masallaci.

<< Hasashena 62Hasashena 64 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×