Skip to content
Part 64 of 66 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Misalin karfe biyu na rana duk mun hallara a part dina don cin abinci rana, Salman, Khaleel, Maama, Affan, Baffa. Ramla, Assidiq, Haidar da ƴan biyu kuma duk suna makaranta.

Salman rungume da Khairiyya yana cin abinci ya ce “Wai Khaleel lafiya, ka yi cool da yawa”

Baffa ya kalle shi kafin ya ce “Wai fushi yake yi an zaɓa mishi mata, ni ina ma ni aka yi ma wannan gatanci, neman mata isn’t easy, ga Shi nan kowa ya samu ya bar ni.

Dariya Affan ya yi sannan ya ce” Kai ma ruwan ido ne ya hana ka, amma duk ƴanmatan da ke Katsina, Kaduna da Abuja ba ka ga matar aure ba”

Ya yi saurin cewa daga lokacin da Abbanmu ya ce kowa ya kawo matar aure duk na daina ganin su”

Ni da Maama da Salman mu ka yi dariya. Ban da Khaleel da ke tsakurar abinci a hankali.

Salman ya ce “Ni ka shirya in raka ka, kake ta wani bata rai, ka ji Baffa ya ce gata aka yi maka”

Maama ta yi zaram ta ce “Aiko sai dai Baffa ya raka shi, daga nan ma ya samo tashi”

Na ce “Me ya sa shi Salman din ba zai je ba?”

“Ba komai.” ta amsa min tana ci gaba da cin abincinta

Affan ya ce “Karya kike yi munafuka, idan dai ba komai to sai ya je”

Na ce “Wlh kuwa Affan”

Fuska ta shagwaɓe ta ce “Auntynmu gidan nan ƴanmata ne da su da yawa wlh, gasu kyawawa, har da wata mai kama da Indiyawa, abu da sun zo sunan Khairiyya na gansu”

Kafin in yi magana Baffa ya ce “Da gaskiyarki ƴar nan, wannan rakiya ni ya kamata in yi ta, ba mamaki mu daidaita da wata a cikinsu”

“Shi ma Salman din sai ya je” na yi maganar babu alamar wasa

Kamar Maama za ta yi kuka ta ce “Kai Auntynmu don Allah!”

Ina kallon ta na ce “Sai fa ya je”

Salman dai dariya yake kasa-kasa

Juyowa ta yi sosai tana fuskantata ta ce “Wlh Auntynmu ƴanmatan gidan nan kyawawa ne, ba ki kalli wadanda suka zo sunan Khairiyya ba, wacece mummuna. Don Allah Auntynmu kar ya je. Da Momy na nan da tuni ta ce ba zai je ba”

Na ce “Ai ba ta nan”

Baffa ya ce “Auntynmu Maama fa da gaskiyarta, don haka Salman ya zauna ni ne nan zan yi wannan rakiyar”

Maama ta yi saurin cewa “Yauwa Ya Baffa”

Nan na bar su, suna hirarsu na haura sama don taɓa ƙailula.

Ban tashi ba sai 4pm,ina kan sallaya around 4:30pm Khaleel da Baffa suka shigo cikin shiri, na kalle su dukkansu, Baffa ya ce “Auntynmu mun fita”

Kai na jinjina alamar eh, ina kara kare masu kallo, Khaleel dai cikin wani royal blue din yadi yake, wanda aka yi wa dinkin zamani mara hayaniya, sosai kayan suka kwanta jikinshi, hular kanshi ma blue ce 6ar ubansu, yadda ya tsayar da hular ba karamin kyau ta kara mishi ba. Kamshi turarenshi mai dadi yana bin shi.

Baffa kuma Ashe color din yadine ya sanya dinkin zamani, dukkansu sun yi kyau wanka ya bi jiki

“Ki bamu address din” cewar Baffa

Na shiga kwatanta musu gidan har sai da na tabbatar sun gane, sannan na basu contact din Maman Hana na ce koda za su bata.

Sannan na ce “Khaleel, ina hada ka da girman Allah kada ka yi abin da ka san bai dace, ko idan mun ji ba zamu ji dadi, please and please.”

Komai bai ce ba, Sai ma ficewa da ya yi daga dakin, na kalli Baffa ina fadin “Don Allah Baffa kar ka bari ya wulakanta yarinyar nan”

Ya ce “In Sha Allah ki kwantar da hankalinki Auntynmu, everything will be perfect”

Kai na jinjina sannan na ce “Allah Ya sa a dawo lafiya”

Ya amsa da amin hade da ficewa.

Duk sai na ji ni ban da nutsuwa, kamar in bi bayansu a yi komai a gabana, har sai da Maama ta fahimci hankalina baya jikina, ta na ba Khairiyya nono ta ce “Auntynmu wai na ga duk kin damu”

Kallon ta na yi kafin na ce “Hankalina yana wajen Khaleel Maama, kar ya yi abin da bai dace ba, ji nake kamar in bi su”

“Hummmm! Don ma dai abin da kake so, amma ni Auntynmu ban ga makusa a jikin Hana din nan ba. Kin ganta kuwa?”

Kai na girgiza alamar a’a

Ta ce “Da fa ita aka zo sunan Khairiyya”

“Wlh ba zan iya tantance ta ba Maama, kin san ƴanmatan da yawa, kuma duk ta fada min sunan sunansu, amma ban rarrabe da su ba”

Zamanta ta gyara sannan ta ce “Aiko sai kin ganta kyakkyawa, ga nutsuwa final year take, ban dai san abin da take karanta ba, amma ta ce min bana za ta gama”

“To Allah Ya sa su daidaita, ba na son a yi wa yaron nan dole”

Shigowar su Ramla ya yanke mana hirar, Sai kuma ga Assisiq da Haidar, shi kenan suka mantar da ni damuwar Khaleel.

Ina kwashe kayan Khairiyya da suke waje su Baffa suka dawo, gabana ya rika faduwa dam-dam, Baffa sai washe min baki yake yi, a famfon waje ya tsaya zai yi alwalar magriba ya ce “Auntynmu akwai labari, bari in dawo masallaci”

Ina kallon Khaleel da fuskar shi take ba kuka ba guda na ce “to ina jira.”

Ana idar da sallah kuwa sai ga shi sun shigo gidan su dukkansu har da Affan da Salman

Suka yada zango a falona, ina kallon Khaleel da ya kwanta silently kan kujera na ce “Khaleel Hanan ba ta yi ba ne?”

Baffa ya yi caraf da fadin “Alkur’an karya yake ya ce wannan yarinyar ba ta yi ba, ba ta da makusa”

Maama ta ce “Auntynmu ba na fada miki ba”

Baffa ya kuma cewa “Maama ba ki yi karya ba, gidan nan kwai ƴanmata kyawawa wlh, kamar su suka yi kansu, muna, ta, wahala da gantali ashe kyawawan mata na cikin gida an rufe su. Na ga mai kama da India din nan”

Ya karasa maganar yana kallon Maama, dariya ta yi ta ce “Ya ka gan ta?”

“Allah Ya yi halitta kawai Maama, magana ta domin Allah ina ciki Auntynmu. Amma sai idan Khaleel ya karbi Hana, idan bai karba ba, gaskiya ni a ba ni ita, wlh, da gaske nake yi ina sonta. Yarinya cool beauty haka, ga nutsuwa. Ai mutum ya samu wannan kawai Allah Ya sallame shi. Ni ina so idan ba ya so wlh”

Duk Khaleel muke kallo wanda ya hade fuska yana tattaba wayar shi

Baffa ya kuma cewa “Allah Auntynmu da gaske nake yi, idan har bai karba ba, ni na karba hannu biyu-biyu, in ya so ya dauki waccan kalar India din, idan indiyawan yake so”

Dogon tsoki Khaleel ya ja, su Affan suka fashe da dariya Assidiq ya ce “Wato Ya Baffa yarinya dai ta kawo light”

“Sosai fa, macece duka dauka, shi kanshi Khaleel ya san babu inda zai ce wannan yarinyar ba ta wanku ba.”

“Ka ce kare mata kallo ka yi” cewar Haidar

“From head to toe kuwa”

Filon kujera Khaleel ya jefa mishi, cike da jin haushi ya ce “Aiko ba ka kara bi na yasin”

Duk mu ka yi dariya Baffa ya ce “Wlh karyarka, abun da na san hanya, ni kawai jira nake ka ce ba ka so in dauka”

Wani tsokin Khaleel ya ja hade da ficewa daga falon, mu ka kuma yin dariya, Baffa ya ce “Ɗan rainin wayau, Sai wani basarwa yake yi, ai ina sane nake fadin haka, tun a mota nake yaba ta, don kawai in kunna shi, tun da na fara yabonta ya hade fuska, har mu ka iso gida bai kara magana ba”

Mu ka kuma yin dariya Salman ya ce “Ba ka da kirki Baffa”

Dariya ya yi hade da kwantawa saman kujera ya ce “Auntynmu a ji da ni kan yarinyar nan kalar India, na fa kyasa”

“Sai ka sanar mata ai”

“Ai wai ki shige min gaba, kin san idan kana da god father a wuri, komai ya fi zo ma da sauki”

“Shi kenan zan yi magana da Maman Hana in ji”

Da sauri ya ce “Allah dai ya biya uwa ta gari, sunan yarinyar Hajara, amma Maama ake kiranta. Duk sunansu daya da Hanan Khaleel”

Kai na jinjina hade da mikewa na nufi dakina, in samu in huta, idan ina falon bakina ba zai yi shiru ba.

Da kaina na kira Maman Hana a kan maganar Baffa, kuma ta tabbatar min ba a yi wa Maama miji ba, don haka kofa a bude take, idan da amince da shi babu damuwa. Time da na sanarwa da Baffa yadda mu ka yi, ba karamin farin ciki ya yi ba.

Shi kam bilhakki yake neman amincewar Maama, gogana ne dai ya zama miskilin karfi da yaji a kan Hana, shi ba za ka ce ba ya so ba, kuma ba za ka ce kai tsaye yana so ba.

Yau Alhamis da misalin karfe 4pm na yamma zaune mu ke a falo, mazan dai kallon ball suke yi, ni kuma da Ramla muna hada humra ne, Ramla ta ce “Ya Baffa ya kamata gobe a kai mu, mu gano su Aunty Maama da Aunty Hana”

Zaune ya mike daga kishingiden da yake sannan ya ce “That’s good idea my dear, kira ƙi sanar mata”

Wayarta da ke kan kujera a bayanta ta janyo hade da aikawa Hana kira, ta saka a hands-free. Tattausar muryar Hana ta bayyana cikin wayar dauke da sallama, Ramla ta amsa tare da yin gajeruwar gaisuwa sannan ta ce “Gobe kuna gida ne?”

“Eh. Wani abu ne?”

“Za mu zo muku yawon juma’a ne”

Muryarta ta bayyana dadin da ta ji, ta ce “Da gaske?”

“Allah da gaske”

“Kai aiko na ji dadi, ke da wa?”

Ramla ta amsa da “Ni da Hassana, Husaini, Ya Affan, Ya Salman, Ya Baffa, Sai kuma Ya Khaleel ko kar ya zo?”

Cikin siririn murmushi Hana ta ce “Ke kika sani”

Ramla ma ta yi murmushin sannan ta ce “Ai gara in nemi permission Idan ba ki so, ya yi zaman shi”

“Sai an jima, ki gaishe da kowa” cewar Hana, har lokacin da dariya a muryarta

Ramla ta yi saurin cewa “Dakata Aunty Hana, ban gane ba, wai ko ba kya son Yayan nan nawa ne, na ga ba kya maganarshi”

“Kina da problem Ramla, don Allah ki kyale ni”

“Allah sai kin fada min”

Dariya Hana ta yi hade da yanke kiran, mu ka kalli Khaleel wanda ya hade fuska kamar baya wurin. Salman ya ce “Yarinyar nan ba ta yin ka Khaleel”

Juyowa ya yi yana kallon Salman sannan ya ce “Ta yi wa kanta”

Baffa ya yi saurin cewa “Ka dai yi wa kanka, kuma kar ka sake ka yi mana bukulu wlh, tun da ka bari na furtawa yarinyar can ina sonta, to kuwa dole ka so wannan, ai sai da na fada ma idan ka san ba ka sonta ka matsa ka ba ni wuri ni.”

Affan ya ce “Bari idan na ganta gobe ni sai mu daidaita in ya so in hada su da Maryam.”

Dogon tsoki Khaleel ya ja ba tare da ya ce komai ba. Haka su ka yi ta tsokanarshi, suna kara kunna shi.

Ranar Juma’a da misalin karfe 11am Zahra ta iso weekend, wannan ya tabbatar min da Bashir yana hanya, idan ba zai dawo ba, na san ita ma ba dawowar za ta yi ba.

Ana sakkowa masallaci, su Affan suka tafi gidansu Hana, bayan sun tafi ne nake ba Zahra labarin abin da ya faru.

Da mamaki ta ce “Ikon Allah, wato gidan nan ko wuni ka yi ba ka nan, idan ka dawo sai ka iske wani abu sabo, yanzu kawai tafiyata sati biyu, shi ne duk wannan abun ya faru, to Allah Ya tabbatar da alkairi”

Na amsa da amin, sannan mu ka shiga tattauna batun aikin Khaleel, da Affan, mu ka Koma kan batun tafiyarmu Saudiya, saboda lokaci na ta kara matsowa.

Yaran basu dawo ba sai magriba, ko wanne fuska dauke da fara’a, Ramla ta shiga ba ni labarin irin karamcin da aka yi musu, har da take away din abin da aka basu aka yi wa Hana, dama na yi tunanin haka, Maman Hana akwai karamci.

Lokaci nata tafiya, yayin da ake ta cimma wasu burukan, wasu kuma lokacin kan wuce ba tare da an cimma su ba. A haka Maama ta gama wanka, ta goma gidan mijinta. Aka kuma samar mata aiki a FMC Katsina. Affan ma a can ya samu aiki a matsayin ENT doctor, Salman kuma ya samu aiki, da kamfanin zirga-zirga na kasa da ke Abuja. Don haka sai godiya kawai.

Duk karshen wata Khaleel ke zuwa gida, wani lokaci kuma sati biyu, kamar yanzu ma da ya zo mana weekend, yana ta shirye-shiryen komawa wurin aiki kuma. Ina zaune a daki Khairiyya na wasanta, kasancewar idan Maama za ta je aiki nan take kawo ta, Sai ta dawo ta biyo ta dauke. Maman Usi ta kwankwasa kofa, kai tsaye na ce ta shigo, bakin kofa ta tsaya a, ladabce ta ce “Dama kasuwar ƴarkutungu zan je”

Hankalina na mayar a kanta, sannan na ce “Lafiya ko?”

“Yallaboi Khaleel ne ya ce in siyo mishi fara tiya biyu”

Da mamaki nake kallon ta na ce “Shi Khaleel din?”

Kai ta daga min alamar eh, na ce “To sai kin dawo”

Har ta tafi mamakin abun nake yi, me Khaleel zai ci da fara har tiya biyu, mutumin da ko ganin ta baya son yi.

Bayan Maman Usi ta dawo kasuwa, su Ramla suka taya ta ta gyara farar tas, ta soya, suya kam ta yi dadi, don ko ni sai da na ci. A cikin farin bucket ta zuba mishi, ragowar da ta rage kuma ta ajiyewa su Ramla, da Maama. Don Maama a cikin abincinta na dare ta zuba, kamar wani nama. Tun da ta dawo aiki take cinta, ba ta ko gajiya.

Yanzu ma da muke zaune masu cin abinci na yi, masu kallo na yi masu taba waya na yi Salman ya ce “Wai ina aka samu fara ne?”

Take ya tuna min da abin da nake son tambaya tun dazu don haka na ce “Wai Khaleel yaushe ka fara cin fara ne? Na ga ganinta ba ka son yi, amma shi ne har da sayen kwano biyu”

Duk suka mayar da kallon su kanshi, ba tare da ya mayar da hankali a kan batun ba ya ce “Waccan yarinyar ce ke so”.

<< Hasashena 63Hasashena 65 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×