Ku san a tare mu dukkanmu mu ka ce “Wace yarinyar?”
Ya dago kai yana kallonmu, kila yadda mu ka muhimmantar da abun ya ba shi mamaki, bai amsa ba ya ci gaba da danna wayarshi Maama ta ce “Wai Hana”
Hankalinshi a kan wayar ya ce “Eh.”
Duk sai mu ka yi dariya, Baffa ya ce “Gulmamme, ana so, ana kai wa nesa”
Maama kuma ta ce “Wai ta koma Abujan ne?”
Ya kuma daga kai alamar eh.
Cikin tsokana ta ce “A can kuke tsinkar furen kenan, ah wannan abu ya kawo light, ashe har an yi nisa haka mu ba mu sani ba”
Harara ya rika aika mata, Salman ya ce “Gaskiya fa ta fada malam, babu wani jan ido da za ka yi a nan, ga shi nan an fara aikenka wlh da a gidan nan ne wani ya ce ka sawo fara a soya a kai mishi Khaleel ba za ka yi ba, koda kuwa ba da kudinka ba ne, amma ga shi nan kana sayen har kwano biyu”
Cikin dariya Affan ya ce “A nan kuma Maama da Ya Salman gaskiya suke fada”
Baffa ya ce “Yo Wai tun yaushe, ai ya dade da mika wuya, Auntynmu sai dai ki bi yaro da addu’a amma an rike shi a wuya yasin. Ko miyau zai haɗe sai da izninta”
Gabadaya mu ka yi dariya, ni kuma na mike ina fadin “Ai ni haka nake so, Allah Ya inganta”
Duk suka amsa da amin, idan ban da Khaleel da yake ta ciccijewa, su kuma suna kara tsokanarshi. Misalin 8am, Maama ta zo ta yi min sallama za su wuce gida.
A satin Bashir ya dawo ya zo min da maganar an tsayar da bikin Khaleel, Baffa, Ramla, da Affan watanni biyar masu zuwa, da na lissafa sai na ga ya kama mun dawo aikin Hajji da sati biyu kenan.
To yanzu kam mun fi mayar da hankali a kan abu biyun nan, biki da tafiyarmu Saudiya.
Bayan sallahr azumi ne mahajjata suka fara tafiya, Bashir ta tura mota aka dakko Umma, da yake da gwamnatin Katsina aka yi mata register. Inna ma ta zo, mu ka hadu mu ka fara zuwa bita, wani lokaci kuma malamin ke zuwa, har gida ya tara mu, ya kara fadakar damu. Har zuwa lokacin da maniyyata suka fara dagawa aikin Hajji, jirgi na uku da mu ya daga.
A karo na biyu da na zo ƙasar Saudiya, a wannan karon ba Umra ba sauke farali, farin cikin da nake ciki baya misultuwa gami da shauki.
Haka mu ka rika gudanar da ibada kamar yadda addini Islama ya tanada, ba ganda ko kuna damuwa a kan wani sabon canji da mu ka riska. Misali turmutsutsu da zafin rana.
Watanmu daya a Saudiya mu ka dawo gida, in da kuma mu ka fada hidimar bukukuwa, ga na Maryam kanwata, wanda za a yi bayan na su Khaleel.
Rahma sun baro India sun dawo Abuodon hidimar biki, ya rage saura sati daya mu ka kai lefen Affan, Khaleel da kuma Baffa. Mun kai nasu da kwana biyu aka kawo na Ramla.
Gida fa ya dauki harama, saboda Anguna da Amare sun fara shagalin bukukuwansu.
A wannan karon ma komai cikin tsari, babu rashin kunya ko yin abin da bai dace ba.
Ranar Alhamis da ya kama gobe daurin aure gida a cike, baƙi ta ko ina, Zahra can da ta tawagarta ni ma nan da tawa. Ranar Juma’a dubban mutane suka shaida daurin auran su Khaleel, abu kamar a mafarki, na aurar da Baffa da Khaleel. Na dade Ina addu’ar Allah Ya nuna min wannan rana to ga shi dai Allah Ya nuna min.
Misalin karfe uku Anguna su Khaleel suka Khaleel suka shigo gida daga wurin daurin aure, da yake nasu aka fara ɗaurawa, sannan aka wuce aka ɗauro na Affan.
Ina daki ina fitar da gifts din yan biki suka shigo shi da Affan, kamshin turarensu ya sanya ni ɗagowa, dukkansu shar cikin fara tas din dakakkiyar shadda wacce aka yi wa dinkin babbar riga, hularsu fara, agogon hannunsu ne golden, amma hat takalmin kafarsu half cover fari ne.
Sun yi kyau sosai fiye da ko wace rana, kasancewar dakin ku san a cike yake da ƴan’uwana da kuma ƴan’uwan Mamanshi sai suka shiga rangada masu guɗa.
Yayin da ni kuma bakina ya kasa rufuwa, har suka karaso wajena, na bude hannayena na rungume su gabadaya, Sai gamu muna hawaye, daga nan ƴan’uwan Sakeena ma suka kama kuka, shi kenan daki ya koma koke-koke maimakon gudar da aka fara. Sai da aka fitar da su Khaleel ni kuma Ya Harbi ta zaunar da ni gefen gado ta ce “Haba Khadija ai yau ranar murna ce ba ta kuka ba, a yau dai amanar da kike cewa Sakeena ta ba ki, kin sauke nauyi, kin rike mata yara tamkar naki, duk wani fadi tashi kuna tare, yanzu ga shi Allah Ya kawo ranar aurensu, ba tare da sun taɓa dakko miki wani abuj kunya ba, to murna ya kamata ki yi. Mu kuma mu gode miki, Allah Ya saka miki da alkairi, halinki na gari ya bi ki, ya jikan magabata, ya ci gaba da dafa miki wajen sauke nauyin da ya hau kanki “
Haka ta yi min nasiha ba ita kadai ba, har da wasu manyan ƴan’uwan Maman Khaleel, irin manyan yayyata kannen mahaifiyarta da kannen Babanta. Sosai na yi kuka, kuma ni kaina na san na farin ciki ne, da Allah Ya nuna min ranar auransu Affan da raina kuma da lafiya ta.
Haka shagalin biki ya ci gaba da gudana, misalin karfe shidda kuma motar amare ta shigo, amma ta Baffa da Khaleel, ta Affan kuma basu karasa bo
Part dina aka fara kawo su, wai in yi musu fada, ni kam komai ban ce ba, mutanen ɗakin suka yi magana, daga nan aka kai su part din Zahra, ana kokarin fita dasu zuwa gidajen mazajensu motor amaryar Affan ta shigo, nan din ma dai mutane suka yi mata nasiha aka kai ta bangaren Zahra, daga nan aka wuce da ita gidan mijinta
Ramla dai dama sai Asabar za a wuce da ita.
Zuwa safiyar Asabar din hatta muryata ba ta fita, saboda hayaniya lallai na san na aurar ƴaƴa, haka ma mutane ke tsokana ta, wai yanzu na aurar da ƴaƴa. Ni kaina na yarda da hakan hidimar ba karama ba ce.
Misalin karfe 10am aka rako Ramla daga gidan Maama, wai mu yi sallama za a kai ta gidan miji, to anan fa matar ta kada mijin.
Dama a kaf auran babu na wanda yake daga min hankali irin na Ramla, Allah Ya sani ina son Ramla ba na son ta yi nesa da ni, ji nake ina ma Maama ce za a kai India din nan Ramla a nan.
Ina zaune gefen gado ina ta jin yadda mutane ke ta yi mata fada da sanya mata albarka, kafin aka matso da ita wurina, a hankali na bude fuskarta, idanunmu suka hadu, yadda idanunta su ka yi jage-jage alamar ta ci kuka ta gaji, hakan ba karamin kara narkar min da zuciya ya yi ba.
Da kyar na ce “Allah Ya yi miki albarka Ramla, Ya albarkaci rayuwar auran ki, don Allah ki yi amfani da duk nasihar da aka yi miki.” shiru na yi ina sakin mayafin nata, saman cinyata ta kwantar da kanta, ta shiga rera kuka, yayin da nake ta kokawa da nawa ruwan hawayen. Mutane kuma na ta kara ba ta hak’uri
A cikin kukan ta ce” Auntynmu a kira min su Yaya Affan, ban gan su ba, ban son in tafi ban gansu ba”
Nan da nan aka shiga yekuwar neman su Khaleel, kamar 10mns Khaleel ya shigo, har zuwa lokacin Ramla na kwance a kan cinyata. Tun daga kofa ya ce “Auntynmu wai in zo?”
Mutanen cikin dakin ne suka ce “Ƴar’uwarka ce ke neman ku, wai ba ta son ta tafi ba ta gan ku ba, ina ɗan’uwan naka?”
Take na ga Khaleel ya yi sanyi, kamar mai koyon tafiya ya karasa shigowa dakin, ya duko daidai saitin Ramla ya ce “Ga ni Ramla ya aka yi”
Hannunshi ta riko hade da fashewa da sabon kuka, cikin kukan ta ce “Ya Khaleel ba na son tafiya, ban son in tafi in bar ku, ni dai na fasa auran nan”
Sosai ya durkusa kusa da ita, cikin sigar lallashi ya ce “Ki yi hak’uri Ramla, muma ba ma son ki tafi, amma tafiyar ta ki a wani bangare abun alfaharinmu ne, saboda ci gaba kika samu. Kin san waye Adnan ai, yana sonki, kuma a can din ma akwai Baba Nura fa, ga Momyn Farhan, ga Farhan Ga faruk da Ya Yusuf, sannan za mu rika zuwa muna ganin ki muma, ki kwantar da hankalinki Ramla, kina zuwa babu dadewa za mu je mu ganki kin ji ko? “kai ta jinjina har zuwa lokacin tana kuka, ni kaina hawayen nake daukewa masu dumi, ya mike da ita hannunshi a cikin nata, daidai lokacin Affan ta shigo, aiko sai ta fada jikinshi ta kuma sake kuka. Irin kukan nan mai ban tausayi, Sai ga shi mutane da yawa suna matar kwalla, a haka Khalil da Affan suka janye ta, zuwa dakin Abbansu, daga can aka kai ta wurin Zahra, sannan aka wuce da ita.
*****
A hankali kaina ya fara ciwo ina daurewa, saboda sallamar baki da muke ta yi, saboda Zahra ta na cikin ƴan rakiyar Ramla Abuja, haka ma Maama, shi ya sa hayaniyar ta kara yi min yawa.
Zuwa la’asar dai gidan ya ragu sosai, idan ka dauke masu zuwa Allah Ya sanya alkairi. Kan nawa ma ya yi sauki da yake Salman ya kawo min magani, safiyar Monday ma haka na dora sallamar bakin da suka rage, zuwa azhur dai gidan ya koma namu, amma har lokacin akwai masu zuwa Allah Ya sanya alkairi. Ni dai wani irin ciwo kaina ke yi. Ina daki Bashir ya kira ni wai in same shi part din shi. Part din da Sai idan ana irin wannan taron yake shiga, amma haka nan dai a part din mu yake bacci, tun da yana da dakinshi.
Tun da na shigo yake kallo na, a gajiye na zauna gefen gadon hade da dafe kaina.
“Ba ki da lafiya ne?” ya tambaye ni cike da kulawa
Cikin dusassar muryata da ta kara dushewa na ce “Kaina ke ciwo”
“Subhnallah sannu, pressure ce kawai da stress, ai an sha hidima, kin sha magani ko?”
Kai na jinjina mishi, ba na son yin magana, saboda yadda muryata take, wahala nake ci
Ya kuma cewa “Zan je Abuja ne yanzu”
Baki na tabe kafin na ce “Haka dai, from Monday to Friday, Allah Ya kiyaye hanya”
Murmushi ya yi hade da zama gefena ya ce “To idan na zauna me zan yi miki? Ke fa yanzu kin girma har da jika gare ki”
Ni ma murmushin na yi ba tare da na ce komai ba.
Jikinshi ya rungomo ni yana fadin “Daga karshe dai Allah Ya cika burin Khadija, na son zama shugaba mai cikakken ƴanci a gidan. Duk abin da za a aiwatar sai da cewarta, duk wata shawara da ita ake yi, duk wani hukunci da ita ake yanke shi, duk wata sabga sai da ita a ciki. Na taya ki murnar cikar wannan burin naki. “
Murmushi na yi cike da jin dadin abin da ya fada, tabbas wannan shi ne burina, kuma ba ni kadai ba, burin ko wace mace a gidan mijinta, mace da aka ware gefe ba ta san komai na gidanta ita za ta fahimci cewa, hakan ba karamar damuwa ba ce. Babu abin da zan ce kam da ya wuce godiya ga Allah da ya kawo ni wannan matakin, ba tare da bin wani malami ko boka, kawai hakuri, juriya hade da jajircewa sune suka kawo ni.
Jin ban yi magana ba ya kuma cewa “Ina alfahari da ke Khadija, har yanzu ina sonki, ina kuma kara kaunarki, kowa ya bude baki alkairinki yake fada. Da irin rawar da kika ta ka, musamman a rayuwar su Khalil, ina fatan rikon da kika yi musu, ya zama shi ne sanadin shigar ki aljanna. Na gode sosai da zama mace ta gari a gare ni. Da ke yara hudu na aurar wadanda nake alfahari da tarbiyyar da kika basu. Na gode sosai Allah Ya jikan magabata, ya biya ki da gidan aljanna “
Da dusassar muryata na ce” Amin Ya Rabbb, na gode sosai “Ina son yin dogon sharhi amma ban iya wa, saboda muryata.
Ina zaune a gefe gadon ya shiga bayi, har ya fito ya shirya ina zaune ban tashi ba, bayan ya gama shiryarwa ne tsab ya ce” Akwai abin da kuke bukata ne? “
Kai na shiga girgizawa, alamar a’a, yayin da shi kuma yake daddana wayar shi, ya dago kai yana fadin” Ga kudi nan na tura miki saboda yaran nan, sun sha hidima, ba lallai akwai kudi a hannunsu ba yanzu. Ki ba ko wannensu 200k kafin in dawo, a siyo musu foodstuff “
” sun gode sosai Allah Ya saka da alkairi “na yi maganar hade da mikewa, Sai dai kafin in daidaita kafafuna na tafi luuu! Bashir ya yi saurin tare ni yana fadin” Subhnallah! Me ya faru? “
Daga kwancen da nake jikinshi na ce” Jiri nake ji”
A hankali ya mayar da ni saman gadon ya zauna, lokaci daya kuma yana kan ga wayarshi a kunne alamun kira.
Bayan ya sauke wayar ya shiga jero min sannu, yana shafa gefen fuskata, ba jimawa Adnan ya shigo cikin dakin dauke da sallama, bayan sun gaisa da Bashir, Bashir din ya shiga rattaba mishi abin da ke damuna.
Fuskar shi dauke da damuwa yake kallo na, a, hankali ya ce “Stress ne, zan je gida yanzu in zo” ya yi maganar yana aika min da sannu, na amsa a hankali, bayan fitarshi ba jimawa Affan ya shigo, gefen gadon ya zauna yana taba wuyana, kafin ya ce “Kawai stress ne, Idan ta samu bacci, Sha Allah za ta warware”
Muna zaune a wurin sai ga Khalil da Assidiq, can kuma Haidar ya shigo tare da Salman. Duk fuskarsu babu walwala.
Affan ya karbi abun awon ya yi min awon low bp Amma normal, ya juya kan high bp nan ma normal. Yau auna temperature ta, ya juya kan malaria.
Bayan duk ya gama ya ce “A sanya mata drip, Idan ta samu, bacci za ta tashi normal sha Allah”
Salman ya ce “Ok” suka shiga hidimarsu ta kwararrun likitoci, bayan sun gama, Baffa ya daura min drip din.
A hankali na ce “Kar ku fadawa Ramla da Maama fa” Khaleel ya amsa da to, duk suka zagaye ni suna aika min da sannu. Tun ina ganin duhunsu har bacci ya dauke ni.
Ban farka ba, Sai wajen biyar na yamma, zuwa lokacin kaina babu ciwon nan, jikina ne kawai ba kwari, ga wata baƙar yunwa da na farka da ita jikina har rawa yake yi. Ban yi mamaki ba, saboda dama tun da aka rufa sabgar nan, ba na iya samun damar cin abinci cikin kwanciyar hankali.
Daidai Bashir ya shigo dakin, da alama waya ya fita ya yi. Da mamaki nake kallon shi na ce “Ba ka tafi Abujan ba?”
Ya ce “Wace Abuja, shugabar gida ba lafiya, ba zan iya tafiya in bar ki ba.”
A sanyaye na ce “Yunwa nake ji”
“Me za ki ci?” ya yi saurin tambaya ta.
“Tea first” na amsa shi, da kanshi ya kama ni zuwa toilet na yi brush, kafin ya kuma zaunar da ni gefen gadon.
yana kokarin hada min tea din su Khaleel suka shigo, Affan ya karbi aikin, da kanshi ya rika ba ni, har na shanye karamin cup din, suna aika min sannu, haka suka ta sani a gaba na yi sallah, kafin na ce zan koma ɗakina. Still haka suka biyo ni, Khaleel ya dafa min indomie, ina cin indomien su Zahra suka dawo, duk yadda suka shigo da kuzari, ganina duk sai suka yi lakwas, tun ba Maama ba. Haka ma Khairiyya, duk rashin jin nan babu.