Skip to content
Part 7 of 8 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ina shiga Ramla na fara dauka da ke koyon tafiya a falon.

“Kin dawo? Na kira layinki ba a daga ba,.” Cewar Maman Khalil  a lokacin da take fitowa daga kitchen

“A gida na manta ta.” na ba ta amsa ina kokarin zama

“Aiko kin tashi hankalin Abbansu Khalil, har asibitin ya je, aka ce kuma kin taho”

Shiru na yi komai ban ce ba, saboda ni haushinshi nake ji. Asibitin ma bai iya kai ni sai matarshi. Idan da ace daya daga cikin yaranshi ne ba lafiya, shi zai kai su.

“To ya jikin?” ta katse min tunanina

“Akwai sauki sosai, malaria ce.” na amsa ta

“To Allah ya sawake.” ta yi maganar hankalinta a ka wayarta da bakuwar yarinyar can ke mika mata.

“Eh, ta dawo, ta manta wayarta a gidana ne.” ta dan yi shiru, Sai kuma na ji ta ce

“Malaria ce aka ce”

“OK” ta kuma fada, hade da yanke kiran ta ce min

“Ya ce ki dauki wayarki zai kira ki”

Yanzu ma ban bi ta kan maganar tata ba na ce

“Akwai ɗan abun tabawa kuwa?” saboda sosai wata irin yunwa nake ji

“Ba za a rasa ba, bari a yo miki kala”

Zobo ta kawo min da dambun nama ya ji kayan hadi sosai.

Muna taba yar hira ina ci da zobon har na cinye, na kora maganina, sai na dakko filon kujera na aje a kasa na kwanta, ba da dadewa  kuwa bacci ya dauke ni.

A cikin bacci na ji muryar Abbansu Khalil yana fadin

“Ya jikin nata?”

“Da sauki.” Ta ba shi amsa

“Sosai saukin, na kira wayar ba ta daga ba.”

“Ai ba ta koma ɗakin ba ma, bacci ya dauke ta” ta amsa shi

“Na manta ban ba ku kudin zuwa asibitin ba.”

“Ai  na ba ta wasu kudi a wurina, ban sani ba ko sun ishe ta.”

“Na gode miki Sakeena, Allah ya saka miki da alkairi kina bin duk wata hanya da zan samu kwanciyar hankali. Da ace du mata za su su yi koyi da irin halinki to da ko wane gida an zauna lafiya. Sannan babu wata mace da za ta tsoraci kishiya.”

Na dan bude idona, don so nake in ga yanayin fuskarta, irin wannan yabo da ta sha.

Da alama tun sa’adda ya fara maganar murmushi take yi har zuwa lokacin da ya kai karshe.

Ga ni na yi ta matso dab da shi, hade da kama hannayenshi biyu suna fuskantar juna

“Abban Khalil ni ce zan gode ma, in yi ma addu’ar fatan alkairi a ko wane lokaci. Zaman lafiyar gida miji ne ke samar da shi, ba ka wulakantani ba ka juya min baya ba, ba ka watsar da lamarina dana yarana ba, ba ka canja ba daga yadda na sanka ba. Wai don ka yi aure, sabanin wasu mazan da kan nuna yaransu da matansu duk basu da wani sauran amfani a wajensu, saboda sun yi sabon aure.”

Sai kuma na ga sun yi hanyar bedroom rike da hannun juna.

Na karasa bude idona ina bin kofar da kallo,, zuciyata tana daci, kishi mai zafi ya taso min.

” Me zai faru a ciki?”

Ita ce tambayar da nake wa kaina

Ji nake kamar in fada cikin dakin ba tare da sallama ba.

Na sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da yunkurawa na mike dakyar zuwa bangarena.

Alwallar sallahr la’asar na yi, don kuwa a lokacin karfe hudu da rabi na yamma.

Bayan na idar da sallahr na kwanta kan sallaya, babu abin da yake min dadi, haushin kowa da komai nake ji, wannan kuwa ba ya rasa nasaba da har zuwa lokacin Abbansu Khalil na bangaren Maman Khalil bai leko ni ba.

“Ya Allah ka rangwanta min wannan kishi.” Na yi maganar a hankali hade da gyara kwanciyata a kan sallayar.

Daidai lokacin kuma aka kwankwasa kofata, na mike jiki ba ƙwari na nufi kofar.

Duk yadda na so in saki fuskata na kasa, time da na bude na gansu tsaye, ko farantin hannun Maman Khalil ban amsa ba, na juya ita ce ta je kan dinning ta aje min tana kara tambayata

“Ya jikin!?”

“Da sauki” Na fada a hankali

Rashin ganin fuska ya sa ta fice, ba tare da ta kuma cewa komai ba.

“Deejanah!” ya kira sunan a hankali cikin salon da yake tunani zai kashe min jiki

A maimakon hakan ji na yi kamar in mike in yi ta kwasheshi da mari sai na ga bakinsa yana jini.

“Deejah!” Ya kuma kiran sunan hade da matsowa kusa da inda nake zaune ina karkada kafa rai bace kamar yaki ya rigani kofar gida.

Janyo ni zuwa jikinsa ya yi, yana fadin “Sorry yau kuma me na yi, irin wannan fushi haka?”

Na kwace jikina hade da ja baya, ina kallonsa cikin ido rai bace

“Ni na gaji da zama a tsakaninku ku biyun nan,don Allah ni ka mayar da ni gida. Ka san kana son matarka ba za ka iya hadata da kowa ba, me ya sa ni ka auro ni?”

Kallona yake mai cike da alamun mamaki.

Ganin ba shi da niyyar magana na ci gaba

“Tun da muka dawo Kano na fada ma ba ni da lafiya, har kiranka na yi jiya a kan ka zo min da magani, amma ba ka siyo min ba, yau din ma asibitin ka kasa kai ni, sai ita ce ka sanya ta kai ni. Na kasa gane kai ne ka auro ni, ko ita ka auro ma ni. Da duk wata hidima tawa ita ce kake ɗorawa. Ita nake aure ko kai, ko dama haka ake yi?”

Na yi tambayar hade da kallonsa. Har yanzu bai nuna alamun zai yi magana ba. Shi ya sa na dora

” To ka sani, daga yau ban yarda a kara dora wata a kan hidimata ba, kuma sannan duk wani abu da ya shafe ni kai ne za ka rika yi ba ita ba. Abinci ma ka fada mata kar ta kara kawo min idan ba zan iya girki ba, ka je kai ka sawo min a waje amma ba nata ba.”

Ina gama fadin haka na wuce cikin bedroom,, ba wai don abun da nake son fada sun kare ba, idan zamu kwana to zan ci gaba da lissafi, kawai duk lokacin dana fadi wani abu da nake ganin rashin adalci ne  ake yi min, to sai zuciyata ta kuma tunzura in ji kamar in rufeshi da duka. Ko in duddura mishi ashar.

Gefen gado na zauna ina fuskantar mirror, kallon yadda fuskata ta zama nake yi saboda bacin rai.

Turo kofar bai sanya na waiga ba, saboda na san waye ya shigo, ina kuma jiran in ji da me ya zo, yau kam a shirye nake, idan zaman, to zaman, idan kuma tafiyar, tafiyar.

Burina dai ya cika tun da na zazzage rabin abin da ke damuna.

Tsaye ya yi yana fuskanta ta, kafin ya ce

“A duk abin da kika lissafo daya ne kawai nake ganin shi laifi, wato da kika ce in taho miki da magani ban yi hakan ba. Kuma wlh mantawa na yi…”

“Dole ka manta, saboda ba matar sonka ba ce ba ta da lafiya ko yaranka.” na katse shi cike da bacin rai.

Ya dan murmusa kadan kafin ya ce “Khadija kenan, da ace kin san wacece Maman Khalil da duk ba ki yi wannan fushin ba.”

“Na sani mana, mace ma fi soyuwa a wurin ka.”

“Da dai da abokaina suke fada min hada mata biyu ko fiye da haka akwai matsaloli, ban yarda ba sai yanzu. Lokacin da zan aureki ‘yan’uwana sai da suka ce, kana zamanka da matarka asirinku rufe za ka je ka dakko wata.”

Ya dan dakata yana kallona, dana bude baki ina kallonsa cike da mamaki.

” Khadija ina sonki, so ba na wasa ba, da ace zan iya ciro zuciyata in ajiye a gabanki, da kin tabbatar da hakan, amma tun da kika shigo cikin nan na fahimci yanzu kin daina yarda da ina sonki. Ba tun yau ba, na fahimci kina da mugun kishi, muddin zan kasance da Maman Khalil sai na gani a fuskarki, kyaleki kawai nake yi in yi kamar ban gani ba. Wannan kuma dalilin ya sanya kike ganin yanzu ba na sonki, ban damu da ke ba, saboda kin sanya kishi a ranki. Komai kankantar abu, Sai ki girman d shi.

To amma abin da nake son ki sani Sakeena matata ce kamar yadda ke ma kike matata. Ina da ikon kasancewa da ita a duk lokacin da na so, kamar yadda nake da ikon yin hakan a kanki, raba kwanaki wannan wani adalci ne kawai aka yi maku. Ya kamata ki rage wannan zafin kishin, ki zo mu hadu mu zauna lafiya. “

” Ai Basheer muddin irin wannan zaman ne, ba zan amince ba gaskiya, kuma dole in ji ba ka sona, saboda ba ka damu da komai nawa ba. Kullum hankalinka ba a kaina yake ba, a kan matarka yake. Idan kana son zaman lafiya, to kuwa shi ne ni ma in zama mata a gidan nan. Ka rika yin duk wani abu da ya shafe ni da kanka”

“Kina ji na ko? zan gina mana zamanmu ne a bisa taimakawa juna ba kowa tashi ta fissheshi ba. Ba ke ce za ki tsara min yadda zan zauna daku ba, ko ita Sakeenar ba ta isa ta tsara min yadda zan zauna da ku ba. Kawai tana bin umarni ne, ko yin abin da zai faranta min, ya kamata ki san wannan. Tun da Sakeena take ba ta taba yin complain a  kanki ba, amma ke kullum idonki yana a kanta, me ye wannan? “

Zuciyata ta zo min iya wuya,  hakan ya sa na mike tsaye tare da fadin

” To dama ita a kan me za ta yi ma complain, tun da ka fifitata a kaina, ai ba ta da matsala ni ce mai ita. Ai duk munafurci ne irin na mata take yi ma. “

Kuma da kake cewa yan’uwanka sun ce kar ka auro wacce za ta bata ma gida me ya sa ba ka karbi shawararsu ba?”

“Ni kike fadawa magana haka?” ya yi maganar yana kallona da wani irin yanayi a fuskarsa da ya tsorata ni.

Shiru na yi ban ce komai ba

“Lallai yaran zamani, tun da nake da Maman Khalil ban taba fada tana fada ba koda kuwa ita ce mai gaskiya. Shiru take yi  sai na gama, ba ta mayar min da martani amma yanzu ga shi nan rashin godiyar Allah irin ta dan’adam na je na auro yar cikina tana fada min magana”

Har yanzu dai Maman Khalil ce abakinsa, yaushe zan goge sunanta ne nawa ya zauna?

Yaushe zai san ni da ita yanzu duk darajarmu daya?

Yaushe zai san cewa ni da ita yanzu babu wani bambanci?

“Kar ki kuma kara cewa matata munafuka idan ba haka ba ranki zai fi na yanzu baci, ban san ba ki da kunya  ba sai yau” ya katse min tunanin da nake yi, kafin in ce wani abu kuma har ya juya zuwa kofar ficewa daga bedroom din.

Tsaye na yi zuciyata tana kuna, ina jin kamar in hada kayana in kama gabana.

“Haka dama aure yake kodai nawa ne ya zo da haka?”

Daga na yi magana a kan neman yancina sai ya zama  tashin hankali,, me ye na fada da ba daidai ba?

Ban san lokacin da na fashe da kuka mai sauti ba, lokaci daya kuma na bude kofar na fito zuwa falo.

Cikin sa a kuwa na same shi zaune, ya jingina bayansa da kujera kansa a sama da alama ya yi zurfin cikin tunani.

“Ka tashi ka koma wajenta, tun da ita ce mai tarbiya, mai kunya. Don Allah ka fita ni ba na son ganinka.”

Cikin kuka nake maganar

“Wannan shi ne zabinki na karshe?”

“Shi ne.” na ba shi amsa

Abun mamaki sai na ga ya mike hade da ficewa daga falon, ko kofar ma bai rufe min  ba.

<< Hasashena 6Hasashena 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×