Bayan fitarshi kuka na saki mai sauti, na yi mai isa ta, har sai da na ji na koshi, kafin na mike na yi alwalar magariba, ban idar da magaribar ba ma aka kira isha’i, shi ya sa kawai na zarce da isha’i har da shafa’i da wutri.
Daga nan kuma kitchen na zarce na nemi abin da zan ci, saboda ko abincin Maman Khalil ban bude ba.
Bacin ran da nake ji bai hana ni bacci ba, bacci na yi sosai, har sai da ana sallame sallahr asuba na tashi. Na yi alwala hade da yin sallah. Ban wani damu da rashin ganin Bashir ba, tun da dama na rufe kofata, kuma na yi alkawarin ba zan bude ba koda ya buga.
Ina kitchen na rika knocking, ta ƴar kofar da ke jikin kofar na leka, ganinshi tsaye da jallabiya ya sa na juya ba tare da na bude kofar ba.
Daga shi har matarshi basu ganni ba, har suka fice daga gidan. Yayin da ni kuma na ci gaba da zaman bacin raina
Har na fita girkina ban yarda ya kara ganina ba, abin da na fahimta dai yana duk wasu hidimominshi ne a dakin baki, Sai kuma bangaren Gimbiyar ta shi.
Saboda hatta matarshi da yaranshi sai da na dauke musu wuta, sau uku tana zuwa bangarena, ganin yadda nake daure fuska ya sanya ta daina zuwa.
Zaman kuma haka baya min dadi amma haka nan na daure hade da takure kaina.
Lokacin da ta karbi girki, Sai na ga kamar tana min abu da gayya, saboda har wani fita yawo suke yi, su dawo da kaya niki-niki, duk kuma lokacin da suka dawo din za ta aiko min da nawa, ni kuma ban karba, Sai in kora yarinyar da ta aiko da kayan.
Kwanaki nan kamar a prison na yi su, sai a lokacin na gane babu abin da ya kai zaman lafiya dadi, ga shi dai ni na hura wutar kuma ta isheni da zafi, maimakon ta kone matsalolin dana hurata don su, sai ma ta kara min wasu matsalolin.
Yanzu kam da kaina nake addu’ar Allah ya sa ya dawo dakina yau, kar ya ce zai kara yada zango a dakin baki, idan ya yi haka lallai akwai matsala, ya fi min ya dawo dakina mu ci gaba da fadan, a kan yana wani wuri daban
Babu wani amfanin fushi da miji ma idan yana da mata, ko ma ka yi sai ya shareka ya tafi wajen wata.
Maimakon ya zama fushin ya kawo masalaha sai ya zama ya barke kofar wata matsalar.
Kamar ni yanzu ga shi nan dai na ba abokiyar zamata kofar kara kusantar mijina, yayin da kuma kimata ta ragu a idon abokiyar zamana da kuma mijina.
“To wai me ye abun yi ne kuma yanzu?”
A fili na yi tambayar hade da gyara tagumin da na yi.
“Abun yi shi ne in ci gaba da zama hade da zuba ido, ana fifita wata a kaina?”
“Kai! Ina! Sam ba zai yiwu ba” wannan karon a zahiri na yi maganar hade da mikewa tsaye ina zagaye falon.
Abokin magana nake nema, amma waye duk wasu yan’uwana suna nesa, wannan ma wani kalubale ne na auran nesa.
“To ta ya zan dawo da mijina wajena?”
Na kuma yi wa kaina tambayar
Shiru ina nazari kafin in dakko wayata, text nake son rubuta mishi.
“To me zan ce?” na kuma tambayar kaina hade da bubbuga wayar a hannuna.
Duk abin da na fara rubutawa sai in goge, in ga kamar na fado kasa ba nauyi ne ko na yi a mai na lashe.
Jin karar bude gate ya sanyani saurin karasawa jikin window hade da yaye labulen.
Yaransa ne suka fito a guje zuwa inda yake, yayin da mamansu ta biyo bayansu.
Sanye take cikin wani farin cotton material mai laushi, wanda aka yi wa ado da fulawa masu kalar lemon (orange) dinkin riga da siket ya bi jikinta ya zauna, tare da fito mata da kyan dirinta.
Kamar ko wane lokaci hannu ta mika mishi, suka gaisa fuskokinsu dauke da murmushi, jakar laptop dinshi ta dauka, yayin da ya bi bayanta suka shige ciki.
“Wayyyo Allahna!”
Ni kaina ban san a zahiri na yi ihun ba, sai da na ji ana buga min kofa da sauri da sauri, mabanbantan muryoyi na tambayata lafiya?, sannan na san kasassabar da na yi
Wiki-wiki na yi da ido ina kallon kofar ba tare da na bude ba, kafin dabara ta fado min, na shiga jan kafata dakyar zuwa kofar na bude.
“Lafiya kuwa?” ya yi saurin tambaya ta
“Me ka ji?” na mayar masa da tambayar ina tura baki, har zuwa lokacin ina matsa kafata, irin dai a nan koma menene yake.
“Ji mu ka yi kin yi kara ” Maman Khalil ta karbe maganar
“Au! Faduwa na yi, amma ban ji ciwo sosai ba, kafata ce kawai ta dan bugu” na yi maganar hade da juyawa ina dangyasa kafata a hankali, zuwa hanyar bedroom dina, ba tare da na rufe kofar ba
Gefen gado na zauna, ina yi wa kaina dariya, jin alamun tafiya kuma sai na hade fuska.
Shi ne ya shigo, tsaye ya yi jikin kofar yana kallo na, yadda ban ce komai ba, haka shi ma, ya gaji da tsayuwar ya juya.
Da kaina na ba kaina muhawara bayan fitarshi, tsakanin mace yar boko gogaggiya wacce ta san komai, ta kuma iya komai, da kuma kishiya yar kauye wacce ba ta waye ba, ba ta iya komai ba, ba ta kuma san komai ba wacce ta fi dama-dama a wajen zama ne?
Haka nai ta kawo points a ka wane bangare ina kuma rugujewa.
Jin kiran sallahr magariba ne ya sanya ni mikewa, alwalla na yi tare da hayewa sallayata.
Sai da na yi sallahr isha’i sannan na sauka, ina shan tea na ji karar kofa alamar wani zai shigo
Dakatawa na yi da shan tea din ina kallon kofar.
Sanye yake ciki jallabiya mai ruwan toka, irin mai walkiyar nan, kamshinsa wanda yake gauraye da na matarsa ne suka cika min hanci.
Kawar da kai gefe na yi, bayan na amsa sallamar dakyar
Kujerar da ke facing dina ya zauna, tare da amsar kofin tean da ke hannuna ya kai bakinsa.
“Ya na ji kamar ba sugar?”
Shiru ban ce komai ba
Labbana ya kama tare da dan jansu
“Kina da rikici, zama da ke sai dai ni kawai”
Zumbura bakin na yi, tare da kawar da kaina gefe bayan ya sakar min labban.
Ci gaba da kurbar tea din ya yi a hankali.
Ni kuwa a kasan zuciyata wani farin ciki ne ya cika ni, domin kuwa koda na yi sallah sai da na yi addu’ar Allah ya sa ya dawo dakina yau.
“Me ya sa ba ki sanya sugar ba,, ko karewa ta yi?”
Daga kai na yi kawai alamar eh
“Karewar ta yi?” ya kuma tambaya
“Eh”
“Shi ne ba ki fada ba?”
“A ina zan ganka in fada?”
“To ai ke ce kika kore ni?”
“Kuma hakan ya ma dadi ai”
“Waye ya ce?”
“Sai an ce ne, abu da na gani, ni na rasa dalilinka na aurena bayan kana son matarka.”
“Za ki fara ko? To ke waye ya fada miki ba na sonki?”
“Ni ce na gano haka”
Wannan karon murmushi ya yi,, ba tare da ya ba ni amsa ba ya dire cup din, hade da shigewa cikin bedroom
Sai da na shanye ragowar shayin kafin na bi bayanshi.
Sosai al’amarin maza ke ba ni mamaki, yadda Baban Khalil ya tafiyar da ni a daren tamkar ba shi da wata mata sai ni kadai, kamar ba daga gurin wata matar ya fito ba.
“Ita ma fa haka yake mata ko?” na yi wa kaina tambayar da tado mini da wani kishi mai maiko, sosai nake jin tukukinsa a zuciyata. Yau kuma dakyar na lallaba bacci ya dauke ni.
Da safe na tashi jikina wani iri, ni mai lafiya, ni ba mara lafiya ba, a haka na kammala break fast danwaken fulawa da garin alabo na yi, ya ji kuka da kanwa, ga yajina da ya sha tafarnuwa, na soya mangyadana sai bakin shayi.
Bayan nan ban yi komai ba, na koma na zauna don ina jinsa a toilet yana watsa ruwa.
Kamar minti ashirin ya fito sanye da jallabiya, abin da ya ba ni mamaki, don na yi tunanin zan ganshi ne cikin shirin aiki.
Kamar zai tsaga jikina ya shige haka ya zauna kusa da ni.
“Har yanzu fushin ne?” ya yi min tambayar hade da yi min kallon da ya kashe min jiki.
Ina mamakin a shekarunsa amma har ya iya irin wannan kallon.
Kai na girgiza alamar a’a
“Amma shi ne ba ki tashe ni ba, na yi shirya don zuwa aiki. Kalli fa agogo”
Ya yi maganar hade da juyar da fuskata ina kallon agogon
8:07am ya nuna.
“Maman Khalil ta fita?”
“Ban sani ba gaskiya, kila ta fita ina kitchen.”
Maganar gaskiya ita ce na ji fitarta, ina kuma sane naki tashinsa, so nake ta ji abin da nake ji ni ma, na hana shi ya zo inda nake kan lokaci.
“Ok” Ya yi maganar hade da janyoni sosai zuwa jikinsa,, gam ya matseni kamar zai shigar da ni kirjinsa, tsawon mintuna kafin ya sassauta rikon yana mayar da numfashi.
Dago kaina ya yi da yake a kan kirjinsa, muka zubawa juna ido kafin daga bisani na lumshe nawa, wanda ya yi daidai da hada bakinsa da nawa.
Mun dade a haka, kafin ya janyeni a hankali ya nufi dinning yana tambayar
“Me aka dafa min ne?”
Shiru na yi, saboda jikina ya yi mutuwar da ko bakina ma ba zan iya budewa ba
“Wowww! Na ji ya fada, a lokacin da ya bude flask din ya ga danwake.
A lokacin ni ma mikewa na yi da kyar kamar mai koyon tafiya na isa kan dinning din, hade da zuba mishi a bowl na kuma zuba mishi bakin shayin da ya sha kayan kamshi.
” Gaskiya yau kin yi min komai, akwai kyauta ta musamman. Ina son danwake sosai, kuma na fi son in ci shi a haka, kamar yadda kika yi, bana son wani tarkacen su cabbage ko kwai. A yadda kakaninmu suka ci haka na fi son in ci shi. Madalla da ke.” ya karasa maganar gami da kamo hannuna ya dan matse daga bisani ya manna min kiss.
Mu ka yi murmushi a tare.
A kasan zuciyata kuma jin dadi nake da ban yi mishi bajintar yanka mishi cabbage dasu tumatur ba, da kuma na kwafsa.
A natse muke cin abincin, hade da hira a hankali wadda a cikinta ne ya sako abin da yake son fada min.
Gabadaya batun nashi a kan zamantakewarmu ne, ta inda yake nuna min in rage kishi, in zauna lafiya da matarsa.
Ni na rasa me yake so in yi, ko so yake in kwanta ta rika takani oho, ni dai abin da na sani shi ne, ba zan taba yarda ya fifita wata a kaina ba.
Wannan shi ne matsayata.