Kamar kada Kwanaki biyun nan su wuce haka na ji, saboda mun yi matukar raya su, na ji ni cikakkar amarya saboda kulawar da na samu, ina ma ace kullum haka nake samu, yau kam da ya koma dakin matarsa sosai nake jin kewa, hatta abinci ma na kasa ci, sai dai in tsakura in ajiye.
Ina jin taba kofa na san shi ne ya zo min sai da safe, hakan ya sa na gyara zaman da na san zai ja hankalinsa.
Ganin Ramla a hannunshi ga Affan biye da shi, sai na ji raina ya dan so su, saboda na san abin da na shirya ba zai samu ba. Gashi tun da Ramla ta ganni take daga hannu alamar in dauketa.
Ni ma na yi kewar yarinyar sosai, Allah ya sani jin kaunarta nake yi a jinina kamar ni na haife ta. Fushin da nake yi ne da iyayenta ya shafe ta.
Wajen kwana takwas kenan ban rabata jikina ba.
Da sauri na mika hannu ina dariya, kawai sai ta fado, don dama ta kosa.
Na kankameta a kirjina, kamshin turarenta mai sanyi na yara da kuma na mamanta suka cika hancina.
Wani lokaci ina jin kamar in ce mata wai ya sunan turaranki ne, sai dai kuma ina gudun yada kai wai sata dakin kishiya.
Na dagata sama ina mata wasa, yayin da Babanta ke tsaye yana kallonmu cikin murmushi, da alama mun burgesa sosai, don har waya ya dakko ya viewing namu.
Sosai na mayar da hankalina kan Ramla da ke koyan tafiya, sai in aje abu in ce ta zo ta dauka.
Da ta fara takawa sai ta zauna, idan kuwa ta iso, sai in dagata sama ina juyi da ita muna dariya.
“Na tafi in ci abinci to, na ga kin manta da zuwana sai yarinyarki”
Dariya na yi kafin in ce “To a ci lafiya, zan kawota”
“ok.” ya fada hade da juyawa
Ramla kam ta debe min duk wata kewa da damuwar da nake ciki, wasa muke yi muna ta kyalkyala dariya, har zuwa lokacin da su Khalil suka shigo.
Salon hirar sai ya canja, muka koma surutun makaranta, da yawan labarin dai Khaleel ne ke bayarwa, saboda Affan mugun miskili ne. Daga baya na fahimci ya fi Khaleel miskilanci, shi Khaleel kafin kusa saba ne.
Misalin tara na dare na ba Ramla tea hade da goge mata jiki na goyata, ba jimawa ta yi bacci, su ma su Affan din duk suka yi bacci.
Karon farko da na ji ina sha’awar su kwana a dakina. Shi ya sa na bar su, na nufi bangaren Maman Khalil don kai mata Ramla
Na kwankwasa kofar falon hade da sallama.
“Wa’alaikissalam shigo.” aka amsa sallamar hade da bude kofar. Yarinyar nan ce dai da ban san matsayinta ba.
“Tana ciki ne?”
Da kai ta amsa min alamar eh. Sai na tsinci kaina da jin kunyar hada ido da ita kuma, rashin kirkin da na yi mata a kwanakin nan akwai kunya in hada ido da ita, muddin na san kunyar.
Ina cikin shawarar mikawa yarinyar nan Ramla in juya, na ji takun tafiyarta.
Daure take da towel, amma babba sosai, saboda ya sauka har saman kwaurinta, Sai kuma hular wanka, da alama wanka za ta yi, ko kuma har ta yi
“Ta yi bacci ne?”
Ta yi tambayar hade da murmushi.
“Eh.” Na ba ta amsa. Kamar in nutse, na san kuma ta fahimci hakan
“Su Affan fa?” ta kuma tambaya
“Su ma sun yi.” na kuma amsa ta kaina a kasa
“Wannan kam sai na tayaki dakkosu, sun yi nauyi da yawa” cikin dariya take maganar
“Ki bar su kawai su kwana a can.” Na yi maganar daidai lokacin da nake kwanto mata Ramla.
“Sannu da kokari”
“Sai da safenmu”
Na fada hade da murmushi a kan fuskata, lokaci daya kuma na fice. Saboda na kosa in fita din, ji na nake yi kamar ina gaban surukata.
Sosai nauyinta da kunyarta nake ji, har bana son hada ido da ita, ban kyauta ba yadda na yi mata, tana bakin kokarinta a kaina.
Bayan na sanya yaran sun yi fitsari, na gyara masu makwanci a gadona mu ka yi kwanciyarmu.
Da safe ma ni na shiryasu, abinci ne dai ba ni na yi ba, ta ce ta ri ga ta yi masu.
Gidan sai ya zama gwanin dadi, gaskiya zaman lafiya akwai shi da dadi.
Tun da kowa ya watse a gidan na shiga zuwa 12pm na gama komai dakin ya fita fes.
Na gaji sosai, hakan ya sa na watsa ruwa hade da shan corn flask na kwanta, bacci mai dadi kuwa ya kwashe ni.
Cikin bacci na ji kamar mutum a kaina, dalilin da ya sanya ni bude ido a hankali.
Idonshi daya ya kanne, hade da yin siririn murmushi.
“Mai ciki?”
Da sauri na mayar da idanuna kanshi, cike da mamaki
“Waye ya fada ma?”
“Likitan da ya duba ki”
Komai ban ce ba, na mike zuwa toilet. Wanka sosai na yi hade da alwala, lokacin da na fito zaune yake gefen gado yana taba wayarsa. Humrah na shafa hade da sanya doguwar riga, na zira hijab na kabbara sallah.
Bayan na idar ne ya ce “Babu abinci?”
Cike da rashin jin dadi na ce “Ban yi ba, saboda ban san za ka dawo ba. Kuma ga shi ba a nan dakin kake ba”
“Ni ma ban san zan dawo din ba, haka nan kawai na ji ina son ganinki”
Murmushi jin dadi na yi kafin na ce “Na gode”
“Me za ki ci yanzu?”
“Cornflakes zan sha, kafin in gama abinci”
Hannayena ya kamo daga kan sallayar, wannan ya sa na mike a hankali. Saman cinyarsa ya dora ni, tare da zare hijab din da ke jikina.
Kanshi ya kwantar a kan kirjina, yayin da hannunshi daya ke kan cikina ya ce “You’re not alone yanzun, ki rika cin abinci mai kyau da gina jiki. Sannan yawan aikin nan at this stage bai kamata ba.”
Kai na jinjina alamar fahimta, yayin da kulawar tashi ta yi min dadi.
“Za ki iya zuwa restaurant mu sawo abinci, ko za ki jira in sawo miki”
Da sauri na ce zan je, saboda na tabbata Maman Khalil ta kusa dawowa aiki, zan yi matukar farin ciki ta shigo gidan ba ta same ni ba, sannan a kan idonta mu dawo tare da mijinta, ahhh har wani takun kasaita zan yi. Na fita da miji ranar girkinta.
Ai da sauri na shirya muka fice, a can din ma haka nai ta shiriritar da shi har la’asar kafin mu ka dawo
Har farfajiyar gidan ya kawo ni, ina fita ya juya, sosai raina ya yi min ba dadi, saboda ban ga motar Maman Khalil ba, zuciyata tai ta yi min sake-sake, ta dawo ne ta kara fita, ko ba ta dawo ba, ko kuma motar ta samu damuwa ne?
Da wadannan tambayoyin na yi knocking kofarta, yarinyar nan ce ta bude.
Cike da girmamawa ta gaishe ni, karon farko da na tambayi sunan ta
“Sunana Suwaiba” ta amsa min
“Kina ta ya ta aiki ne?”
Kai ta jinjina alamar eh
“Ta dawo ne?”
“A’a basu dawo ba”
A cikin zuciyata na ja tsoki hade da juyawa zuwa bangarena.
Sai kuma duk na kasa nutsuwa, saboda ba ta saba kaiwa har wannan lokacin ba ta dawo ba. Ko motarta ce ta lalace sha Allah zuwa uku tana gida shi ne ma ta dade.
Wayata na dauka hade da dialing lambarta.
Ita ce ta fara cewa “Kin ji mu shiru ko?”
“Ai kam dai, na ce ko lafiya?”
“Lafiya kalau, na biya wani wuri ne, amma ina hanya sha Allah”
“To Ma Sha Allah, Sai kin kara so”
“To na gode sosai”
A tare mu ka yanke kiran, alwalar sallahr la’asar na yi, a kan sallayar na zauna bayan na idar ina taba chat, da ƴan’uwa da kuma kawaye.
After 10mns na ji karar motarta, ina zaune a wurin dai na ji an taba kofata alamar ana shigowa. Kofar na zurawa idanu har zuwa lokacin da Affan ya shigo hannunsa rike da bakar leda.
Na san ba magana zai yi ba, shi ya sa na karba hade da budawa,, magarya, kurna, aduwa da kuma taura na gani a ciki.
“Waye ya ba ka?”
“Mamana.” ya ban amsa a hankali.
“Ta ce ka kawo min?”
Daga kai ya yi alamar eh
“To je ka, ka ce na gode.”
Bayan fitarsa na kuma bude ledar ina karewa kayan kallo
“Kenan matar nan ta san ina da ciki? Waye ya fada mata?”
Shiru na yi ba tare dana amsa tambayar ba, har zuwa lokacin da na lalubo amsar
Na san ba mai fada mata sai mijinta.
Kenan ni ban da sirri, komai nawa sai ya fada mata.
“Mtswww!” na ja dogon tsoki, a bayyane na shiga fadin “Gaskiya ba zan yarda ace ba ni da sirri ba, ace komai nawa kishiya ta sani bayan ni bai fada min komai nata.
Allah ya kaimu ya dawo, wannan karon ma zan magantu.”
Dalilin da ya hana ni zuwa sashenta, Sai ma na mike zuwa kitchen, yayin da na aje ledar tarkacen a kan dining.
Aiki nake yi, sai dai raina Sam babu dadi, na kosa ya dawo kamar in sanya igiya in janyo shi.
Misalin 6pm kuwa ya dawo, 6:30pm ya shigo bangarena cikin shirin masallaci.
Time din hakimce nake a kan kujera ina taba wayata. Da kyar na amsa sallamar da ya yi
“Me ya faru na ga kamar ranki bace?”
Ya yi tambayar idanunshi a kaina.
“in yi magana ka ce bana son zaman lafiya.” na amsa shi cikin tabe baki
“Ki yi ina sauraronki.”
“Me ya sa don Allah ba ka son rufe sirrina?”
“Sirrinki kuma, me kike nufi?” ya yi maganar hade da tattara duk hankalinsa a kaina.
Yunkurawa na yi hade da mikewa zaune na ce
“Ni ba ina son tsara ma yadda za ka zauna damu ba ne, amma yana da kyau ka rika boye sirrinkanmu, me ya sa za ka fadawa matarka ina ciki?”
“Ni din?” sosai fuskarsa ta canja a lokacin da yake maganar zuwa nuna alamar damuwa
“To idan ba kai ba, wa? Ni dai ban taba fada ma wani ina da ciki ba, idan ba ta san ina da ciki ba, me ya sa za ta kawo min wannan?” na karashe maganar hade da dakko mishi ledar da ke kan dinning ina bude mishi.
Kallon abin da ke cikin ledar yake kafin ya ce “Yanzu kawai don ta kawo miki wannan shi kenan sai ki yi zargin ni na fada mata kina da ciki? To wai ma me ye don Sakeena ta san kina da ciki? Mayya ce ita da za ta lasheki, kafin ki yi ciki ba ita ta fara ba. Wai me ya sa kullum kike son tayar min da hankali ne Khadija?”
Rai bace ya karasa maganar, haka yanayinsa ma ya canja.
Ni kaina sai na ji jikina ya mutu,, na kuma yi nadamar maganar da na yi.
Kafin in yi wani yinkuri tuni wayar da yake kokarin kira ta shiga
Hands-free ya sanya lokacin da ya fara magana
” Sakeena!”
“Na’am” na ji ta amsa da alamar tsoro. Kila ba ya kiran sunanta kai tsaye haka, Sai da babban dalili
“Kina ina?”
“ina daki” ta kuma ba shi amsa da yanayin mutuwar jiki a tare da ita
“Zo bangaren Khadija ina son ganinki.”
Bai bari ta bayar da amsa ba ya kashe wayar.
Yayin da ni kuma na yi tsuru-tsuru hade da fargabar abin da zai faru.
Ko minti daya ba ta hada ba, ta shigo falon nawa.
“Ke ce kika ba Khadija wannan?” tambayar da ya fara jefa mata kenan bayan ta shigo, lokaci daya kuma yana nuna mata abun da ke cikin ledar da ya karbe a hannuna.
“Eh ni ce” a tsorace ta ba shi amsa, saboda ganin yanayinsa.
“A ina kika samu?”
“Malama Maryam kawata ce da ta yi tafiya, shi ne da muka biya dazu wajen ta, ta ba yara. , sai na dan debar mata na ga abun marmari ne” Har yanzu a tsorace take maganar
“Shi kenan.”Ya fada hade da ajiye ledar ya fice ya bar mu a tsaye kowa jiki a sanyaye.
Ni dai a bangarena yadda lamarin ya tsaya haka ba karamin dadi ya yi min ba. Yanzu rigimar tsakanin ni da shi ne. Kai barka bante.
“Me ya faru?” ta katse min tunanin da nake yi
“Ba komai, ya dauka na fita ne wai bayan kun fita”
“Au ho!” ta ba ni amsa hade da ficewa.
Fitar ta ke da wuya na shiga bubbuga kafafuna, cikin rashin sanin abun yi.
“Wallahi idan akwai abin da ya kamata a budewa mata aji a kansa shi ne yadda za su zauna da kishiya. Gabadaya na damalmale komai, na zama sakarya wawiya, ina son cusa kiyayyata a zuciyar mijina da kaina.”
Hannu na kai na share hawayen da ke bin fuskata.
Ni sam ban san haka zama da kishiya yake ba. Ashe dole sai ka iya takunka, idan ba haka ba, Sai a samu matsala.
Lallai wannan kalubale ne ga yan’mata masu shirin auran mai mata, kuma suke tunanin cewa, ta gida ta kasa ne, ko an gama yayinta shi ya sa ake son kawo ki, wannan babban kuskure ne muke yi, sai mun shigo kuma zamu gane hakan.
Kamar ni yanzu uwargidana ai babu abin da zan nuna mata, kyau, ilmi, hankali, tsafta, girki, kula da miji duk ta iya.
Akwai wadanda kuma suke da nakasu, amma kuma dole dai ke amarya ki bi su, kafin ke ma ki zama yar gida.
Kamar yadda uwargida ke fuskantar kalubale idan aka mata amarya haka ita ma amaryar ke fuskanta muddin tana da uwargida.
Ni dai yanzu ganau ce ba jiyau ba. Na bata darena na gobe kuma
Don ya yi fushi irin wanda ban taba gani ba.