Skip to content
Part 2 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Jikin yarinyar yayi zafi sosai kuma wani ikon Allah sai zufa ke tsiyaya ajikinta inda Luba ta rude tana neman agajin likita sai kuma taga jikin Safiyyar na kyarma tamkar wadda ake jijjigawa.

Ta kankame ta tana kuka “Allah kayiwa yarinyar Nan Sakayya Akan wannan ta addancin da aka nuna Mata ba Zan yafe ba ! Wallahi ba Zan yafe ba…

“Mami …” Taji Safiyya ta kirata ta dago tana kallon ta taga kamar tana mata murmushi…

“Me kike so Safiyya? Ta tambaye ta sai tayi mata nuni da gabanta wanda Allah kadai yasan yadda take jin…

“Kiyi hakuri kinji Safiyya Allah zai dubeki da duban Rahamar sa… Ruwa Mami…

Ta Bata Ruwan tasha sosai kamar ba cikinta ta ke kaiwa ba. Tabi ta da kallo tana tausaya mata… “Mami… Abba… Sai zufa ta barko mata har tana zuba Luba ta soma yi Mata firfita inda taga fuskar yarinyar na kallon wani wuri kafin ta lumshe idonta ta kuma sauke wata ajiyar zuciya (Allah kayi Mana kyakkyawan karshe ka karbi ruhin mu muna muminai masu Imani Safiyya dai Anzo iyaka) gaban Luba ya sara duk da bata san mutuwa ba, amma jikinta ya bata akwai wani Al’amari.

Ta kamo hannun Safiyya amma sai taji ya saki ta soma juyata daidai da shigowar Bello ya karaso da sauri ya karbi Safiyya amma jiki kurum aka bar musu Ruhi kuwa ya koma inda ya fito.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un. Allah Kaine Allah. Cewar Bello inda Luba ta zubawa bakin shi ido tana kallon yana motsi amma bata ce ga abinda yake cewa ba. HAWAYE kawai take fitarwa ta kasa cewa komai ya dubeta HAWAYE na zarya a idonshi.

“Mu yi hakuri Luba Allahn da ya bamu Safiyya ya kuma karbe abinsa. Ya fada yana kankame Safiyya tare da fashewa da kuka. Luba dai sai kallon take raba musu shi da gawar yarta Safiyya ta kasa cewa ko uhum banda Hawaye.

Da haka aka sallamesu suka taho gida aka yiwa Safiyya sutura zuwa gidan ta na gaskiya gidan dake dakon dukkan wani mai rai ya rage garemu mu aikata komai kafin zuwan mu can.

Wata sabuwa kuma Luba ko gaisuwa aka yi mata bata bude baki ta amsa sai dai ido kurum. Babu wanda zaice yaji bakinta tun bayan rasuwar yar ta Safiyya.

Wasa ya zamo farin girki da farko anyi zaton kid’ima ce da zafin Rashi yasa hakan.

Kafin asan abinyi kuma sai ciwo yayi mata sallama kuma har kawo yau din da take kwance magashiyyan bata cewa ga inda ke mata ciwo bare ajiyo amon muryar ta.

Bisa dole aka kwashe ta zuwa Asibiti tun tana gane wanda ke kanta har ta zamo dai idon nan shi kadai ne abinda ka iya kararwa a gareta.

Bello kam tashin hankali ya zame mishi biyu . Ga Alhinin rasa Safiyya wanda duk dare sai yaci kukan shi ya godewa Ubangiji. Ga kuma rashin lafiyar Luba wanda ya tabbatar mutuwar Safiyya ce ta kawo komai ga Luba. Bai manta yadda aka Sha damuwa ba kafin a samu Safiyya wadda sai da aka shekara biyar kafin a haifeta. Bayanta Kuma shekara Hudu Babu Wanda ya biyo bayan ta Ashe kuwa damuwa ta zama dole.

Yana zaune gefen gadon da Luba take yana rike da hannunta HAWAYE na zuba . “Allah Na gode maka da wannan kaddarar. Allah kasa na cinyeya ba tare da tayiwa imanina Kan tafi ba. Allah kafini sanin hikimar ka anan kafini sanin tanadin da kayiwa bayin Nan naka Allah ka taimakeni da juriya da gode maka in na Rasa…

Yaji hannun Luba na riko tafin hannun shi ya juyo ya kalleta sai yaga shi take kallo….

“Me kike so Luba? Ya fada Yana share HAWAYE. Kina son Ruwa? Ko na Baki fura? Ya Soma jero Mata tambayoyi Wanda dama sune Yake mata idan tana son abinda ya zano din sai ta daga mishi Alamar tana so. Sai dai yau din nata daga kan ba sai ma wani mamaki da ta shayar dashi.

“Kuka kakeyi Bello? Kayi hakuri Haka Allah ya zano Mana Allah yasa ka cinye jarabawa…

“Allah Nagode maka Luba bakin ki ya dawo . Allah ya Baki lafiya.

Tayi wani murmushi kafin ta amsa da. “Ameen to Bello. Amma bana ji ajikina zanyi tsawon Rai. Da ace Ina daga cikin Wanda zasuyi tsawon Rai da ban yarda na bar jinin Safiyya ya tafi abanza ba. Amma Zan Roki Allah da ya tona asirin wancan mutumin da yayi min sanadin Rasa Safiyya. Allah ka Hana wata Uwa Irina Dan danar bakin ciki irin Wanda naji. Allah ka Hana wata yariya irin Safiyya shiga wancan hadarin.

“Na yi miki alkawari Luba. Nima ba zan taba barin jinin Safiyya ya tafi wofi ba.

Nagode Bello ina neman yafiyar ka a tsawon zamana da ,kai don Allah don Annabi ka yafe min kar ka manta dani ko bayan rai na don Allah ka yi Mana ADDU A.

Ta fada da Rushin kuka kukan da ya Dame lissafin Bello

“Me ya kawo wannan maganar Kuma Luba? Ta dube shi, “Ka manta na Gaya maka Nima mutuwa zanyi? Wallahi Bello mutuwa zanyi don Allah ka nema min gafara wurin iyayena da dangina har da makota na.

Kuka shima Bellon yake don ya gama sallamawa rayuwa indai haka take da tarin kalubale

Suna tsaka da kukan mahaifiyar Luba ta shigo ta same su a haka.

“Haba Bello ayi hakuri Mana komai fa yayi zafi maganin sa Allah. Da Haka Bellon ya hakura har mamar ta duba su ta koma gida itama jikinta asanyaye da kalaman luban na neman yafiya gareta da mahaifin ta har da Yan uwa da dangi. Kanwar maman ce ta Zo da zummar zaman jinya. Ranar da mahaifin nata yazo Asibitin don ya dubata ya Kuma tabbatar Mata da yafiyar shi gareta a Ranar ne Kuma Ubangiji yayi ikon shi Akan Luba ta koma ga Ubangiji babu Rabon su gana da mahaifin nata Bello Kuma ya koma gida ya dauko Mata Kaya don anyi Mata wanka babu kayan canzawa

Ya dawo da kayan da za a sauya Amma ya Tara’s da labarin ya sauya daga Wanda ya sani zuwa sabo Dal

Mahaifin ta tsaye akanta Yana Mata ADDU AR zuwa cikin Aminci da dacewa. Yayin da Anty hurera ke kuka. Baya bukatar Karin bayani Dole ya sallama Akan kaddarar da Ubangiji ya zano mishi Dole ya Mika hannu ya karba.

Shi da kanshi ya saka Luba a makwanci Yana me nema Mata Rahama ga Ubangiji

Zaman kwanaki bakwai aka yi ana karbar gaisuwa kafin kowa ya watse aka barshi shi Daya kwal sai Wanda yazo mishi gaisuwa irin Wanda baya kusa lokacin mutuwar

Ya Kan shiga Rudani idan yayi karo da wani Abu na Luba ko Safiyya kuka Kam yayi shi koma ace cikin yin shi Yake

Sati biyu cif da rasuwar Luba wadda tayi daidai da cikar sati hudun Safiyya Yana kwance agida tunanin shi ya hango mishi unguwar sardauna Estes da motar nan da ya kasa mance launin ta da gidan da motar tashiga sai kawai ya mike tsaye ya rufe gidan ya nufi titi ya tsayar da napep ya nufi sardauna Estes…

<< Hawaye 1Hawaye 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.