Skip to content
Part 21 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Mai Kano Bai Kara kwana guda Daya agarin katsina ba ya wuce Lagos don ya gama gano inda gizon yayi sakar.

Alh Aminu ya fito daga gidan zuwa lauje inda yake a Rude Akan yaron can Mai Kano.

“Sai fa kayi a sannu mutumina domin ko yaron can shine karfen kafar ka kamar yadda ka zamewa Uwar sa karfen kafa.

Cewar lauje. “Na Rasa yadda akayi yaron ya gano gidana da ba kowa ya sani ba ya Kuma tutsiye Ni Akan wayar Uwar sa.

“Bakaji nace maka shine karfen kafar ka ba? Ina me tabbatar maka da yaron can in ba sannu kayi ba zai gano komai da kake kullawa tun daga jinin uban su da ka shayar da Zubaina har zuwa hutun da kake da Uwar sa. Idan kuwa hakan ta tabbata zai Kai ka kasa warwas !

“Zan kuwa shayar da jinin shi ga Zubaina uban kowa ya huta

“To Haka dai yafi don wallahi in ba sannu kayi ba zai zame maka Dan hakkin da ka Raina. “Barshi ya sake dawowa naji da karatun da zaizo idan na Gane ya San komai to zai ksuce domin kuwa zai zamewa Zubaina Madara.

Laujen ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya Mai Kama da kukan jaki. Kafin yace
“Yaya mutumiyar taka Halima?

Alh Aminu ya shafi sajen shi Yana murmushi. “Halima tana Nan lauje muna ta tsinkar fure .

“Amma yaushe Rabon da kabawa dodon kod’i jinin Al ada? Ya dubi Laujen don har ga Allah ya manta da batun dodon kod’in tunda ya Dora sanwar begen Halima.

“Wallahi lauje nafi wata takwas. “Ka kuwa Kira Bahar maliya wata takwas fa kace? Ya Mike a Rikice ya fice daga gidan laujen ya nufi gidan shi inda iyalan shi suke ya nufi makewayin shi inda ya aje Dan ksramain akwatin Wanda ke dauke da kwarkwaron dodon Amma ga mamakin shi sai kwarkwaron kawai ya gani Babu halittar dodon me dauke da kahunna. Ya jijjiga kwarkwaron Amma Babu halittar a ciki

Da sauri ya jawo wayar shi ya Kira lauje. “Wallahi lauje babu halittar Nan a ciki sai kwarkwaron kawai.

“Yayi fushi ne tunda suka biya maka bukatar ka ta biya Kai Kuma sai ka Fara mantawa da su har kayi wata takwas baka biya su ajandar ku ba.

“Kaga lauje tambayar min shi inji abinda Yake so ayi mishi tunda ai ba a taba yin hakan ba. Yanzu dai kayi maza ka Nemo jinin Al adar Nan ka jefa kwarkwaron kafin muji abinda Yake bukata Wanda zai huce haushin nashi.

Da sauri ya lalubo wata Yar Duniya Mai suna Auta dake kawo mishi kazantar jinin Al ada Yana biyan ta duk inda take idan ya kirata zata kawo mishi nata ko na wata. Ai kuwa sai ga Auta dauke da jinin ta sameshi a inda suka Saba haduwa don Bai yarda ta San muhallin shi ba ya biyata suka Rabu Kwanan dodon kod’i biyu cikin kazantar jinin Al ada inda laujen yace ya duba idan ya samu halittar acikin kwarkwaron to ya taho mishi da dodon kod’in. Ai kuwa Yana dubawa ya samu halittar ta bayyana don Haka ya dauki Dan karamin akwatin ya nufi lauje.

Lauje ya bude Yana karewa dodon kod’in kallo kafin ya dauko shi ya saka cikin Ruwan kwaryar dake gaban shi sai ga wuta na tartsatsi kafin kwaryar ta tarwatse Amma ga mamaki sai Babu ko dis na Ruwan dake cikin kwaryar bare dodon kod’in da aka saka.

Suka dubi juna a lokaci Daya lauje da Alhaji Aminu.

“Ni nasan Babu lafiya don dodon kod’in Nan yafi Zubaina iya ta addanci.

“Kirawo Zubaina lauje muji abinda zamu toshe bakin dodon kod’in Nan. Lauje ya hada garwashi ya zuba garin magani dakin ya turnike da kaurin hayaki kafin suji an kyalkyale da Dariya cikin wata murya me kama da gogen tsumma.

“Dariya kike Zubaina? Cewar lauje. “Uhummm tace Bata Kuma cewa komai komai ba .

“Me akayi ne gimbiyar dodon kod’i? Me ya fusata Mai gidan naki haka?

“Ba fushi yayi ba sai dai gargadi ga wannan marar I’manin na gabanka don ya kusa halaka shi ya barshi da yunwa tsayin shekara saukin shi guda da Yake lasar jinin hailar matar shi bacin Haka da ya mutu. Yanzu ma mahaifar matar tashi Yake so ya sadaukar mishi kafin ya huce !

“N bashi yaje ya dauka Amma daga mahaifar bance ya taba Mata ko farce ba ! “Ya gode. Cewar Zubaina dake Zama hayaki ta fice ta taga. Sai ga kwaryar lauje ta dawo har da dodon kod’in a ciki.

Ya tsamo shi ya na mikowa Alhaji Aminu. Ya karba ya mayar cikin akwatin

Ya ajewa lauje damin kudi kafin ya taho gida inda ya samu haj wasila cikin, matsanancin ciwon ciki sai murkususu take inda Husna ke faman jera Mata sannu har tana cewa da ta iya mota da ta Kai ta Asibiti sai ga Alh Aminu ya shigo.

Da sauri ya karaso gareta inda ya samu har jini ya kece Mata Yana ta zuba tamkar an yanka Saniya. Husna ta taimaka mata ta sauya kayan jikin ta da suka jike da jini kafin su ka wuce Asibiti. Da kyar likita ya shawo Kan matsalar suka dawo gida jikinta yayi masifar saki saboda Tasha wahala. Shi yasan kome kenan dodon kod’i ne ya cizge Mata mahaifa inda ita kuma take hasashen tsarin da tayi ne Yake neman kawo Mata matsala har ta yanke shawarar da ta warke zataje a cire Mata Robar dake makale ajikinta.

Hala kuwa akayi ta samu sauki taje aka fidda inda take kwakwar sake haihuwa Bata San ita da haihuwa ba sai dai ko a kiyama.

<< Hawaye 20Hawaye 22 >>

1 thought on “Hawaye 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×