Skip to content
Part 22 of 34 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Safa da marwa kawai yake yi hannuwan shi goye da bayan shi inda yake mamakin abinda Alh Aminu yake nufi da mahaifiyar su Halima.

Baya ko shakka Yana sane da inda take tunda Babu abinda Bai sani ba . Babu abinda mahaifiyar shi bata sanar dashi ba Amma da wace hujjar zai Kama shi?

Wane irin mataki zai dauka akanshi?

Yayi iyakar iyawar shi Amma ya kasa samo amsa Dole ya hakura ya Kuma bawa kwakwalwa aikin hada lissafin da zai hada biyar da biyar din da goma zata hadu Akan Dan ta addar mutumin can Alhaji Aminu.

Tsayon lokaci Halima ta kwashe a gidan da aka kawo ta ana cin zarafin ta Bayan an gusar da hankalin ta ta hanyar sakar Mata bacci Wanda baya nasarar Hana ta fahimtar abinda ke faruwa da ita.

Tun tana kuka a duk lokacin da zata farka taga halin da take har kukan ya Kama gaban shi ya barta da kunar zuciya.

Kan kace me ta fahimci sauyi me yawa inda ta Gane wani Al amari na Shirin faruwa koma ya farun.

Cikin wannan lokacin ne tayi yunkurin guduwa ko don abin kunyar da take Shirin saukewa kanta da Ya’yan ta har ma da iyayen ta Amma ta Ina zata gudun? Ta jaraba hakan yafi a kirga ga kasala da ta sameta ko sallolin farilla sai tayi da gaske bacci ke barinta saukewa bare kukan da ta saba kaiwa Ubangiji.

Alhaji Aminu ya shigo ya sameta zaune ta zabga tagumi.

Ya zauna kusa da ita Yana sauke Mata ta gumin da ta zuba

“Ban San ya kike kallon Rayuwa ba Halima da Kika Faye matsanta wa kanki. “Babu abinda ba Zan iya mallaka Miki ba Akan abinda nake so a gareki. Me ke da wahala? Meye zai ragu a gareki? Naso ace kin fahimta tun farko da Bata kaimu ga Haka ba da yanzu bama Nigeria Amma Kika kasa fahimar canjin da Duniya tazo dashi.

“Ka gama da Rayuwa ta Aminu ka gama da Ni a Nan Duniya sai dai nace Allah yayi min Sakayya kawai. Da zaka taimake Ni da ka kasheni ko don na huta da Bakin ciki. Banga amfanin zaman da nake anan ba tunda Rayuwa ta ta tarwatse.

“Rayuwar ki Bata tarwatse ba tunda Ina numfashi Kuma Ina kaunar ki. Ta Yaya kike tunanin Zan iya kasheki Halima?

“Ai tuni ka kashe Ni da Bakin zaluncin ka don zanfi kaunar Wanda ya nuna min bindiga akan abinda kayi min.

“Kinji abinda kesawa nake gwada Miki karfi Halima bakya tausayi na akan son ki.

“Har abada babu so a tsakanin mu cuta ce kawai a tsakanin mu na Kuma barwa Allah yayi min Sakayya Akan ka.

Ya Mike Yana Shirin ficewa kafin ya juyo ya dubeta. “Kauna zata ci gaba da Aikin ta a gareni ke Kuma sai kiyayya tayi nata Aikin a gareki. Ina so ki sani Zan Hana kowa da komai sanin yadda aka faro da yadda Za a Kare.

“Amma baka Isa Hana Allah ya fallasa mugun Aikin ka a idanun masu ganin kimar ka ba har girma ya Fadi nayi maka alkawarin hakan. Yayi murmushi kafin ya fice ya barta tana kukan Al amarin dake Shirin tabbata koma ya Riga da ya tabbata.

Baya Rufe sati ba tare da ya Isa masanawa da tarin kayan Arziki ba ga hajiya wadda har gobe bata ga mutumin kirki ya shi ba.

Zuwa goma zai fada Mata ana Nan ana kokari dai akan Halima Kuma za ayi nasara.

Kudi Yake bawa hajiya ba na wasa ba kafin yayi Mata sallama ya wuce tana Rako shi da fatan ALHERI da samun Rabon Duniya da lahira . “Kai samun mutum irin Aminu me Rike igiyar zumunci a wannan zamanin sai an tona.

Lokaci bayan lokaci husna da sulaiman sukan Zo gaishe da hajiyar har ma su nemi labarin mahaifiyar su. Hajiya Kan sanar dasu Alh Aminu na bakin kokarin shi Kuma za a dace.

Mai Kano ya faye yin mugayen mafarkai Akan Halima har ya kasa samun nutsuwa wadda taso shafar lafiyar sa.

Kamar dai yau da yayi mafarki da ita tana keta gudu a dokar daji Alhaji Aminu na biye da ita da wuka . Har Allah ya Bata sa ar ketare wani Rami me fitar fa harshen wuta shi Kuma ya fada aciki. Karar da yayi CE tayi amsa kuwwar da ta tashi Mai Kano dai dai da wani ladani ya rangado Kiran sallar asubahi

Ya farka da barin jiki yayi salla kafin yayi wanka yayi shiri don ya gama tsara yadda zata kaya tsakanin shi da gayen can Alh Aminu. Tuni ya bugo hanya ya nufo garin katsina.

Jakar shi kawai ya sauke a gidan su don baije gidan hajiya ba sai ya sallami mutumin can kafin ya karasa gidan hajiyar.

Kai tsaye ya nufi unguwar sardauna Estes napep ya direshi a kofar gidan ya sallami me napep din ya tunkari kofar gidan Yana duka tamkar zai balle ta.

Me gadin ya leko ta kafar makullin ya hango Mai Kano sai kawai ya koma ya yi zaman shi ya barshi da dukan kofar har ya gaji da dukan ya koma gefen gidan yayi zaman dirshen don bayajin yau zai matsa ko Nan da can ne har sai sunyi ta ta takare

Yana zaune ya na faman huci da wurga idanuwa tamkar zaici Babu har dare ya Soma kawo jiki Amma baiji zai iya Barin wurin ba cikin sa a kuwa sai ga motar Alhaji Aminu tana tunkaro gidan inda ya bi motar da wani matsiyacin fushi tamkar zai hadiye motar.

Duhun Daren ya Hana Alhaji Aminu ya lura dashi har ya Soma Danna horn inda me gadin ya leko ta kafar makullin yaga motar me gidance sai yayi maza ya Soma kokarin bude gate din har motar ta silalo ya mayar da kyaren ya Rufe

Yana juyowa yayi ido Hudu da Mai Kano tsaye tamkar wani aljani don wallahi baiga ta inda ya shigo ba.

Yana tsaye suna kallon kallo da Mai gadin yayin da tuni Alh Aminu ya shige cikin gidan shi ba tare da yasan yayi babban bako ba.

Mai Kano yaja tsaki ya nufi cikin gidan inda ya ga Alhaji Aminu ya bi har Yana waiwayowa Yana hararar Mai gadin da son ko zaice wani Abu? Amma Sai yaga ya zauna ya bishi da kallon ka fito lafiya.
.

<< Hawaye 21Hawaye 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×